Showing 6001 words to 9000 words out of 22537 words

Chapter 3 - NAGA RAYUWA 3

02 Dec 2025

69

zama ya ce mamana acan garinsu
bashida kowa tuni iyayensa suka mutu kuma
bashi da yan uwa sai yan'uba Akwana atashi
cutar ajali ta riski mahaifina bai wani dade yana
ciwo ba yamutu yabarmu da . tarin tashin hankali
saboda duk kauyen ba asonmu Ana haka
kwatsam mahaifiyar mu ita ma tafara cutar ajali
Zuwa lokaci kalilan tace ga garinku nan wannan
mutuwa ta daga hankalinmu nida yayana muftahu
da, kanwata samira shi kenan daga mutuwar
mahaifiyar mu sai rayuwa ta sake juya mana
baya ba wanda yake ta,tamu agarin nan wani
lokacin abincin dazamu ci ma gagarar mu yakeyi
ganin zaman hakan ba zai yiwu ba ya sa ranar
nayanke shawarar shiga gida-gida neman aikatau
Alokacin shekaruna sha biyar Duk gidan da naje
ban samu ba har na sare zankoma gida sai
natuna da gidan maikudin garin wato gidansu
Imamu Atake awajen Zuciyata tayarje min naje
gidansu imamun Nakuwa isa bakin gate din gidan
har mai gadin ya fa ra yimin hargagin bazan
shigaba sai ga mahaifin Imamu nan dattijon arziki
shi ya leko yake tambayar maigadin yadda akayi
maigadi yace Rabu da ita Alhaji irin makarya tan
mutanen ne masu basaja wai aiki tazo nema
kona wanke-wanke Alhaji yadubeni yace baiwar
Allah daga ina kike? Nayi kasa dakaina nashiga
rattabo.A RAYUWA book 3 part 6
NAGA RAYUWA book 3 part 6
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:07
masa daga inda nake Alhaji yagirgiza kai yace
kice yar gidan muhammadu mai hula ko? Na
daga kai Alhajin yace Allah yajikan muhammadu
mai hula shigo ciki muje wajen hajiyar Tun daga
bakin tsakar gidan nafara jin hargagin fadanta da
alama da ya'yanta take nan take naji zuciyata ta
harba nayi fatan Allah yasa tayi maraba dani
Alhajin da sallama yashiga hakan baisa tarage
zazzaga kwandon masifarta ba tabi ni da kallo
kafin tace lafiya Alhaji wannan bakuwar wace?
sannan yakai duban sa kan Imamu yace Babana
me kayi ne take zazzage maka fada? jinayi
hajiyar tace min ke daga ina ban waye fuskarki ba
Nayi kasa dakaina ina wasa da zoben hannuna
Alhaji yace Aiki take nema na ga kuma kina da
bukatar yar aikin tun da waccan tatafi shiyasa
nace tashigo tsaki tayi takuma zabga min harara
tace yo don ina bukatar yan aiki nace maka yan
mata nake nema? . Alhaji dasauri yace hajiya
kidai duba marainiya ce diyar muhammadu mai
hula haba ko danaji kace min diyar tubabben
mutumin nan ce shiya sa naga fuskar tayi yanayi
data kabilu. . To na amince amma da sharadi
idan na samu dattijuwa zata dire min aikina don
ni ba na son kwashe-kwashe cikin kwashe-
kwashen ace har kabilu kawai kajanyo min
jangwan-gwan Nidai farin ciki yamamaye ni danaji
ta yarda ta amince Bawani aiki bane shara ce filin
tsakar gidan sai wanke-Wanke kasancewar matar
gidan mace mai kazar- kazar ba komai take zama
jagwab ayi mataba Da kadan-kadan shakuwa ta
fara shiga tsakanina da imamu wasa-wasa sai
nafara jin matukar son imamu azuciyata wanda
har idan ban ganshi ba banajin dadi Har wata
rana takai natambaye shi da kaina Imamu inajin
soyayyarka araina kaifa? . murmushi ya saki hade
da dage gira daya daga cikin abinda yake sake
burgeni dashi yace fateemah ina matukar sonki
sai dai kafin haduwata dake ina soyayya da wata
yar'uwata Amma hakan bazai hana ni aurenki ba
kidaici gaba da addu'a jikina ne yayi sanyi don
nasan mawuyacin abune hakan yatabbata tunda
dai ya sanar da ni yar'uwarsa ce shikenan na
kaddara azuciyata ba zan auri imamu ba Tafi-
Tafi soyayyar Imamu tana sake . bunkasa
azuciyata duk da ina kokarin naga na yakice
hakan amma abu ya faskara kwatsam wata rana
ina cikin aikin yamma sai naji hajiya tana batun
sa ranar Imamu tana aika yara gida-gida akansu
je sufada Nashiga wani lungu agidan don kuwa ji
nayi hawaye,na surnano min kwatsam sai ga
imamu ya zagayo yakama hannuna muka shiga
dakinsa. Rarrashin duniya da ban ba ki babu
wanda bai,yimin ba amma na gagara yin shiru har
sai da yayimin alkawarin aure na bayan bikinsa
sannan hankalina ya kwanta Haka inaji ina gani
akashiga gudanar da bikin Imamu duk da zuciyata
na tukukin haka na hakura ina kuma taya imamu
murna Bayan bikin Imamu da amaryarsa sai naji
labarin wai a kano zasu tare, hankalina ya tashi,
amma Imamu yasake jaddada min alkawarin aure
kafin tafiyarsu hakan yakwantar min da hankali
sai dai ko da suka tafi Imamu bai sake
waiwayata ba ko ya zo kuma sai ya yi tahade
min yana wani cin magani harnagaji. Wani zuwa
da yayi nake tambayarsa ko ya janye kudurinsa
na aurena bawani ja'inja ya shaida.Min eh ya
fasa . Raina yabaci amma sai nasake tambayarsa
menene dalili? amsar da ya ba ni ta gigitani
domin cewa yayi fatima gaskiya ina matukar son
matata kuma tana jajircewa wajen yi min biyayya
ba na jin zan iya yimata kishiya domin yin hakan
tamkar kawo wata barazanane ga rayuwar
aurenmu zan miki addu'a Allah ya zaba,miki
abinda yafi alheri...." Wani kallo nabishi dashi
hawayen bakin ciki na zubowa akwarmin idona
ahankali na lumshe ido nace Imamu ka cuce ni
sai dai ina maka albishir da komu dade ko mu
jima sai na dau fansa" Wannan dalilin shiyajanyo
min koma wa rayuwar banza Na kuma kaddara, a
Zuciyata sai na yima ramuwar gayya wanda ake
cewa ta fi ta gayya zafi . kwatsam sai muka wayi
gari anshiga har anyi wa kanwata datake bina
fyade, lokacin yayanmu yatafi Lagos. Nayi kukan
bakin ciki kamar raina zai fita nakuma ja bakina
na tsuke ban gaya wa kowa ba saboda ba na son
zancen ya bazu a garin ina gudun kada sunan mu
yaba ci Al'amarin Allah bayan watanni sai ciki
yabayyana na sa ta agaba tagayamin ko ta gane
fuskarsa take . Tasanar dani kanin Imamu ne don
yasha yaudararta da kudade tana kin bashi hadin
kai shine ranar dayaga ba kowa agidan yashigo
yakulle ta yayi mata fyade wani ashar nazunduma
sannan namike nazira hijabina ina fadin wallahi
ba a isa ba sai naje hargidansu Imamu tunda dan
kanwar babarsa ne da take riko ita zanje na
sanarwa idan taki ji hukuma tabi mana hakkinmu
Akofar gida nahadu da baban Imamu banbi
takansa ba ina huci ina komai nashige gidan don
kuwa tabbas zuciyata a sama take na bankada
labulen dakin ko sallama banyi ba Hajiyar ta dago
tana kallona ke lafiya? . wane irin iskancine zaki
shigomin ko sallama babu? Na shaka da yawa
kafin nace Ba alheri ya kawo ni ba nazo nasanar
dake ta'asar da danki ya tafka" Ahanzarce ta
kalleni tace Hmmm ba shakka yanzu na gano
bakin zaren ai wato saboda kin makale yasoki
yaki shine Zaki yimasa sharri? Ina lura fa da
take- takenki duk binbinin da kika dunga yimasa
ido nazuba miki na ga iya gudun ruwanki.Don
kuwani banga me Imamu zaiyi da diyar da ba
asan asalin ubanta ba..." . Da sauri na daga mata
hannu"saurara! Ba zancen Imamu yakawo niba
zancen Hamidan ya kawo ni yaje yadibga ma
kanwata ciki tahanyar fyade kuma wallahi ba zan
yarda ba sai nakai shi ga hukuma" "Kikaishi ga
hukumo ba hukuma ba saboda tsabar sharri yaro
dan shekara sha bakwai zai iya yin ciki? Kwaje
can inda kuka samu cikinku kuji dashi amma ba
za alikawa dan marayan Allah ba yo dama har ku
din wasu nagari ne ai barewa ba ta gudu danta
yayi rarrafe wayasan asalin ubanku muhammadu
mai hula mutumin da muka ganshi zikau agarin
nan da girmansa har yakarar da nagartarsa... . "
Lafiya nake jin hayaniya.?Baban Imamu yafada
yana shigowa gidan Hajiya taja tsaki Duk bakai
ka janyo mana wannan shirgin ba ga ta nan ta zo
da sharri wai hamidan yayiwa kanwarta ciki kai
kaji wata tatsuniya yaro dan shekara sha
bakwai..." Alhaji murmushi yayi yace kada ki ja
da ikon Allah yaran yanzu ba irin shaidancin da
ba su sani ba ke dagaske kike ko wasa? Alhaji
yatambayeni rantsuwa nayi akan cewa dagaske
nake yagirgiza kai "To kinji hajiya . Sai asan
abinyi Nidai data kai batun nan gahukuma gwara
ayi hakuri adaura musu aure da zarar ta haihu
Hajiya ta zabura "Au me? aure da wa? Allah ya
kiyaye jinina yahadu da jinin shege kuma karya
take kaf zuri'armu ba karuwa ba dan'iska Don
haka ni ban amince da cewa hamidan yayi wa
kanwarta ciki ba sudai da suka gado iskancin sa
sunsan inda tayo ciki amma mu kam kaf
zuri'armu 'yan mutuncine Duk yadda Alhaji
yabulla sai matar nan ta bulla sam ta ki yarda
hamidan ne yayi wannan ta'asar Haka inaji ina
gani naja sangalalin kafata cikin mutuwar jiki
nakoma gida ina kuka Abu yabazu akauye nan da
nan aka shiga yimana gori ba shiri na hade
kayanmu muka yi kaura kano inda na kama mana
hayar daki awani gidan karuwai ta silar wannan
abubuwa dasuka,faru ni da kanwata muka
tsunduma kanmu acikin karuwanci kafin wani
mutum Alhaji muhammadu ya mayar damu
gidansa,mutum ne mai kudin gaske sai dai ba
ya,haihuwa . matarsa mutuniyar arziki yar garin
Bendel tayi mana rikon mutunci Daga,lokacin
nafara binciken yadda zanga Imamu . don daukar
fansa kwatsam ranar an Kai uwar dakinmu asibiti
na hango shi shi da matarsa bai ganeni ba kasan
cewar hijab nasaka da nikab nikuwa nan nashiga
bincike amma har na gano gurin family doctor
yake kai matarsa awo alokacin tsawon shekara
goma bansan ya shi a idona ba.Kawai zuciyata ta
rayamin DAUKAR FANSA wannan shine dalili"
Gaba daya kotun tadauki hayaniya Abbana
yadanyi murmushi don ya fuskanci daukacin
jama,a shi suke jin haushi . "kina ganin yanzu
ramuwar da kikayi akaina batayi.Yawa ba? 'yafa
kika saka aka sace min sukutum sannan kika ba
da ita ga magajiyar karuwai ta koya mata
tarbiyya irin tata duk adalilin naki na aureki" Ya ja
ajiyar zuciya hakika kincuceni iya cuta fateema Ni
bazance miki komai ba sai dai Allah ya shiryeki
Akarshe daga yau shari'ar ta bar hannuna
takoma gun abokin aikina kasan cewa abin
yashigo da ni aciki kuma shine zai kawo karshen
wannan shari'ar" Daga haka Abbana yabuga
guduma jama'a suka furta kotu. Nan da nan aka
fa ra watse,wa muma jikinmu asalube muka
mike,da niyyar. RAYUWA book 3 part 7
NAGA RAYUWA book 3 part 7
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:09
Tafiya gida ummana kuwa tana hada ido da
shany take tasaki kuka Nasan radadin abinda
takeji Nikuwa,damuwata daya ce mamina yanzu
Abbana da wane idon zai kalli mamina
kai.Jama'ar gidanmu ma gaba daya me za suce
da ita? . Duk da tarin zargin da akayi
marattabbas ancuceta ankuma zalunce ta shi
kansa na lura Abba na jikinsa amatukar sanyaye
yake don ko da yadawo gida sashen sa ya,shige
yakulle kofa Nikuwa idan na kalli yar'uwata
Shany sai naji tausayinta ya sake kwarara
azuciyata Don itama kuka take sosai tare da
sauran yan'Uwanta su shida. . Ummana tana can
kuryar daki nayi sallama nashiga da kyar ta dago
idonta da yayi jajur takalleni na,zauna a gefenta
na ce Umma wai me yasa kuka damu kanku? Ba
za ku yi hakuri ku gode wa Allah ba da ya
kaddara muku saduwa, da diyarku tun kuna raye?
Umma ta dago tana duba na Aysha Allah shi ne
abin godiya ba komai yake damu na ba sai yadda
wannan matar ta gurbata min tarbiyyar yarinya
yanzu ta ina kike tunanin zan fara gyaran
tarbiyyarta? Abu na gaba da yake damuna shine
maminki . yanzu da wane ido Abbanki da
yayyenki zasu dubeta? wannan shine matsalata
Ajiyar zuciya naja nace Umma duk wannan mai
sauki ne tarbiyyar shany dai ki kaddara Allah
shine mai shiryarwa ki ci gaba da rokonsa ya da
fa miki awajen tarbiyyarta da ta sauran
yan'uwanta Mamina kuwa insha Allahu
matsalarta mai sauki ce Umma girgiza kai tayi
tace Bamai sauki bane fateema na da riko kuma
tadau zafi sosai a maganar nan ba ita kadaiba
ma gaba daya danginta kuma tabbas yakamata
su aikata hakan ko fiye da hakan don kam tabbas
an bata musu . shiru nayi don kam ni ma
shaidace da yadda yan gidan mamina suka dau
Zafi kuma tabbas yacancanta ayi hakan don an
bata musu Umma ta ja ajiyar zuciya kafin tace
Tashi kije kija yan'uwanki ajiki Aysha don Allah
musamman yar'uwarki duk da Abbanki yace zaisa
ayi tayi musu addu'a amma tarbiyyarsu kam sai
antashi tsaye. Jikina asanyaye namike nafice
daga dakin don na lura Umma babu abinda yake
ta yar mata,da hankali sai yadda za ta daidaita
nutsuwar Shany ta dawo abar kwatance. .
Tabbas wannan matar tacuci iyayena kuma
wannan shi ake cewa ramuwar gayya wacce tafi
ta gayya zafi Nayi Alkawarin zantaimaka mata da
gyaran tarbiyyarsu Afalo natararsu gaba daya
suna zaune sunyi jugum-jugum sosai tausayinsu
ya,tsirga min na zauna kusa da Shany tare da
janyota jikina."Please! ya kamata ku cire damuwa
daga ranku haka tunda dai duniya ta shaida ba
ku da laifin komai tarbiyya akayi muku ahaka
kuma ita ta cuci kanta duk da itama tashi tayi ta
tsinci rayuwarta a haka amma bai kyautu ace ta
dora da nata mugayen halayen ba" Shany ta ja
ajiyar zuciya kafin kwalla ta,zuba sharr daga
idanunta tace Sister ina jin matukar bakin ciki
idan na tuna,rayuwata ta baya haka kawai banji
ba bangani ba don wata manufa aka rabani da
nagartattun. Halaye na aka,kaini wata banzar
rayuwa banjiba banganiba wallahi Allah ya isa
bazan taba yafewa wadannan mutane ba Ta sake
fashewa,dakuka Ni kaina kukan ne yaci karfina
can daya daga cikin kawayenta tace Kukan dadi
kikeyi shany,saboda ke yanzu yar gata ce
kinsamu iyayenki. . Mu a ina kike tunanin zamu
ga namu iyayen? shegu ne mu bamu sani ba
itama tafashe dakuka gaba daya gurin,sai muka
saka kuka, Daidai lokacin Umma tafito tana
sallallami yanzu mezan gani haka kuda zaku
godewa Allah da rayuwarku ba ta kare ahakaba
amma shine kuke kuka?, Dasauri ta fice nalura
itama Umma kukan takeyi da kyar na mike bayan
naji ana kwala kiran sallar la'asar nace musu
muje muyi sallah jikinsu asalube suka mike tare
da haramar alwala Abinda ya ba ni mamaki bai
wuce ganin yadda suke sallah ba gaba daya
dungurawa kawai sukeyi tausayinsu ya sake
kamani Don kam na tabbatar ba karamin gyara
suke nema a addininsu ba . nadauki damarar
koyar dasu sallah kafin komai da daddare gaba
daya muna zaune awajen da ake cin abinci bayan
angama Abba yadube mu yace masha Allah" kafin
ya karasa naji mayataccen kamshin Ahmad
yacika harabar gidanmu take nahade raina sosai
don ba na son abinda zai hada ni da Ahmad cikin
takunsa na isa yakaraso wajen yan matan Abba
kuwa, tuni suka zuba masa ido tsiyar namiji
maikyau kenan. . Duk inda yashiga sai kallo Na
kaddara hakan araina har rige-rigen yimasa
sannu da zuwa sukeyi Shany da sauri tamike ta
shimfida masa darduma "Nagode" yace mata
cikin tausasshiyar murya sannan ya zauna ya
sake rankwafawa ya gaida su Abba yasa ke
jaddada musu murnarsa na bayyanar yarsu shany
Ni kuwa tuni nazare jikina nashige dakin umma
wai kuma sai naji ina kishin kallon da yan'Matan
Abba sukewa Ustaz Na zauna turus akan kujera
hade da dafe kunci inatunanin Ustaz da irin
tsananin kyan da yayi . Yau shigar wata jallabiya
yayi dark-blue sai shaking take. Ta kwanta lub
ajikin lallausar fatarsa wanda yala-yalan gashin
yakwanta ajikinta Asalin balarabe dole duk macen
da ta ganshi ta kyasa Atake na dokanta naji
Ustaz ya kirawo ni koda masifar da na saba na
zazzaga masa. Sai dai shiru makatau take naji
wani abu ya tsaya azuciyata na tabbatar yanzu
Ustaz ya gama yayina Don haka kone mana ba
ya yi Shany ce tashigo dakin tana murmushi tace
"Sis,wannan ma dan' uwan mune?" Da sauri na
dago nawur ga mata wani kallo ina son . Gane
me take nufi da tace hakan Ban hango komai
akwayar idontaba don haka hankalina yadan
kwanta Ahankali nace mata "MIJINA NE" amma a
da fa Takuwa bude ido tace Wow! Amma meyasa
kikace a da kina nufin yanzu kun rabu? Cikin
sanyin murya na fara sanar da ita labarin
Ustazuna kafin nagama kuwa tuni hawaye ya fara
zarya, akan kumatunta Da safe kuwa kasancewar
lahadi ce yawanci surukan gidanmu anan suke
wuni sai dare suke tafiya harda mazajensu da
'ya'yansu muna zaune na saka .khadija da
A.Nafisa matar ya usman atsakiya sai hira muke
cikin nishadi don ni sauran matan yayyena ba sa
gaba na don dana shiga halin da za a tausaya
min ba wacce ta kula dani tamkar khadija Abba
ne yashigo yana kiranmu nida 'yan matansa
Afalonsa muka zauna anan kuma muka tarar da
wasu matasa daga ganin su ka ga malamai don
yanayinsu ya nuna haka Abba ya nuna 'yan
matansa yace "Alhamdulillahi, gasu nan su
takwas ne nakeso kafahimtar dasu addini don
basu san komaiba game dashi malami daya
yagyara zama yace "Alhmdllh" sunana m.Kawu
kuma . Zan dunga koya musu Alkur'ani zamu
soma daga fatiha insha,Allahu" Dayan ma
yagyara zama yace sunana M.Aminu zan koyar
daku fik'hu da hadith insha,Allah" haka dayanma
yagaba tar da kansa "sunana M.Amadu da yar
dar Allah zandauke ku darasin Sirah da tauhidi."
Abbana yasake gyara zama yace Alhmdllh nagode
Allah dama na sanar da su labarinku duka sun
kuma matukar tausaya muku da wannan dalili na
san insha,Allahu zasu jajirce wajen koyar daku. .
Ga aysha nan ma za ta sake tunasar daku
abubuwan da ba ku, gane ba kaina yana kasa na
dago inda muka hada ido da malm.Aminu yace
A'a Aysha tana gidane? . murmushi nayi da yake
na sansu malaman mune na tahfiz nasan
M.Aminu da tsokana Abbana yace Aysha ta ki
zaman aure yafada yana dariya Da,sauri na mike
nashige gida da gudu Don ba na son fadan
malamaina nasan su kamar yunwar cikina
musamman malam amadu Tun daga ranar Abba
yace adunga kiran shany da humaira tunda itama
sunanta Aysha bazai yiwuba mutashi a suna daya
sun kuma da ge sosai wajen karatu kuma duk
inda zasu hadda hijab . suke zuwa Sosai nake jin
kunyar haduwa da Mamina don haka haryanzu na
kasa Zuwa gidansu duk da ba ni nayi mata lefin
ba amma na ja janta tabargazar da Abbana yayi
mata Na jin jina mata laifin da ba nata ba
abinda,yafi komai ciwo arayuwa azarge ka da
abinda ba,ka aikata ba . Ranar Lahadi sati biyu
da faruwar lamarin gaba daya muke zaune
aharabar gidanmu har da yayyena da matansu
kawai mukaji sallamar MAMINA kafin kace me
tuni yaya.farouk da yaya.Ali sukayi wani tsalle
suka gudu can bayan gida mamina ta shigo cikin
zumbulelen hijabi da nikab Da murna ta natashi
ina tsalle na rungumota ita din ma rungumo ni
tayi tana sakin murmushi Ummana ma da sauri
ta mike ta tarota cikin murmushi mai kama da
yake take fadin mamin Aysha kece da rana haka?
Ba tayi magana illa bi na da tayi da kallo tace .
aysha,wajenki nazo don tayaki murnar kubuta
daga kangin da kika shiga In kuma tayaki murnar
ganin yar'uwarki akarshe nayi miki sallama zan
tafi England karo karatu" Tuni hawaye suka
sulmiyo min daga idona nace novels / NAGA RAYUWA book 3 part 8
NAGA RAYUWA book 3 part 8
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:11
. "Mamina kina nufin ba za ki dawo gidannan ba
kin.Rabu damu har abada? Hannu ta saka tasha
remin hawayena kafin nata digon hawayen ya
dirgo akan kuncinta tace "Na rabu da kowa daya
dangance ki Aysha amma ke da usman bazan iya
rabuwa da ku ba Ina tare da ku a waya ko
lokacin da zanzo hutu ki kular min da kanki
Ayshata" . Daga haka ta zame hannunta takuma
juya da azama da sassarfa Zata,wuce Umma
turus ta tsaya idonta na kwalla nikuwa da sauri
nabi mamina shima yaya usman ya fello da gudu
muka tsare mamin da magiya Daidai lokacin
Abba ya shawo kwana zaishigo sukayi ido biyu
da mamina Cikin sassarfa yajuya da azama yabar
gurin shi kansa nasan kunyar gamayyarsu da
mamina yake Mamina ta kalleni tayi murmushi
ahankali ta furta . "SAI WATA RANA AYSHATU" .
Daga haka ta zame tafice Tuni na durkushe
awajen na saka kuka don sam gwiwata ta ka sa
daukana yaya usman yakama hannuna muka
shiga gida shi kansa na lura jikinsa yayi sanyi
sosai Abba naji yana kwalamin kira cikin sanyin
jiki na mike na isa falonsa Tarar dashi nayi
idonsa . Yayi jajur da alama shima kukan yayi
yace Ayshatu mamin naki ta tafi? cikin sanyin
murya nace "Ta tafi Abba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login