Showing 177001 words to 180000 words out of 209775 words
kudi ne.....zan nema yarinyar da ba kasafai namiji ke burgeta ba kaman yadda kudinsa yake burgeta ba......za muyi contract da ita na auren fu'ad zuwa wani lokaci.......zata shayarmin dashi ta ciyarmin dashi daga dukkan wani abu da akeso yaci ko yasha da zai jawo min hankalinsa.......daga sanda buqata ta biya zan sallameta daga dukkan adadin kudaden da takeso tayi kuma nesa da rayuwarsa.....a sannan ne kuma tayimin tawa shimfidar da zan soma tawa tafiyar".
Idanu hajja ta zubawa maamah sosai.....ga bikin zuwa kuma babu zanin daurawa.....tabbas wannan tsari nata yayi.....kuma komai zai iya tafiya ya kuma wanzu kaman yadda ta tsara din muddin akayi katari da kalar yarinyar da zatayi aikin.
A jikinta takejin wannan aikin nata ne,wannan kuma su za'a yiwa.....wannan aikin JANAN dinta za'a yiwa ba kowa ba......zata soma tata shimfidar ne itama a sanda mariya ke tunanin zatayi tata.....a sannan zata wanzar da nata tsarin da zai kauda na mariya,dole ta tsaya kai da fata ta taya mariya fafutukar wannan tsarin ya tabbata,to amma ta yaya zaiyi accepting?. Yaron da yake da tsananin kafiya da tsaurin da bokansu ma ya gaza juya akalarsa?.
"To amma ta yaya kike zaton zai karbi maganarki ta sauqi irin haka?" Hajja ta yiwa maamah tambayar da taketa cin ranta.
Wani murmushi maamah ta ajiye tana goye hannuwanta a qirji,daidai sanda sabreen ke shigowa wajen tana takowa cikin nutsuwar nan tata me fusgar hankali,sai maamah din ta dauke idanunta daga kanta ta maida ga hajja ba tare data bawa ganin data yi matan muhimmanci ba,amma abu daya taji ya darsar mata a rai
"Da mata masu kyau irin haka ya kamata ta yiwa fu'ad din fatsa.....domin su din suna da saurin kama zukatan mazaje".
"Komai lalacewar uwa uwa ce.......hakanan komai lalacewar d'a yasan me ake nufi da uwa.....ballantana fu'ad da nasan me na haifa?,nasan iya matakin kaifinsa da kafiyarsa......wannan ba wani abun damuwa bane".
Ba tare da jira ko neman izini ba taja spare kujerar dake gefansa ta zauna. Shimfidadden kyan nan dake fusgar zuciyarsa tunda can baya wanda ya jashi zuwa ga wanzuwar alaqa tsakanin su a yanzun sai yakega ya ninka yadda yake a baya. Fuskarnan a rubuce da dabi'ar miskilanci baro baro samanta.
"Zuwa da kai ai yafi saqo ko?......ka nema qanwar ga yayar tazo da kanta.....zaifi kyau a sauka ta inda aka hau". Tayi maganar a jejjere da wani irin aji da kintsi daya qara kwarjantata a idanunsa.
Zuciya da ruhinsa suna masa d'ari d'ari gami da gargadinsa a kanta,to amma kuma wani sashen na zuciyarsa na bashi tabbacin tabbas yaci wasan ne......lallai ta fuskanci cewa shike da nasara wannan dalilin ya sanya tsananin wayonta ya bata shawarar tayi gaggawar bada kai.
Wata irin dariya ya kece da ita yana kallonta gami da gyara zamansa sosai
"Haba 'yammata?,irin wannan karaya haka da sauri?"
"Karaya kuma?......sabreen bata taba karaya ba.....hakanan ba zata karaya akan wulaqantaccen mutum maras daraja irinka ba". Mamaki ne ya lullube farincikinsa,a hankali yanayin fuskarsa ta sauya.
"Daga yanzu zuwa sanda zaka isa gidan birsin ka fara qididdige yawan adadin haramtattun kudadenka da zasu salwanta bayan cafke jirgin da aka boye cocaine me nauyi,wadannan kudaden an samesu ne ta hanyar maida mutane zuwa dabbobi wajen basu gurbatattun magungunan bugarwa da sanya maye.....kaga kuwa garin banza a farau farau din banza yake qarewa".
Wani irin shock ya shiga saboda kiran sunan jirgin da ayau yake sanya ran isowarsa. Ya lissafa yau a ranar sa'a a gareshi.....zai aike mata da sakamakon abinda tayi masa ta jikin 'yar uwarta......hakanan kuma zai maida gurbin hasarar da yayita jiran cikewar gurbinta.
Bai qara koda motsi daya ba sautin takun ma'aikatan cikin sassarfa da hanzari ya karade gurin. Hankalin kowa dake wajen ya tashi yayin da aka soma kallon kallo a tsakanin juna.
"Kada wanda ya motsa.....munxo kama me laifi ne.....kowa yana cikin aminci.....amma kada ku motsa har sai mun gama mun bada umarni" Daya daga cikin ma'aikatan da ba'a iya ganin fuskarsa yayi maganar a gaggauce.
Ance mara gaskiya ko a ruwa gumi yakeyi......wannan ya sakashi miqewa da zummar samun hanyar fecewa,saidai kuma tuni suka ankara suka masa qofar rago gami da fadin
"U are under arrest!". Wadannan din ba irin ma'aikatan daya saba gani bane,rana dubu ta barawo,ya tabbatar idan har ya saba kubce musu to a wannan karon babu wannan damar,don haka ya tsaya kyam jikinsa yana kyarma har suka gama.
"Koda ka sake samun rayuwa a nan gaba.....kayi komai da lura" Ta furta tana nuni da gefen kanta,sannan ta juya a nutse ta fara takawa
"Thanks for the information" Daya daga cikin ma'aikatan ya furtawa sabreen din da ta fara barin wajen. Murmushi ta saki kadan
"Wannan aikin kowanne dan qasa na gari ne"
"Gaskiya ne" Ya furta yana saluting nata,yayin da suka waiwaya zuwa ga Naseer suka riqeshi sosai suka sanyashi a tsakiya suna fita dashi ta daya qofar cikin hararrami da tsaurara masa tsaro.
"Keep calm......you're safe guys.....kowa yaci gaba da sabgarsa". Mutumin da yayi musu jawabin farko a yanzu ma ya fadi sanda yake bin bayan abokan aikinsa da sassarfa.
"Tabbas akwai wata boyayyar fuskar a bayan wannan" Muryar hajja ta daki kunnen maamah wadda idanunta ke kan hanyar da sabreen ke wucewa.
Dauke kallonta maamah tayi zuwa kan hajja
"Kada dai ace tunaninmu yazo daya?"
"Me kenan?" Hajjan ta cewa maamah tana dubanta
"Na samota.....inaji a jikina zata iya.....inaji a jikina ba iya fuskar da muka gani yanzu ce kadai a tattare da ita ba.....zo muje" Maamah ta fada tana jan hannun hajja zuwa hanyar da sabreen tabi.
"Inason insan wacece.....inaji munzo nan ne a yau domin cikar burina" Maamah ta fada tana jin wani irin nutsuwa da fuskar data gani din.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 91
Agogon fatar dake daure a hannunsa ya duba bayan yadan gyara shirt din jikinsa. Lokacin da yake hutu na mintuna ashirin zuwa talatinne a yanzu.
Iska ya furzar daga bakinsa yana duba adadin mutane da jerin sunayen wadanda keson ganinsa ta qaramar computer gabansa wanda mutumin da yake kula da sashin da zaka soma tsaiwa kafin ka samu damar ganinsa ya tura masa wato mr abdulhaleem.
Mikail shine mutum na farko cikin jerin sunayen,to amma baya buqatar ya fara da ganinsa,don hakan zai iya hasala fushinsa ya gaza ganin sauran mutanen dake da muhimmanci su ganshi din.
Me sunan malam ya kira,ya bashi apple da strawberry sai ruwan dumi. Mintuna goma kacal ya bawa kansa sannan ya fara bada umarnin shigowar baqin.
Duk wani mutum me muhimmanci sai daya kammala da ganinsa kafin ya bada umarnin shigowar mikail,wanda zuwa sannan yayi imanin inda za'a auna jininsa yakai dari biyi qila harda talatin ma.
Sanda yake shigowar fu'ad din yana tsaye daga bakin book shelve din da aka yiwa wani kyakkyawan tsari cikin office din. Dukkan documents din da suka shafi case din yake cirowa a nutse yana qoqarin danne yadda ranshi yakeyi yana baci.
Ba kaman kwanakin baya kadan da suka shude ba.... Lokacin da yake da daraja da martaba ta gaba gaba cikin kamfanin......a lokacin da zaiyi sallama cikin girma da mutunci cikin office din,ya tako kaman kowanne ma'aikaci da Allah ya tarfawa garinsa nono yake iya idanu biyu da muhammad jadda din kai tsaye ba tare da shamaki ba. Akwai dubban ma'aikatan dake kamfanin wanda basu taba idanu biyu dashi ba......amma shi yana cikin wadanda zasuyi tattaki har zuwa cikin office din su zauna saman kujerar da ake bawa kowa don ya tattauna da CEO din.....a yau din sai gashi a matsayin qasqantacce,me tarin laifukan da baisan ta inda zai fara kare kanshi ba. Ya fadi gaskiya?,wadda ya tabbatar fadar nata wata faduwa qasa ce wanwar......yayi qarya?,ita kuma ta zame masa alaqaqai da babbar matsala a duk sanda me jadda din ya gano ainihin matsalar.
A nutse ya juyo abinsa ba tare daya kalli sassan da mikail ke gurfane saman gwiwoyinsa ba. Baice komai dashi ba sai daya koma saman kujerarsa sannan ya motsa bakinsa a nutse
"Tsugunna kazo kayimin ko bayyana min gaskiya?....idan kuma duka ba wannan ba ka shirya amsa tambayoyin muhammad fu'ad?" Ya qarashe qarshen maganar yana dauke idanunsa daga kan file din yana zube masa su.
Kallonsa kadai ka sanya razani a zuciyar mutum,ballantana ma mutum irinsa maras gaskiya ko qanqani?.
"Na shirya sir.....don Allah kayimin rai"
"Gaskiyarka kadai ita zata fiddaka.....am listening" Ya furta yana dora qafarsa daya kan daya,sannan yayi relaxing bayansa sosai da fuskar kujerar tana juyata a hankali,wanda banda motsa kujerar da yakeyi idan ka kalli kyakkyawan fuskarsar nan me shimfidadden kwarjini zakayi zaton bacci yakeyi.
Bai boye masa komai ba......ya gaya masa komai yadda ya wakana......saidai statement dinsa na qarshe da harshensa yaso sarqafewa
"Saidai.....daga b.....dag.....ga baya na gano da ita da wan....."
"Da wancan tsohon dan cacan UBA NE DA 'YARSA BA ka gayyatosu suka taba dukiyar da gumin halal ya tarata?!" Ta furta da wata irin tsawar da hatta mutumin dake qofar farko bama reception na office dinsa ba zai iya jiyo tartsatsinta,bayan dukan table din da yayi da hannunsa abinda ya sanya wasu files din da takardun misplacing daga inda suke.
Har cikin tsokarsa yake jin fushin yana masa tasiri.....bai taba ganin an raina masa wayo kaf rayuwarshi irin wannan lokacin ba. Sanda yake kammala binciken da sakamakon daya karba daga hannun wadanda yasa suyi nasu binciken ya duba yaga conclusion nasu yayi daidai da nasa.....saidai duk da haka zuciyarsa tana masa kokwanto.
Ta yaya 'ya zata zama KARUWA?.....yar fashin YANAR GIZO.....MAYAUDARIYA ME SACE XUKATAN MAZA DON KAWAI TAYI AMFANI DASU?. Sannan kuma ace uba ya zama DAN CACA?,WANDA ZAI IYA ZUBA KOMAI A CACAR NAN DON NASARA TA ZAMA TASA CIKI HARDA TAKARDUN GIDAN DA MARAYU KE ZAUNE A CIKI?.
Dukka jikin mikail bari yake kai kace wanda aka watsawa ruwan qanqara ne cikin hunturun matsanancin sanyi.
"Kayi haquri yallabi.....tuba nake.....kayimin gafara kayimin aikin rai....wallahi banci komai a ciki ba sir.....ko sisi sai nawa kudaden ma da suka narke!"
"Will you shut your mouth or not?!" Ya sake fadi da wata gigitacciyar tsawar data sanya fitsari balle ma mikail din,ya kuma koma yayi zaman dabas a qasa don ya gama sarewa.....ya kuma yi imani bashi da sauran mafita.
"Ni zaku mayar dan iska?,dukiya ta halalina a gidan caca?,a wajen karuwai?,a wajen sabon Allah?.....ko an gaya maka ni ban san dadin rayuwa ba?,sai kai?......to daga kai har su wannan shine zai zame muku aikin ashsha na qarshe da zaku aikata.....daga kaina ba zaku sake marmarin sake aiki irin wannan ba......ka tashi ka fita ka bani guri.....zan nemeka.....idan kaso ka gudu duk inda kakeso" Ya fadi yana huci idanunsa da suka sauya launi akan fuskar mikail da yayi jalaf da gumi da fitsarinsa.
"Na roqeka sir......kayimin duk kalar hukuncin da zakamin a yau basai wani lokaci ba......amma ka yiwa Allah kada ka koreni daga bakin aiki koda zaka sauyan matsayi".
"Naci gaba da biyanka albashi kaci gaba da shan barasa da neman mata.....ka bacemin a wajen tun ban gama tunzura ba!' Ya amsa masa yana sake jin zuciyarsa tana hasala.
Ajiyar zuciya gami da iska zazzafa ya dinga fesarwa bayan fitar Mikhail din. Ya sake komawa yayi relaxing sosai yana jin wani irin huci yana fita daga fuskarsa. Ya tsani dukkan wasu ayyukan ashsha......mikail yayi masa abu mafi muni....abu mafi munin koda dashi kadai ya kamashi cikin company dinsa zai iya zama silar korarsa ko rasa aikinsa....NEMAN MATA.....zina itace abinda yafi qyamata cikin rayuwarsa bayan shaye shaye,dukka rayuwar mikail ta dagula ta kuma gurbata cikin wadannan ayyukan. Wata qyama ta mikail dama yarinyar gaba daya suka sake kamashi,ya waiwaya fannin caca......abar data tabbata da nassi cewa haramun ce itama qarara.....
"Wadanne irin ahali ne wannan?" Ya furta a fili qasa qasa zuciyarsa na masa wani irin ciwo. Baisan girman tsanar da ya yi musu ba....ko don ya taso ya samu nagartaccen mahaifinsa ko yaushe yana jaddada musu su guji su kuma nisanci wadannan abubuwa iya gudunsu?.
Wanne hukunci ya dace yan yankewa mikail?,tsohon dan cacar da kuma 'yar kwaltar Yarinyar?. Wannan tambayar ce har ya gama zamansa a company na wunin ranar bai samo amsarta ba.
Yau koda ya koma gida sai yaqi zaman sassansa.....ya zauna sosai sunyi dinner dukkansu kaman yadda suka saba a duk sanda dama ta basu irin haka dukansu su shidan. Sun jima suna hira tsakaninsa da abba,wanda anni na gefe tana jin gwarazan 'ya'yan nata. Qauna da kuma wani alfahari dasu yana ratsata.
Sha daya saura ya sanya qafafunsa a sassansa,wanda kamar tunanin yana tsaye daga bakin qofa yana jiransa ya mamayeshi. Yaja dogon tsaki kamar zai tsinke harshensa......ya taka a hankali yana zarcewa toilet bayan ya sanya me sunan malam ya sallami kowa,masu kwanciya sun kwanta,masu kwana bakin aikinsu sun kama wajen tsaiwarsu.
Shafa'i da wuturi yayi a kebantaccen wajen daya ware saboda ganawarsa da ubangijinsa. Koda ya idar sai yayi zaune saman abun sallar. Yana jan hasbunallahu da duk dare bata wuceshi qafa dubu da la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin. Iya wadannan abubuwa guda biyu ya tabbatar suna taka rawa me yawa cikin rayuwarsa,sun kuma zame masa mabudin sirrin nasararsa.
Har ya kammala ya kasa tsaida hukuncin da zaiwa kowannensu,har sai daya hau saman lalallausan gadonsa,ya dauki qaramin remote yana sauke rumfar gadon da ke tattare ba lallai ka lura ma da ita,kyakkyawan net din ya sauko ya lullube gadon ruf yana bada wani dim light da ke bawa bacci nutsuwa.
Numfashi me zurfi ya sake ja yana jingina bayansa da pillow hadi da lumshe idanunsa kana ya budesu. Kamar wannan kawai ake jira yayi qwaqwalwarsa ta fara aiki.
"Mikail ya dade da zama korarre daga dukkan wani aiki da yake da nasaba da jadda diamondchore resources company......kamfanin dake kano ko lagos.....koda kuwa aikin shara ne cikin kamfanin........mutumin da ake kira da samaila fa?,idan yace ya dawo masa da dukkan abinda yaci nasu horo ne me sauqi.....dole ya hada masa da wani abun....YARINYAR KUMA FA? .
Jan duvet dinsa yayi yana lullube fuskarsa har zuwa kanshi. Koda a qasan zuciyarsa bayason tunata. KARUWA wani suna ne daya samu gurbi cikin kunnuwansa tun yana da shekara goma sha uku a duniya.
_"mariya......bansan me yasa idanunki suke makancewa ba da barin daidai.......kina matsayin matar aure.....wadda ke auren sunna da yara har guda biyu,me zai hadaki alaqa da qawance da karuwai?"
"Karuwai?,hmmmm.....bakasan a yanzu babu wanda yakai karuwa mutunci ba?,saboda zaunannun kudi gareta da zata yiwa duk wanda taso ihsani.....kyautar ban girma da ban mamakin da ke da kike qarqashin inuwar aure baki isa ki sameta ba.....kaga kuwa karuwanci ai ya biya su".
Muryoyin dukansu su biyun da irin zancan da sukayi a sannan ya dawo masa tarwai cikin kwanyarsa abinda ya sake qarawa zuciyarsa wani irin zafi da radadi. Abbansa dake kwance a qarqashin qasa yanzu......da kuma maamah din da take rayuwa dasu a yanzun hakan itama. Wani yanayi ne da bayason tunashi......wasu abubuwa da binnesu yafi zama alkhairi a gareshi duk da yadda kullum suke qona masa zuciya da mafi zafin ciwo da suka.
"Dole ta fuskanci hukunci me girma....." Ya fada yana bude idanunsa,ya dauki wayarsa ya aika gajeran saqo sannan ya koma ya kwanta yana qoqarin tilastawa kansa yayi bacci.
Kwanaki ukun da ya dauka yana dakon jiran kira daga wajen Muhammed jadda sai suka zame masa tamkar me jiran ranar mutuwarsa ne. Komai ya tsaye masa cak.....wata iriyar nadamar sanin sabreen dake a mazaunin fateema a wajensa tana mamayarsa irin nadamar dashi kansa baisan yawanta ba.
Ranar da saqo daga kamfanin jadda din kwana yayi yana zawo. A gobe jumaa....juma'ar da baisan yaya zata kasance masa ba.