Showing 39001 words to 42000 words out of 209775 words

Chapter 14 - Duniyata 1 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

11 Nov 2025

495

din ba. Oily eyes dinta sun cika taf da qwalla

"Kamar asibiti tafi buqatar a kaita" Ta kasa haquri har sai da bakinta ya furta hakan

"Zaifi kyau dai gaskiya don da alama tana buqatar iska sosai".

Dai dai sannan wayarta data watsar ta dauki ringing. Matar ce ta matsa ta miqo mata,ta sanya hannu ta karba tana fadin

" Na gode" Tana duba me kiran.

Busari ne,ta latse wayar tana karawa a kunnenta

"Na qaraso,ina dab da bakin masallacin"

"Ka karba kayana wajen me gadi,gani nan fitowa asibiti zamu wuce" Bata tsaya sauraren abinda zai fada ba ta katse kiran.

Idanunta ta mayar saman fuskar matar. Wani abu taji ya taba zuciyarta,sai takejin kamar umminta ce ta dawo,sai takejin tamkar lokacin data rasa umminta. A duk sanda take mutum me dauke da irin ciwon tsananin tausayinsa yake kamata,duk da itama abar tausayin ce. Duk sanda taga babbar kaman haka yana fafutuka da wannan ciwon sai ta dinga tuna umminta.

Su biyun suka tallafeta don taji qwarin jikinta,suna takowa a hankali da ita har suka fito zuwa inda Kekenapep din yake

"Zan samu face mask a wajenka?" Ta tambayi busari.

"Eh hajiya" Ya amsa mata da sauri yana bude aljihun motar ya fidda shi sabo fil ya bata.

A kusa da ita ta zauna tana riqe da face mask din,saita sauke idanunta qasa tana jujjuyashi.

"Zan saka miki wannan saboda iskan mota,motan bana gida bane". Idanunta saman fuskar yarinyar,har zuciyarta tana jin qauna da jinjina taimakonta a kanta,ta lura tana d'anjin wani nauyi da kuma rashin sakewa. Qaramar yarinya haka me zuciyar taimako?,sai abun ya qayatar da ita.

Mintuna ashirin daidai suka qarasa private hospital din,wanda a nan file nata dana qannenta dukka yake. Tuntuntuni ta sallama asibitin gwamnati,yana daya daga cikin muhallan da suka samarwa rayuwarta gibi,yana daya daga cikin guraren da suka dasa qaton tarihi a rayuwarta,suka kuma ajiye mata wani tabo na har abada,shi ya sanya daga sanda ta samu dama ta nisanta kanta da dukkaninsu daga asibitin gwamnati.

Private hospital ne daya amsa sunanshi,babu nau'in wata kulawa da mara lafiya baya samunta,saidai kuma kudi ne zasu fita sosai daga aljihun majinyaci ko ahalinsa.

Private room suka bata,cikin mintuna goma sha biyar kacal suka bata dukkan taimakon daya dace,bata samu nutsuwa ba sai da suka shafe awa guda taga bacci sosai ya dauketa tana sauke numfashin a hankali ta cikin oxygen din da suka maqala mata saboda yadda taso galabaita sosai.

Zama tayi kawai gabanta bayan taja kujera,ta maqale hannunta a qirji bayan ta zube idanunta a kanta tana dawo da bayanan da likita yayi mata a kanta.

"Ta samu mummunan attack ne,tana samun kulawa sosai to amma kuma kaman yanayi ya nuna ba'a kiyaye wasu dokoki na masu ciwon,sannan kuskure ne ta dinga fita hakanan ba tare da inhaler ko wani a kusa da ita ba".

Idanunta ta qanqance sosai tana ci gaba da nazarin maganganunsa. Hakanan sai taji ranta yayi matuqar baci,indai har mace me irin wannan shekarun bata samu kulawa ba sai yaushe?,indai har ba za'a kula da dokokin da aka bata ba meye amfanin makusantanta?. Dukkan alamu sun nuna,tun daga suturar jikinta da komai nata ma cikin wadata da sukunin rayuwa take ainun,to meye zai hana su su bata kulawa su ahalin nata?.

Idan zata iya tunawa mutum daya ne ta gansu a tare a tsaye cikin store din,har tana bada umarnin a kira mata wani data kira a cici da kuma yawale. Yawonsu kenan yafi musu kasancewa da ita?,yanzu haka fa mahaifiyarsu ce amma sun gwammaci tafiya yawo akan su bata kulawa?.

Iska me zafi ta sake fesarwa ranta yana sake tunzura musamman bayan data duba agogon hannunta. Aqalla awa daya harda rabi da barowarsu store din amma har yanxun basu biyo address na asibitin data barwa wancan matar sun biyo bayan baiwar Allahn ba?. Sake juya wayarta tayi su huda suna fado mata a rai. Ta tabbatar zuwa yanzun sun dawo gida,suna can kuma zaune su daya a daki. Karon farko da taji kaman ya kamata ta siya waya ko qwaya daya ce ta ajiye cikin dakin saboda lalura irin haka,ko ba komai ba zata barsu cikin zulumi ba,zata kira taji lafiyarsu suma suji lafiyarta,duk kuwa da cewa komai runtsi a gida takeyin magrib.

Daidai sanda tunaninta yakai nan taji an murda handle na qofar. Kyakkyawan matashin ne ya fara bayyana. Dogo me matsakaicin haske. Kai tsaye idan kace masa kyakkyawa bakayi kuskure ba,yana da cikakkiyar suma me santsi tun daga kansa zuwa habarsa.

Yana sanye da dakakkiyar shaddar getzner Neautaral color daketa yauqi da sheqi. Yanayin dinkin da aka yiwa shaddar yayi masifar dacewa da structure na jikinsa. Dinkin zamani dake nuna zallar gogewa da wadatar arziqi na wanda suturar ke kwance a jikinsa. Yadda shaddar ke walqiya hakanan hular kansa,wadda koda ba'a gaya maka kudinta ba zakasan cewa bada qaramin zare aka saqata ba. Qafafun sanye cikin takalmin Batozzi,hakanan cikin qasa da second biyar dakin ya gauraye da sassanyan qamshin turarensa.

"Hamma mun sameta,gata tana bacci" Ya furta da kwantacciyar muryarsa da alama kuma yana magana ne da wani a wayar dake manne a kunnensa,dukka hankalinsa da idanuwansa suna kan matar dake kwance cikin mazari yana d'okin isa gareta.

"Okay hamma......in sha Allah" Ya sake fadi da sauri sannan ya jefa wayar a aljihunsa yana isa inda take kwancen ba tare daya damu ya kashe wayar ba.

Rusunawa yayi sosai a gabanta yana riqe da hannunta da dukka hannayensa biyun. Yayi wani irin laushi,don idan ka kalli hannunsa da kyau kana iya ganin yadda suke danyin rawa.

Dauke dubanta tayi daga kansa haushinsa yana saukar mata,saita maida kallonta akan wanda suka shigo din tare. Shine dai wanda ta gansu cikin store din tare wanda ta bari ya biya kudin siyayyar da tayi.

"Kamar kece kika kawota ko?" Ya fadi saboda hada idanu da sukayi. Maganar tashi taja hankalinsa,yadan sassauta riqon da ya yiwa mara lafiyan ya kuma waiwayo da dukka nasa idanun yana dubansu,don shi sam sam bai ma lura da kowa ba a wajen.

Kamar yayi mata susa ne a inda yake mata qaiqayi,sai ta miqe a nutse tana saqala Jakarta a kafadarta,haushinsu yana sake turniqeta

"Eh nice bayan kun yasar da ita kun kama gabanku ba?,waishin kunsan muhimmancinta kuwa?,kunsan yadda ciwonta ke buqatar a dinga yawan kulawa da ita musamman ita da shekarunta suka fara yawa?.

Ji yayi maganganunta sunyi girma ainun,tasan wace ita din a wajensu har da zataga gazawa da kasawarsu?. Saidai bai datseta ba saboda yadda yaga hawaye suna cika idanunta

"Mutane da yawa basusan muhimmancin iyaye ba sai sanda suka rasasu......amma ku sani cewa......yadda suka baku kulawa a sanda bakusan muhimmancin rayuwa ba.....ba komai bane don kun basu kulawa a sanda sukasan muhimmancin nasu rayuwar......ba kowa a kusa da ita.....ba inhaler.....yanzu inda numfashinta ya katse fa?" Ta qarashe fada adan tsawace hawayen na fara gangarowa ta idonta qwaya daya,sai tayi hanzarin kauda kanta gefe ta dauke hawayen da yatsanta. Su kadai sukasan yanayin da suke shiga idan ciwon ya tasar musu shi yasa babu me fahimtar abun sai wanda ke cikin yanayin

"Kuji tsoron Allah ku kula da ita yadda ya dace,don yadda muke amana a hannun iyaye haka suma amana ne a hannunmu,kuma Allah zai tambayemu game da yadda muka kula da tsufansu" Tana kaiwa nan ta soma takawa tana ficewa daga dakin.

Gaba daya mamakinta ya cikashi,yadda take haqiqancewa ba tare da tasan komai a kansu ba. Mahaifiyarsa itace rauninsa har abada.....wani abu guda daya me matuqar tsada da muhimmancin da ba madadinta. Har ta fice ya kasa tsaidata kaman yadda yaso har sai data bacewa ganinsu.

"Bita ka tsaidata......a qalla ko godiya ya kamata muyi mata,sannan kuma muji yadda za'a maida mata kudaden data kashe tunda na samu an biya bill na komai"

"Okay" Ya furta a girmame yana juyawa ya fice a dakin.

Kamar wayar dake aljihunsa yaji yana motsi,ya dafe wayar sai kuma ya sanya hannu ya fiddota da sauri. Mamaki ya kamashi,ya akayi bai kashe wayar ba. Hamman ne har yanzu akan layi,duka mintunan da sukayin wayar na a kunne,sai ya maida wayar kunnensa

"Waye yake mata fada saman kai?" Ya furta nutse

"Wanda ta kawota ne daga can store din"

"Don ta kawotan take ma mutane fada?" Ya furta adan harzuqe

"No hamma...." Ya fadi da sauri. Numfashi yaja yana ware idanunsa sosai

"Stop......banason a sake mata hayaniya a wajen nan....if not ran kowa zai baci"

"In sha Allah hamma"

"Idan ta farka ta dawo daidai give me a call"

"Done" Ya fada a taqaice kafin ya yanke masa waya,yana gama fadin kuwa yaji qit ya gintse wayar,saiya cireta daga kunnensa yana girgiza kai.

"Hamma.....hamma" Ya maimaita sau biyu.

Koda cewa tayi fada cikin yanke hukunci akan abinda bata sani ba.....bata da yaqini amma shi baiga laifinta ba,ya mata uzuri......hasalima ta burgeshi qwarai,dukkan alamu yana nuna tasan darajar dan adam ne,sai ya maida hankalinsa akanta yana duba shiga da fitar numfashinta.

*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*

*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722

Nousaiba lawali maradi

1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks@:Huguma*

https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997

PAGE 22

__________________________

*_ALBISHIR A GAREKU!!_*

*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_*

*_KAMAR SU_*

Atamfofi

Laces

Shadda

Materials

Takalma

Jakunkuna

Mayafai

Trolley

Sarka da dan kunne

Oil perfumes

*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*

Numbers

08034469681

08135142610

Handles

Instagram @ummu_mahnoor_luxuries

TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries

Facebook ummu_mahnoor_luxuries

*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*

____________________________

Batasan me yasa ba,batasan dalilin da ya sanyata takejin bacin rai sosai akan abun ba. Ta dinga fidda numfashi me dumi a hankali daga baki zuwa hancinta. Cikin nutsatsen takun nan nata take nufar inda tabar busari yana jiranta. Takun da yayi matuqar tafiya da hankali da tunaninsa baya ga zubin mamallakin takun.

"Wai har yanzu akwai irin mata masu wannan ajin?" Ya furta qasa qasa ba tare da yasan a waje yayi maganar ba,tana ta'allaqa dubansa a kanta,yana jin tana tafiya da gaba daya kuzari tunaninsa dama hankalinsa gaba daya.

Tamkar an zungureshi ko kuma anyi masa qaimi,sai ya saka hannu da wani irin hanzari yana bude murfin motar. Sam gaba daya ya manta da dalilin daya kawosu asibitin,ya kuma manta ma da waye yake tare,burinsa guda daya tal! A yanzu,ya samu isa gareta,yakuma samu daman yin magana da ita.

Sallamar tashi ta ratsa kunnenta a sanda take dab da isa wajen da Kekenapep din yake. Ta lumshe idanunta a nutse tana riqe masaqalin jakarta da kyau. Dama tasan hakan zata iya faruwa duba,zaiyi wahala a kallon farko da tayi masa ya iya tsallake halaye da kuma dabi'uj data hanga kai tsaye daga gareshi.

"Assalamu alaikum.....don Allah....." Ya katse maganar tashi da kan kanshi lokacin da yasha gabanta idanunsu suka gauraya waje daya.

Wani kwarjini na musamman,wani yanayi ya tsarga masa irin wanda bai taba jin irinsa ba. Nashi idanun ya janye a hankali yana qoqarin daidaita kansa tare da zallar mamaki yana kuma tambayar kansa

"Meye haka?,ita din wace?". Baisan iya adadin kalar matan daya gani ba tun da ya fara zama cikakken namiji zuwa yau. Baisan adadin matan da yayi mu'amala dasu ba daga jinsin yare daban daban,amma yau daya wata mace da baya tunanin ta rufa shekara ashirin da biyar a duniya na neman yi masa kwarjini?.

"Lafiya?" Ta jefa masa tambayar tana tsuke fuskarta tare da sake bada tazara tsakaninsu. Qoqarin daidaita nutsuwarsa yayi,sai ya sake mata murmushi hadi da gyara tsaiwarsa sosai a gabanta,yana jin ba wata mace da zata iya kaucewa tarkonsa muddin ya d'ana shi.

"Ba lafiya ba......maganar gaskiya kenan.......akwai gagarumin tashin hankali" A mamakance take duba fuskarsa tana yamutse tata tare da qoqarin sakeyi masa sabon karatun da baisan tana yi ba

"Amma fa a zuciyata" Ya qarashe maganar yana dafe qirjinsa.

Numfashi taja sosai har cikin huhunta sannan ta fesar tana kauda kanta gefe hadi da juya qwayoyin idanunta. Ba shine mutum na farko data taba gamuwa dashi me irin wannan salon ba,don haka tafiyar dashi bazai bata wahala ba.

Dukkan wani d'a namiji da zai ratso rayuwarta tayi imanin QADDARARSA ce a nan.......da kuma zallar tsautsayi. Mafi rinjaye daga cikinsu kuma SON RAI da SON ZUKATA.

Ba kasafai ta fiya bada kai ta farat daya ba,koda ta tsara amsarka,don tuni ta fahimci duk wani abu da akeson yayi daraja.....kar a bari samuwarsa ta zama ta sauqi. Don haka ta soma tattaki da zummar kubcewa daga gabansa.

A gaggauce ya sake tare mata gaba yana dubanta cikin marairaicewa

"Ranki ya dade.......na tabbatar girmanki yafi gaban a tsaidaki a hanya....to amma muddin na barki kika wuce din nayi imanin sa'ata ta rayuwa ce ta kubcemin gaba dayanta......ki tallafeni ki sammin minti uku kacal" Ya furta yana nuna yatsunsa guda ukun.

Juyowa ta sakeyi a karo na uku tana kallonsa. Ya fiya zaqin baki da yawa,maza irinsa suna da wani hali da dabia da tuni ta gama karatunsa. Tabbas akwai wani abu tattare dashi da wata qila take nema......tana hasashen yiwuwar samun wata qaruwa me girman gaske. Taga irinsa ba daya ba.....ba biyu ba....ba uku ba,har ba zata iya tantance adadi ba.

Duk da wannan hasashen amma bata yarda ta nuna masa komai ba. Sai ta sake kau da kanta tana yamutsa fuska

"Matsawarka daga hanyata kamar zaifi zame maka alkhairi akan ci gaba da tsaiwar......ina da tarin abubuwa a gabana....."

"Bansan ko me ke jiranki ba......amma na tabbatar koda baikai wannan tsaiwar tamu alkhairi ba bazai wuceta ba" Ya fadi a zaqe da fatan samun nasara

"Na roqeki kada ki watsan qasa a idanu,ki wofantar da wannan kyakkyawar damar a garemu gaba daya" Ya fadi yana marairaicewa tare da miqa mata wayar hannunsa yana kasheta da idanu gami da karyar da wuya da raunanar da idanun nasa.

A nutse ta sauke kallonta akan wayar ta kalla. Tsaleliyar iPhone 16 wadda kana dubanta zakasan bata wani jima da baro dumin kwalin da aka qerata ba. A yangance ta dauke kanta daga kai ta sake maidawa gefanta bayan.

Wani numfashi ya fusga da qyar bayan ya gama sauraren jerin lambar wayarta data karanto masa. Sautin muryar nata yana masa wani irin amsa kuwwa a kunnensa. Karon farko daya yadda cewa muryoyin wasu matan kadai suna iya haddasa fitina a zukata da gangar jikkunan maza. Sai yakejin yana sake zurfi ason ya kasance a tare da ita

"Sai nakega kaman girma da martabarki ya dara kihau napep.....da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login