Showing 60001 words to 63000 words out of 209775 words
daya zan fita,zamu gana da ceo na Labrilliante company,zan miqa musu iya abinda zasu samu.....don abba wannan karon tunanina ya fara sauyawa" Maganar fu'ad cikin tatacciyar nutsuwar nan tasa da wani irin jan aji kamar mace ya dawo da Alhaji hamza daga tunaninsa
"Wanne tunani ne fu'ad?" Zamansa ya gyara sosai yana bawa abba dukkan kallo da hankalinsa
"Abba......a yadda mutanen nan daga kowacce qasa suke rububin siyan resources namu da muke fiddowa daga qarqashin qasar da Allah ya shimfida mana kadai ya isa ka fahimci suna amfani damu ne suna kuma amfani da damarsu......yanzu haka a daren jiya kafin na kwanta sai dana karba kira daga wani company dake japan bayan ainihin kamfanin da muke kaiwa kaya......suna taya kayanmu akan farashin da wancan kamfanin basa bamu......wannan shi yasa nayi wani nazari......abba ya kamata qasarmu ta amfana da wadannan ma'adanai masu tsada da daraja,wanda mu Allah ya mallakawa su.....abba inda a qasarsu wadannan ma'adanai suke,babu wani baqar fata daya isa ya sameshi.....it's hardly ka iya isa wajen......nayi tunanin bude babban company da zai dinga sarrafa wadannan ababen zuwa kayan qyale qyale na mata.....don dama company daya muke da na alhaji rayyan(dangantakar zuciya),shi kuma duwatsu masu daraja suke sarrafawa ba gold ko diamond ba".
Shuru abba yayi yana girgiza kai. Tabbas fu'ad din yazo da tunani me kyau daya kamata ace tuntuni sun yishi
"Na yarda da wannan tunanin naka.....to amma fu'ad qarqashin haka akwai tarin matsaloli da qalubale......"
"Na sani abba......insecurity na qasarmu ma kawai qalubale ne......amma a hakan.....ya zama dole mu raya qasarmu da kowanne qaramin chance da muka samu a rayuwarmu......tsoro da tunanin asara ko faduwa shine abinda zaici gaba da kasheta kowacce rana......bayan tsoron dauko shi akayi aka dasa mana shi a zukatanmu......kuma ake da buri da fatan ganin ci gaba da wanzuwarsa har zuwa rayuwar na bayanmu"
"Best son ever" Abban ya furta yana sakin wani irin murmushi tare da jin qarin alfahari da fu'ad din,gefe guda kuma yana taya ainihin mahaifinsa murnar samun nagartaccen yaro mara tsoro irin muhammad fu'ad din.
Qas yayi da kansa cikin girmama abban
"A tayamu da addu'a abba"
"Kullum cikinta muke"
"Allah yaja kwana,ya qara lafiya me amfani" Ya masa addu'ar da yake jinta har cikin zuciyarsa.
Agogon dake manne a bango ya kalla,sai ya miqe a nutse yana cewa
"Zan qarasa ciki abba na shirya kada na sabawa lokaci"
"Hakan yayi kyau" Abba ya fada fu'ad din yana sake burgeshi saboda yadda ya dauki alqawari da matuqar muhimmanci kaman yadda yake girmama lokaci.
A nutse ya tura qofar dakin da sallama a bakinsa,duk kuwa da yasan ba wanda zai taras a ciki. Dakine da duka duka basufi sati guda a cikinsa ba......amma har ya kama ya kuma rine da sassanyan qamshin nan nasa dake iya bawa zuciya nutsuwa da kwanciyar hankali koda cikin radadi da qunci take.
Towel din hannunsa ya rataye,ya kuma matsa gaba kadan ya ajjiye takalmin motsa jikinsa wanda daga ranar da suka tasamma barin Korea sunansa shara. Baya yawo da kaya,kowacce qasa zaije,koda kwana nawa zaiyi single yake tafiya abinsa,saidai yana sauka a qasar komai da zai buqata na amfani zai sanya a tanadar masa,yana gama amfani dashi kuma a nan zai barshi ya qara gaba.
Matsawa gaba kadan yayi gaban wata mini dispenser da tafi kama da tulun zamani wadda ke zaune saman wani kyakkyawan table kusa da mirror,ya dauki disposable cup ya matsi ruwan dake da madaidaicin yanayi ya fara sha a hankali bayan yayi tsaye gaban madubin idanunshi a kai kamar me karantar yadda yake zuqar ruwan zuwa cikinsa.
Ya gama ya ajiye saman madubin yana fidda siririyar iska yana ci gaba da kallon fuskarsa a madubin. Kyakkyawar sumar kansa data wadatu da tsafta ya taba sannan ya gangaro zuwa madaidaiciyar qasumbarsa data hade da gemunsa wadda ta zamawa fuskarsa wani lafiyayyen ado daya qara fidda zahirin kyawun fuskarsa,ta kuma qara masa wani mahaukacin kwarjini. Gemun da qasumbar daya zama topic of discussion a wajen 'yammatan da suka marmace a kansa. Kusan kowacce tana gayawa kanta namiji babu gashi a fuska ai mace ne,bata taba ganin qasumba da gemu da yakai kyan nasa ba......tsabar macewa a soyayya ne.....ko kuma zallar tsagwaron gaskiya suka fadi?.
Rigar jikinsa ya yaye zuwa sama sannan ya zareta ya ajjiyeta saman gadon,wannan ya bawa Ginannun muscles din jikinsa bayyana muraran. Muradden jikin da zai gaya maka adadin lokutan da aka bata ana bashi kulawa ta fannin lafiya da cin lafiyayyen abinci me gina jiki. Yayi taku daya don dauko bath set nashi zai wuce toilet sai ya fasa,ya dawo da baya ya dauki wata farar samsung dake ajjiye saman mirror din.
Yaga miscal amma sai ya fara maida hankalinsa ga dalilin daukar wayar,ya latsa ya fara lalubar magaji. Umarni ya bashi na abincin da zai hada masa kafin ya fito,saiya maida wayar yana shirin ajeta kira ya shigo wayar.
Cak ya tsaya yana kallon sunan dake tsalle saman wayar. MOM kaman yadda farouq ya dauka da hannunsa yayi masa saving. Kafe sunan yayi da idanuwa,wayar tana kadawa hade da zuciyarsa. Sunan yake tuna ma'anarsa da kyau cikin kwanyarsa.....wadda aka maqalawa sunan ta cancanci wannan sunan kuwa anya?......ta dace data karbi sunan?,nata ne sunan da gaske?.
Kamar bashi da idea akan yadda ake daga waya,haka yaci gaba da kallon wayar har ta qaraci ringing ta katse. Ya sake daga qafarsa zai wucs kiran ya sake shigowa. Kamar dai dazu a yanzunma haka ta gama kadawa ta katse,kira na uku kuma ya sake shigowa immediately,saidai akasin dazu,yanzu sunan daya fito akai ya banbanta dana dazu.
Lovy dovy shine sunan daya bayyana,sai ya saki qaramin murmushi yana dawowa baya kadan. Kafin ya daga sai daya kalli lokaci,tabbas ya tsaya saurarenta ya tabbatar saita kwakwashe masa duka mintunan daya tsara zaiyi a gidan ya fice zuwa Labrilliante amma hakan bai sanya ya fasa dagawa ba,ya sanya wayar a kunnensa.
Da siririyar baby voice dinnan nata tayi masa sallama. A nutse fuskarsa a sake ya amsa
"I will call you back habibty.....nan da one hour haka?"
"Yes habibee.....byeee" Ta fada cikin rashin damuwa da kuma fahimtarsa a duk sanda ya sako mata uzurinsa. Wayar ya mayar ya ajjiye yana murmushi,daidai sanda a daya BANGAREN.........
Ta daga kai ta kalleta sanda take zaune a gabanta
"Waya yake amsawa hajiya" Ta fadi tana sauke wayar daga kunnenta bayan computer ta gaya masa ana amfani da layin ta hanyar amsa wani kiran
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 32
___________________________
“Waya kuma ake amsawa?” Ta tambaya cikin wata irin isa sa ginshiri tana qanqance idanunta,qwayar idanun nata suna kan wadda tayi maganar. Kai ta jinjina mata cikin bata tabbaci
“Eh haka ne”. Juyawa tayi ta zauna sosai tana fesar da iska me zafi daga bakinta. Ta qanqance idanu sosai tare da zubawa guri daya idanu,abinda zai baka tabbacin akwai wani radadi me yawa da take ji daga cikin zuciyartata
“Alamu kenan suna nuna yaga kiran,nice dai…….nice dai da bazai amsa wayata ba,nice dai da bazai saurareni ba sai a sanda yaga dama ko kuma aka bashi umarni?” Ta qarashe maganar ta hanyar yiwa kanta da kanta tambayar. Tambayar da bata haifar mata da komai ba sai qarin qunci da bacin ran da ya sanyata miqewa tsaye.
Hannunta ta dunqule ciki juna,ta fara kai kawo tana naushin tafin hannunta da daya hannun data dunqule waje guda. Ba shakka tayi sake ba dan qarami ba,ba shakka kuma hajiya mariya tana son jefa kanta tsakiyar shingen da ba nata ba. A baya tayi tarin ayyuka game da hakan,amma idan har tace taga nasara tattare da hakan to tayi qarya me yawa ma,zata iya kiran ayyukanta na baya da JIYA I YAU,tana tsaye a waje daya babu sauyi ko qanqani,zata zuba idanu ne abubuwa mafiya daraja da kima a rayuwarta…..kuma mallakinta amma ace suna ci gaba da subuce mata?,suna ci gaba da zama haramiya a gareta?,shin zata yarda da zamowa ‘YAR RAKIYA ko kuma taci gaba da wanzuwa a mazaunin ‘yar kallo?.
“Ba zata sabu ba!” Ta furta a zabure sannan ta juya da sassarfa tana daukan mayafinta dake yashe saman kujera
“Tashi samira muje” ta bawa hadimar tata umarni,wadda ke zaune tun dazu guri daya tana duban kai komo da maganganun da takeyi ita daya
“Ina hajiya?” Ta tambayeta murya a lanqwashe. Tayi imanin tunda har ta buqaci fita irin wannan afujajan ba shakka ba alkhairi a cikinta sam
“Gidan alhaji hamza!” Ta bata amsa a tsawace da salon abun nan da ake cewa haushin kaza huce kan dami. Tsam ta miqe tana gyara daurin zaninta sannan ta wuce da sassarfa zuwa shiyyar dakunansu don dauko hijabi.
Cikin jerin amintattu kuma lafiyayyun dakunan da mansion house din na alhaji hamza kibiya ya mallaka. Zaune take tsakiyar wani lallausan rug dake a gefe daya na dakin wanda aka masa rukuni da lausasan sofas qwaya uku da suka zamewa wajen tamkar wani dan qwarya qwaryar falo ne na cikin bedroom. Wani irin lafiyayyen daki ne da ba zai barka kasan safiya ko dare ba,zafi ko sanyi,damuna ballanta rani ba muddin ka kasance wanzajje a dakin.
Daga saman rug din take zaune saman abun salla da zai baka tabbacin bata jima da kammala sallar walaha ba. Salla ceda bata taba wuceta a rayuwa muddin ba wani qaqqarfan dalili ya gifta ba,tun zamanin quruciyarta har kawo yanzu da girma da shekaru suka hau kanta. Shine kuma ya same mata sila da tsani na dawowa rayuwa hamza a shekarun baya,a sanda ta yanke zato da tsammani daga sake rayuwa dashi da kuma yaranta da suka zame mata sanyin idaniyarta.
Wataqila nutsuwa da kamalar da fuskarta ta wadatu dashi yana da alaqa da wannan din,yawan ibada,yawan bautar Allah,yawan azumin tadawwu’i da babu wanda yayo gadonta a wannan fannin qafa da qafa irin muhammad fu’ad.
Akwai haske sosai saman fuskarta,tana saye da atamfar chiganvy gold mekauri kyau da asalin tsada. Jikinta lullube da mayafi me kauri,yayin da yatsarta ke maqale da qaramin carbi irin na ma tsawa.
Daga gefanta saitin kafadarta shine a kashingide,kana kallonsu zakasan magana sukeyi,magana kuma irin ta da da uwa,hira cikin nutsuwa qauna da kuma kulawa
“Nikam saddiq……sake kiramin wayata mana,jakata tun ranar da akayi asibiti dani ban sake ganin gilmawarta ba,akwai muhimman abubuwa a ciki,harda kudaden Amna data bani ajiya” idanu ya zaro sannan ya miqe yana zama sosai
“What?,anni?,dollars fa?”
“Wallahi sadiq” ta fada a nutse.
“To Allah ya tsananta rabo,don auta ta saka buri akan wannan ajiyar,naji tana lissafin abinda zatayi dasu idan ta dawo” ya fada yana cusa hannunsa a aljihu yana laluben wayarsa. Fuskarta anni ta shafa tana fadin
“Idan har ba’a gansu haka zata haqura ai,tsautsayi da qaddara tana wuyan kowane bawa”.
Shuru sukayi dukkansu suna saurareb sautin din…..din,sautin dake gaya musu lallai kiran ya isa ga wayar anni dake tare da documents dinta da kuma sauran kudade masu kauri cikin jakar.
Kamar cikin mafarkinta ta dinga jin wani sauti mara qarfi yana ratsa kunnuwa zuwa kwanyarta.
Shuru tayi ba tare data motsa ba,daddan ring tone din mara hayaniya yana tasowa can qasa qasa,da alama akwai abinda ya sake rage kaifin sautin.
Sai data fahimci ba cikin bacci bane sannan ta qarasa bude fararen idanunta da suka qara girma saboda bacci. A hankali ta yamutsa fuskar tata sannan ta sanya hannunta ta maida lallausar sumarta me tsaho data rufe rabin fuskarta baya,ta juya daga rub da cikin da tayi zuwa rigingine sannan ta miqe ta zauna sosai tana wuwwurga idanunta zuwa kowanne sashe na dakin don gano ainihin ta inda sautin yake fita.
Ba kowa a dakin,don tuntuni su huda sun gama shiryawa sunyi abincin safe kaman yadda suka saba sun wuce makaranta,don ko idanunta bata iya budewa tace dai kawai su buda jakarta su dauki kudin makaranta su kuma ja mata qofan idan sun fita.
Fes dakin yake kamar kullum kamar kuma ko yaushe,sai ta saka hannunta ta tattare gashinta ta qulleshi tsakiyar kanta idanunta ta tsaiwa kan medium luggage din dake cike da tsarabar da aka kawo mata,wadda ko samun damar budeta batayi ba.
Tayi matuqar gajiya a jiyan,tana fita kusan kowacce rana.....amma bata yin awanni masu yawa kaman haka a wajen. Komai nata yana da lokaci tsari da kuma iyaka. Ta zube fararen qafafunta saman qaramin carfet data sanya musu daga gaban gadajen nasu saboda sanyin tile,ta jawo dankwali me santsi ta daura sannan ta miqe tana isa gaban luggage din.
Sai a sannan ta kuma gasgatawa daga cikin qaramar handbag dinta sautin ke fita,jakar ma da gaba daya ta mance da ita tun ranar data je musu siyayya ta dawo,ko tarkacen ciki bata kwashe ba. Hannu ta zura tana laluben meye yaketa qara din haka cikin jakar,sai kawai ta wuce gaban gadon ta zazzage jakar gaba daya saman gadon.
Kyakkyawar purse baquwa ta gani cikin jerin tarkacen dake cikin jakar wanda ta tabbatar duka nata ne. Onion color me ratsin maroon a jiki. Hannu ta miqa ta jawota,ta dagata a hannunta tana jujjuyata cikin mamakin a ina ta samo ta?,kuma ta waye?,tun yaushe take cikin kayan nata?. Kamar anason sanar mata da amsar duka tambayoyinta ne sai wannan siririn sautin da ya tasheta a bacci ya sake kadawa daga cikin jakar.
Kai tsaye ta zuge jakar,ba wani ba wata ta sani waya ce. Wayace qila da take da alaqa da mamallaki ko mamallakiyar jakar.
Wata siririyar Samsung ta gani,ta sanya hannu don cirota da gaggawa gudun kada kiran yanke,take sabbin dollar din dake maqale a zip na daban na jakar suka biyota suka fada saman cinyarta hade da qananun hotunan passport. Ba wannan bane a gabanta,don haka batabi ta kai ba ta fara duba sunan dake yawo saman screen din wayar
MUSADDIQU NA....shine full name din dake jikin number. Tadan tsaya tana sake duba sunan da kyau tare da bitar karantashi,sai kuma tadan tabe baki kadan sannan ta daga kiran ta Kara wayar a kunnenta
"Alhamdulillah.....an daga anni" Musaddiq ya fada yana sanya wayar a kunnensa.
Shuru tayi tana sauraren motsin dake fita daga daya bangaren,kafin daga bisani sallamarsa ta maye gurbin shurun. Muryarsa a nutse dake dauke da kamala yayi cikakkiyar sallama data sanyata motsa bakinta