Showing 117001 words to 120000 words out of 209775 words
yake dab da qofa. Kansa kawai ya gyada masa yaja ya koma ya zauna,ba jimawa ya dawo da butar,ya karba ya fara dora alwalar a gaggauce,ya gama ya bashi ya karba ya maidata wajenta
"Zo muje malam said" Fu'ad ya fada yana ware hannun rigar sa.
Tare suka jera shida malam saidu din,duk da yadda yaso ya zuqe saboda girmamawa,me sunan malam kuma yana daga bayansu kadan ta yadda bazaiji wani abu da suke tattaunawa ba
"Magana zamuyi" Ya fada a nutsensa
"To....to" Ya fadi da hanzari
"Tambayoyi ne amma sai bayan mun idar da sallah zan saurari amsoshinsu"
"To ba laifi ai" Ya amsa masa,don ya saba lokaci lokaci dama yakan masa tambayoyi game da gidan ya kuma buqaci amsarsu.
"Waccan matar da suka shigo da hajiya meye sunanta?,wace ita a wajenta?,yaushe ka fara ganinta a gidan?,sannan kamar sau nawa ta taba zuwa ko take zuwa?,ita kadai ce koda wasu?,tana dadewa cikin gidan?,suna yawan fita tare ko aah" Yakai qarshen dukkanin tambayoyin nasa sanda suka kai bakin masallacin,don haka yayi shuru yana adduar shiga masallaci a madadin tarin tambayoyin.
"Lallai na sake yarda da maganar bokan can.....lallai akwai aiki qwarai akan yaronkin nan" Hajja ta fada duk da nata yaron da matarsa data shanya a waje kowanne cikin motarshi yana jiran fitowarta.
Labba maamah ta cije kadan sannan ta saki sanda take maida riga maras nauyi a jikinta
"Ni kuma cewa nayi miki zan qyale wannan aikin ya cimmani?,na zuba idanu naga iya gudun ruwansa na yau kawai......amma duk abinda yakai gobe zakiji kirana......a gobe nakeso mu koma a fara aikinnan"
"Ai da zafi zafi akan bugi qarfe....." Hajjan ta fadi zuciyarta na saqa mata abubuwa masu yawa.
Har bakin gate din farko ta tako tana yiwa qawartata godiya da ban gajiya. A nan suka gaisa da yahaya da matarsa. Yadda ta samesu a jere kowanne da mota yana jiran dakon fitowar hajjan ba tare daya isa yabar wajen ba ba bisa umarninta ba ya sake ninka kwadayinta itama na kaiwa wannan bigiren,sai taji kamar ta jawo wadannan kwanakin da tayi imanin suna dab da zuwa......ranar ea zata nunawa aminatu da hamza cewa ruwa ba sa'an kwando bane.....hakanan koda giwa ta fadi tafi qarfin wawa.
Haka siddan?,daga maqotaka?,ba sidi ba sadada a kama mata yara a musu muguwar mallaka?,bayan ko sanda ta tafinma suna da wayon da zasu iya kula da kansu?. Da wannan qananun mitocin ta isa cikin gida.
Ya kusa minti ashirin yana fuskantar gate din gidan,harde da hannayensa kawai yana duban qofar kwanyarsa tana digesting maganganun da sukayi da malam saidu daga hanyar masallaci zuwa dawowarsu. Baisan a wanne matsayi zai ajjiye maamah din ba.....karo na uku da wani abu ya sanya yake tunanin ANYA ITA DINCE TA HAIFESU?,anya ita din UWACE?,akwai zuciya irin ta uwaye a qirjinta kuwa?. Me yasa kullum DUNIYA itace a gabanta sama da komai?,yayi tunanin shi da kowa ma zata canza ko kuma ta canza din.....amma sai kuma akasin tunaninsu ya biyo baya.....akasin tunanin da shi kadai gani na zuciya da lura da bin takunta sannu a hankali suke karanta masa komai a kanta....karatun da idanuwa kadai sunyi kadan su iya fahimta ko ganeshi.
Hannayensa ya sauke jikinsa a mugun mace,baya jin zai iya komawa cikin gidan nan,idanma yace zai koma din abinda zai wanzu tsakaninshi da ita bame dadi bane. Ko haduwarsu na 'yan mintuna kadai ya sake wani karatun. Ya dawo lafiya?,wacce nasara ko qalubale ya riska?,duka ba damuwarta bane......damuwarta shine KUDI.....me yasa bai turo ba?. Abu guda daya da bai taba faruwa tsakaninshi da anni ko abba ba......basu taba neman anini taro ko sisi daga hannunshi ba.....a hakan take neman kudin da zata rabashi da Alhaji hamza da aminatu?,mutanen da su suka bashi RUHI na rayuwa da yake yawo a jikinsa a yanzu?.
Kansa ne yaji ya sara,sai ya sake qara azamar barin qofar gidan ya juya zuwa nasu gidan. Gidan da a baya shine gidan maqota a wajensu amma a yanzun basu da gidan daya kaishi.
Tun a gate ya sallami kowa,ya gaya musu da wuri zai kwanta don gobe zasu fita da wuri,duk da baida yaqinin goben a yadda zai tashi saboda wani nannauyan ciwon kai daya saukar masa yanzu yanzu.
Tun bai qarasa sassansa ba ya kashe duka wayoyinsa,yabi ta qofar baya don bayason kowa yasan ya shigo din ya wuce sassansa.
Bai kunna kowanne fitila na sassansa da zai bada alamar yana ciki ba,sai ya wuce a hankali kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki zuwa study room dinsa,ya tura qofar ya shiga ya maida ya rufe.
Zaune kawai yayi saman sofa idanunshi a kulle,yayi nisan nazarin da shi kansa baisan wane zare a tunanikansa zai kama ba. Abu daya ne da yafi daure masa kai da dagula masa lissafi,qoqarin da takeyi da gaske na sai ta raba tsakaninsu,indai haka ne wannan fitar tasu tana da alaqa da qudurinta.....indai haka ne kudin da take nema lallai yana da alaqa da qudurinta......indai kuma haka ne tabbas wannan BAQUWAR FUSKAR akwai tata rawar cikin mission din......duk da yasan wannan din tsohon quduri ne dake ranta.....amma dukkan alamu sun nuna ta samu MAKAMASHI.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 59
Shuru ne ya biyo baya tsakaninsu,babu wanda yace da dan uwansa komai tsakanin ita da anni din. Daga yanayin tsaiwarta da yadda take bin komai da wani irin kallo ta tabbatar ba alkhairi bane ya kawota,don haka taci gaba da abinda takeyi din ba tare data ce komai da ita ba.
Baifi minti biyu ba kacal sai ga amna ta dawo
"Yace gashi nan...." Ta bata amsa tana sake binta da kallo tamkar a tsorace,sannan ta qarasa ta dauki plate dinta ta koma kusa da annin ta naniqe ta zauna tana ci gaba da satar kallon maamah din.
Da sallama ya shigo falon cike da kamalar nan tasa dake shimfide saman fuskarsa,sanye yake da jallabiyya ruwan qasa,kansa sanye da qaramar hula tashi ka fiya naci.
Amna da anni ne suka amsa sallamar tashi,yayin da maamah ta dubeshi kadan kafin ta dauke kanta
"Mariya ce?,....bismillah......zauna mana" Ya fada yana zama kujerar dake daura data anni. Kamar tace ba zata zauna ba,to amma kuma zaman yafi kamata tayin,don tanason daga qarshe ta gasa masa maganganun da indai ya haifu zai fara janye jikinsa daga dukkan wata mu'amala ta fu'ad dama rayuwarsa gaba daya,yabar mata 'ya'yanta kamar yadda kowacce uwa keda iko da nata yaran.
"Muna lafiya.....ina fata kuma lafiyar ko?" Gyara zamanta tayi sosai tana dora qafarta daya kan daya,sannan ta saka idanunta sosai cikin nasa
"Wajenka nazo hamza" Ta fadi kanta tsaye,abinda yaja hankalin anni kenan tadan daga kai ta dubeta,sai kuma ta saukar tana son kwashe hankalinta sam sam daga kansu.
"To ai gani.....Allah yasa lafiya" Fuska ta qanqance tana dubansa idanunta a ciki.
"Al'amarinku yana bani mamaki hamza yana kuma dauremin kai.........duk duniya ban taba ganin inda ake irin haka ba sai a kanku,hankaka mai da dan wani naka?......amma mu ajjiye wannan batun......tunda kun zab lallai sai na zama maqasqanciya a gabanku akan 'ya'yana?......ba laifi don komai da ka gani a rayuwa lokaci ne.....kuma iyaka gareshi......" Ta furta qasan ranta tana hangen iya adadin lokacin da ya rage musu wanda alaqar uwa da uba zata wanzu a tsakaninsu.....da tazarar lokacin da alaqar zata juye zuwa alaqar gagarumin abokin adawar da duk duniya fuad din zai wayi gari bashi da abokin adawa irinsa. Burinta shine ta bude idanu taba tsabtsar gaba da adawa mai qarfin gaske ta qullu tsakaninsu......irin adawar da zata bawa kowa mamaki ta kuma shiga sahun tarihi......tabbas saita fanshe dukkan wani baqinciki da suma cusa mata......hakanan ba zata qyale ba sai sunyi aman duk wani da sukaci daga cikin arziqin fuad......koda kuwa wannan gidan da suke ciki yana cikin jerin sahun mallakar fu'ad din.
"Wai nikam hamza.......ban sani ba ko cikin duhu ne a sannan?......hadaka da kuma gamayya kukayi da ubansu fu'ad yayin samuwar cikinsu?,ma'ana tare kukamin cikinsu ko kuwa?" Ba alhaji hamza kibiya kadai ba,hatta anni dake zaune daga gefe ba tare da shiga shirginsu ba sai data cira kanta da sauri maganar tana dukanta
"Subhanallahi.......innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Alhj hamza ya fada zallan mamaki yana saukar masa,idanunsa akan fuskar amna wadda ta yunqura tana miqewa ba tare data tsaya daukan plate din abincin ba saboda yadda maganar ta girmimi kunnuwanta.
"Mamaki kukayi?,to ai ba abun mamaki bane duba da yadda kuka qanqame min rayuwar 'ya'ya hamza" Ta kuma fadi cikin izza ba shakka ko d'ar a cikin idanunta.
"Mariya cikin hankalinki kike kuwa?" Anni ta gaza jurewa ta fada tana kafeta da idanunta. Wurga kallonta tayi zuwa ga annin
"Kinga ina iface iface ne ko yage yage da zakiyimin wannan tambayar?"
"Shin mene marabar dambe da fada mariya?,ai hauka nau'i nau'i ne.....nakin ina kyautata zaton ta wannan fuskar yazo"
"Kamar yadda cutarwarku tazo da sigar yaudara da damfara ba.......na rantse da Allah a yau inda fu'ad yana a faqirinsa bashi da komai da tuni kun watsashi shi da dan uwansa........."
"Kaman yadda zamantowarsu halittar da zaki iya mora ta sanya kika dawo cikin rayuwarsu ba?....bayan kin watsar dasu a sannan kina zaton su din ba masu amfani bane,nauyi ne kawai a wuyanki?". Anni ta maida mata amsa ta hanyar katse numfashinta bacin rai yana fara nuna alamun tasiri cikin muryarta
"Ya isa aminatu......ban yarda ki sake cewa wani abu ba" Alhaji hamza ya fada yana daga mata hannu. Ya gama karantar akwai abubuwa masu tarin yawa a bunne cikin zuciyar maamah din,biye matan da annin zatayi shi xai bata damar furzar da maganganun da idan suka qyaleta basu tanka mata ba har ta mutu saidai ta mutu dasu a cikinta.
Dole ta ninke dubban maganganun da suke tsinkulinta a rai kawai don ta bawa abban girmansa,amma bawai don abinda take da shirin furtawa itama ya qare ba,ta kauda kai tana hadiye fushinta ba tare data sake jefa baki a maganarsu ba
"Ka gaya masa ya bini.....domin kuwa duk duniya ba wanda akace aljannarsa tana qarqashin qafarta face ni.....komin lalacewata......ka taimaka ka sakar masa mara ya rabu dani lafiya kaman yadda na tabbatar ka rabu da naka lafiya......ka shaida masa yazo ya bani kudin dana buqata a hannunsa.......bawai alfarma nake nema ba......ka gaya masa dole ne yayimin...." Tana kaiwa nan ta miqe tsam,idanunta akan anni da tayi kaman batasan da wanzuwarta a wajen ba. Taso ace annin taci gaba da ja,don tana da tarin maganganun da takeso ta amayar mata
"Wallahi duk d'an da ya hana uwarsa bacci.......shima bazai huta ba" Ta furta tana juya hankali kwance tana barin falon.
Shuru ne ya biyo baya,duk kuwa da cewa ta gama ta kuma fita daga gidan ma gaba daya
"Hasbunallahu wani'imal wakil" Alhaji hamza ya furta gauraye da wata ajiyar numfashi me nauyi idanunsa na kallon waje daya.
Baisan wanne irin abune yake dawainiya da mariya ba......baisan kuma wanne girman laifi sukayiwa rayuwarta haka da take musu kallon wasu manya manyan abokan adawarta ba. Anni batace komai ba kaman yadda shima bai buqaci tace ba,tanata qoqarin sarrafa bacin ranta da ganin ta hadiyeshi ba tare data barshi ya mata tasiri ba
"Ina muhammadu?" Alhaji hamza yayi tambayar yana duban annin
"Bansan ina yayi ba.....mun rabu dashi a dazu kan zai shiga wajenta" Ta amsa masa a taqaice. Karkacewa yayi ya ciro wayarsa daga aljihun jallabiyyarsa ya soma trying number din fuad din.
Sosai yayi nisa cikin tunani,a haka idan ka ganshi zaka dauka bacci yakeyi,saidai ba ko guda daya. Wasu mintina ne daketa wulga masa tsakanin bacci da ido biyu wanda a ciki baisan ainihin abinda yakeyi ba
A silent wayar take,amma hasken da take fitarwa ya ratsa rufaffun idanunsa a cikin duhun dakin.
Kamar bazai bude idanun nasa ba amma sai ya budesun a hankali yana saukesu akan wayar. Yayi tsammanin ya kashe duka layukan,sai a sannan ya lura guda daya ya kashe. Sunan daya gani saman wayar ya sanyashi sauke qafafunsa a hankali yana maida hankalinsa a kanta,ya miqa hannu ya daukota daga inda take ajiye yana qoqarin dagawa.
Sallama yayi amma muryarshi ta maqale,yadanyi gyaran murya sanda yajiyo muryar abban yana masa sallama
"Ina ka shiga ne?" Alhaji hamza ya tambayeshi
"Ina cikin gida abba"
"To fito......inason ganinka.....ka sameni falon anninka"
"To abba" Ya amsa masa a ladabce. Remote ya laluba ya dauko ba tare daya tashi a gun ba ya maida hasken dakin. Take yayi tarwai da haske kaman yadda ainihin dakin yake
"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla.....wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita sahla" Ya furta muryarsa can qasa,yana jinsa gaba daya ba kuzari,tun daga zuciyarsa har zuwa gangar jikinsa.
Bai wani bata lokaci ba ya sauya kayan jikinsa sannan ya wuce sassan annin. Sallama yayi hankalinsa na kaiwa fuskar anni. Tun bai zauna ba jikinsa ya bashi akwai wani abu,don ba kasafai kake ganin fuskar annin a haka ba. A nutse ya qarasa shiga ciki,kai tsaye kuma ya nufi inda Alhaji hamza yake,wanda bai motsa ba daga wajen tunda maamah din ta fita ta barsu.
"Bismillah.....zauna" Alhaji hamza din ya masa nuni da kujerar dake kusa dashi. Sanda ya zauna din ita kuma anni ta miqe da zummar barin wajen,abban ya maida dubanshi kanta
"Zama kema zakiyi......ina zakije?" Duban abban tayi,kaman zatayi magana sai kuma ta fasa,ta koma ta zauna ba tare data sake cewa komai ba.
"Muhammadu" Abba ya kira sunanshi kai tsaye,abinda ba kasafai hakan ke kasancewa ba. Mamakin ya hanashi amsawa saidai ya daga kai kawai yana duban abban.
"Muhammadu ya ina yabonka sallah zaka kasa alwala?" Abban ya sake fada idanunsa still akan fu'ad din,tausayinsa kuma yana ratsa zuciyar abban.
"Abba....." Fu'ad ya motsa labbansa a hankali da zummar yin magana
"Me dame mariya tace maka tana da buqata wanda bakayi mata ba?" Ya masa tambayar Kai tsaye don sauqaqe masa wahalar tunani.
"Abba.....ba wani nauyi ko haqqi daya kamata na bawa maamah wanda bana bata shi......bana tunanin akwai wani abu da ya zama nauyi ko haqqi da ubangiji ya doramin wanda na gaza dauke mata shi". Har cikin zuciyarsa abban ya gamsu da wannan,saboda shi kansa ganau ne bawai jiyau ba akan hakan
"Na sani Muhammadu......amma don me yasa idan tana da buqatar kudi daga hannunka kake hana mata?". Sam baima kawo wannan zancan bane,sai ya sauke boyayyar ajiyar zuciya yana sauke kanshi qasa.
Rashin amsawarsa ya bawa abba amsar tambayarshi
"Me yasa kusan ko yaushe matsalarka da ita akan tana neman kudi ne ka hanata?,bayan Allah yayi maka wadatar da zaka iya bata ko nawa ne Muhammadu?" Ya qarashe maganar ta sigar tambaya idanunsa a kanshi,can qasan ransa yana mamakin abinda ke kawo musu matsala akan abinda yasan ya jima da fin qarfinsa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 60
"Ka sani cewa......duk d'a aljannarsa tana qarqashin qafar iyayensa?,kuma haramunne jayayya dasu bare su buqaci abu aqi ayi musu?"
"Na sani abba.......amma bazan iya bawa maamah ko sisi ba". Sosai maganar ta bawa abban mamaki,har anni dake zaune daga gefe itama ta daga kai tana kalleshi
"Akwai abubuwa masu yawan da baka gama saninsu ba abba akan maamah......akwai boyayyun sirrikan dana ajewa cikina abba.......akwai wasu abubuwa masu yawa wadanda ba zasu fadu ba......amma koma meye cinta shanta lafiyarta dama suturarta wani abu ne da bazan taba iya hana mata su ba ko don albarkacin haihuwa da Allah ya bata........amma batun kudi abba........bazan iya bata ba"
"Dalili?,dalili nakeso naji Muhammadu" Abba ya sake tambaya cikin tsananin mamaki. Bai taba umartarsa da abu ba ya saba.....sai gashi s yau yana qoqarin bijire masa.......tabbacin akwai wani qaqqarfan dalili da kuma hujja kenan
"Abba...." Ya kirayi sunansa yana jin nauyin abinda zai furta din. Shurunsa ba abinda zai harfa tsakaninsa dashi sai gurguwar fahimta,bayaninsa din kuma bawai abu bane me dadin ji ko sauraro ba.
"Kasani Muhammadu.....koda baka bayar ba ni zan dauka na bata da kaina"
"Zan bayar abba.....zan bata amma bawai don zuciyata tana so ba......"
"Zuwa yaushe kenan?" Ya sake tambayar sa
"Zan yiwa sadiq magana,zai saka mata"
"Kirashi yanzu yanzu" Ya sake bashi umarni kai tsaye. Dole ya fidda waya ya turawa sadiq din saqon umarnin fidda kudaden,sannan ya aje wayar yana duban abban
"Zai sanya mata in sha Allahu". Ajiyar zuciya abban ya sauke. Shi