Showing 105001 words to 108000 words out of 209775 words
Cikin nashi tsananin kulawar da kallon kewa yake amsa mata,fuskarsa ta wadatu sosai da fara'a yana tambayar lafiyarta dama ta jama'ar gidan gaba daya.
Hankalinsa yana kansu,qauna da kulawar dake tsakanin anni da abba sune abu guda daya tak da suka rage wadanda suke bashi hope din wataran qila zai iya aure. Soyayyar da sukema juna wani irin dasashen abu ne da har yanzu yake tasiri a tsakaninsu,babu alamun gushewa sam sam. Yanayin rayuwarsun yana burgeshi,wata irin mu'amala annin kewa abba,irin mu'amalar da bai taba ganinta ba tsakanin MAAMAHnsa da ABBEY dinsa ba. Mu'amalar da bai taba zaton akwaita tsakanin miji da mata ba sai a wajen annin.
Gabanta ya qarasa shima kaman ko yaushe,cike da ban girman nan da yake jinsa har cikin ruhinsa ya tsugunna yana gaidata. Bata iya tsaiwa saman kanshi ba saboda girman shima da take bashi sakamakon sunan MUHAMMADU da yake dashi......da wata ajiyayyar kima da martaba da take ganinsa dashi saboda dattakon halinsa data sani tun bai cika shekara sha takwas bama a duniya.......uwa uba yadda yake tattalin farincikinta kadai ya sanya kowanne lokaci takejin tamkar jikinta ya tsaga ya fito.
"Lafiya alhamdulillah me babban suna.....jiki na warware tun tuni......dama ta jima bata tashi ba,akasi kawai aka samu a ranar,nafi tunanin kuma matar da mukayi salla tare ne turarenta yayimin qarfi da yawa".
Dan qwarya qwaryar zama sukayi cikin falon na duba lafiyar juna,qananun zolaya tsakanin amna farouq da musaddiq abban yana shiga yana raba gardama kafin daga bisani anni tayi umarni
"Abinci ya zama ready.....zaku shiga ku watsa ruwa tukunna ko?" Ta fada tana duban abba me gayya me aiki
"Hakan yana da kyau ko me babban suna?" Ya maida tambayar ga fu'ad. Murmushi kadan ya saki,suna girmama ra'ayinsa qwarai,sunan da yake dauke dashi ya bashi wannan girman a iyalin da suka san girma da martabar sunan. Wani abu da sam sam bai gani ba ga maamah,tana iya kiransa a lokacin quruciya da sunan ta kuma zabga masa zagi fada da sauransu
"To abba" Ya amsawa Alhaji hamza yana miqewa. Farouq ne ya miqe ya dauki luggage din fu'ad din yana nufar qofa
"Muje na taka maka badon halinka ba......don wallahi ka shiga uku duk sanda mukayi aure muka barka kai kadai a gidan nan". Yayi maganar qasa qasa yadda su abba ba zasuji ba.
Harara fu'ad ya zabga masa yana jan qaramin tsaki
"Sannu tattabara sarkin aure?,yanzun ma idan kaga dama ka koma mana ka gani?......ni gwara fa ku qara gaba ku barni daga ni sai anni ko mayi kumari". Dariya ya fashe da ita harda buga qafa kadan
"Kayi asara wallahi.....kai ta qara qiba ma kake,kaci gaba da gandamewa a gaban annin?,idan bakayi wasa ba gaba gaba sadakarka za'a bayar Allah......"
"Munyi asara dai ni dakai mayen aure......idan kun tashi kuyi shelata a masallacin juma'a".
"Basai munkai ga nan ba......owner na diamondchore resources company guda.......ko a sirrance akayi shelarsa mugun ciniki zamuyi Allah,a zaba maka guda hudu qwarara......matsalar kawai har yanzun ni kaina bansan color na macen da kakeso ba.....". Shammatar farouq din yayi yakai masa wani wawan duka sai daya qame,don maganar ta fara isarsa,yasan kuma farouq baisan bari ba,baisan ya isa ba.
"Kaci bashi......sai na dauki fansa.....ka qarasa cikin da kanka na fasa rakiyar" Ya fada yana jingine masa luggage dinsa daidai qofofin sassansu
"Tafi nono fari" Fu'ad din ya fada yana zura key ma qofan sassansa yana budewa,saidai fuskarsa kwance take da murmushi yana juya halin farouq din. Shi daya farouq din yakewa haka.....kamar yadda shima farouq din kawai ke akwai 'yar hakan a tsakaninsu.
"Alhamdulillah" Ya furta a sarari murya can qasan bayan ya isa ainihin bedroom dinsa,yana jin ma'anar godiyar daga qasan zuciyarsa. Tarin godiya ce fal zuciyarsa game da ubangijinsa,godiyar da har wani lokacin ya dinga jin baisan ta yadda zaiyiti ba takai gurbin da akeso. Ubagijinsa ya gama masa komai.....ya kyautata rayuwarsa fiye da yadda yake tsammani.
Komai na sashen nasa a killace a kuma tsaftace akan tsari fiye ma da yadda yakeso. Wani irin qamshi ke tashi,abinda ya sanyashi sakin wata nannauyar ajiyar zuciya data sanya yaji wani nauyi ya ragu sosai daga saman zuciyarsa. Yana yiwa qamshi wani jarababben so,a duniya qamshin yana daya daga cikin jerin abubuwan da yafi qauna. Qamshi yana sanyashi maqalewa waje,kaman yadda akasinsa ke sanyashi rabuwa da waje.
Yana iya baiwa farouq dinsa komai amma indai ta fannin abinda ya shafi turare ne to zaka iya jin musunsa dashi. Bai yarda ba a taba masa turaruka,gwara ka zaba ko na nawa ne ya siya ya baka kyauta.
Kayan jikinsa ya dinga zarewa har sai daya rage saura fara qal din vest din jikinsa da gajeran wandon da bai qarasa gwiwarsa ba. Muradadde kuma ginannen jikinsan nan dake dauke da wasu lafiyayyun muscles dake alamta ainihin qarfi na siffa ta zahiri da badini ya bayyana,lullube da wadatattun gargasa ta ko ina. Wankan yakeson yayi amma shigowar kira ya hana masa hakan,tilas ya samu saman sofa bed ya zauna yana amsa kiran.
Amsa kiraye kirayen ya daukeshi lokuta masu tsahon da har musaddiq ya dinga zuwa dubashi zasuci abinci. Daga qarshe ya basu excuse akan suci din idan ya kammala zai fito.
Fitowar da bai samu daman yi ba kenan,don sanda ya fito a wankan gaba daya kasala da tsohuwar gajiya ce ta saukar masa,dole ya haye gadonsa bayan ya maida da dakin dark ta sakin dukka manya manyan curtains dinsa,ya kuma kashe kowacce fitila da zata iya bashi haske don baya son bacci a duhu sam sam. Koda baccin yakeyi kana kunnata ka tasheshi. Sunsha fafatawa da farouq akan hakan,don shi mutum ne da kwana cikin haske bai dameshi ba. Wannan dalilin yasa ko a yanzun yafi sha'awar kowa ya zauna a sassansa,ba kasafai ya fiya son takurawa mutum da salon tsarin rayuwarsa ba.
*****Su biyun dukansu suna zaune ne saman buzu na fatar dabbar da basusan wacce iri bace. Kaman yadda dukkaninsu jikinsu ke sanye da sutura ta alfarmar da zaka fahimci rayuwa ta basu sukuni yadda ya dace,saidai tasu salon miqa godiya wa mahaliccinsu da suka munana hanyarta.
Daga atamfar jikin hajja har lace din da maahma ke sanye dashi wanda ya darawa atamfar hajjan tsada isashen jari ne ga mutane masu yawan gaske. Kaman yadda jakar maahma din da takalman data sanyawa qafafunta suke wani jarin me zaman kansa ga wasu mutanen. Takalmin da fu'ad din yayi mata order dinsa da kanshi tun daga qasar Italy.
Kusan yadda ta bawa mutumin dan duqurqushi me zubin wada hankalinta hajja bata bashi nata haka ba.
Daya daga cikin qoqunan gabansa da suke kife ya daga,qoqon da babu komai amma saiga haske ya cikashi. Tafukan hannayensa ya saka yana rufe qwayar da hannunsa nasa. Idanunsa ya runtse,wasu irin maganganu ya dinga furtawa da ba'a gane abinda yake fadi,tun yana fada a hankali a hankali har ya fara furtawa da sauri da sauri da kuma qarfi har muryarsa tana amsa kuwwa. A hankali jikinsa ya fara wani irin kakkarwa tamkar wanda aka jonawa shocking. Da wani irin sauri yan fusge hannayensa daga saman qwaryar yana yarfar dasu kamar wanda wuta ta taba,sai kuma ya sake maidasun yana canza salon yaron da yakeji ba irin na dazu ba.
Ya kusa minti biyu a haka,wata irin zufa da basusan daga ina take ba ta gama jiqeshi sharkaf.....a hankali a hankali ya soma sassauta muryarsa sannan ya fara daidaita yanayinsa kafin ya bude idanunsa da suka ninka ja akan asalin jan da suke dashi.
"Matso!" Yace da maamah a tsawace. Tsoro ba kalma bace da ta santa ba kaf ray uwarta......qafafunta sun taka gurare da dama amma a yanzun saita samu kanta cikin shakka da d'ar d'ar har ta matso zuwa inda yake mata nuni
"Ba shine wannan ba?" Ya fada da qarfi yana nuna mata qoqon.
Fu'ad ne kwance saman gadonshi yana baccinsa hankali kwance kaman yadda ya kwanta a ainihin dakinsa dake gidan Alhaji hamza kibiya. Mamaki ya qarasa cikata,ba shakka fu'ad ne,kuma dakin ya mata kama da dakunan gidan Alhaji hamza,sun dawo kenan kaman yadda yake shaida mata dazu da sassafe kan suna hanya?.
Daga ita har bokan ba wanda ya samu cewa wani abu dif hoton dake cikin qwayar ya bace kaman an dakeshi harda tartsatsin wata wuta.
"Kin gani ko?,ba mutumin da muka sha wahalar kawoshi zuwa garemu saishi......baya ga haka kinga yadda surarsa ta dauke da gaggawa......abinda ke bamu tabbacin aikinsa yasha banban da dukka ragowar aiki da muka taba yi a baya......akwai tashin hankali......akwai wahala.......akwai kuma qalubale!!!" Ya furta da kakkausar muryarsa mara dadin amo da sauti bare sha'awar saurare.
Dukkan kayan aikin nasa ya tattara ya zuba cikin qwarya daya daga cikin qorai biyu dake gabansa,take suka bace bat tamkar ba'a taba halittarsu ba a wajen.
Jajayen idanunsa da babu rahama,musulunci ko imani a ciki ya daga ya kalli maamah dake dubansa babu ko qiftawa.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 54
Idanu yadan zuba mata na wasu mintuna da har sai data dan sha jinin jikinta. Sai kuma ya saki wani busashen murmushi da yafi kama da kukan jaki yana kallonta
"Ba shakka kin haifi jarumi......kin haifi yaron da taurarinsa suke da tsananin hasken da ba kasafai ake samun galaba ayi kutse a cikinsu ba ko asha kansu.......yaronki yana tattare da abubuwan al'ajabi da baiwarwarki masu yawan gaske wadanda ko ke uwar da kika haifesa bakisan yana dasu ba......cikin mutane dubu guda daya ake iya samu irinsa......". Kai kawai take jinjinawa tana sauraronsa. Tun sanda ta haifi fu'ad din tasan daban yake da sauran yara,to amma a yanzun kalamansa daga mata hankali sukeyi,kamar sunason shinshina mata rashin nasararta ne......kamar suna shinshina mata rashin yiwuwar aikinta?.
Maganarsa ta gaba ta bata amsa ta kuma yanke mata dukkan zatonta
"Aiki a kansa ba qaramin abu bane me girma......akwai tsari a jikinsa......yana da addu'a sosai tare da kare kowanne abu da musulunci yayi umarni akai.....baya shan giya.....baya zina.......baya kallace kallacen abubuwan haramun......hasalima azumin da addininku yace a dinga yi litinin da alhamis baya wuceshi.....abinda zai bada mamaki banda wannan uwar goyon nasa da uban goyonsa ba wanda yasan yanayin wannan azumin koda farouq makusancinsa......."
"Kana nufin yanzu mallakar da nakeso ayi masa.....da shiga tsakaninsa da iyayen goyonsa bazai yiwu ba kenan?" Ta dawo dashi zuwa ga ainihin amsar da takeso taji.
"Zaki iya samun biyan buqata.....zaki kuma iya samun faduwa......biyan buqatarki ya ta'allaqa da adadin sadaukarwar da zakiyi da kudaden da zaki ajiyewa shaqiqanmu don suyi miki yadda ya dace......amma fa....." Ya fada yana daga yatsa
"Tabashi abune da zai iya zuwa da hadari......mafi qarancin sakamako shine a gaza yin nasara a kansa......muddin rashin nasarar ta zarta haka kuwa.....dani da dukkan wani shaqiqi da mukayi aiki dashi zamu iya samun nakasa,harda shudewa daga rayuwa ma idan ta dauro,saboda haka......aikinki aikine me tsadar gaske " Yayi maganar yanayin muryarsa daga qarshe yana canzawa alamu dake nuna saukar mutanen boyen da yake aiki tare dasu a kansa.
Tsoro yadan shigeta kadan amma ta dake
"Kamar nawa zai kai?" Ta fada a dokance
"Kalli nan!" Taji an furta daga bakin mutumin amma da mabanbantan muryoyi marasa dadi da batasan mutum nawa bane suka hadu suke maganar.
Waiwayawa tayi tana duban inda ya daka,saiga lambobi a jere wanda data dubesu da kyau suka bayyana kansu a matsayin million goma.
Sosai adadin ya daketa,duk da tasan a qa'ida tana cikin arziqin data bawa wannan adadin baya amma kuma batakai ga samunsu ba zuwa yanzu. Ta waiwaya ta kalli hajja dake zaune tana kallon komai,don dokarsa shine me matsala dashi yake magana. Da idani ta mata tuni da tsarinsa,baya yanka kudi a nemi ragi.....daya daga cikin kusakuren da zaka iyayi wanda zai tunzurashi kenan.
Kamar wadda wuyanta ya qage ta maido dubanta gurin,saidai zuwa sannan lambobin da hasken da suka nuna mata yawan abinda zata biya din ya shafe daga wajen ba komai. Ta maida kallonta ga duqurqushin bokan da kamanninsa suka juye,saita gyada kanta
"Na karba na aminta"
"Karki qara minti daya a wajen nan......kizo da sadakin aikinki kuma nan da kwanaki uku kacal" Daga haka ya bace shi da dukkan sauran tarkacen dake wajen,sai gurin ya rage daga ita sai hajja din. Zumbur suka miqe kaman yadda ya umarta,suna riqe da hannun juna suka fara fitowa daga sarqaqiyar har suka cimma inda suka faka motarsu.
Sau biyu hajja tana juyawa tana kallon maamah wadda ta kafe kwaltar da driver ke zabga gudu akai. Tunda suka fito daga wajen bata ce komai ba,magana bata hadasu da kowa ba. Tun a dazun ta fahimci tayi nisa ne qwarai a tunani,kaman ta qyaleta amma sai ta kirayeta don tanaso taji ta bakinta
"Banji kince komai ba tunda muka fito?" Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke sannan ta dora idanunta akan na hajja din
"Daga yanayin ayyukansa,da kuma bayanansa kawai na gamsu cewa aikinsa me zafi ne......abinda kawai ya tsayemin a rai yanzu shine ta yadda wadannan kudaden zasu samu" Tayi maganar alamunta suna nuna lallai lallai a matse take da buqatar mafita
"Danki ne,dole ki bashi umarni yabi don babu wata uwa sama dake......idanma hakan bai yiwu ba,cikin kadarorinki ki saida wani abu.......ko kice masa wasu zaa yiwa wani abu da kudin da zarar yasa anyi abun ki saida abun kiyi zarafin gabanki". Ajiyar zuciya ta sauke ranta yana mugun baci
"Yanzu har takai idan ina da buqatar abu a wajen dana saidai nayi qarya ko na biyo ta wata hanyar?" Ta yiwa hajja tambayar.
"Biyan buqata ai yafi dogon buri,kome ya faru.....kuma kome kika saida,wuyarta aiki yayi yadda akeso......sai kin maida ninkin baninkin da bakisan adadinsa ba......sai kin karba kin gaji......saikin tara fiye da yadda kike buri......saikin zame musu tamkar abun bautarsu wajen yi miki biyayya.....a yanzun da zan kira auwal dake wata qasar,nace masa ya dawo nigeria yau yau inason ganinsa.......na rantse miki da Allah a qasar nan zai kwana,koda babu jirgi bazai kwana a gida ba saidai a airport.......saidai idan nice nace masa ya koma gida ya kwanta ya taso gobe......koda ya koma bashi da cikakken nutsuwa har sai gari ya waye ya kawo kansa gareni......bari yau zan nuna miki qarfin ikona ki gani da kanki" Ta fada tana fiddo wayarta daga jakarta.
Kai ta jinjina kawai tana dubanta,tana jin inama ace itace hajja?.....tana hasashen ranar da wannan damar zata samu a hannunta?.....tabbas saita sanya aminatu kuka da idanunta........sai ta sanya zuciyar aminatu da hamza sun buga da qasqancin da zasu gani daga yaran da su suka rainesu har suka zama abinda suka zama a yanzu
(Tabbas gaskiya ne da akace ka guji sharrin wanda ka kyautatawa.......me makon jin dadi kyakkyawan fata da kyakkyawan mu'amala ta shiga tsakaninsu da mutanen da suka maida mata 'ya'ya mutum.....amma ga nata salon sakamakon,Allah kayi mana tsari daga sharrin dukkan wani abu me sharri mutum ko aljan,me rai ko maras rai ameen ya hayyu ya qayyumu).
Bugu daya tak aka daga kiran da hajjan tayi,muryarsa ta fito tarwai yana gaidata. Cikin kulawa ta amsa masa sannan tace
"Kaga yahaya.......naje unguwa ne sai na sallami driver da xummar zan tuqo kaina na dawo gida......."
"Me yasa hajja?,ta yaya zakiyi tuqi da kanki?" Ya fada a tsananin firgice kaman wanda akace masa ta hallaka. Murmushin qasaita ta aje
"To ai yanzu ma gashi na kasa dawowa din da kaina duk kasala ta rufeni...."
"Bari na kira driver din ya dawo ya maidaki" Ya furta da hanzari
"Kaga dakata.....wanne irin driver?" Ta fada tana bata rai
"Yi haquri hajja,me kk so?" Ya sake fada a rikirkice
"Matarka nakeso ka turomin ita zata maidani......kace ta kirani na bata kwatancen inda nake yanzu haka ina jiranta......kada kuma ta batamin lokaci" Ta fada tana bata rai
"An gama" Ya fada zuciyarsa na rawa.
Ta rigashi ajiye wayar ta waiwaya tana kallon maamah cikin murmushi
"Kinsan matar da nace a kiramin?" Kai maamah ta girgiza tana shakkar yiwuwar wanzuwar umarmin da hajjan ta bada yanzu yanzu
"Matarsa ce......itace taso dagamin yatsa taso tayi fito na fito dani,a zatonta tana da malaman da xasuyi mata aiki fiye da nawa......tanaso ta mallaki yahaya ta mallakeni.....har na sanya ya saketa na sakashi ya dawo da ita don tazo taga iyakarta......taga iya mizanin nawa aikin.....don tazo