Showing 3001 words to 6000 words out of 44304 words

Chapter 2 - SULTHANA complete Hausa Novel

25 Jul 2025

1424

Yarone cikin Almajiran Baffa ya shigo cikin gidan dah Sallama Saida Ya Russuna Sannan yace
"Wai ana Sallama da......

*Ummy Abduol*✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: 💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
*SULTHANA*
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐💐💐

By *Ummy Abduol*

*Page 21 to 25*

"Wai ana Sallama da Hafsatu"
Dah mamaki Mama ta K'alli dan Aiken
"Dah Sassafen nan"
Tsaki Baffa yayi
"Ina Ruwanki, Kai jekace tana zuwa"
Hafsatu naji ta fito dasauri ta dire bokitin a Tsakar gida ta shige dak'i, A Gurguje ta shirya koh karyawa bata tsaya yi bah tayima Mama sallama Ta fice, Binta da K'allo Sulthana tai tareda girgiza kai dan Tasan bai wuce Ahmad Mayan matan nan..

Tsaye ta Sameshi a Kofar Gida sai k'ara kallan kayan jikinshi yak'e, da Fara'a ta k'arasa inda Yak'e tace
"Barka da Zuwa Habibyna"
Dan Murmushi yayi yana Cigaba da K'allanta
"Haba Hafsy nah, nifah na Lura bah sona kike bah"
Waigawa Zaure tai Sukayi ido hudu da Sulthana dake Zaune sai Kallansu tak'e, Hararanta tai Sannan ta juyo ta K'alleshi
"Mubar nan dan Gadon Gulma da munafinci na Sauraronmu"
Baice komai bah suka jera suna Tafe suna Hira har kusa da Makarantan su
"Kaima Kasan Ina Sanka Habiby, Bani dah Tamkar kah duk duniyan nan"
Murmushi yayi tareda shafa sumar kanshi dake Cike dam Bakyan Gani
"Banga Alamar Haka bah Hafsy, Dah kina sona dah kin bini Partyn dana gaya miki a Birni, Anma kin ki"
Marairaice Fuska tai Tana K'allanshi K'asa kasa
"Bah Laifi nah Baneh habiby kai kanka Kasan Halin Baffa, Mai zai hana tho ka turo gidanmu ai mana aure kaga Shiknan sai ka kaini Birni mu rinka zuwa Partyn tare koh"

Gintse dariya yayi ya gyada kai kawai
"Kaji" cewar Hafsatu data Marairaice
"Naji Hafsy but inaso na sauyaki, Ki waye ki zama yar birni Sosai, Ki koma sah kaya irin na yan birni ki fita daban cikin matan Kauyen nan. Bt Kudi neh yamin Cikas, Anma karki damu danaje birni na dawo komai zai daidaita"
murmushi jin dadi Hafsatu tai tana cigaba da K'allanshi, Harga Allah tana Matukar san Ahmad, musamman yanda ya fita daban Cikin Mazan Kauyen, Gashi dan Gayu mai zuwa birni, Gashi Kyakyawa san kowa kin Wanda Ya rasa..

Bell din makaranta Aka kada ta K'alleshi tana Yar Murnushi
"Habiby Mu hadu Anjima da Magriba a dandali"
Bata jira mai zaice bah ta shiga makaranta dasauri. Murmushin cin nasara yayi a ranshi Fadi yak'e
"Keh kina tunanin ni Ahmad Aurenki zanyi, Baridai na Samu abinda nake nema bak'i kara ganina a garin nan"..

Yauma kamar jiya Baffa dakansh ya diban mata Gyadan ta Dafa ta Fito Talla, Mutane sai kallanta suke da Mamaki dan basu taba ganin yayan Mallan jamilu da Talla bah, Bakin Kasuwa taje Yauma Anma Tai Rashin Sa'a Baifi Gwangwani hudu aka siya bah Har Gaf da Magriba, Ganin Dare na Neman Yi yasa ta dawo Gida cikeda Fargaban Abinda Baffa Zaiyi mata, Bata sameshi a gida bah Yana Wajan Almajiransa, a Kofar dakinshi ta aje Gyadar ta Shiga aikinta na Yanma..

Sai Bayan Isha'i ya Shigo Gidan dasauri, Gyadan da ta ajemai a kofar dak'i ya K'alla yayi kwafa ya Shiga Cikin Daki, Baifi Minti Goma Bah Ya Fito Dasauri Ya Shiga Dakin Mama
"Saratu! Saratu!!"
Mama data Sallame Sallah ta K'alleshi da Mamaki
"Lapia Mallan Kake Kwalamin Kira haka??"
Kin Shiga dakina neh kin dauki Kudi"
Kallanshi tai da Alamar Mamaki, "Ban ganeh Kudi bah, na Taba daukan kudinka ban fadama bah"
Bai kara cewa komai bah Ya fita daga Dak'in, Sulthana ya soma Kwalama Kira, Ta Shigo Tsakar Gidan Dasauri tareda Rusunawa
"Na'am Baffa"
Ido Ya zazzaro yana Kallanta
"Kudina Zaki bani da Kika dauka"
Mama ta Kalla dasauri sannan ta maida dubanta ga Baffan dake Tsafe ya Kafeta da Ido
"Wallahi Baffa ban dau Maka Kudi bah"
Ameenatu Dake Dak'i ita da K'awarta habiba ta fito dasauri
"Baffa Lapia"
Kudi na Ajiye a daki ko kin Gani?"
Girgiza kai tai dasauri
"Aa banga kudi bah"
Ina Hafsatu? Cewar Mama
Dan Jim Ameenatu tai Sannan Tace
"Tunda Akai Magriba ta fita Bata Dawo bah"

Dak'i Baffa Ya shiga Chan sai Gashi da Dorina katuwa mai Baki dayawa, Mama ta Kalleshi
"Meh Zakayi Mallan"
Keh! Nan da nan Jikin Sulthana yadau Rawa
"Wallahi Baffa Bandau maka kudi bah, Dan Allah kai Hakuri Karka dakeni"
Daka Mata Tsawa Yayi
"Ki Fito Min da Kudina, Oho! Wato dan nace bazan saki a makaranta bah shine kika satan min kudi dan ki koma makaranta koh"
Kuka sosai Sulthana take
"Wallahi Baffa ban dau maka kudi bah, Dan Allah Karka Dakeni."
Hakuri Ameenatu ta soma bah Baffa anma ko Kallanta Beyi bah, Bulalan dake Hannunshi ya soma dukanta Dashi ta koina, ihu Sulthana take Tana Rokonshi Anma ina. Rike bulalan Mama tai a Fusace
"Haba Mallan, Wannan Wane irin rashin imani neh, wanne tabbaci kake dashi na cewa ita tadau maka kudi"
Huci sosai Baffa Yake
"Sakar min Bulalan nan Saratu, Yayana basa Sata, Saida Wannan Yar Iskan Yarinyan ki sakar min Bulala nace"
Bazan Saki bah, mallan Kaji Tsoron Allah"
Wani Tsawa ya saki tareda Fizge bulalan Daga Hannun Mama, Rusunawa Ameenatu tai tana Kuka tareda Rokon Baffa, Anma Ko Kallanta Beyi bah, Saida Ya duketa San Ranshi Sannan Ya Kyaleta. Kuka Sosai Sulthana take, Duk Jikinta ya Farfashe. Dakyar ta Mike Tsaye, ya Kalleta a Harzuk'e Ficemin Daga Gida Karna K'ara Ganinki a Gidan nan..

Kuka Sosai ta k'ara Fashewa dashi tana bashi Hakuri, Binta yayi da Bulalan ta Falla a guje tabar Gidan ya koma Ciki ya rufe Kofa, Yana Shiga Yaga Mama ta fito Sanye da Hijabi, Ya kalleta da Mamaki, Ina Zaki?
"Gaskiya Mallan bazan cigaba da zama a gidan nan kana Azabtar da Yarinyan nan bah Na gaji Gaskiya"
Kafada Ya daga Tareda Cewa
"Idan Har kika fita kofar gidan nan tho ki sani a bakin Aurenki"
Ameenatu da har lokacin tak'e Tsugunne a Kasa tana Kuka ta dago ta Kalleshi da Mamaki...

*Ummy Abduol*✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: 💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
*SULTHANA*
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐💐💐

By *Ummy Abduol*

*Page 26 to 30*

Ameenatu da har lokacin tak'e tsugunne a kasa tana kuka ta dago ta kalleshi da mamaki
"Mallan Yanzu dah bakinka kake Fadin irin wannan maganan" cewar Mama Tsaki yayi batare da yace komai bah yayi shigewarshi dak'i
Dosar kofan fita Mama tai Ameenatu ta mik'e dasauri ta kamota tana cigaba da kuka
"Mama dan Allah karki tafi, kiyi Hakuri"
Hawaye ne ya gangaro a idon mama

"Na gaji da zama ana Azabtar da Yarinya ina kallo banida halin magana, Duk inda naji sai aita nunani ana gulmana mutane sai suyita tunanin ni nake wahalar da Sulthana"
Hawayen idonta Ameenatu ta Share
"Mama karki manta idan har kika fita kin saku, Dan Allah Mama karki fita kiyi Hakuri, Idan Kika fita Zamu Shiga wani hali"
Murmushin takaici Mama tai
"Ameenatu duba ki gani yanda ya Kori yarinyan nan da Daren nan, Ina Yake tunanin Zata? Yanda Kauyen nan Yakeda Hatsari kuma gata K'arama"
Shiru Ameenatu Tai nadan wani lokaci.

Sallaman Hafsatu sukaji ta shigo Gidan Rik'e da Bak'ar leda ganinsu Mama a tsaitsaye Yasa Ta K'araso kusa dasu
"Mama lapia meya Faru?"
Ameenatu ce ta shiga zaiyana mata duk abinda ya faru, Dan Murmushi tai tareda Girgiza Kai Sannan ta Kalli Mama
"Tho Mama mu ina ruwanmu, tunda ya koreta ai shiknan mun munma huta wallahi"
Tsaki Ameenatu taja
"Hafsatu kinada Matsala, Bansan Keh inda kikasa gaba a rayuwarki bah"
Turo baki tai ta kauda kai..

Mama ta dafa Kafadar Ameenatu
"Ameenatu kuje ku nemo Sulthana dan Allah, Kunga Dare neh Akwai hatsari"
Kara turo baki hafsatu tai tana Gungunai
"Ni Mama na Gaji Wallahi"
Tsawa mama ta daka Mata, Hijab Ameenatu ta koma ta dauko suka fito itada Kawarta Habiba suka Fita Hafsatu na Binsu a Baya, Sallama Habiba tama Ameenatu ta wuce gida, Ameenatu ta juya ta Kalli Hafsatu dake tafiya kamar wacce kwai ya fashema a ciki
"Haba Hafsatu ki dago kafa Mana Wai meye Haka"

Dogon Tsaki Hafsatu taja nifa Gaskiya Ya Ameenatu kun Takura min, Allah badan Mama ta matsaba bah Abinda zai kara fito dani da Dadaren nan. Girgiza kai Kawai Ameenatu tai ta cigaba da Tafiya tana haske hasken Hanya da Torch light..

Sulthana kuwa tana Fitowa Gudu kawai take batareda tasan inda ta nufa bah, Saida tai mai isarsa Sannan ta Samu guri ta zauna Tana kuka sosai mai Sauti, Kuka take kamar ranta zai Fita
"Umma meyasa kika tafi kika barni? Meyasa baki bari mun tafi tare bah. Ina sanki Umma, ina Kewanki"
Kuka ta cigaba dayi gwanin ban tausayi, duk ilahirin Jikinta zugi yake mata bin jikinta tai da K'allo taga duk Baffa ya fafasa mata jiki. Nan da nan jikinta yayi zafi, Idanunta suka fara Lumshewa. Kangon Ginin Kasan dak'e Gefenta Ta mik'e dakyar tana Ganin Jiri ta k'arasa ta Shiga Cikin Kangon ta zauna, Jin Jirin tai na K'aruwa ta lumshe ido da k'arfi ta Bude tareda Girgiza kai. A hankali ta Sulale a Wajan..

Bah Indah su Ameenatu basu jeh bah, Tun daga Gidan Kawayen Sulthana Har Wuraren dah suk'e zaton Zata Iya boyema, Anma bata bah Alamarta. Hankalin Ameenatu Yakai Kololuwa Wajan Tashi, Ganin Dare Yayi sosai Yasa Suka Koma Gida. A tsakar gida Suka samu Mama sai kaiwa da komowa take, Tana ganinsu ta K'araso dasauri
"Yaya kun Ganta?"
Kasa magana Ameenatu tai, Hafsatu ce ta Yatsine Fuska
"Duk inda Muke tunanin Za'a sameta munje bamu ganta bah"
Bata jirah mai Mama zatace bah ta Wuce dakinsu..

Kuka Ameenatu tahau yi a hankali Kanta a K'asa, Mama ta dafata itama hankali tashe,
"Kiyi Hakuri Ameenatu, Insha Allahu Za'a ganta jeki kwanta kinji"
Kai kawai tai k'arfin Halin Dagawa ta Nufi dakinsu jiki a Sanyaye...

Hasken daya Haska mata Fuska neh Yasa ta Bude ido dak'ar, Ganin Gari ya Waye Tangaran da Alamar Rana mah ta Farayi Yasa ta Mik'e Zaune Dakyar tana Yatsine Fuska. Wanne Irin Mugun Ciwo Kanta keh mata da duk ilahirin Jikinta, dakyar ta mik'e tsaye Ganin Har yanzu tana Jin Jiri Yasa ta koma ta Zauna Tana Hawaye a Hankali. Abubuwan da Suka Faru jiya suka Dawo mata, Kuka ta Fara Sosai Tareda Daura Hannayenta Biyu akai
"Umma Ki Dawo dan Allah, Ina Sanki meyasa zaki tafi ki Barni, Wallahi Baffa naso ya Kasheni. Dan Allah Umma ki dawo mu zauna tare, Kin Barni Cikin..."
Kukan neh Yaci Karfinta, Sulalewa tai ta kwanta Tana Shafa Ciyayin Dake Kasan wajan tana Cigaba da Kuka..

Ta dade a haka Sannan Ta daure ta Mik'e ta Fito daga kangon Tana tafiya Saboda Yanda Takejin Jikinta yana mata Ciwo. Duk inda Ta Wuce K'allanta ake, Sai Yanzu ta Tuna Koh Dan kwalli babu a kanta. Runtse ido tai wasu Sabbin Hawaye suka gangaro Mata, Direct Gidansu Sadiya Ta Wuce dan Duk Kauyen nan ita kadaice Tasan Zata iya Taimaka mata da Wani abun...

*Ummy Abduol*✍🏻
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: 💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
*SULTHANA*
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐💐💐

By *Ummy Abduol*

*Page 31 to 35*

_kuyi min afuwa jina shiru da kukai, Hakan ya faru neh bisa Rashin Lapia danai. Anma Alhamdulillah naji sauqi, Nagode Sosai da Kulawarku a Kaina_


Dis page x 4 uh besty *Ayoosh Gidado Yar'adua "My Gidos"*

Direct Gidansu Sadiya ta wuce dan duk kauyen nan ita kadai tasan zata iya taimaka mata da wani abun. Dakyar ta karasa gidan ta Shiga da Sallama, A Tsakar gida ta Samu Sadiya tanayi ma Mamanta Sallama Zata tafi makaranta.
Juyowa tai ta K'alleta da Mamaki
"Sulthana! Daga ina kike? Jiya su Yaya Ameenatu nata nemanki"
Waje ta samu ta zauna a tsakar gidan tareda tafe kai, Dasauri Sadiya ta karaso inda take
"Mama! Mama!! Fito kiga Sulthana"
Mama da Baba suka fito a Tare dasauri,
"Lapia Sulthana meke Faruwa" cewar Mama
Kuka ta Fashe dashi Kanta a Kasa, Baban Sadiya neh ya K'alleta Cikeda tausaya wah
"Sulthana, Yi Magana Mana"
Kasa magana tai sai kukan data K'ara Fashewa dashi, Mama ta K'alli Baba tana nunamai Sulthana Hankali Tashe
"Mallan Kalli jikin Yarinyan nan, Duk yanda akai Duka Akai mata"
Sai a Sannan Baba ya lura da Raunukan dake Jikinta.

Girgiza kai yayi
"Hajjo dau Yarinyan nan ki kaita Ciki, Taci abinci tai wanka. Idan ta huta sai muji Koma menene"
Rungumeta Sadiya tai itama tana Kukan
"Kiyi Hakuri Sulthana, Mallan meh koh?"
Kasa cewa komai Tai sai kanta kawai tada Gyada. Da taimakon Sadiya da Mama ta Mik'e Mama ta kaita Dak'inta Ta zaunar da Ita, Dumamen tuwon dayaji man Shanu Mama ta kawo mata
"Sulthana ci abinci nasan Bakici Komai bah"
Kallan Abincin tai Sannan ta maida dubanta ga Mama
"Dagaske inci"
Gyada mata kai Mama tai Cikeda tausayawa wah, Hannu tasa Cikin Abincin ta soma ci tana Lumshe ido, Ganin Yanda takecin Abincin Hannu baka Hannu Kwarya Yasa Hawaye ya Gangaro ma Mama, Dasauri ta Mik'e tabar dakin Tana sharan Kwalla..

A tsakar Gida tai Kicibus da Sadiya tanata Safa da Marwa
"Keh Sadiya, Makarantan fah"
Turo baki tai tareda Kauda Kai
"Ni Mama bazanje makaranta bah, Kinga fah Sulthana batada lapia"
Sakin Baki Mama tai da Mamaki, A Ranta Fadi take
Lallai Sadiya Nasan Sulthana. Batace Komai bah Sai Girgiza kai datai tabar wajan, Sadiya na Ganin Tabar wajan ta Shiga Dakin Dah Sultanan keh Ciki. Zaune ata sameta Tana Cin Abinci, Kusa da Ita ta Zauna Tana Kallanta

"Sulthana Baffa neh koh?"
Nan da Nan hawaye suka cika Idonta, Sheshekan kuka ta Fara kanta a kasa
Matsowa kusa da Ita Sadiya tai ta Dafata
"Kiyi Hakuri kinji, Zancema Baba ya dawo dake nan gidan mucigaba da zama tare muna zuwa makaranta"

Dagowa Sulthana tai Da Fara'a
"Dagaske Sadiya"
Kai Sadiya ta Gyada itama da Fara'a kwance a Fuskanta.
Saida ta Cinye Tuwon Tas Sannan ta Dago ta Kalli Sadiya dake zaune kusa da ita
"Sadiya Kaina na Ciwo tun Jiya"
Dasauri Sadiya ta mik'e batare datace komai bah ta fita daga dakin, Chan Sai gata dauke da Wani jikon Magani
"Gashi Mama tace Kisha, Sai kizo kiyi wanka"

Jim tai tana K'allan Sadiya, A Sanyaye Tasa Hannu ta K'arba Maganin Tasa Sannan Ta Mik'e, Zani Sadiya ta mik'a mata ta Amsa sannan tabar dakin. Kayan jikinta ta cire ta daura zanin Sannan ta Fito, A tsakar Gida tasamu Mama Bakin Murhu Tana Iza Wuta
"Sulthana kin Fito?"
Kai Ta gyada kanta a kasa
Murmushi Mama tai
"Maza kije ga Ruwa chan a kewaye kiyi Wanka"
Tho Tace ta Nufi Bandakin Idonta Cike da kwala, Zama Tai a Bayin Ta Fashe da Kuka a Hankali, Kuka take Sosai mara Sauti
"Umma meyasa zaki tafi ki barni, Dan Allah ki dawo nima kirinka sona kamar yanda Maman Sadiya ke santa"
Jin Muryan Mama a Wajan Yasa tai Saurin Goge hawayenta ta Fara wankan..

Tana Gamawa ta Fito tasamu Mama ta fito mata da Kayan da Zatasa, Saida ta kimtsa Sannan Baba Ya shigo dakin shida Mama, Tana Ganinshi ta Zame ta Zauna a Kasa. Kallanta yayi cikeda kulawa
"Sulthana fadamin meya Faru"
Hawaye neh ya Gangaro a Idonta, Duk abinda ya faru ta Sanarmusu.

Shiru Dukai Mama ta Kalli Baba
"Mallan Abinda Mallan Jamilu yake Baya Kyautawa, Sai kace Bashi Ya Haifeta bah, Niko a Mafarki Bantaba Ganin Irin Wannan bah, Abinda yakamata kishiyar mahaifiyarta tayi Sai kuma a Sameshi Wajanshi"
Shiru Baba yayi na Wasu mintina, Chan Ya dago Ya Kalli Sulthana
"Kiyi Hakuri Sulthana, A Matsayina na Aminin Mahaifinki Zanyi kokari Naga nayi mai magana ki koma Makaranta Sannan Ya daina Daura miki Talla"
Turo Baki Sulthana tai Idonta Ya kawo Kwalla
"Baba Ni bazan koma bah, ni Anan zan Zauna"
Mama neh Tai Saurin Cewa
"Mallan idan shi Mallan Jamilun Baya Santa Akwai Masu so dayawa, Wallahi da Zai amince ni Zan Iya rik'e Sulthana."
Murmushin Takaici Yayi tareda Mik'ewa
"Hmm Hajjo knan"

Ummy Abduol✍🏻
💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
*SULTHANA*
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐💐💐

By *Ummy Abduol*

*Page 36 to 40*

Murmushin takaici Yayi tareda mik'ewa
"Hmm Hajjo Knan"
Bai jirah mai Mama zatace bah yabar Gidan...

Harya Fita ya dawo
"Sulthana dauko Hijabinki Muje"
Narai Narai da Ido tai Tana K'allan Mama
"Mama Dan Allah Kada mu Maidani ni banasan Gidan Baffa, Kullum Dukana Yakeyi"
Sadiya ce Ta Shigo dakin Dasauri Tareda Durkusawa
"Dan Allah Baba Kada a Maida Sulthana a Batta mu Rinka zuwa makaranta"

Hade Rai Baba yayi ya Kalli Mama
"Miko mata hijabi mutafi"
Jiki a Sanyaye Mama ta mikama Sulthana Hijabin Sadiya dak'e ratayi jikin Gado mai runfan dake dakin. Karba Sulthana tai tana kuka sosai, Saida tasa Sannan suka fito daga dakin, Kuka sosai Sadiya take tana Rokon Baba, Baiko Saurareta bah ya kama Hannun Sulthana suka bar Gidan..

Gidan Mallan Suka nufa, A Runfan da Almajiranshi Suke Baba ya hangoshi, Juyawa yayi ya K'alli Sulthana daketa Sharan Kwalla
"Tsaya a nan ina zuwa"
Tho Tace Ya nufi Runfan Mallan da Sallama
"Hade Rai Mallan Yayi Ganin Tareda Sulthana Suke"
Baba ya Mik'a ma Mallan Hannu suka Gaisa
"Mallan Jamilu Wurinka Nazo" cewar Baban Sadiya
"Tho Mallan Sani ina Sauraronka"
Jim Baban Sadiya yayi tareda Girgiza Kai

"Mallan Jamliu a matsayina na amininka mai kuma baka shawara, kuma kana Dauka. Yauma nazo da Nasihar nan da nasha maka Akan Y'arka Sulthana"
Tsaki Mallan Yaja Tareda Kauda Fuska
"Mallan Sani Na fada maka ka daina sa bakinka a Wannan maganar dan Sam bazan fasa abinda nai niyya bah"

Murmushin Takaici Baban Sadiya yayi Kanshi a Kasa
"Mallan Jamilu Knan, Nasan kasha fadamin haka Anma a matsayina na Aminin kah ya kyautu na Baka shawara ka dauka. Dubah kaga yanda kaima Yarinyan nan duka, Haba Mallan Sulthana Fah Amana ce a Gurinka"
Shiru Mallan Jamilu Yayi yana Cika yana Batsewa
"Ina mai rokon arzikin Kai hakuri yarinyan nan ta koma gida, saboda bai kamata Yarinya karama kamar Sulthana na Gararanba a Gari bah. Dan Allah kai min Wannan Alfarman"
Guntun Tsaki Mallan Jamilu yaja Sannan Ya Kalli Baban Sadiya
"Taci Darajan Kah, Anma dah bah haka bah bazata zauna min a gida bah"
Murmushi Baban Sadiya yayi ya Mik'a mai Hannu sukai Musabaha Sannan sukai Sallama..

Inda Sulthana take tsaye Baban Sadiya ya Nufa
"Sulthana Maza Shiga Gida Baffanku Ya hakura"
Nan da nan Fuskanta ya Chanza
"Dan Allah Baba ka tafi dani gidanka ni banasan Gidan Baffa dukana Yakeyi shida Yaya Hafsatu"
Jim Baban Sadiya yayi na Dan Lokaci, Shi Kanshi Yana Tausaya mata Yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login