Showing 33001 words to 36000 words out of 44304 words

Chapter 12 - SULTHANA complete Hausa Novel

25 Jul 2025

1432

a guje. Fareed ta wuce dake falo zaune yana kallan news ta fita tsakar gidan, dai dai lokacinda Ayoush ta fito d'aga motansu ta fara knocking gate din gidan..

Sulthana na bud'ewa suka rungume juna suna dariya, Ayoush ce ta fara cewa

"I missed uh besty"

Dariya Sulthana tayi tace

"I miss uh 2"

Hannun Ayoush ta kama suka shiga cikin gidan, a falo suka samu Fareed yana k'allo Ayoush tad'an rusunna ta gaidashi ya amsa fuska a sake Sannan suka shiga dakin Sulthana. Ciye ciye sukai kala kala, Sannan Suk'a barke da hira.. Ayoush ta d'ade a gidansu Sulthana, sunyi exchanging phone number Ayoush ta tafi cikeda kewan k'awar nata da kuma mamakin ganin bah kowa a gidan sai Fareed da Sulthana..


A kauye kuwa ciwon Mallan neh ya tashi gadan gadan, Hafsatu ta fito a guje ta nufi gidan Mallan sani aminin Baffa tana kuka sosai. A tsakar gida ta sameshi yana cin abincin rana, ta k'arasa inda yake zaune ta tsugunna tana sheshekan kuka

"Baba dan Allah kazo ciwon Baffa neh ya tashi"

Maman sadiya dake gefe ta tab'e baki tareda kauda kai dan ita ta tsani Baffa saboda wulakancin da yayima Sulthana. Rufe abincin Baba yayi ya mik'e ya wankr hannu yana k'okarin sa takalmi

Mama tace

"Ina zaka Mallan baka gama cin abinci bah?"

Yad'an waigo yana cewa

"Barinje na gani yanzu zan dawo"

Batace komai bah anma ranta a b'ace yake, tare suka fito da Hafsatu tana tafe yana binta a baya har gidan...

Ummy Abduol✍🏻

💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
*SULTHANA*
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐💐💐

By *Ummy Abduol*


*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*



*Page 176 to 180*


Na sadaukar da wannan page ga parrots din Deejatou novels grp *Deejatou, Fateema Ashemi, Meela adeel, Nafeesah Hasheer n Zee naseer*

Batace komai bah anma ranta a b'ace yake, tare suka fito da Hafsatu tana tafe yana binta a baya har gidan. Ameenatu ce a tsakar gidan tsugunne tanata kuka ganin Mallan sani yasa ta mik'e dasauri ta k'araso wajanshi tana nunamai d'akin da Baffa ke ciki. Dakin ya shiga ya tarar dashi kwance yana tari sosai idanunshi sun kakkafe, gefenshi Mamace itama kukan take..

Addu'a mallan sani ya soma tofama Baffa shima hankalinshi tashe. Ameenatu da Hafsatu na tsaye daga bak'in kofan cirko cirko suna hawaye sukaji Sallama a k'ofar gida, hafsatu ce ta fita. Wani mutumi ta gani tsaye sanye da Bak'ar jallabiya yana rik'e da qurani a hannunshi na dama, dayan hannun kuma ya rataya jakar fata..

Gaidashi tayi ya amsa yana cewa

"Naji labarin tashin lafiyan Mai gidan nan shine nazo na gwada sa'ata da wani magani ko Allah zaisa a dace"

Shigo kawai tace mai tamai jagora har cikin d'akin, har yanzu Tarin yake idanunshi a kakkafe. Zabura Mutumin yayi yana k'allan Baffa da mamaki, jikinshi ne yayi sanyi ya k'alli Mama yace wannan bah komai baneh face jinnu kuma insha Allahu zai samu lapia..

Mallan sani ya k'alla yace

"Ka rike min shi namai karatu insha Allahu za'a dace"

Rik'eshi Mallan sani yayi shi kuma mutumin ya soma karatu, nan da nan Mallan jamilu ya soma ihu tana bank'are bank'are tareda buge buge, Mama ita ta rik'eshi ana cigaba da mai karatun. Ganin su biyu bazasu iyaba yasa Mama ta kwalama su Ameenatu kira, duk suka taru suka rik'eshi Mutumin na cigaba da karatu..

Chan Mallan ya soma magana cikin wata murya da batasa bah

"Kayi hakuri karka konamu, zamu fita daga jikinshi"

Mutum ya tsagaita yace

"Meyasa kuka shiga jikin bawan Allahn nan kuna Azabtar dashi"

Wata murya ce ta soma magana tana cewa

"Mutumin nan bah Allah a ranshi, yana wulakanta ma d'an sarkin mu wacce yakeso shine mukazo mud'au fansa shima ya d'andana"

Mutumin yace

"Wacecce wace d'an sarkinki keso"

Wata muryan tace

"Sarauniya Sulthana"

Duka y'an dakin suk'a kwalalo ido suna kallan juna. Cigaba da magana sukai

"Kayi hakuri karka k'onamu zamu fita"

Mallamin yace

"Ku fita daga jikinshi kuma ta hanci nakeso ku fita. Karku k'ara dawowa idan har kuka dawo saina k'onaku"

Yana gama fadi Baffa yayi Atishawa sau uku sannan ya sulalle Barci mai nauyi ya daukeshi harda munshari. Mallamin ya share zufan daya k'aryo mai yace

"Alhamdulillah sun fita yanzu zan baku magunguna da hayaki da za'a rinka mai da kuma wasu Adduo'i"

Godiya su Mama suka hau mai baice komai bah ya bud'e jakar fatanshi ya ciro wasu magunguna ya mik'ama Mama tareda fada mata duk yanda ake anfani dasu sannan ya mik'a mata wata takarda wacce take kunshe da Adduo'i..

Godiya sukamai sosai baice komai bah ya mik'e hawaye suka gangaro mai a fuska. Mallan sani ya k'alleshi da Mamaki

"Lapia mallan meke faruwa?"

Hawayen idonshi ya share yace

"Idan yaji sauk'i inasan Magana dashi, akwai wani magana mai mahinmanci danakeso mu tattauna"

K'allan kallo suka hau yi yan dakin, mallamin ya musu Sallama ya bar gidan yana cigaba da hawaye...

Saura sati biyu su Sulthana su koma makaranta su shiga Ss1, yau Tana falo zaune tana k'allo lokacin Fareed na Asibiti. Masroor ne ya fado mata a rai ta runtse ido ta bud'e hawaye suka gangaro mata muryanta na rawa tace

"I miss uh ya Masroor"

Wayanta ne ya soma ringing ko ba'a fada mataba tasan Besty ce ta d'auka da fara'a tace

"Besty ya dai yau saura two weeks mu koma skul muma mu zama daga cikin seniors din nan"

D'an dariya Ayoush tai

"Gaskiya fah, kinsan meyasa na kiraki?"

Kai Sulthana ta girgiza sannan tace

"Aa"

Ayoush ta cigaba da magana tana cewa

"Inaso ne ki rakani muje wajan wata friend dita"

D'an jim Sulthana tai sannan tace

"Saidai ki tambayi ya Fareed anjima idan ya dawo i will flash uh sai ki kira na baki shi"

Ayoush cikeda jin dadi tace

"Ai indai ya Fareed ne banida matsala dashi"

Hira sukai k'adan daga bisani sukai Sallama. Fareed bai dawo gidan bah sai wuraren k'arfe tara na dare dan saida ya biya ya gaida Masroor dan bashi da lapia sosai...

A falo ya tarar da ita ta cika tayi fam. Yana k'allanta ya fashe da dariya hakan yasa ta k'ara kullewa ta fashe da kuka ta mik'e ta shiga daki tana cigaba da kukan, mik'ewa yayi yabi bayanta zuwa dakin, zaune ya sameta kan gado tana sheshekan kuka. Zama yayi kusada ita ya kamo hannunta ya hada da nashi cikin muryanshi mai sanyi yace

"Queen kin cika rigima, me kuma ya faru?"

Turo baki tayi ta shagwabe fuska tace

"Bah kai baneh ka fita tun safe sai yanzu ka dawo bah kuma ka barni inata jin tsoro"

Murmushi yayi har saida fararren haqoranshi suka fito yace

"I'm sorry swthrt kiyi hakuri patients ne sukamin yawa kuma na biya na gaida wani friend dina neh bashida lapia."

Gabanta ne ya fadi tad'an dago tace

"Allah ya bashi lapia"

Ameen yace sannan ya mike yana cewa

"Kin hakura?"

Kai ta gyada tana murmushin yak'e dan tunda yace abokinshi bashida lapia taji jikinta yayi sanyi ga kuma faduwar da gabanta yakeyi..

Cikinshi ya shafa yace

"I'm hungry"

Kan tai magana wayanta yad'au ringing, batareda bata lokaci bah ta d'auka ta kara a kunne sannan ta mik'a mai tace

"Besty ce zatama magana"

Amsa yayi ita kuma ta fice daga dakin a sanyaye. Tana cikin zubamai abincin ya k'araso ya zauna kan dinning din yana k'allanta

"Wato abinda kuka shirya knan koh?"

Turo baki tayo ta kauda kai. Ajiyan xuciya ya sauke yace

"Shiknan Allah ya kaimu goben Lapia, n na fada mata karku dad'e"

Murmushi tamai tareda godiya ta mik'a mai abincinshi suka cigaba da hira..


Washe gari wuraren k'arfe sha biyu na rana Sulthana ta gama shirinta tsaf, yau batasan meyasa bah bugun zuciyarta yafi na jiya. Falo ta zauna tana jiran wayan besty, batafi minti biyar da zama bah kiran besty ya shigo wayan. Ta mik'e dasauri ta rufe gidan ta fito waje, drivern ta gaishar sannan ta shiga motan suka bar kofar gidan

Sunyi nisa Ayoush ta juyo ta kalli Sulthana tana murmushi

"Kin t'aba shiga government house?"

Kai Sulthana ta girgiza, Ayoush tace

"Chan zamu"

Zaro ido Sulthana tai da mamaki

"Wah kike dashi a government house? Tho ai ma baza'a barmu mu shiga bah"

D'an dariya Ayoush tayi k'asa k'asa tace

"Bakiga motan da muke ciki bah? Na government neh so bah wani bincike zamu shiga, tho bakima sani bah y'ar governor din ce k'awata tare mukai school. Kuma Maminta k'awar mum dita neh"

Gyada kai Sulthana take da mamaki, dai dai lokacin da suk'a karaso gidan gwamnatin. Booth dinsu aka duba sannan aka bari suka shiga, tafiya sukayi mai nisa gada gate din gidan. Sulthana ko sai raba idanu take tana k'allan cikin gidan cikeda sha'awa, wani dad'i ke ratsa ta yau gata a gidan gwamna. A d'ayan bangaren bugun zuciyarta ne ya tsananta...

A bakin wani d'ank'areren gini sukai parking, Ayoush ta bud'e marfin kofan motan ta fito, itama Sulthana ta fito tana cigaba da k'arema Gidan kallo. Hannunta Ayoush ta rik'e tana mata magana a hankali

"Ki daina k'alle kallen nan kada a raina mu"

Nan da nan ko Sulthana ta d'aure, Ayoush taja hannunta suk'a nufi wani k'ofa dake gefensu. Bodyguards neh a wajan murd'adu bak'ake, hannu Ayoush tasa a jaka ta ciro wani i.d ta nuna musu, a take suka bud'e mata kofa taja hannun Sulthana da jikinta keta rawa ganin bodyguards din..

Tangamemen Falo neh mai cik'e da kayan Alatu, wata maid ce ta fito dasauri tana musu Sannu da zuwa tareda tambayanta wanda tazo gani. Noor tace atakaice, maid din tadau wayan dake falon ta soma kira, saida ta gama Sannan ta k'allesu tace

"Bata nan taje Shopping"

Ayoush ta shafa goshinta

"Oush!"

Ta k'alli sulthana wacce ta shagala da k'allan Hadad'en Falon tace

"Gashi banida numbernta I loose her contact"

Sai a sannan Sulthana ta k'alleta tace

"Mud'an jirata idan bata dawo bah sai mu tafi"

Maid din najin haka tace

"Uh can come in"

Tafe take suna binta a baya har zuwa wani had'adden falo mai kyawun gaske. Sakin Baki Sulthana tai tana k'allan Falon, Ayoush ta zungureta tana kyafta mata ido. Nan da nan saita kanta...

Waya Ayoush ta d'auka ta soma kiran mum dinta tana d'auka tace

"Mum Noor batanan wai taje Shopping, kuma kinga banga Mami bah. D'an Allah kid'an kirata a waya dan ni banasan rainin wayan Maids din nan"

Tana gama wayan ta kashe ta kalli Sulthana fuska bah Annuri,

"Zakisa a raina mu wallahi, sai kalle kalle kikeyi"

Murmushi Sulthana tai ta duk'ar da kanta k'asa. Wata Maid ce ta shigo tace

"Follow me"

A tare suk'a mik'e suna biye da ita har zuwa wani falon, shima falon ya tsaru sosai har yafi sauran da suka baro. Wuri maid din ta nuna musu suka zazzauna, chan sai ga wata ta kawo musu kayan motsa baki ta fita..

Sunkai minti sha biyar a falon a zaune sai ga Mami ta shigo falon da sallama sanye cikin kaya na Alfarma, Gaban Sulthana ya yanke ya fadi ta k'asa dagowa ta kalli Mami. Ayoush tad'an rusunna ta gaida Mami, Itama Sulthana ta Rusunna kanta a k'asa ta gaidata. Amsawa Mami tai Fuska a sake tareda tambayanta Mutan gidan, Ayoush ta amsa da Ameen..

Tunda Mami ta shiga Hankalinta na kan Sulthana haka kawai yarinyan taji ta burgeta, ta kalli Ayoush tace

"Sai kuma gashi bata nan taje Shopping kuma kindai san Halinta idan ta fita"

Murmushi Ayoush tai

"Eh haka aka fada mana, tafiya zamuyi yanzu bt zamu dawo wata rana. Muma zauje wani guri neh"

Mami ta gyada kai tace

"Ai gwara ke akanta, ita yaushe rabonda naga ta shirya da sunan zuwa gidanku"

Murmushi kawai Ayoush tayi batace komai bah. Mami ta k'alli Sulthana tace

"Wai k'awarki bata magana neh"

Ayoush ta kalli Sulthana tana Murmushi

"Hmm Queen ai haka take"

Ayoush ta mik'e tace

"Mami zamu tafi"

Sulthana itama ta mik'e har lokacin kanta a k'asa,

"Tun yanzu?" cewar Mami

Dariya Ayoushi tayi

"Ai zamu dawo"

Mami ta mik'e tana cewa

"Tho ina zuwa"

Chan sai gata dauk'e da brown envelops guda biyu, Ayoush ta mikamawa tace

"Gashi keda k'awarki tunda tak'i sakin jiki"

Itadai Sulthana nai Murmushin dole take kanta a kasa. Godiya Ayoush taima Mami itama Sulthana murya a sanyaye tace

"Mun gode"

Mami tai Murmushi tace

"Bbu komai"

Sallama Sukai mata Suka fito suka shiga motarsu suka d'au hanyan Fita..

Suna K'okarin fita Motarsu Mahnoor ta shigo gidan, sam su Ayoush bata lura da suwa ke cikin motan bah. Itama Mahnoor din k'anta na k'asa tana chating a wayanta. Kamar ance ta d'ago ta sauke idanunta kan Motarsu Ayoush, Zaro ido tayi bakinta na rawa tana nuna motarsu Ayoush bakinta na k'okarin furta Wani abu..

Ummy Abduol✍🏻

💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐💐💐
*SULTHANA*
💐💐💐💐
💐💐💐💐💐💐💐💐

By *Ummy Abduol*


*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*


*Page 181 to 185*

_na Yank'e labarin neh saboda banasan nakai har bayan Sallah ban gama bah Ina fata zakumin afuwa. Fans naga sakonin ku dayawa ina godiya Sosai Allah ya barmu tare_


Kamar ance ta d'ago ta sauke idonta kan motarsu Ayoush, zaro ido tayi bakinta na rawa tana nuna motarsu Ayoush bakinta na k'okarin Furta

"Sul..Sulthana"

Kamin ta ankara motarsu Ayoush har yabar cikin gidan a guje..


Alhamdulillahi Baffa ya samu sauk'i sosai Mama dasu Ameenatu sai murna suke. Yau yana kishingide akan tabarma a tsakar gida Mama na mishi fiffita, duk abinda ya faru ta kwashe ta sanar ma Mallan ga mamakinta sai gani tai ya tab'e baki baice komai bah..

Sallama akai a kofar gidan, Mama ta kwallama Ameenatu kira taje chan sai gata itada wannan Mallamin. Tun kafin su k'araso Mama tace

"Ga Mallamin nan"

Tashi Mallan Yayi ya zauna duk da bai jin k'arfi, wuri Mallamin ya samu ya zauna suka gaisa da Baffa da Mama. Godiya Baffa ya soma mai yayi saurin dakatar dashi da hannu, daidai lokacin su Hafsatu suka zo suka zauna tareda gaidashi. Ya amsa fuskanshi bah walwala, Magana ya soma cikin rawar murya

"Dama nace idan kaji sauk'i zan dawo dan akwai wata muhimmiyar Magana danakeso mu tattauna dakai"

Baffa ya gyara zama su Ameenatu suna k'okarin tashi Mallamin ya dakatar dasu

"Aa ku zauna dan ku zama sheda"

Komawa sukai suka zauna, mallamin ya soma magana yana hawaye

"Ni d'an garin zamfara neh, iyayena duk yan chan neh. Mahaifina Mallami ne sananne a chan garin mu, Shekara goma sha biyar da suk'a wuce na kasance banajin magana duk abinda iyayena suka umarceni da nayi bana yi. Banida abokanai sai y'an isa marasa ji yan uwana"

Tsagaitawa yayi ya share hawayen fuskanshi Sannan ya cigaba

"Duk wani kayan maye da aka sani ina sha, muna farauta da abokanaina sannan mu kashe mutum a wajanmu bah wani abu baneh. Sacce sacce da fashi duk babu wanda bama yi munyi k'aurin suna sosai a garinmu. A haka har muka fara bin gari gari muna shiga gidajen mutane muna fashi"

Ya d'ago ya kalli Baffa wanda shima Mallamin yake Kallo ya cigaba da cewa

"Akwai wata rana da mukazo garin kano inda mukai wata mummunar fashi har muka kashe wani babban d'an siyasa a kofar wannan kauyen"

Zabura Baffa yayi ya gyara zama

"Dama ku kuka kashe Alhaji tijjani isiyaku?"

Kai Mallamin ya gyada kanshi a k'asa ya cigaba da cewa

"Bayan munyi fashin da kwana biyu rannan ina kewaya wannan kauyen naganka kaida wad'ansu mutane kuna cinikin gona. Tsayawa nesa daku har kuka gama cinikin aka damk'a maka kudinka a hannu, binka na somayi har xuwa gidan danaga ka shiga Sannan na juya na tafi. A ranar da daddare na kawoma gidanka Samamme"

Duk da rashin karfin da Baffa yake dashi baisan lokacin daya mik'e tsaye bah tana nuna mallamin bakinshi na rawa

"Da..Dama kaine ka shiga gidana? Ka rusamin farincikin dake gidana??"

Kuka Mallamin ya fashe dashi yanaba Baffa yakuri, Mama tace

"Tabbas na tuna lokacin nan, a Gidan marigayiya Mahaifiyar Sulthana koh"

Girgixa kai Mallamin yayi yana cigaba da hawaye

"Bansani bah, nadai san ita wacchan kamar buxuwace"

Baffa ya rintse ido ya nunashi da Yatsa shima hawaye na fita a idonshi yace

"Kun ganshi nan shine Mahaifin Sulthana, a daren ranar aka samu cikinta"

Ameenatu ta mik'e dasauri ta dafe k'irji

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"

Mallamin ya d'ago da Mamaki yana k'allan Baffa

"Ban ganeh meh kake nufi bah"

Baffa ya share hawayen idonshi yace

"Bayan ka kwanta da matata ta samu ciki kuma harta haihu yanz..."

Katseshi Mallamin yayi da cewa

"Wallahi tallahi ko kurani zaka bani na dafa na rantse zan dafa ban k'wanta da Matarka bah. Nadaiyi niyya ta hadani da Allah na fasa"

Baffa ya zaro ido yace

"meh kake nufi"

"Wallahi ba abinda ya shiga tsakanina da matarka wallahi"

Kuka sosai Baffa ya fashe dashi harda d'aura hannunshi aka, Mama tace

"Mallan kamana bayani yanda zamu fahimta"

Zama baffa yayi yana cigaba da kuka ya fara magana

"Kamar yanda ya fada shekaru baya da suka wuce wani barawo ya taba shigowa gidan tsohuwar matata mahaifiyar sulthana knan, ya shigo da k'atuwar bindiga ya bukaci mu bashi kudin dana saida gona. Dama na bata ta ajemin dan haka nace taje ta d'auko mai, tasata yayi a gaba har cikin d'akin barcin mu ni kuma ina falo ya kulleni harda bakina gashi ya kulle kofan ba halin dazan fita nai ihu azo a taimakemu"

Matse kwalla Baffa yayi ya cigaba dacewa

"Ban ankara bah naji maganan d'an fashin nan nacewa riba biyu yakeso ya samu ya amsa kudin ya kuma kwanta da Matata. Bansan sanda na fashe da kuka bah ina nan zaune a falon, ihunta naji tana bashi hakuri shi kuma yana dariya. Chan sai gashi da kudin a leda ya bud'e kofa ya fita, ita kuma tazo ta kwanceni tana kuka sosai"

"Bayan sati biyu da Faruwan hakan tazomin da labarin tanada ciki, tun a lokacin na fara hantaranta dan nasan bah cikina baneh"

Baffa ya fashe da kuka ya nuna Mallamin yace

"Ka cuceni, Allah ya isa tsakanina dakai."

Mama ta matso tana kuka itama

"Kai hakuri Mallan shima ai gafaranka yazo nema"

Kuka baffa yake wuiwui

"Bah irin rantsuwar da batayi bah akan bah abinda ya shiga tsakaninku anma ban yarda bah. Ashe dagaske ne"

Ya k'ara rushewa da kuka

"Ki yafeni Rabiatu, ban miki aldarci bah naci amanar dana dauka naki. Ki yafeni"

Kuka yake sosai yana cigaba da cewa

"Kah cuceni ka rusamin farinciki, yanzu dama Sulthana y'ata ce naketa mata wannan kiyaiyar"

Zumbur ya mik'e yana k'okarin sa takalmin shi. Mama itama ta mik'e

"Ina zaka Mallan?"

Yana kuka yana cewa

"Zanje neman Sulthana ta dawo gida, ta yafeni rashin sani neh"

Mama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login