Showing 168001 words to 171000 words out of 209775 words
aiki ne......muddin a yau bata samu yadda takeso ba batajin gobe warhaka zata kasance a bigiren da take tsaye akai a yanzu......dole ta tafi plan B da zafi zafinta kuwa.
"Zuwaira.......maza leqa ki gaya masa ya qaraso ciki amma shi kadai......bana ko qaunar kallon fuskar yarinyar ballantana gangar jikinta ya shigomin cikin gida".
Sosai zuwaira taji nauyin aiken saboda ba qaramin kwarjini fu'ad din yakeyi mata ba,amma ba zata iya musa umarnin uwar dakin nata ba.
Da bismillah a bakinsa yake shirin sanya qafarsa a step na farko da zai sadaka da qofar falon zuwaira ta fito. Kai ya daga ya kalleta a nutse ganin kamar an jehota,sai tayi qas da kanta cikin tsananin qanqan da kai ba tare data iya hada ido dashi ba tace
"Maamah tace ka qaraso ciki.....amma so samu tanason ganawa da kaine kai kadai". A nutse ya waiwaya ya dubi amna,suka hada ido sai ya zare idonsa daga kanta,ya miqa mata hularsa yana cewa
"Riqemin yanzu zan fito" Bata musa ba ta sanya hannu ta karba,ta koma daga gefe ta zauna kawai jikinta a sanyaye,don inda ya barta gida zata koma,sai yanzu ta tuna gidan waye ta biyoshi?. Matar da totally ita tsoro take bata tun ranar data shigo gidansu ta kuma ga abinda tayi musu.
Bai fasa duka addu'anshi ba kafin ya sanya qafarsa cikin matuqar kula da takatsantsan. Tana zaune saman sofa qafarta daya saman daya tana kadata a hankali. Ciki ciki ta amsa masa sallamar ba tare data masa wani dogon kallo ba. Ya qarasa ya tsugunna cikin girmamawa yana fadin
"Barka da safiya.....kin tashi lpy?"
"Koma ka zauna muhammadu" Ta furta kai tsaye wanda baice komai ba ya miqe din ya koma ya zauna sosai.
"Wacece mahaifiyarka ne muhammadu?" Tayi masa tambayar da wani sauti dake cike da izza da kuma bacin rai. Kanshi ya daga ya kalleta suka hada idanu,ta tsareshi da ido sosai da kuma tarin abubuwa daya gansu kwance cikin idanun nata.
"Kece" Ya amsa mata a gajarce.
"To amma banga alama ba.......banga alamar hakan ba......yanzu ace samuwar farincikina daga gareku sai ya gagara?,yanzu ace samun kulawa da danuwarku a kaina sai ya zamemin aiki?" Ta jefa masa tambayar da ba abinda tayi tasiri a kai sai tuna masa da baya da tayi. Ta tuna masa sanda suke da tsananin buqatarta a daidai wannan lokacin ta tattara hankalinta zuwa ga wani waje daban. Ya tuna tun shekarunsa basu kai ya koyi wasu abubuwa masu yawa harda ma wadanda sukafi qarfinsa saboda rashin samun kulawarta. Ya tuna yadda yake kasa yiwa mahaifinsa dake jiyya abubuwa da yawa saboda bashi da qarfin da zai iya dagashi zuwa toilet da sauransu,saidai su zauna shi kuka shima kuka. Sau tari maganganunta da lafuzzanta sunfi masa kama da na mutanen da idonsu ya rufe......mutanen da buqatar gabansu kawai suka sanya a gaba,mutanen da ba ruwansu da damuwar kowa sai tasu......mutanen da ba wani burbushi na nadama a tare dasu ballantana dana sani.
"Kiya haquri" Ya jefeta da kalmar da yakejin iya ita kadai kawai zai iya furta mata don bashi da wani sauran abun fada.
Sake zube masa idanunta tayi tana sake jaddada zallar miskilanci da taurin fu'ad din. Ba wani alamun sarewa ko saukowa a tare dashi?,tamkar ma an sanya fetur da ashana an qone dukkan wata qauna ta mahaifiya dake zuciyar kowanne d'a. Anya ba zancan hajja harira bane akan hanya da take hasashen hadda farraqu hajiya ameena ta sanya akayi musu?.
"Zanje abuja yau din.....nace bari na sanar miki,sai mun dawo" Ya furta bawai don yana sanya ran zata masa addu'a ko wani abu daya dace ba,don yana kaiwa qarshe ya miqe yana gyara hannun rigarsa.
Dan runtse idonta kadan tayi tana hasashen yau dinma kenan babu nasara?. Da qyar ta iya controlling kanta da fadin
"Sai ka dawo" Duk kuwa da tarin tambayoyin da takeson masa akan me zaije yi abuja?,yaushe zai dawo?.
Binsa tayi da kallo har ya fice daga falon,taja wani mataccen numfashi idanunta na qanqancewa saboda bacin rai.....dole suje plan B bata kuma fatan su isa plan C don zaifi kowanne mataki wahala a gareta dasu gaba daya
"Yaro baisan wuta ba sai ya taka.......yaro man kaza......idan kasan wata bakasan wata ba" Dukka ta furta a sarari tana daukan wayarta gami da kiran hajja harira.
Cikin wani iri ya dawo cikin gidan. Saidai yayi qoqarin daidaita yanayinsa lokacin daya isa parlor din anni.
Can babban dining area din dake parlor din ya samesu saman dining. Anni abba da farouq suna breakfast,yaja kujera kusa da anni ya zauna yana gaida abba da basu samu haduwa ba sai sannan.
"Abba.....nace ya kamata ace tare muka fara hawa jet dinnan". Dan murmushi ya saki yana ciro tissue cikin tissue box.
"Nikam wannan jumaar a kibiya zanyita me babban suna......indai muna da rai ai za'a yita hawa ko don zuwa ibada qasa me tsarki.......yanzu kam ku wuce sabgar gabanku.....saidai kads ku manta da addu'a,Allah yasa a shiga a sa'a,ya kauda dukka abunqi"
"Allah yasa a fara hawa cikin sa'a,ubangiji yasa rai aka yiwa" Anni itama ta furta tana murmushi. Har qasan ranta tana jin dadi gami da jin alfaharin kasancewarta uwar goyo a gareshi. Koda muhammad bai kasance me dukiya da arziqi kaman haka ba.....shi din abun alfahari ne ga dukka uwa me hankali......yana da wasu nagartattu kuma kebantattun halaye na daban da ba kowanne dan adam yake samun baiwar mallakarsu ba.
Da dukka zuciya da idanu ta takawa hasken idaniyar tata har zuwa sashen da kowannensu zai hau mota tana rakasu da addu'o'i na neman kariyar ubangiji da kuma tsarinsa. Abban yau sunyi kibiya shi da musaddiq,wanda dama kusan kowanne qarshen wata ko sati idan ya samu chance acan yake sallar juma'arshi,hakanan yakan tafi musu da tarin alkhairai daga arziqin da Allah ya wadatashi dashi bayan wasu daga cikin 'yan uwan da suke zaune a gidan. Wannan din wata dabi'a tasa ce dake qara masa farinjini da soyayya wajen al'ummar garin,domin kuwa alkhairinsa ba wai iya ga 'yan uwansa kadai ya tsaya ba......ya kewaye kowa da kowa.
A saman idanunta dukka motocinsu suka tashi,sai gidan ya rage daga ma'aikata sai ita sai musaddiq.......sai mutanen dake can boys quarter da ba kasafai suke iya jiyo motsin abinda ke faruwa cikin ainihin gidan ba ko kuma su aji nasu.
Idanunsa lumshe cikin jirgin,sanda yake lulawa dasu sararin subhana daga abujar birnin tarayya zuwa kanon dabo. Abujan da duka duka awa biyar sukayi cikinta suka fito. Acan sukayi sallar jumaa cikin centra mosque abuja,daga nan suka wuce unguwarsu fanna.
Rashin sabo da wannan sabgar ya sanya mintuna talatin kawai yayi gidan ya cewa farouq zan dan kama masauki na wucin gadi da yafi kusa da airport.......zai tura masa location din sai ya sameshi a can su wuce.
Shigarsa masaukin yayi arba da abinda ya sake tsuke tunaninsa ya kuma sake dora masa mamaki me azabar nauyi......ya shiga daidai sanda mashkur ne gangarowa daga sama riqe da wayarsa a mugun gigice yana cigiyar hotonta daya buda cikin wayarsa. Hoton da yakebin duk wanda ya gani da tambayar
"Don Allah kaga wannan?,yanzun nan ta sauko daga dakina fa.......ta yasheni ta kwashemin komai daga accounts dina guda biyun". Da irin wannan bayanan ya tareshi sanda yake yunqurin kiran elevator ya haura dashi zuwa sama bayan yabar guards dinsa guda cikin reception din.
Duba daya tak ya yiwa hoton ya dauke idanunsa a hankali ya maida fuskar mashkur da tayi wani irin hautsinewa.....da alana ta zare masa kudi masu yawan da tsaf zai iya taba rayuwarshi. Wacce irin hatsabibiyar yarinya ce wannan?,fu'ad ya yiwa Kansa da kansa tambaya sanda elevator din ya qaraso ya bude ya soma shiga. Har a sannan yana jin muryar mashkur dake bulayin neman wanda ya ganta.
Lumshe idanunsa yayi yana jin wani mummunan bacin rai yana saukar masa. Yana buqatar qarin information a kanta abinda ya raya kenan a ransa,ya fiddo wayarsa yana neman Jordan,sukayi maganganun da zasuyi,dab da zai ajiye wayar kuma kiran abdus_samad ya shigo masa.
Dukkan wasu bayanai ya karanto masa akan rufai ahmad mu'azzam.
"Caca" Shine alaqar data hadasu da mikail?,ta yaya zai zama mutumin banza yana zaune kudinsa ya tafi ta qazantacciyar hanya irin caca?.
"Thanks for your effort" Ya amsa masa yana gintse kiran. Still yana shiga dakin daya kama din kiran saddiq ya shigo masa
"Hamma......mikail keta neman haduwa dakai......" Idonsa yadan lumshe kadan kana ya bude kaman yadda ya saba a duk sanda ranshi ya baci yake kuma qoqarin hadiyewa
"Ya samawa kansa mafita.....koda bai kawo kanshi ba tabbas zan sanya a kawomin shi.......bani da time na ganinsa yanzu......sai zuwa Monday......ka tuntubi Easter kan investigation da na saka suyi cikin company"
"Itama tayi dropping min massage.....tace in sha Allah zuwa Monday din komai zai kammala"
"Alright" Ya amsa a taqaice kanshi yana sake shiga rudani.
Wannan din shine abinda ya zurfafa tunaninsa cikin jirgin,har sai da farouq ya magantu
"Wani abu ya sake faruwa ne?" Idanunshin da suka sauya launi ya bude a hankali sannan ya girgiza kai
"Nothing.....kawai dai kaman akwai abubuwan da nake ganin ba haka ya kamata su tafi ba.....but everything will be fine". Kai farouq ya kada masa yana dubansa da kyau
"Whenever you need assistance........kada ka manta farouq na side dinka.....am ready to be a good partner". Dan qaramin murmushi ya sakar masa yana gyada kai
"Na sani tuntuni".
Tun kafin sabreen tayi nisa da gida ta zura hijabinta zuwa gurin daya gaya mata ta duba zaya ajjiye mata sabuwar waya torch. Yadda ya kwatanta matan haka ta sameta a wajen,ta dauketa cike da murnar zataji muryar da tayi kewa qwarai ta wuce zuwa gida.
Murmushi ya saki bayan informers dinsa dake wajen ba dare ba rana sun shaida masa abinda ya faru
"Yadda zaki bare sabuwar wayar nan yarinya haka zan bareki nan da kwanaki uku kacal masu zuwa" Yayi maganar cikin shauqi da wassafa ta yadda a ranar zaici karensa babu babbaka,ya dauki tiyo dake maqale da bututun tukunyar shisha ya zuqi hayaqin har cikinsa ya fesar,sannan ya kalli matashin dake gefansa.
"Aikinka na yau tunda ta dauki wayar zai fara da tura mata zazzafan saqo da zai nuna asalin kewa da shiga rudani da rashin jin muryarta"
"An gama oga" Ya fada yana bude wayar ya fara abinda aka umarceshi,shine kuma kwangilar daya dauko takanas zai yiwa naseer din.
Jikinta har rawa yake sanda ta kunna wayar saqon ya shigo. Tana gama karantawa taji idanunta sun cika da qwalla,tausayinsa ya cikata.
"Allah sarki bassam.....bazan sake yarda adda sabreen tayi silar yin nesa dani ba" Tayi maganar yana yunqurin kiransa saiga nasa kiran ya shigo.
A yadda ya marabceta a yau din sai da zuciyarta tayi narkewa da qwalla ta fita.
"Tun daga ranar bani da lafiya huda.....fargabata na mutu ba tare dana cika muradan zuciyarmu ba....baqincikina kuma sai na jima a kushewata qilan kafin labarin mutuwata ya riskeki....."
"Allah ya kiyaye.....in sha Allah ba zaka mutu ba" Ta fada muryarta tana rawa tana tuna yadda ta rasa abbanta da umminta,yanzu kuma sai ace shi?.
"Ganinki ne kawai zai sanya na warke huda.....ki taimkeni muddin kinaso na farfado naci gaba da rayuwa kizo na ganki"
"Bansan gidanku ba.....bansan inda zan ganka ba"
"Indai zakizo din huda zan tura miki da adress....ki taimakeni kizo......amma karki takura kanki daga nan har zuwa litinin,har sai kin gamsu da kanki na cancanci kizo din na ganki.....".
Ko kusa ko alama bata ji saukar damuwa saman zuciyarta akan mashur ba,wanda ta tabbatar ta masa gagarumar barnar da zaiyi wahala ya maida gurbinta.
Wani tabbataccen labari data samu a daren jiya akan mashkur shi daya ya qara mata qwarin gwiwa da jin cewa ya cancanci ta rabashi da komai da yake sanya shi jin xai iya shiga ko bata rayuwar dukka diya macen da yaso a sanda yaso.
Da confidence dinta take takowa zuwa cikin gidan nasu. Kamar ko yaushe bata damu d kallon me kallo ba......bata damu da hasashen me hasashe ba......hakanan bata damu da zunden me zunde ba,ta keta a hankali har ta isa qofar dakin nasu da tayi tsammanin samunshi a bude saboda lokacin lokaci ne da tasan suna makaranta a irinsa.
Da mamaki hadi da wata cakudaddiyar fargaba ta murxa qofar ta tura ta bude tana shigewa,saita samu kanta da takawa a hankali har zuwa qarshen falon.
Ba kowa,kuma wajen yana tsaftace kaman kullum,don haka ta juya tana sanya kanta cikin dakin tana mamakin waye yake magana haka kaman masu gulma?.
"Nayi maka alqawarin xuwa ka ganni muddin ba'a wata qasa kake ba.....zanzo har inda kake don ka tabbatar da ingancin son da nake maka!". Qididdigaggun jimlolin da suka zamewa sabreen tamkar saukar aradu a tsakiyar kanta.
Wuta ce gaba daya taji ta dauke mata sanda take iya hasken waya a kunne huda.
"Anya huda ce?,meye hakan yake shirin faruwa?,d waye take magana haka?.
"Waya" Taji an rada mata cikin kunnuwanta,abinda ya sanyata xabura ta kuma sanya hannu ta yaye blanket din da hudan ke ciki,take ta bayyana kwance maqale da waya tana ta doka murmushin samun abinda zuciya takeso.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 87
Bayyanar haske cikin duhun blanket din ya sanya huda zabura,haduwar idanunta kuma dana sabreen ya sakata miqewa cikin matuqar kaduwa da zabura har wayar na neman subucewa,saidai kuma kafin yakai qasa sabreen din ta sanya hannu da zummar tarota,abinda ya bawa huda qaimi itama takai nata hannun don bawa wayar kariya.
Sabreen din ta rigata samun nasara,batayi wata wata ba ta sanya wayar a kunnenta,lokacin da Naseer keta faman maimaita kalmar
"Hello......hello baby?" Wani abu taji ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin qafafunta. Wannan muryar ba baquwa bace a wajenta da zata iya bacewa daga kwanyarta.......ba muryar naseer ba......maza da dama da suka taba shiga qaddarar rayuwarta,suka kuma ratsa ta DUNIYARTA bata wasa da komai daya shafesu bare ta bari ya bace mata
"Nnn......" Tayi niyyar furtawa,sai kuwa ta dunqule maganar ta hadiye ta maidata cikinta,ta sauke wayar tana katse kiran sannan ta maida dubanta ga huda dake tsaye tana fuskantarta idanunta fes kan fuskar sabreen.
"Ki bani wayata adda" Ta tattaro dukka qwarin gwiwar daya rage mata ta furta tana miqawa sabreen hannu. Saidai maimakon ta bata wayar yadda ta buqata sai ta maye gurbin hakan da ajiye mata lafiyayyen mari saman fuskarta,sanda take yunqurin maido hayyacinta cike da matsanancin mamaki ta sake sauke mata wani marin a daya kuncin nata. Gigicewa tayi duka ta sanya hannayenta ta dafe kuncin nata gaba daya,wannan baiwa sabreen din ba cikin matsanancin fushi ta turata ta koma saman gadon tayi zaman dabaro sannan ta bita tayi tsaye a kanta tana damqe hannunta a cikin matuqar dimuwa da gigita.
"Kinsan waye wannan?,kinsan waye kike tare dashi huda?....kinsan hadarin da kike shirin jefa rayuwarki dama mu gaba daya?,kinsan waye Naseer?!" Taqarasa fada idanunta a waje sosai suna nuna girma da yawan bala'in data tarko musu.
Gaba daya ido ta zubawa sabreen din tana mamakin maganganunta
"Wayeshi din?" Hudan ta fada zuciyarta a tsaurare.
"Ba sunanshi naseer ba,sunanshi bassam". Ta sake fada tana ji a ranta ya kamata itama tayi tsaiwar daka har sabreen din ta fuskanci nata zabin.
"Basma......bassam.....innalillahi" Sabreen ta furta duka a tare tana komawa qasan dakin gaban hudan ta zauna jabar.
"Tun yaushe kuke tare?,kun taba haduwa?,shine ya baki waya?,dame dame yake gaya miki?,tun yaushe kike waya dashi?!" Tayi maganar wani irin zafi yana taso mata daga qasan zuciyarta. Iya kallon da huda ke mata.....iya abinda take gani daga idanun hudan kawai sun isa bata amsar zuciyarta ta fara soyewa.
"Dake nake magana huda!" Ta furta da wata gigitacciyar tsawa data ratsa hudan ainun ta cakude da radadin marin da baibar fuskarta ba har yanzu.
"Ki barni yaa sabreen.....ki barmin zabina......bassam ya cancanta,shi nakeso kuma yayimin alqawarin bani kulawa kaman