Showing 204001 words to 207000 words out of 209775 words

Chapter 69 - Duniyata 1 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

11 Nov 2025

502

ba

"Surukinka ne yake kira" Yayi maganar qasa qasa ta sigar zolaya da muryar da iya su kadai zasu iya jin maganar. Kadan yadan daga fararen idanunsa ya jefa masa harara,sannan ya maidasu kan wayar yana ci gaba da abinda yakeyi din ba tare daya ce dashi komai ba.

Idanunta suna lumshe,amma kuma yadda kawun yake wayar cikin matuqar girmamawa kai kace sune sama dashi sai bacin rai ya sake zuwa mata wuya......ba wannan bane a gabanta,abu mafi muhimmanci shine ya sanya wannan qattin su janye daga qofar gidansu,don haka ta saka kunne sosai tana sauraron muryar farouq dake fita tar tar ta speaker din wayar kawu,wanda ya sakata ne a speaker don ta samu tabbaci kan duka hukuncin da ya yanke a kanta.

Haka kawai cikin ranta takejin bashi bane yake magana,daga yadda farouq din ke magana adan sake ya sake baya yaqinin haka.

"Yallabai din yana kusa?,akwai saqo da aka bani zan isar masa....."

"Yana jinka uncle......bari na saka a speaker......though dai zaiyi kusan two weeks idan ya wuce.....zai dawo one week before the wedding". Kansa fuad ya sake dagawa ya watsawa farouq wata harara,don me zai zauna yana bayani musu akan abinda shi kadai ta shafa

"To ma sha Allah......ma sha Allah.......dama sabrina ce ke neman izinin rage masu tsaronta......sannan kuma a yau din tana buqatar ya bata izinin fita.....".

"Ban yarda taje ko ina ba....koda kuwa qofan gida ne". Wannan dakakkiyar muryar tasa dake cike da ginshira ta ratsa wayar ta kuma samu kyakkyawan damar isar da saqo ga kunnuwanta.

Kaman ya yarfa mata ruwan zafi haka taji. Tsam ta samu kanta da miqewa,ta zauna sosai tana zubawa kawu rufai idanu wanda zuwa sannan har ya fara haramar rufe maganar hanyar fadin

"To in sha Allah.....in sha Allahu ba damuwa......". Bai ankara ba,baisan kuma ta yaya ba sai tsintar wayar yayi a hannunta,kai tsaye ta zare wayar daga hannun kawun ta maidata kunnenta cikin wata fusatacciyar murya

"Ina fatan kana kan waya!" Sautin da yaja hankalin farouq da wayar ke hannunsa,da kuma shi kansa fuad daya soma takawa zai wuce ciki don ya isar da saqon da yakeson isarwa din.

Taku uku farouq ya cimmasa,sai ya zura masa wayar kawai a aljihun gaban rigarsa yadan matsa gefe yana karantar yanayin fuad din

"Ban nema izini ba......hakanan bance a nema min izinin komai daga wajenka ba......umarni ne kawai kan ka janye wadancan halittun da babu sanin kimar dan adam ko daya a tattare dasu......kafin su tafi kuma ka tabbatar sun karbi komai naka daka bada da sunan dukiyar aure"

"Au haba?" Ya fada da wani irin calmness zuciyarsa da kwanyarsa na qidddige wasi cikin halayenta.

"Ashe bayan qwamushe girman kai harda rashin kunya kika hado?.......abun yayimin daidai......i salute you ma'am........zaki ci gaba da zama cikin gida har na tsahon sati biy cur ba tare da kin taka koda qofar gida ba.......wannan shine punishment mafi sauqi a gareki".

"But....who are you?" Ta tambayeshi a zafafe tana jin zallar rainin wayo cikin maganganunsa.

"Relax mana.......so soon haka?,saurin me kikeyi nason jin waye muhammad fuad?,bayan sanin nasa suine babban barazana a rayuwarki?". Yakai qarshe yana ajiye numfashi,bai kuma barta ta sake cewa komai ba yace

"Kina zaton zan barki ba masu tsaremin ke.....don nasan kadan daga aikinki ki fecemin da dukiyar aure na.......wannan wasan zaiyi dadi sosai.......but......kisan dawa zaki bugashi......idiot!". Qit ya katse wayar,ya kuma zarota a gaggauce daga aljihun nasa. Abu daya zai sanya ya buga wayar a qasa,ta fito daga wajen mutum me matuqar girma da mutunci a rayuwarsa.

"Don't ever never try it.......kasan bana shiri ko jituwa da mara kunya......wayarka taci saa data kasance taka ce,da daga yau ba zata sake amsa sunan waya ba" Sai ya sake masa wayar shi kuma ya cafe,yayin da ya qara gaba yana wucewa cikin kaman yadda yayi niyya.

Yadda ya qara zafin nama cikin tafiyarsa kadai zai gaya maka zuciyar 'yan maza ta motsu sosai,ya bishi da kallo sosai. Yadda yayi doguwar magana haka yau cikin fada,ya tabbatar koda ya bishin bazaice komai dashi ba.

Kasa bawa kawu wayar tayi har sai daya sake kwatsa mata tsawa

"Bani wayata nace!" Saita miqa masa wayar wanda miqawar ya hadu da silalowar siraran hawaye daga fuskarta. Da gudu gudu ta qarasa shigewa dakin,tana jiyo sababin kawun da yaketa yarfa ruwan masifa kamar xai ari baki

"Kinsan wayeshi?,kin kuma san matsayinsa da har kika gaggaya masa magana haka?,kinsan idan ran mutumin nan ya baci ya kama duka danginki ya kulle basu da saidan me fiddasu?".

Maganganun kawu ba sune suke dawo mata akai ba,yadda ya dinga yaba mata magana kalma bayan kalma kuma murya a kwance.....hankalinsa ma a nutse shine yafi mata matsanancin ciwo.

Wunin ranar haka ta dinga juyi cike da baqinciki da takaici,tanaso tayi kuka amma tana hana kanta,tana ganin tafi qarfin tayi masa kuka(ni kuwa nace anya sabreen?,ba girin girn ba tayi mai).

Tana daga kwancen tana irgen yadda awanni suka shuda suka kuma zama silar tafiyar ayshatu india ba tare data yiwa yarinyar kallon qarshe kamar yadda taso ba. Da wannan juyin ta qarar da wuninta kaf da tunaninta na yadda zata samu zullewa tsakanin qattan garadan nan ta fice a gidan,ta kuma nisanci kowa ta yadda zai kasance kafin zuwan sati biyun da ya ambata saidai ya dawo ya tarar ta zama tarihi a garesu gaba daya.

********"kai jama'a,qalu innalillahi wa inna ilaihi raji'un,mudai mun hadu da masifa,wannan bala'in har ina?,kai da gidan mijinka amma duk shiga ko fita wani qato yana tsaye,shi xai bude maka qofa shi xai rufe maka?". Muryar bibo kenan dake sakin buhun data dawo dashi daga kasuwar saitin dakinsu sabreen din,don tana so dukka maganganun da zata fada ya samu wajen zama na din din din a kunnenta.

A kwanakin sam bata da aiki sai fadin baqaqen maganganu da kuma tarin habaice habaice,tana neman duk wata hanya ne da sabreen zata kulata ta lanqaya mata sharrin da har masu gadin nata zasuji su kuma isar dashi ga uban gidan nasu,wataqila hakan ya zama silar fasa auren. Sosai auren ya tsaye mata a rai,ta laluba ta kuma bincika inda zata sake ganin matan nan don ta sake jaddada musu 'YAR BARIKI fa dansu zai aura.....amma bata samu ma wanda ya gansu ba ranar da sukazo unguwar ballantana ya tayata neman su. Ita din a yanzu tsoron taba sabreen din takeyi,duba da iya mutanen da suke gadin gidansu ma gaba daya ba ita sabreen din ba,wannan dalilinne kawai yake taka nata birki akan abubuwan data qulla aiwatar mata. Abu daya take jira shine ranar da zaa ce zaa kawo lefe,tana sanya ran ranar ta zame mata ranar nasara tunda ba wani daya danganci sabreen,a ranar sai tayi mata tonon silili cikin jamaar kawo lefen,ta tabbatar za'a tafi da ita a baki,kuma dole saqo zaikai kunnen wadanda suke da iko da hana abun ko aiwatar dashi.....randa zasuzo karbar kayan aurensu kuwa tasan dukka yadda zatayi.....koda tsiya koda bala'i ta juya abun ya koma kan hadiyyarta.

105

A wannan lokacin sabreen din na kwance saman doguwar kujerar falon nasu,a kwance take rigingine tana kallon ceiling,saidai kuma manyan idanunta dukkabiyun a rufe suke kai kace bacci takeyi.

Banda yar qaramar fankar dake bada iska me dadi a falon ba zakace akwai wutar nepa ko sola cikin dakin ba. Ta kashe tv ta kashe dukkan wani qwai da zai iya bada haske.

Kwanakinta shida kenan tana irin wannan kwanciyar,musamman lokaci irin wannan da yara suka wuce makaranta. Zuwa yanzu kwanyarta da tunaninta dukka sun gajiya kan yadda zata sanya wadannan qattan subar qofar gidan,abinda zai bata damar sakewa kenan ta qarasa aiwatar da plan dinta. Ta lura daidai da second basa gusawa daga qofar gidan bare ta samu wata qaramar dama ma da zata gifta. Dukkan wani tunani nata ya soma gajiyawa,hakanan ta fara gajiya,bataga wani alamu na samun cikar nasararta na nesantasu da wannan gidan ba.

Kulli yaumin Allah shine da kullum sai kawu ya shigo dakin ya sameta a haka,qarfi da yaji ya zama me wa'azi yayin da ita kuma ta zama kurmar dole. Ta sake qaranta magana da wawalwalarta,ta sake zama miskila sosai,sai yayi maganarsa ya qare ya tashi kan wa'azin biyayyar na gaba da muhimmancim aure bata ma bude idonta ba bare tace dashi ta tafasa a sauke ba.

Wannan abun da take masa yana sake razanashi,yasanta cikin miskilai ma nata halin na daban ne,wannan ya sanya ya dauki matakin da bata taba zato ko kawo cewa zai dauka din ba......don a daidai sannan kunnuwanta suka jiyo mata sallama da wata murya da take kyautata zaton ta santa......ta mata kyakkyawan sani ba in general.

Daga sallamarta ta farko har zuwa ta biyu dukansu suna ji,amma tsananin mamaki ya saka suka kasa amsawa har sai data sake bayyana sosai a gabansu.

Bahijja........matar da a yanzu haka suka shafe shekara goma sha daya basu sanyata a idanaunsu ba.....haihuwar haneefa......haneefa daa yanzu girma da shekaru suke bayyana kansu a tattare da ita.

Kasa kowanne motsi tayi,saboda tana jin komai ne a mazaunin mafarki,sai kawai idanuwanta data bude ta zubawa qofa idanu tana sauraren isowarta don taga da gasken itace?.

Daga cikin al'ummar gidan da suka shaidata suma kallon mamaki suke binta dashi. Fuskar da ta bace musu tun wani zamani baya. Da idanu take qarewa gidan kallo kawai tare da al'ummar gidan da ba wanda ya iya fusgar sunanta sai daada.

"Ikon Allah.......kina nan bahijja?". Murmushi ta saki

"Ina nan daada...." Ta amsa mata dashi tana ji a jikinta lallai akwai tarin qalubale masu yawa.

Kasa daidaita nutsuwarta tayi lokacin da take sallama zuwa cikin falon nasu. Ta sauko gaba daya daga saman kujerar cikin wani irin hanzari tana dosarta. A murya tana jin tamkar ummenta ce ta dawo,haka nan wani sashe na kamanni,duk jikinta rawa yakeyi,hawaye kuma suka balle mata,irin hawayen nan da suke zama tilas zubarsu a idanu. Cak komai nata ya tsaya sanda ta fada jikinta tana sakin kuka lokacin da muryar uncle abdulk'adir. Muryar data sake sanya kowanne sashe na jikinta rawa,ta zare jikinta daga na bahijja ta daga kanta kaman me ciwon wuya tana ware fararen idanunta da suka sauya kala akan uncle abdulk'adir din dake takowa zuwa cikin dakin.

Yana nan dai kaman yadda suka sanshi,giant dashi me yawan daurewar fuska. A wancan lokutan basu da shekaru sosai,wannan ya sanya basu fiya fahimtar rashin sakin fuskar nasa ba saboda yana da fara'a ga yara. Sai ta riqe bahijja sosai wadda suke kira da didi,itama ta kama nata hannun tana shirin zaunar da ita.

◦•●◉✿ "Oh.....Allah na gode maka" Abinda kawai ya iya fada kenan. Tako ina yana jin gumi yana tsatsafo masa,tsakanin me jadda da sabreen baima san wanda yafi wani sakashi a masifa ba.

Hannun kujera ya samu ya zauna yana share fuskarsa da hannun babbar rigarsa,yana jin gaba daya duniya ta juya masa baya cikin qanqanin lokaci

✿◉●•◦𝘽𝙖𝙮𝙖𝙣 𝙖𝙬𝙖 𝙪𝙠𝙪 ✿◉●•◦

Dukkanin wani kuka a yanzu a kuma wannan lokacin ta yishi,kukan faduwa da rashin nasararta da kuma rashin hango galaba qarara daga kaucewa wannan birkitaccen auren da yafi kama da auren bauta.

"Ba abinda zaki mana.....ba abinda zakiwa kanki ki kyautatawa kanki da rayuwarki sai aure......a wannan shekarun zaman me kike tunani zakiyi?,har kice bakison aure?,idan bakison aure me kikeso sabreen?.....kisa a ranki idan har bakiga afkuwar auren nan ba to daya ne a cikin ku biyu ya mutu.....ko ke ko shi".

"Ya Allah......kasa ya mutu.......ya Allah ka sanya wannan tafiyar da yayi ya yita kenan" Ta samu kanta da furtawa a zahiri. Adduar data baiwa kowa mamaki a wajen banda kawu rufai dake zaune daga gefe. Gigitacciyar tsawar da uncle abdulk'adir ya sake mata ya sanyata runtse idonta kawai ba tare data motsa ba tana sauraren bugun zuciyarta,ko qas zuciyarta bata rusuna ko ta canza ba game da adduar data masa,saita dinga ninks wata can qasan zuciyarta tana maimaitawa akan Allah ya kawo duk wata sila ko hanyar da zaiyi nisa da rayuwarta ya barta ta huta kamar kowacce 'yantacciyar d'iya.

"Wai ina amanar da nake yawan tambayarka akai rufai game da yaran nan?,ya akayi ka bari sabreen ta zama haka?". Wani lafiyayyen gumi ne ya yanko masa,baisan iya adadin qaryar sunan nan lafiya qalau da ya yiwa abdulk'adir ba......baisan iya adadin saqon da ya aikowa yaran ya handame ba ba tare da yabar kowa yasan ma anyi aiken ba.

Idanunta kawai taja ta rufe lokacin da didi keson jin ko tana da wata matsala ko kuma damuwa ne game da auren bayan kasancewar ita ce batason mijin?.

"To ta cewa didi me?,ta gayawa didi mamarsa tana da manufar aurawa danta shi?,while shi kansa batasan me yasa ya nemi aurenta ba da kanshi?. Tana jin bata da sauran option a yanxu illa ta tsaya ta zuba idanu kawai a buga wannan wasan da ita.......waye zai zama WINNER?.....WAYE KUMA LOSER a tsakanin mutum ukun?.

𝐒𝐚𝐛𝐫𝐞𝐞𝐧

𝐌𝐮𝐡𝐚𝐦𝐦𝐚𝐝 𝐟𝐮𝐚𝐝

𝐌𝐚𝐚𝐦𝐚𝐡 𝙜𝙖 𝙠𝙪𝙢𝙖

𝐇𝐚𝐣𝐣𝐚 𝐡𝐚𝐫𝐢𝐫𝐚

Daga gefe da nata shirin da KO MEYE SHI?.

Abu daya ne zata ce ya sanya wani dan siririn haske da sanyi cikin mummunan yanayin da take jin kanta a ciki.....shine samun wani haske a dakin da ya zama tamkar makwafin uwa a garesu. Yadda haneefa huda da nadra suka sanya didi a gaba tamkar ummensu ce ta dawo. Ita kuma tana tsakiyarsu,hira sukeyi tamkar xasu kwana a zaune ita dasu,su din kamar zasu koma cikinta,yayin data rungumesu da kyau itama kasancewar Allah bai bata haihuwa ba.....dangin mahaifinsu ko a wancan lokacin na rasuwar yayarta musamman kawu rufai su sukayi tsayin daka suka hanata koda haneefa da take qarama a sannan,sai haqura tayi badon zuciya bata so ba.

Kwana da wunin da sukayi da sabreen ba wani abu daya canza daga yanayinta. Ta riga tayi giving up tun bayan da kawu abdulk'adir ya wuce yabar didi bahijja da zummar zata zauna dasu a nan har sai lokacin biki yazo za'a share biki da ita sannan ta koma.....komai ya qare kenan!,abinda ya rage mata daya ne shine......ta maida kanta kan tsara yadda zata maidawa kowa aniyarsa......amma har yanxun tana jin abun kamar ba gaske bane.....tana jin kamar a mafarki ne.....yaya akayi wadannan mutanen suka mamayeta har haka?,suke shirin juya rayuwarta dare daya daga wani bigiren zuwa wani......bigiren da bata taba tunanin zata tsinci kanta a ciki ba har abada.

✿◉●•◦𝙎𝙖𝙣𝙣𝙪 𝙨𝙖𝙣𝙣𝙪 𝙗𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙣𝙖 𝙯𝙪𝙬𝙖......✿◉●•◦

Isowar akwatinan auren muhammad jadda zuwa gidansu sabreen ahmad kadai ya sake gigitar da tarin jama'a na cikin gida dana waje. Wasu irin qasaitattu kuma lafiyayyun luxury akwati kala daban daban da suka tasamma jimillar akwatuna talatin da shida wato dozen hudu dalla dalla inji munafukai da 'yan gaza gani akwatina d'ai d'ai har arba'in da takwas kenan.

Iya kwati set qwaya daya tal kawai idan aka fiddata aka saidata banda kayan cikinta sun isa musulmin jarin cikakke ga mutum a qalla goma sha kyan kyan. Wasu sabbin designers akwatuna da sabreen din ta zama mutum na farko cikin jerin ahalin iyalan masu arziqi data mallakeshi.

Fadin irin tarin dukiya da suturun alfarma dake ciki ma bata baki ne. Lefe ne da aka zubawa kayan ado na gold da diamond a ciki kamar yadda yake shine ainihin sana'ar muhammad jadda,wanda duk wanda ya gani sai ya tabbatar lallai sun cika kayan aure daga wajen mamallakin kamfanin diamond da gold.

"Anya bayan wannan sana'ar kuwa baya yankan kai?,suna kyautar mota kaman suna kyautar sweet.....bayan motar da aka hado mata da ita a kayan aure yanzun guda biyu suka sake sakawa akai kayan lefen fa,wai kyautar uban ango da uwar ango.....nabeela wannan wacce irin baqar rana ce?" Hadiyya da labarin lefen ya hanata zaune ya kuma hanata tsaye cikin dakin hostel din nasu ta fada da idanunta da sukayi jajur don kuka.

Wadda ke zaune a gefensu ta saki murmushi

"Kina wasa da bariki.....ai indai kin cika macen bariki me wayo to tabbas kafin ta bare dake kike kama kanki.....ki samu wani alaj din kiyi wuf dashi ki shige

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login