Showing 3001 words to 6000 words out of 22537 words
shany wadanda aka tsare awani daki daya
bayan daya suka dunga fitowa Shany ce atsakiya
gaba dayansu cikin.Wasu dogayen hijabai dasuka
saukar musu har kasa ammafa fuskarsu ta nuna
bazaman dadi akayi akotunba Abbana yakalle su
daya bayan daya . sannan yace da jami'an tsaro
sufito da da mama Atine wacce akayi nasarar
kamo ta kwanaki biyu da suka wuce kanta akasa
tafito amma daga ganin ta ka ga cikakkiyar yar
duniya mutane kuwa suka zuba mata ido ciki
kuwa hardani da nake mamakin karfin hali irin
nata . nakuma yi tur da ita harcikin zuciyata Allah
dai yashirya musulmi Abbana yace kece Atine? ba
ta re dabata lokaci ko tsoro ba ta amsa da nice
Atine kinsan wadannan yaran dasuke gabanki?
Nan ma cikin comfidence ta amsa Nasan su."
Abbana yace mene ne hadinki dasu? dan tabe
baki tayi sannan tace akarkashin kulawata suke
karkashin kulawarki kamar ya? kina nufin
ya'yanki ko ya'yan yan uwanki . kike riko? Anan
kam tsit tayi takuma sunkuyar dakanta azuciyata
nace munafuka Abbana yadan girgiza kai yace
malama atine muna sauraronki koko zargin,da
ake miki gaskiyane kamar yadda yaran suka ce
babu wata alaka atsakanin ku dukansu yan
tsintuwane? ta daga kai alamar eh yace kina
nufin dukkansu tsintarsu kikayi? to a ina? kuma
da yaushe? awanne gari kikatsinci har mutum 35
musamman waccen yarinyar danake hasashen jini
nace saboda matsananciyar kamar dasuke yi da
diyata,Aysha dasauri takai dubanta,kaina ta sake
mayar da dubanta akan yar rikonta Shany atake
naga tasaka,hannu tana yarfe.Gumi alamar rashin
gaskiya kuru-kuru yabayyana afuskarta . Abbana
yadanyi rubutu sannan yadago yasake ce mata
malama atine kinyi shiru inason sanin labarin
wannan yarinyar shany da yadda kika sameta
gaskiyarki ce hanya mafi sauki dazata kubutar
dake karya kuwa itace zata tsunduma ki akogin
nadama matukar na,gano gaskiyar lamari
Ahankali ta dago kanta sanin cewa babu mai
kubutar da ita hakan yasata shiga rattabo bayani
"kamar yadda . ka fada dagaskene wadannan
yara tsintarsu nayi wasu kuma aasibiti nasamesu
shekaru da dama dasuka wuce nima karkashin
wata mata nake da sana'arta kenan . FATAUCIN
YARA MATA . kai har da mazan ma idan tasamu
faraga "asibitoci takebi don samun yara marasa
galihu kodai shegu kokuma wadanda iyayensu
sukayi accident suka mutu akarasa danginsu
kokuma idan anhaifi yan biyu tayi cinikin daya da
nurses ko likitoci subata daya batare da mai
haihuwar ta saniba Nikaina a irin hakan tasameni
ma'ana ni shegiyace duk abinda takashe mana
muna yara to idan mungirma fanshewa take
akanmu kodai ta mayarmu karuwai kodai tayi
futaucin wasu zuwa wata kasar ta yadda za
adunga bata,kudi duk karshen wata wadanda
tamayar karuwai kuwa da zarar sungirma andaina
yayinsu ba ta samun komai atare dasu to sai ta
sallamesu sukama gabansu don takan fada ba a
aikin banxa akano . A irin haka nima nafito Ne
acikin wadanda aka sallama nima nakama gidan
kaina saina tsunduma kaina cikin harkar da takeyi
na shahara sosai harnaso nafita nima asibiti nake
. zagayawa aduk cikin kasashen Nigeria wannan
yarinya da kake magana ina,matukar alfahari da
ita aduk cikin yarana saboda tana da kwazo da
basira wayo da hikima shiyasa bana manta
tarihinta . A ASIBITI NA SAYO SHANY.... . Gaba
daya naga abba yadago yana sake kallon ta
muryarsa na rawa yace mata wa...wanne...wane
asibitin? shiru tayi da alama,tatafi tunani sai can
tazaro wayarta,ta kunne tashiga bincike kotun
kuwa zuwa lokacin tuni tadau kace nace har
saida Alkali yatsawatar sannan Atine ta dago
kanta tace Na sa mota a . NASHE SPECIALIST
HOSPITAL . aranar lahadi 17 gawatan july
shekarar1995..." gaba daya naga Abbana yazaro
ido umma kuwa arazane tamike tana nuna Atine
da yatsa muryarta na rawa,kincu.Cemu... .
tabbas wannan yatace jininace! ranar dana haifi
ayshata kenan kuma a asibitin nashe..." novels / NAGA RAYUWA book 3 part 4
NAGA RAYUWA book 3 part 4
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:04
Gaba daya hankalin jama'a yakoma kan umma
Abba ne yadaka tar da umma tahanyar yimata
umarni tazauna umma tazauna tanajan
"Innalillahi" Ni kaina bugun zuciyata alokacin
yakaru Abba yace Atine ina jinki Awajen wa kika
siyeta? likita? ko nurse? shiru tayi har saida
yadaka mata tsawa,sannan tace awajen likita ne
bisa jagorancin wata mata "wata mata wa?
yasunanta? Abba yafada cikin matsanan cin
mamaki Girgiza kai tayi tace gaskiya na manta
saidai na bincika shiru . Abba yayi yashiga
rubuce-rubuce sai can ya dago yace ina
tunanin.Tilas sai annemo matar nan sannan kotu
za ta san hukuncin dazata yanke matar ce da
likitan zasu tabbatar mana da shany diyar wace
ce don haka asakamakon haka kotu ta dage
zama zuwa nan da wata guda za atsare Atine har
zuwa lokacin kuma kotu ta ba da belin yarancan
tunda ga babbar me lefi ankama sai dai zasu biya
minista makudan kudaden da suka daukar masa
idan yana bukatar hakan koda muka isa gida
jikina asanyaye nake jan kafata ina lura da umma
ita ma nata jikin asan yaye yake matuka . har
raina ajagule yake gaba daya fatana daya kada
Allah yasa zargin danake yatabbata bakomai
kuwa nake tunani ba sai kada Allah yasa
MAMINA tana da hannu dumu-dumu acikin
wannan shari'a ba idan hakan ta faru ya
makomar mamina zata kasance? wasu hawaye
naji sun sulmiyo min. . haka na kwana da zancen
azuciyata da safe ma ko karyawa, banyiba
nasamu umma dazancen murmushi tayi tace ni
ma ina tsoron faruwar hakan sai,dai kunyi daya
da abbanki shima zargi da hasashen dasuka
shiga zuciyarsa kenan sai dai zankwabeki kamar
yadda na kwabe shi kada ku daga zan cen nan
wani yaji don ba lallaine tunanin yaxama gaskiya
ba amma ya,rantse idan dasaka hannun ta bazai
mata,sassauci ba" Ahankali naja numfashi hade
da furta kai jama'a duniya abar tsoro ce . wallahi
sam hankalina yagaza kwanciya saboda tsoron
kada akama mamina da wannan gundumemen
laifin hakan yasa nayi saurin shiga wanka ina
fitowa, ko mai bansha fa ba nazira doguwar riga
ta da hijab Adaki nataradda umma karya naimata
akancewa zanje gida nadebo wasu kayana bataki
ba sai dai tacewai natambayi mijina kamar
nafasa zuwa sai dai kawai,natura masa, text
nasanar dashi zanfita, banga amsa ba amma
haka nashir gama umma karya nace yace sai
nadawo . Daga nan nasaka kai ko direba
bannemaba don ba na so asirina yatonu,hakan
yasa natare adaidaitasahu . . sai Nasarawa
gidandsu mamina da sauri nafada gate,din gidan
bayan na sallami mai adaidaita sahun A falo na
sami hajiya da mami wannan karon hajiya da
walwala fal afuskarta ta amsamin har mamaki
abin yabani mamina kuwa tashi tayi ta rungumo
ni tana fadar oyoyo ayshata . nidai murmushin
yake nake saki bayan munshiga daki mamina
tadubeni tana murmushi ayshata ya aka kare da
zaman kotu? wannan karon tun da naga kintsira
nace to mekuma zankoma nayi? dan murmushi
najefeta.Dashi "Aikuwa da kinsha kallo don
wannan yarinyar dai ana kyautata zaton nida ita
twins ne...." da sauri mami tazaro ido tace Inji
uban wa kuma? Nagyara zama cike da mamakin
irin razanar da mamina tayi nace Inji matar data
rainesu ta shaida haka Don kuwa rana daya da
lokaci da asibitin da aka haife mu duk dayane
matar ta tabbatar siyenta tayi a asibitin bisa
jagorancin wata mata" Sake firgita tayi tace
What? kina nufin ta fadi sunan matar? . girgiza
kai nayi nace kodaya sai azama na gaba Abba
yace lallai anemo wannan matar da likitan don
sune za su . ba da tabbacin komai mamina
zagaye ta shiga yi a dakin idan ba idona ba ne
yagaya min sai naga kamar gumi take sai can
tace Allah ya kyauta amma hakan da mamaki
matukar gaske Ban dade sosai ba nabar gidansu
mami yanzu kamzuciyata ta aminta,da zargina
don haka na ratse wani lungu na sha kuka na
Innalillahi kawai naketa ja harna isa gida sai
danaje kofar gidan sannan na tuna karyar dana
shirgawa ummana nacewa, kaya zandebo don
haka dasauri najuya nanufi gidansu Asma'u Allah
yataima keni tana nan Nadebo kayanta sannan na
nafo hanyar gida Adai-dai sabon gidansa
nahango shi da wannan kodaddiyar matar tasa
da alama fita zasuyi haka, kawai sai naji wani iri
araina bansaniba ko kishi ne oho. . Na sa kai zan
wuce ba tare da na kulasuba amma, namakaro
donjin Uztas nayi yana fadin yan mata ina kikaje?
Najuyo namasa wani irin kallo mai fassara kala-
kala gani nayi yasake wani fari yayi kyau fiye da
lokutan baya Ban saniba ko don yanzu hankalinsa
ya kwantane take naji wani kululu ya cake min
zuciya bansaniba ko kishine . kishin da ake fada
wucewa nayi ba ta re danace masa ko "A" ba
Babu abinda,yafi bani haushi saiganin danayi
Uztas kobi takaina bai sake yiba yakoma gurin
matarshi hakan yasa naji wasu zafafan hawaye
sun zubo min tabbas . KISHI MASIFA NE . ni
kaina kuma na san ina da matsanan cin kishi don
haka na sake damkewa araina na rabu da auren
Uztas har abada koda soyayyarsa zata zama
ajalina Azaune nasa mu ummana afalo ita da
shany mamakine yayi matukar ka ma ni danaga
shany da yan'uwanta kamar umma ta sani
tashiga rattabo min bayani Ga shany nan da yan
uwanta Abbankine ya kawosu suzauna kafin
agama shari'a asan yadda za ayi dasu murmushi
kawai nasakar musu nashige dakina saboda sam
bana jin dadi aduk sanda natuno mamina nakuma
tuno Uztas da shegiyar matarsa sai naji tamkar
na sa kuka sai yamma sannan na fito daga, daki
bayan da sakon Abbana ya sameni akan yanason
ganina Da sallama nashiga falon abbana ya amsa
cikin walwala da sakin fuska na durkusa agefe
"Kinga yan uwa ankawo miki ko? Don Allah
kidage wajen koyar dasu . addini don nalura babu
batun sanin addini a al'amarinsu sonake koda
angama shari'ar na roki alfarma gwamnati tabar
min rikonsu koda yakasance shany ba 'ya ta bace
balle ina ji ajikina Aysha su zama tamkar
yan'uwanki kada kiyi la'akari da laifin dasuka
aikata a baya duk ba laifinsu bane idan da ma
mai laifin bai wuce uwar rikon suba,Nadaga kaina
nace "Insha Allah abba zan kokarta yauwa aysha
nagode na sanke diyar albarkace wai yakukayi da
mijin ki batun komawarki? shiru nayi nakuma
sunkuyar da kai na ce Abba bazan.Koma ba Abba
yayi saurin zaro ido yace meyasa ayshata?
Nadan sake sunkuyar dakaina kafin nace Abba
lokacin da abin yafaru ba irin kyara da hanta rar
da baiminba duk ba ma wannan ba Abba gaskiya
indai zaku kyaleni nafi kaunar na zurfafa ilimina
shiru Abba yayi sai can yace shikenan.Aysha
bazanso takura miki akaro na biyu ba kije Allah
yazaba abinda yafi alkhairi.Tun daga ranar naja
su shany ajikina nake koya musu al'amuran
addini don nalura babu abinda suka sani idan dai
ba boko ba don kam sosai na . lura sudin kwarine
aharkar boko don shany idan tana turanci yadda
kasan baturiyar ingila tsabar kwarewa har
mamakin tanake yi idan naji tacanja harshen ta
Zuwa turanci wanda yake da dadin sauraro mun
shaku sosai kuma Abbana yawadata su da suturu
iri-Iri nima kuma na basu nawa idan muka zauna
waje daya da shany bazaka taba bambance muba
sai dai ita tana da rawar kai kuma ni ina da
tawadar Allah agefen kuma tuna ita kuwa akasan
habarta take dashi Idan suna ba ni labarin irin
damfarar da Atine ta sa su ina tausaya musu
matuka da gaske Atine ta cucesu sai dai abu
daya ne yan group dinsu ba su yarda dashiba
shine keta musu haddi har yanzu suna nan a
matsayinsu na yan mata cikakku ta wannan
bangaren kam na sa ra musu don bakaramar
dabara sukayi ba don budurcin mace shine abin
tinkahonta kuma babban jarinta Bayan ta gama
bani labarin nace Amma an taba kawo min wani
hotonki da anyi tsammanin nice (na ba ta
labarin) nace kusan dai nace a tsirara kike
ahoton.Murmushi suka saka gaba dayansu
sannan shany tace ina . yaudarar maza da jikina
saboda nasan ina da diri mai kyau sai ka
sakankance barci ya dauke ka sai mu yashe ka
tas mutafi haka nan sukayi tabani labarinsu na
Al'ajabi nayi na dariya kuwa na saki murmushi .
*** *** **** . KOTU . Ranar da aka koma kotu
wannan karon cikar haryafi na kullum don mutane
abin ba a magana ba dauki lokaci sosai ba Alkali
Abbana yazo aka fara wata shari'ar kafin azo
kantasu shany dasuke tsaye a layi reras cikin
shigar mutunci da ta dawo musu da martabarsu
da mutuncinsu na ya'yamata bayan dogayen
jawabai da Abbana ya bayar dangane da shari'ar
da aka guda nar sannan yadubi Atine yace
Dafatan atine kin gamsu da abinda kika fada?
Atine ta daga kai kamar kadan garuwa wannan
karon jikinta yayi sanyi sosai da alama ta hango
ba ta da mafita kokadan Abbana yadanyi rubuce
rubuce sannan yadago yadubi dandazon jama'ar
da suke kotun yace, "A sakamakon bincike da aka
gudanar kotu tabinciko likitan da yayi cinikin
yarinyar da ake kira SHANY sannan har ila yau
kotu ta binciko matar datayi.novels / NAGA RAYUWA book 3 part 5
NAGA RAYUWA book 3 part 5
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:05
jagorancin cinikin..." Sosai hantar cikina ta kada
don babu makawa nasan mamina ce don ban
ganta awajen ba babu mamaki tana can saye
acikin wani wajen Abbana yakalli dansanda
[police] yace Ashigo da likita kafin azo da matar
ko minti biyu ba ayiba police din yashigo da
likitan wani shirgegen kato baki-kirin da alama ba
bahaushe bane yazo kuwa yahau kan step din
fuskarsa tacika da furfura alamar yafara tsufa ya
tsaya shirim dashi Azuciyata nace cikakken mugu
Abbana yadago yana kallonsa nasan yana
mamakin tsananin muguntarsa ne naraba ya
da,uwa tana cikin jinin haihuwa Abbana yayi
gyaran murya kafin yace kaine Dr.Emmanuel? .
yadaga kai alamar eh Amsa nakeso naji da baki
ko baka jin.Hausa? inaji sosai ma muryarsa
tangararan tamkar bahaushen asali "menene
dalilinka na Siyarwa da waccan matar jaririya
tuntana cikin jinin haihuwa? sannan kuma muna
son mu san yarinyar yar waye? . zare ido yafarayi
da alama baisan dalilin da aka kaso.Shiba kenan
ya kuma dubi Atine sukayi kallon-kallo Abbana
kuwa ya daka masa tsawa hade da fadin . kai
muke sauraro! ina da record din komai agurina
don haka idan kana shirin yin karya ne kashirya
ta dakyau don kuwa ina da labarin komai ina dai
so ne kawai ka gaskata dakanka Emanuel yayarfe
gumi sannan yadago a sanyaye "yace tabbas da
na san wannan ranar za ta zo daban
aikata,abinda na aikata ba kaicona ni Ema ina
cikin tarin dana sani dana biyewa son zuciya yau
gashi yacillani cikin kogin nadama . " "sunana
Dr.Emmanuel ina aiki ne a nashe specialist
hospital tun tasowata na kasance mutumne ni
mai matukar son kudi hakan yasa sam banida
wani tunani sai na hanyar da kudi zasu shigomin
"Ba na manta wata rana data kasance ranar
lahadi ina zaune agidana dayake Ring Road,nayi
baki ba wasu baki bane sai wannan matar
yanuna Atine da ita da wata mata da ake cewa .
HAJIYA FATEEMAH" . Shikenan tatabbata .
MAMINA CE! . gaba na yasake faduwa jin gashi
sunanta ma ya bayyana Amma kuma ai fateema
da yawa da sauri nadaga nakalleshi jin yaci gaba
da labarin "Nayi matukar murna da zuwansu don
kuwa fateema akwai alheri ni likitan gidansu
babansu ne ALHAJI MUHAMMAD" Dasauri nadafe
kirjina donkuwa shikenan tafaru takare wallahi
maminace Allah sarki MAMINA why.? . meyasa
kika aikata hakan duk tarin alherinki agareni? .
Likita yaci gaba "Naba su lemo da ruwa sannan
na zauna ina fuskantar su don son sanin mene ne
yake tafe dasu bayan sun dan sha drinks din
sannan ita fateema ta dubeni tace Dr.ema shin
kasan dalilin Ziyarar damuka kawo maka yau? na
girgiza kai Akwai wata mata datake zuwa
asbitinku awo Abinda nakeso dakai da zarar
tahaihu kazare dan ko yar ka saka matacce idan
ansamu idan kuma ba a samu ba kasan dai
dabarar dakayi kasace abinda tahaifa ba ta re
da,kowa ya sani ba zaka yi wannan aiki akan
naira miliyan biyu Da sauri na zaro ido jin yawan
makudan kudi bakina a sake na sake maimaita
sunan batare da ba ta lokaci ba na amince da
bukatarsu Nakuma tambayi sunan matar batare
da bata lokaciba suka sanar da . MATAR IMAM
KHALIL . A take nagane ta don ni nake mata awo
da kaina nadaukar musu alkawarin ANYI
ANGAMA" Sam ji nayi na daina gani saboda
wannan.rikitaccen al'amari daya dumfaroni don
kuwa yanzu yawuce zargi tabbas,mamina ce
da,hannu dumu-dumu awannan KUNGURMIN
LAIFIN umma nahango tamike tsaye tana zare ido
kai duk . yayyena ma mike war sukayi yayin da
naga Abbana yana ta sakin murmushi nayi
mamaki matuka lallai ko ya ya kuke da kishiya ka
guji sharrinta Na ayyana araina hawayen tausayin
iyayena ya sulmiyo min daga ida nuna Abbana
cikin matukar hade rai yadaka wa Emmanuel
tsawa ina jinka! . Emmanuel kuwa yaci gaba da
ba da labarin mai kamar almara "Ba ta dau lokaci
tana zuwa awo ba rana daya aka kawota tana
nakuda wanda kafin lokacin idanuwana suna kan
masu labor.Na sha alwashin ko kashe wani jaririn
sai naje nasaka mata na dauki nata kuma naje
dakin jarirai wanda iyayensu suke guduwa suna
barinsu ko dai na saci na wani ko ma ya nidai
burina kawai kudi da murna ta na karbeta kasan
cewarta matar manya yasa na kaita special room
nakuma hana kowa shiga Ta sha matukar wahala
harta fita hayyacinta kusan awa biyu daga bisani
tahaifi yayanta yan biyu MATA ZALLA Tausayi ta
bani ganin irin wahalar da tasha hakan yasa
nabar mata 'ya daya ina murna ganin.Allah ya
taimakeni na gudu da daya ba tare da sanin ta ba
don lokacin hankalinta . Baya jikinta Bayan wani
lokaci sukazo suka amshe ta, sai dai nasanar
dasu gaskiya cewa yan biyu tahaifa sai dai ina
kokarin dauke dayar wani likita yashigo haka
yasa tilas da daya natsira wannan shine iya
gaskiyar abinda nasani" Gaba daya kotun aka
dauki kabbara bayan sauraren wannan abin
Al'ajabi Bayan rubuce- rubuce da Abbana yayi ya
umarci wani police yashigo da fateema zuciyata
taci gaba da bugu tamkar zata faso kirjina ta fito
nakumayi saurin sunkuyar da kaina don sam ba
naso nayi ido biyu da MAMINA acikin wannan
yanayin cikin wani zumbulelen hijabi MAMINA
take da kuma nikab afuskarta takuma rufe kirif
dashi Alama ce ta cewa ba ta muradin aga
fuskarta Abbana yadan dube ta ya girgiza kai
ahankali bakinsa yayi furucin . FATEEMA
MUHAMMAD wanda muryarsa bata bayyanaba
sannan yaja ajiyar zuciya yace Fateema zanso
kiyiwa kotu cikakken bayani da dalilin daya sa
kikayi silar da aka sace diyar mutane tun tana
cikin jinin haihuwa? "Bakomai yaja ba sai .
RAMUWAR GAYYA . Tafada da dakakkiyar
muryarta . Abbana yajinjina kai Ramuwar gayya
kamar ya ya? inaso kiyi wa kotu karin
gamsasshen bayani hannu tasa tayaye nikab din
da yake fuskarta Atake na zabura na mike wa na
gani? Hamdala nayi ga sarki Allah alokacin
danayi arba da ita . BA MAMINA BACE . madadin
inga fuskar mamina kamar yadda nake zato a'a
wata mata na gani fara da alama fulanin dajice
Don naga tsagun fulanin atare da ita sai dai daga
ganin ta ka ga cikakkiyar 'yar duniya ina kallon
yadda umma itama tahau zare ido tana nuna ta
da alama ta shaidata don naji ta ambaci sunanta
da fateema fulani Abbana yayi rubutun da zaiyi
sannan yadago yadubeta fateema munaso muji
dalilinki nacewa ramuwar gayya kikayi kuma
waye ya miki laifi da har kike ikirarin kinyi
ramuwar gayya ta hanyar illata rayuwar yarinyar
da bata san komaiba? . Azafafe tadubeshi "I dan
kai kamanta abubuwan dasuka faru abaya Imamu
ni bazan manta ba komai yana cikin kwanyata Ba
irin rayuwar da ban fa da ba duka adalilinka da
furucin 'yan kauyenku Imamu wane irin wulakanci
ne banganiba acikin gidanku . duk adalilin nace
inason ka zan aureka..." Tafada tana.Huci
fuskarta ahade tasake cewa ko yanzu kasuwa
tatashi wallahi dan koli yaci riba Abbana yace
"Duk munji fada min dalilinki nasace yarinyar da
kika sa akayi kowa yaji" Taja ajiyar zuciya
sannan ta dubeshi "ya zama dole nafada kodon
duniya tashaida sunanka MAYAUDARI danginka
kuma AZZALUMAI . "sunana Fateema muhammad
nida iyayena mazauna.Potiskum ne amma cikin
kabilar IBRA munta so matsayin unguwa daya ni
da su Imamu duk da ba wata alaka da take
tsakaninmu saboda kasancewar mahaifina
akabilar Ibra mahaifiyata kuma yar jihar yobe ce
itama sai da aka kai ruwa rana kafin iyayenta su
amince ta,auri babana duk a dalilin kasancewar
sa ba bahaushe ba mahaifina mutum ne mai
nagartattun halaye kowa yashaida hakan Bacin
rai ne yasa yabaro can kabilarsu yadawo
potiskum da