Showing 9001 words to 12000 words out of 22537 words
ta sanar dani cewa wai
karatu zata tafi England Amma Abba me yasa
bakaje biko ba? Abba yaja ajiyar zuciya,yace
"Dalilai da dama Ayshatu ina matukar son
fateema amma ina jin kunyar.Tunka rar ta da
sunan biko Bayan tarin abubuwan da suka shude
da wane ido zandu bi mahaifinta? . mutanen
masu nagartar halaye ina jin kunya Aysha..."shiru
ni ma din nayi don kam akaf hasashena ban
hango mafitaba cikin dakiyar zuciya nace Abba
kadai jarraba tura manya nasan babanta mai
fahimta ne insha Allahu zai fuskance ka" Allah
yasa ayshatu tashi kije" jikina asanyaye na mike
na fice Amma ko dana shiga kasa katabus nayi
na roki yaya usman yakaini gidan mamina sai
dai,abin takaici anan take hajiyarta take sanar
dani sunwuce Abuja tacan ne jirginsu zai tashi
Hakan yasaka,na saka kuka don na tabbatar
yanzu kam mamina tayi min nisa musamman
idan ta auri wani mijin bai zama lallai ya bari
mu'amalar mu tayi nisa ba. . ******* ********
******* . Wani lokaci ina kwance lamo akan
gadon Ummana matsanan cin tunanin Ustas ne
yadabaibaye min zuciyata kwana da kwanaki ban
samu labarin sa ba Hakan ya dan daga hankalina
hade da tunanin Ustaz yagaji da wulakan cin da
nake yarfa masa shiyasa ya ajiye ba tu na agefe
amma kuma ai har alokacin bai furta min kalmar
saki ba bai kuma aiko da takarda ba meya ke nufi
da jingine ni da ya yi? . Ni kadai nake wannan
tuna nin Na rasa wazan tunkara da
wannan.Tambayar tawa gashi ni kuma jan'ajina
bazai bari na kirashi ba Fitowata daga wanka
kenan ina zaune da karamin towel ahannuna ina
tsane ruwan jikina Humaira tashigo da sauri
tamkar an cillo ta Na bi ta da kallo saboda,ta
inda muka bambanta kenan ita akwai dan banzan
rawar kai "Aysha Sis,kije Abba yana kira" Ina
zuwa shine zaki shigo kamar an cilloki har yanzu
kin gagara koyar sallama idan zaki shiga waje. .
Murmushi tayi ta fice da dan tsallenta, Nabi ta da
kallo ina mamakin yadda kullum ta Allah Humaira
acikin walwala da farin ciki take ba ruwanta da .
Miskilanci irin nawa Allah kenan mai halitta gashi
yayo mu iri daya amma sai ya bambanta mu
tabangaren halayya Na zira riga sannan nafita
falon Afalon natarar da duk samarin Abba ko nace
magidanta mamaki ya ka mani tare da tunanin
taron me ake ne gefe daya yan matan umma ne
sun za gayeta gaba daya cikin shigar mutunci
suke don yanzu sunyi matukar nutsuwa tamkar
ba wadannan tantiran na wancan lokacin ba Na
isa nazauna agefe ina fuskantar Abba da son
sanin dalilin kira na . . Abba yabude da addu'a
kamar kowanne lokaci idan za.Ayi,taro sannan
yasake dubana yace "Aysha wannan taron naki
ne, so nake inji me kika yanke game da aurenki
ko kuwa har yanzu kina nan akan bakanki akaro
na uku bazan takura miki ba kamar yadda na
gaya miki wancan lokacin ra'ayinki zan bi" Ustaz
ya isheni yazo da kansa ya aiko,don haka yau
nasanar dasu zan fada musu abinda kika yanke"
Tamkar nace masa zankoma amma ina sai nayi
tuna nin yadda Ustaz ya yasar dani don haka,
dole ni ma inja ajina. "Ina jinki"Abba ya fada Na
dago fuskata nace . "Abba ba zan koma gidansa
ba karatu nakeso nayi..." Daidai lokacin Ustaz
yayi sallama da wannan mayataccen turaren nasa
Da sauri gaba na yahau bugu ganin azabar kyan
da ya yi Cikin jallabiya dark cofee 'yar Asalin sai
dai miskilanci na ya kawar da wannan kudurin Ina
so ayau na ga karshen miskilancin Ustaz na san
idan yaji ba nason sa hankalinsa ba karamin tashi
zai yi ba Cikin fara'a Abbana yace "yauwa dan
halak yanzu ake zancenka gwanda da Allah ya
kawoka Aysha sake maimaita abinda,kikace"
kaina akasa nace ."Abba ba na son sa karatu
nakeso nakoma akasar waje . " Murmushi Abba
yayi yace to kaji kai Ahmad sai ka ba ta
takardarta ayanzu kuma ayau zansanar dakai na
maye maka gurbin Aysha da yar'uwarta
Humair..." Tuni hantar cikina ta kada tamkar na
janye batuna nazaro idona ganin Ustaz ya zaro
jotter da biro a aljihu ya shiga rubutu tsaf nade
na fahimtar me ake. . Cewa gashi miskilancina
yahana namaganu karshe runtse idanuna nayi
daidai lokacin Ustaz yamika wa abba takardar
yana fadin . "Abba nagode Allah yabar girma" .
"Ya juya yana kallon daukacin mutanen falon
yace ku yani murna,da wannan karamcin na
Abba" Abba yace Bakomai Ahmadu kaidin mutum
ne mai nagartar halaye sam ba zan so na,rasaka
cikin ZURI'ATA ba Tamkar wani maganadisu haka
idanuna suka game da idon Ustaz kawai sai naga
ya dagan hannu ya saki murmushi alamar . SAI
WATA RANA . Daga haka yayi wa Abba sallama
ya fice jikina asalube namike har juri nake ji
nashige gida zuciyata cunkushe da tunani
nakuma tabbatar da cewa wata makarkashiya
Ustaz yakullamin ya dai ga yanzu humaira tafi
kwanta,masa azuciya kenan da sake-sake sam
ba na ganin laifina nikuwa,ko son sa,zai kasheni
bazan taba nunawa na damuba sai dai hakan
yazama AJALINA . Ji kake kut nahadiye wani abu
da ya tsayamin amakogwaro sai asannan hawaye
ya zuba akan kuncina zuciyata cunkushe da tarin
bakin ciki nadama da da na sani kuwa fal raina
Nafara jin haushin humaira tamkar itace tace ta
na sonsa Ban da ni jinin tace wallahi da sai nayi
mata abinda za ayi na damar hada ta da mijina
sai kuma nafara jin haushin kowa . Agidan da
tunanin sun fi son humaira akaina Ni kam nasan
narasa MAI SO NA MAMINA . Don haka wunin
ranar ban yi magana da kowa ba koda nayi sallar
asuba sake komawa barci nayi duk da ada ba na
komawa barci da yanmatan umma muke haduwa
mu gyara gida yau kam ko kallonsu banyiba balle
susa ka ran zanyimusu karin karatu kamar yadda
na saba duk Asabar din duniya Da humaira da
maryam da khadija muke kwana daki daya wani
lokacin kuma humaira ta tafi dakin Umma
sukuma sauran biyar din suna dakinsu da yake a
bangaren mami muke tare jin hargowar shirinsune
yasa nabude idona cike da jin haushin su nace
malamai kunda.Meni fa kunhana ni bacci .
Humaira tadiro,gadon ta haye bargon da nake
kwance nace ke meye haka? Langabe kai tayi
tace "Am sorry Sis, kinmanta da batun komawa
kotun kiyi sauri kishirya kibisu bros ni Ustaz zanbi
wani kallo nazu ba mata ina shirin kunduma mata
ashar sai kuma natuna ita din wacece da kuma
matsayinta a wajena Tsaki naja nace kuje kawai
ba na jin dadi bazan samu zuwa ba daga haka
YUWA book 3 part 9
NAGA RAYUWA book 3 part 9
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:12
. ba na son wani Silly queastion ina kallo suka
fice sai ga Umma ta shigo maganar duniya nayi
shiru kamar mai barci don ba na son ta gane
yanayin da nake ciki Inaji tace . "Humaira muje
takoma bacci ma" suka juya suka fice Nabi
bayansu da kallo ina sake jaddada jin haushin
humaira acikin zuciyata sai azahar suka dawo
inajiyo hayaniyar su umma nayi bulun-bukui
adaki inajin umma ta sake dawowa dakinta
dubeni wannan karon na bude idona har nayi
mata sannu da zuwa, cikin wata cunkushasshiyar
murya Umma da mamaki ta dubeni Aysha kalau
kike har yanzu kike kwance?,kaina ne yake ciwo
kunda wo umma? Ta gyada kai mundawo Nace
ya shari'ar ta kaya angama kuwa? Umma tace
shari'a angama tsaf an yanke wa fateema
hukuncin zaman gidan wakafi na shekara biyar ko
tarar miliyan biyar .Shikuwa doctor daurin shekara
biyar babu tara Atine kuwa daurin rai da rai tare
da tilasta mata wajen fadar inda,sauran
'yan'uwanta suke. Najijjiga kai hade da fadin
hakan shine daidai da su ai umma " Umma tace
kowa haka yake fada amma Aysha anya babu .
Abinda yake damunki kuwa? Na ce babu komai
Umma amma don Allah kiyiwa Abba batun
komawata makaranta inda hali gaskiya,nafison
nabar kasar nan? Umma ta girgiza kai da alama
tana tunanin yadda za ta fuskanci Abba da
wannan maganar ne batace komai ba tamike
tatafi Nikuwa na rintse idona don kam zanfi son
barin kasar nan ko ba komai bazan san lokacin
da aka daura auren ba balle Zuciyata tayi kunci
Don yanzuma jinake tamkar ciwon zuciya zai
kama ni. . Shiru har kwana biyu banji amsa daga
bakin Abba ba na tabbatar bai amince ba kenan
hakan ya sanyayar min da gwiwa Ina kallon,
Humaira kullum nanike da waya akunnenta na
san ba komai take ba sai hirar soyayya da Ahmad
hakan yasake bakanta min rai harnaji tamkar
nacanja daki sai dai hakan ba zata yiwu ba don
nasan kiri-kiri za ace BAKIN CIKI nake, . sai dai
kullum fa ina cikin uwar daki har umma tagaji da
tambaya ta taja,bakinta ta tsuke ina lura da ita
kullum tana kitchen tana koyawa yan matan
girke- girke ta tattara al'amarina ta saka agefe
Hakan yatabbatar min danayi . Rashin UWA MAI
SO NA MAMINA Yau da daddare bayan mun
gama cin abinci har namike tsam zantafi Abba
yasa baki yaki rani Bina yayi da kallo yace
kishirya da wuri gobe akwai tafiya potiskum duk
na lura yanzu kintsiro da wani hali na zama ke
kadai ba tare da munsan laifin da aka yi miki ba"
Mikewa kawai nayi nace to Allah yakaimu sam
banso wannan tafiyar ba amma babu yadda zanyi
Da asuba babu wanda yakoma barci har humaira
da ta kusan raba dare tana waya,da ustaz Na
lura ustaz,har yafi sonta akaina saboda bini-bini
yayi mata waya ita kuma tamkar mayya kullum
tana makale da waya babu jan aji babu komai sai
wani rawar kai shiri suke haushinsu kawai nakeji
sosai araina suna ta caba kwalliya nikuwa wanka
kawai nayi nazira wata bakar doguwar riga
ta,mai na shafa kawai kai kace nidin matar
mamaci ce wacce take takaba karfe 9:00 muka
hau motar yaya usman na fada da sauri yaja mu
dani da matarsa yana yimin tsiyar ramar da yaga
nayi bayan hankali ya kwanta murmushi kawai
nayi masa ba tare da na tofa ba shi ma din bai
sake . cewa komai ba duk da na so yace din
kodon na gaya,masa abinda yake,sani rama sai
dai gani da zurfin ciki Ba kasafai nake iya fadar
matsalata ba ba tare da an tambaye ni ba Haka
har muka isa potiskum Ni dai ina zaune cikin
mota jigum sai yaya usman ko matarsa sun
sakoo ni azance sannan nake shiga sai gaf da
la'asar muka shiga garin potiskum din munriga
kowa isa Hajiya da sauri ta tareni cikin farin ciki
take cewa kaga baiwar Allah tun dazu nake zuba
idon ganinku Ayshatu fargabata daya dawane
idon zan dubeki? Murmushi kawai nayi na
durkusa nagaishe ta Don ni dama ba sosai na
kware da wani wasan jika da kaka ba Ta kama ni
Zoki zauna nasake jaddada ban hakurina a
wajenki Duk da dai,kince kinyimin afuwa
Akunyace na zauna nace hajiya kibar maganar
tariga ta wuce Daidai lokacin Abba da Umma
suka shigo Abba dafada yashigo yana fadin ina
usmanun wai kai yaushe zakayi hankaline? . ina
ce har waya nayi maka akan cewa karage gudu
yaya usman yace Abba ai banyi wani gudu ba
Nan suka zauna suna gaisheta hajiya kuwa
bakinta . A bude,take kallonmu,ni da humaira fadi
take Ba shakka ga zahiri nan babu bambanci ko
digo tsakanin ku Umma ta tuntsire da dariya tace
uhm-Uhum,da bambanci sosai Ayshatu bata da
kwaramniya humaira akwai dan banzan rawar kai
humaira ta zunbura baki tace kai umma nidin? ya
muhammad yace sosai ma kuwa kike da rawar
kai Abba yace humaira kam ba da ma humaira
kuwa gaba daya ta fara dire-diren kafa tana
kukan shagwaba ya faruk ne yakamo hannun ta
yace Quite my friend kada kiyi kuka rabu dasu Me
za ayi da mutum mai kunbiya-kumbiya? Da abu
aransa ya fada yana kunshe dariya aciki Nakuwa
zabga masa,harara don na san dani yake. . ***
*** *** . Kwana biyu mukayi a potiskum,bayan
munzagaye dangi muka dawo gida Nidai fara'ar
dole, nakeyi a kan babu yadda zanyi tunda muka
dawo Umma tafara zancen shirye-shiryen sa
ranarsu Don ance wai suhudu za a aurar su yaya
muhammad kowa daidaya guda uku kuma
malaman mu ne suka nemi aurensu don nuna
tausayawar su garesu Ranar laraba 'yan sa ranar
sukazo 'yangidan su Ahmad ne harda kanwarsa
khadija ta saka ni adaki tana tuhuma ta akan son
jin dalilin dayasa naki dan uwanta har aka
musanya masa da kanwata murmushi kawai nayi
na ce KADDARA CE! . zo kaga lefen humaira
akwatina goma sha biyu harda nasaka rana
kayane sosai dankar aciki tamkar ba asan ciwon
kudi ba wata uku aka saka cif Humaira sai rawar
kai take bini-bini ta daga waya kaji tana kashe
murya hade da,cewa my Only wannan iyayi da
take,shiyake dugunzuma min zuciya Nayi tunani
ita ko kunyata ba ta ji Nashige daki kuka kawai
nakeyi har zazzabi ya rufeni ruf ba ta re da sanin
komaiba sai ga shi nice har da kiran wayar Ustaz
amma sam yaki dagawa . sai rejecting call dina
yake Balle na bashi hakuri ya janye kudurinsa na
auren kanwata Yau da safe ko fita banyiba daga
daki maryam tashigo take sanar dani wai ana
kira na Afalon abba da kyar na mike nazira
hijabina na isa falon Abban shi da yan uwansa,da
suke yan maza har su baba yahya suke zaune
sun tasa kayan lefen humaira agabansu Allah ya
sa su ruguza maganar Auren... . na ayyana hakan
araina su kansu na san sunsan hakan baidace ba
sai dai sabanin haka ji na yi Baba yahya ya rufeni
da fada da nasiha yace "Yanzu Ayshatu saboda
wannan kaddara ta afku shike nan sai kice
kinrataye sunnar manzo {S.A.W} kice wai ke
abarki kitafi karatu waje? . to tur da wannan
shawara taki Adanginmu kaf ba mu bar maza sun
tafi waje karatu ba balle mubar mace kuma gata
daya da za muyi miki shine kifitar da miji kiyi
aure shine mutuncinki mutuncinmu mu ma yanzu
tunda Ahmad ba kyason sa wa kika tsayar? .
kasa ce musu komai nayi ruwan hawaye ya fa ra
ambaliya akuncina nace babu wanda na tsayar To
mun baki sati kifitar da miji tunda dai..ovels / NAGA RAYUWA book 3 part 10
NAGA RAYUWA book 3 part 10
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:14
Mijinki na baya ya sanar da mu bai dora miki
idda ba Tashi ki tafi Allah ya kawo nagari Da kyar
na ja jiki na isa daki "Na shiga uku" . Nafada
ahankali Najawowa kaina masifa meya,kaini furta
ba na son Ustaz? Nasan halinsu baba yahya sarai
da zafin rai tunda ya furta sai na fitar da miji abu
ne mawuyaci ya janye kaina yayi dum sakamakon
rasa mafita da nayi alokacin kam na san tabbas
na yi rashin uwa da da mami akusa, da duk
hakan ba ta sameniba ga shi ko kira lambar da
takira ni bana samunta Hakan yatabbatar min da
bayan mungama waya canja layi tayi Nasake
rintse idona wasu zafafan hawaye, suka zubomin
Da daddare kamar wasa na dau Ipad dina da
niyyar duba facebook ko whatsapp, wanda rabon
da na bude su harna manta sakon Mamina ne
yashigo ta Whatsapp da sabon account din data
bude kawai.Cewa tayi Aysha yakike? cikin
tsananin farin ciki na tura mata hoton dan aljani
mai alamar kuka akasa na rubuta;"Rayuwa ta
yimin zafi MAMINA, . saboda rashinki akusa dani
wallahi mami yanzu na tabbatar ni marainiyace
na rabu da, . Ustaz an maye masa gurbina da
humaira kanwata kuma Allah mami inason sa
haryanzu Gashi Baba yahya ya rantse sai na fitar
da miji mami na rasa yadda zanyi kibani
shawara" . Tsawon lokaci ina sauraron amsar
mami shiru har na fitar da ran samun amsar ta
saikuma ga sako ya shigo . "Aysha kenan
haryanzu kinason Ustaz meyasa kika cuci kanki
wajen rabuwa dashi?" . cikin kuwa na sake rubuta
mata "mami wallahi kaddara da kuma son ja
masa aji." Dariya taturo min sannan taturo min
"kisami Abbanki ki sanar dashi ba ki da wani Zabi
yazaba miki miji da kansa idan yaji kince hakan
nasan zai fuskanci har yanzu kina son mijinki
idan yaso sai adawo da auren kanki."Murmushi
natura mata alamar jinjina cewa tayi kawai "Sai
da safe ina karatune" . Daga haka ta bar online.
Kwanciya nayi akan gado ina dariya Na tabbata
shawarar nan ta mami tayi don haka nake Allah-
Allah safiya tayi Da azama na mike nashiga toilet
nayi alwala ina rokon Allah yasa abinda nake
nema yatabbata da sassafe nayi wanka na shiga
don tanadar, wa Abba hadadden . Break fast
koyaji dadin amsa bukatata Da sauri ina ta
addu'a azuciyata ina kallonsu humaira suna jifana
da kallon mamaki ganin yadda nake sakin fara'a
a zuciyata kuwa fadi nake . "yarinya kwaleleniki
mijina yafi karfin ki ko ta kaka sai na kwato shi" .
Ina yi ina wakar MAI SONA MAMINA Umma dai
murmushi kawai take yi dakaina nakaiwa Abba
breakfast bayan na gaishe shi cikin mamaki yake
cewa Ayshatu yau cutar tawarke ne naga kina
walwala? . Murmushi nayi na sadda kai na kasa
Abba yasake cewa ko ansamo min surukine?
Nasake sunkuyar dakai nace "Dama Abba akan
zancen ne..." Da sauri yace sunce zasu turo ? Na
girgiza kai ina wasa da hannu na nace
da...da...dama Abba cewa zanyi na... baka dama
kazaba min...mijin" . murmushi yayi yace yar
albarka kenan ni da kaina kai amma naji dadi
Insha Allah kuwa zan miki zabe na gari dazakiyi
alfahari da shi Akwai wani kanin abokina dama
ya dameni da maganar aure, . mutumin kirki ga
nutsuwa da kamala yana da iyali zakuyi daidai da
shi...sam ba na fahimtar sauran zancen don dai
naji da gani . nayi sai can naji yace shikenan
Ayshatu zaki iya tafiya Ubangiji yayi miki albarka
Adaddafe na mike nashige cikin gida Awani lungu
nashiga na zauna turus ina tunanin wace
tabargaza nasake ragargazowa,kaina.?Innalillahi
wa inna ilaihirraji'un nake ja, wannan shine ba
wan ba kanin Na dade ina kuka amma da na
shiga gida ko kallona Umma batayi ba hakan ya
sake tunzira zuciyata Na tabbatar yanzu ba ta ta
tawa tunda ta samu humaira yanzu wa zankaiwa
kukana? . Ya usman ba ya nan yayi tafiya haka
na kwanta lamo ina tunanin wai ni zan auri
babban mutum mai iyali Duk wani shirye- Shirye
na bikin yan matan ya kankama don yanzu har
saura kwana uku Idan kaganni na rame nayi
fayau don yadda naji wai tare za ahada da
tariyata Hakan ne yake dagamin hankali Da
safiyar Ranar da za akama amaren Abba yakira ni
dakinsa kaina akasa yake Anan naji ya sanar dani
wai yau zaiyi bako da azahar . ."Ayshatu kiyi
masa tarba ta mutunci don babban mutum ne ba
naso kiyi abinda zai zubar da mutuncin gidan nan
daga kai kawai nayi hade dajin wani . Nauyi
yadanne kirjina yana cewa tashi kije ki tanadar
masa abin saukar baki wannan karon kasa
amsawa nayi na mike da niyyar tafiya amma ina
sai daddafa bango nayi sai dai banyi aune ba
najini kasa ji kake yif. . Ban farka ba sai agadon
asibiti na ganni ana yimin karin ruwa Nabude
idona jama'a ne birjik afilin dakin Gaba daya aka
shiga yimin sannu. Ummana taka ma hannuna
cikin nata ta sake cewa sannu Aysha,ina yake yi
miki ciwo yanzu? girgiza kai nayi alamar bakomai
Abba,da yake gefe yace Allah karo afuwa Daidai
lolacin likita yashigo sanye da kayansa na likitoci
yaja hannun da ake min karin ruwan ya zare
robar da take sadar da ruwan zuwa cikin jijiya
sannan yamaida dubansa gare ni yace meke
damunki yanzu? . Muryata adashe nace masa
"Bakomai" domin ba shida maganin da muwata
yasake aunani da abin awonsu na likitoci sannan
yadubi Abba yace ta samu sauki sosai kamar
yadda na ga ya maka ciwon nata yana tattare da
damuwa sakamakon bincikenmu yanuna ba ta
samu hawan jini ba amma dai ta rage damuwa
saboda nan gaba . Ta iya samun hawan jinin
Abba ya daga kai yace Insha Allahu za a kula
daga haka ina kallo likitan ya saka kai yafice
Daidai lokacin mayataccen kamshin turaren Ustaz
ya mamaye asibitin hakan ya tabbatar min
dashine ya iso Hakan yasa nayi saurin lumshe
idona don ba na kaunar na ganshi ma Da sallama
yashigo dakin sannan naji muryar humaira hakan
yatabbatar min da cewa tare suke Da