Showing 6001 words to 9000 words out of 42008 words
nannauyan baccin da ya ɗauke ta har ya gayyato mata mafarkin da ke neman wargaza kwanyarta. Ajiyar zuciya take saukewa akai-akai sannan ta jingina da bango, da ta ga zaman ba zai kai ta ba ta faɗa banɗaki ta yi wanka ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar asuba, a lokacin da tuni rana ta jima da fitowa.
Kamar a mafarki haka ta ga bishiyar na sake tunkaro ta, a yadda take a zaune a ƙasa ta fara ja baya ilahirin jikinta na karkarwa. Wata irin iska mai haɗe da guguwa ce ta taso, Baiwa Maimuna ta sa hannuwa biyu ta rufe idanunta jin ƙura na shigar mata ido. Kamar an yi ruwa an ɗauke haka Maimuna ta ji wurin shiru tana buɗe idanunta ta nemi bishiyar ta rasa, a zabure ta tashi ta ci gaba da gudu kamar wacce ake bi a baya za a zare ranta. Ta jima tana abu ɗaya sannan ta ƙarasa ta bayan masarautar, a lokacin tuni gari ya waye. Sai da ta fakaici idon Dogarawan da ke gefen hanya sannan ta yi sauri ta shiga cikin gidan, tafiya take kamar za ta tashi sama don kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci kwanciyar hankali ya yi ƙaura daga gangar jiki da ruhinta. A haka da samu ta ƙarasa sashen matan sarki tana gab da shiga sashen Fulani Umaima ta ci karo da Uwar bayi, ƙare mata kallo ta yi sama da ƙasa sannan ta ce. "Maimuna daga ina kike haka?" Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, take Maimuna ta yi fiƙi-fiƙi baki na rawa ta furta. "Amm da ma... Yanzu..." Daga can baya Jakadiya ta katse ta, "Uwar Bayi tare muka kwana da ita a sashen Fulani babba yanzu haka gyare-gyare ta gama yi mana." Jinjina kai Uwar bayi ta yi sannan ta wuce, Jakadiya ta ƙarasa wurin Maimuna ta ce. "Ya kamata ki riƙa sara kina duban gatarinki, ki riƙa gayyato nutsu kina yafa wa a gangar jikinki. Kin san sarai wace ce Fulani Umaima." Ajiyar zuciya Maimuna ta sauke ta amsa wa Jakadiya sannan ta wuce sashen Fulani Umaima jiki a saɓule. Tun da ta doshi sashen take jin gabanta na faɗuwa ta rasa dalili, gani take kallo ɗaya idan Fulani ta yi mata asirinta zai iya tonuwa. A haka ta lulluɓa mayafin jarumta ta shiga cikin gidan tana karkaɗe jikinta da ya yi butu-butu da ƙasa.
"Barka da hutawa ranki shi daɗe." Ƙuri Fulani Umaima ta yi wa Maimuna tana karantar yanayinta. "Binne jariri tamkar wacce ta yi dambe da jarumai biyar, Maimuna me yake faruwa na ga jikinki kamar wacce aka tono daga rami?" Ras! Gaban Maimuna ya faɗi, murya na rawa ta ce. "Ranki... Shi daɗe... Dama... zuwa na yi na sanar da ke an aiwatar da komai... Cikin nasara." Shekararta kusan hudu da Maimuna, ta karanci halaye da ɗabi'unta sarai. Take ranta ya yi mummunan ɓaci don ta fahimci zallar ƙarya a saman harshenta. "Me ya sa na amince za ki iya yi mini komai ban aiwatar da kaina ba?" Fulani Umaima ta yi maganar cike da murmushin yaƙe. Ɗakinta ta faɗa ta ɗauko ƙaho cikin shigar ziyarar Boka Bamaguje, ba ta tanka wa Maimuna komai ba ta miƙa mata hannu, zaro idanu Maimuna ta yi ta ji wani abu yana tsarga mata. Babu yadda za ta yi ta ɗora hannunta a kan nata, ba su jima ba sai ga su a fadar Boka Bamaguje. A wurin da ta saba zama koyaushe yanzun ma a nan ta zaune, gumi ya jiƙe jikinta sharkaf zuciyarta na dakan lugude kamar za ta hudo ƙirjinta.
Fulani Umaima ta ce, "Bamaguje ina zargin Maimuna da cin amanata." Bamaguje ya saki murmushi. "Ba zargi ba ne domin yanzu haka duka jariran Sarki Abdul'aziz suna raye a doron ƙasar nan. Ba ta kashe shi ba kamar yadda kika buƙata." Wani yawu mai ɗaci Fulani Umaima ta haɗiya, ta wurgawa Maimuna kallon tsana. A firgice Maimuna ta zube bisa gwiwoyinta hawaye bibbiyu na zuba, "Ki gafarce ni uwar ɗakina wallahi..." Daga wurin da Fulani take ta ɗaga mata hannu. "Kin wargaza mini shirina Maimuna. Na yi rantsuwa da abin da ya busa numfashina sai na shayar da ke ruwan uƙuba mai tsanani."
"Faɗuwa ce ta yi daidai da zama."
"Ban fahimci kalamanka ba Bamaguje."
"Ina nufi sarane za a yi a kan gaɓa. Kin san akwai muhimmin aikin da na alƙawarta miki kwanaki, zan sadaukar da shi a kan baiwarki. Idan kuma za ki samo wata sai a aiwatar a kanta." Jin kalaman Bamaguje ya sa Fulani Umaima dariya ta sauya fuska cikin damuwa. "Amma kafin aikin Bamaguje ya aka yi aka haihu a ragaya? Na yi tsammanin kunamar da ka ba ni za ta hallaka jaririn Fulani? Ina fa tsoron kada wankin hula ya kai ni dare." Wata baƙar mujiya Bamaguje ya ɗauka ya sa hannu ya fige fukafukanta da ranta, ta saki wani kuka cike da azaba sannan ya jefa ta cikin wani daskararran jini. Ya shiga gudanar da al'amuran tsubbunsa, yana cikin yi ya ga tukwanen gabansa sun rushe. A razane ya ɗago yana ɗan ja da baya, ya sake kai hannun da niyyar sake aiwatarwa kamar saukar aradu ya ga wata baƙar kwari da baka ta faɗo tsakiyar tukwanen. Tashin hankalinsa ne ya tsananta, ya ɗago yana sharce gumin fuskarsa da ke cike da gashi. Garin wata farar ƙasa mai walwali da ɗaukan ido ya ɗebo ya watsa, nan take wata narkekekiyar baƙar saniya ta bayyana jingine da kwari da bakar nan. Da bayyanarta babu jimawa duka wutar wurin ta ɗauke, ƙirjin Bamaguje ya buga ya ɗago ya dube ta. "Tabbas wanzuwarsa a doron ƙasa akwai sanadi, ban san wacce kalar baiwa da matsayi ruhinsa ke ɗauke da shi ba. Sai dai a duk bincikena na garara gano taƙamaimai wane ne shi? Abu ɗaya shafin ƙaddararsa ya buɗe mini shi mai nasara ne, sai kuma samun goyon baya da taimakon ruhi da ke lulluɓe da fatarsa..." Cikin rashin fahimta Fulani Umaima ta katse shi, "Ban fahimci gurbin da kalmanka suke neman samun zama ba, wane ne shi wanda kake magana a kansa?"
"Jinin Sarki Abdul'aziz wato jaririn da kika sa aka fitar da shi, tabbas akwai ɓoyayyan al'amari a tattare da wannan yaron. Babban kuskuren da kika tafka kenan, da kika sa aka fitar da shi daga masarautar ba tare da shawara da ni ba. Zancan da nake yi miki yanzu ruhinsa ya yi nisan kiwon da babu hallitar da ta isa ta kawar da shi daga doron ƙasa. Ba zan ɓoye miki ba, daga ni har sauran matsafan da ke doron ƙasa ba na jin akwai wanda zai iya bankaɗa miki labuben sirrinsa, ba ina miki magana a kan masakin ɗan'uwansa ba domin wannan da shi da gawa marabarsu sauka da hawan numfashi. A yadda kika gan shi a haka zai ƙare rayuwarsa a nannaɗe, hatta ruwa da abinci idan ba a ba shi ba sai dai ya dauwama da yunwa. Shi kuwa wance ingarma ne mai ɗauke da rikitattun al'amura, amma ba zan yi miki iyaka ba Umaima idan har kina ganin za ki jarraba wani masanin fiye da ni ga fili ga mai doki." Wata gwauruwar ajiyar zuciya ta sauke fuska ɗauke da damuwa ta ba shi amsa, "Ba zan ja da kai ba Bamaguje domin na tabbata zaɓenka da mahaifiyata ta yi a matsayin madogara ba za ta yi zaɓen tumun dare ba, a halin da nake ciki babban burina bai wuce masarautar Huddam ɗin nan ta dawo ƙarƙashin ikon abin da zan haifa ba wala Takawa yana raye ko baya raye." Bamaguje na ƙarasa jin kalamanta ta ɗauko wani baƙin ƙaho ya kai shi saitin idonsa na hagu ya haske wani allon farin ƙarfe mai ɗauke da rubutun jini, ƙahon da ke hannunsa na fesar da wani tartsatsin jini a jikin kaskon. Ƙuri ya yi yana kallo yana sake fahimtar al'amuran da ke wanzuwa a kwarmin ƙwayar idonsa, kamar kazar da aka jefa da gishiri haka Bamaguje ya ajiye ƙahon ya dube ta. "Za ki haifi gawurtacce kuma ingarman matashin saurayi, mai cike da isa ƙasaita da izzar mulki. Kuma zai kasance sarki wato magajin karagar sarki Abdul'aziz..." Murmushi da murnar Fulani ya katse kalaman Bamaguje ta ce. "Tabbas da kuwa mun shimfiɗa mulkin da wani mai numfashi bai taɓa aiwatar da makamancinsa ba. Sai na shayar da Fulani babba ruwa mamaki domin sai na gasa mata tsakuwa a tsakiyar tafin hannunta." Bamaguje ya kafe ta da idanu yana faɗin, "Haba Umaima me kike ci na baka ma zuba, ai duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu. Kuma duk gaggawar asara ta jira yi samu. Kamar yadda na gaya miki jininki zai kasance sarkin ƙasar Zazzau ne kaɗai bisa taimakon jini da ruhin wata hallita, ban san ya zan fasalta miki ita ba amma ta kasance mai ɗauke da rikitattun al'amura. Wanzuwarta a doron ƙasa sanadi ne, kuma ta kasance abar farautar al'umma da dama ciki kuwa har da mahaifina wanda ya shafe shekara da shekaru cikin halwar tsafinsa yana dakon zuwanta. Ban gama tabbatar da abin da nake zargi ba amma tabbas na ga walƙiyarta a cikin masarautar Sarki Abdul'aziz, wannan zai sauƙaƙa miki cim ma muradinki..." Da sauri Fulani ta katse shi cikin ƙagauta.
"Wacce irin hallita ce? Me ne ne alaƙarta da masarautar Huddam? Shin dole sai da taimakonta ne abin da zan haifa zai kasance Sarkin masarautar Huddam?"
"Akwai ɓoyayyun al'amura game da ita, a sura ta zahiri ta kasance bil'adam kamar kowa. A baɗini tana da ɗauke da al'amura masu hautsina kwanya. Halwar tsafina bai fayya ce mini komai ba, sai dai ina mai shawartar ki da ki tabbatar kin yi nasara a kanta. Ina daga nan zan ci gaba da dafa miki domin ni ba iya boka kaɗai nake a wurinki ba, akwai wata ɓoyayyar alaƙa mai ƙarfi a tsakaninmu. Ba don na yi wa mahaifiyarki alƙawarin binne wannan sirrin ba da tuni na fayyace miki shi, amma ko ga iya haka na dakata na yi miki jurwaye mai kamar wanka don haka dabara ta rage wa mai shiga rijiya." Da yake hankalin Fulani ba ya jikinta ya sa ba ta fahimci inda kalaman Bamaguje suka dosa ba, tana shirin yi masa magana ta ji ya ci gaba da ce wa. "Tana da matuƙar hatsarin gaske don haka dole ki yi takatsantsan, wannan shawarar ina baki ita ne ba a matsayina na bokanki ba ina ba ki ita ne a matsayina na makusancinki. Wani abin da ɓatattu da dama irina ba su sani ba wannan hallitar na da wata tawaya ɗaya wacce da a ce an santa da tuni an yi galaba a kanta..."
"Wacce irin tawaya gare ta?"
Bamaguje ya wara hannuwansa haɗe da faɗin, "Ni kaina ban santa ba, sai dai allon tsafina ne ya alamta mini haka. Ammma zan baki wannan sirrintaccen littafin mai ɗauke da labarin abin da ya taɓa faruwa a masarautar Daura, wannan al'amarin ya faru a shekara ɗari da hamsin baya da suka shuɗe. Ƙa'idar littafin ba a karatunsa kowacce rana sai ranar Lahadi ko Laraba daga bayan la'asar zuwa sallar isha'i. Ki bi shi a sannu ki karanta zai taimaka miki matuƙa. Umaima!" Boka Bamaguje ya ambaci sunanta cikin wani irin yanayi. Fulani Umaima ta dube shi cike da ƙwarin gwiwa babu alamar karaya ko tsoro a tattare da ita.
"Jarumta da dakakkiyar zuciyarki na matuƙar birge ni, tabbas kin cancanci shiga sahun mace mai kamar maza. Na yi imani da abin bautar da nake bauta tare da siddabarun da na gada a wurin iyayena da kakanni sai na ci gaba da dafa miki kin kasance mai nasara har ƙarshen rayuwarki." Fulani Umaima ta saki murmushi. "Ai dama duka ɗaya baya kada sadaukan jarumai, don haka na dulmiya kogin azaba na yayyafa wa ruhi da gangar jikina don kada wani hatsari ko firgici ya razana ƙwarin gwiwata." Umaima ta ɗora tafin hannunta a saman tukunyar tsafinsa ta runtse idanunta ta ci gaba da cewa, "Na yi imani da kai Bamaguje kuma na yi maka alƙawari wallahi sai jinina ya mulki ƙasa da masarautar Huddam bakiɗaya." Bamaguje ya jinjina kai sannan ya ɗauko wani irin littafi mai ɗauke da bangon ƙarfe wanda yake ɗauke da launin ruwan zaiba. A tafin hannunta ya ɗora mata, wani irin zuuuu ta ji a tafin hannunta kafin ta ankara ta ji wani sauti na furta. "Hidayaaaa!" A razane ta buɗe idonta suna haɗa ido Bamaguje ya jinjina mata kai, "Kamar yadda majiyar sautinki ta jiye miki haka ne wato Hidaya ba zan ce miko komai ba, domin amsar tambayar ki na cikin kundin littafin." Fulani ta rungume littafin ƙam kamar wani zai ƙwace shi, sannan ta waiga wurin da Maimuna ke zaune kamar gunki ta gagara motsa koda yatsanta ne. "Bamaguje ka aiwatar mini da duk abin da ka yi niyya a kan waccan la'ananniyar." Bamaguje na jin haka ya bushe da dariya, Maimuna ta fara mutsu-mutsu tana son tashi ta gudu amma ta gagar tashi. Yana daga wurin da yake zaune ya turmutsa hannunsa a cikin wani kabari, ya ɗauko ƙoƙon kan mamacin da ke ciki ya fara takawa har ya isa wurin da take zaune. Ɗora mata kan ya yi a kanta na ɗan lokaci take jikinta ya fara karkarwa, ya jima a haka sannan ya saka wata ƙaramar tsafatacciyar wuƙa ya yanki tsokar jikinta. Wajen kabarin ya koma ya tura fatarta a cikin kabarin sannan ya furta. "Wannan da kike ganinta a zahiri ne take tamkar rayayya amma ba ta da amfanin komai kuma za ta zame miki tamkar raƙumi da akala. Yanzu ki tafi da ita zuwa turakar Sarki Abdul'aziz, kuma a wannan ranar nake son ki sa Sarki Abdul'aziz ya kusanceta ta gaba da baya." A firgice Fulani Umaima ta ɗago ta kalle shi cikin tashin hankali.
_Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚
07062062624.
[10/4, 11:48 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.
SHAFI NA HUƊU
Wani irin kallo Fulani Umaima ta watsa wa Bamaguje, shi ma ya yi ƙuri yana kallon ta da daƙwa-daƙwan idanunsa jawur kamar sabon barkono, ta katse shirun da ce wa. "Ka na nufin Baiwata Maimuna ce Takawa zai kusance ta? A saboda wanne dalili kuma ba ka ganin tamkar na miƙa kai a kan hanyar da asirina zai tonu?" Bamaguje ya girgiza mata kai. "Matuƙar ina numfashi kullin za ki kasance lulluɓe cikin bargon rufin asirin da babu wani mai numfashi ya isa ya yaye miki shi, dalilin da ya sa na ce ki aiwatar da wannan aikin matuƙar Sarki Abdul'aziz ya kusanci Maimuna ta gaba da baya za ki sha gaban kowa. Wane na mai faɗa a ji a cikin ƙasar Huddam?"
"Sarki Abdul-aziz." Umaima ta amsa masa.
"Ki saurare ni da kyau. Ba akwai wata baƙar rijiya mai baƙin murfi a turakar Mai martaba ba wacce suke kallon juna ita da tsohon shuri mai tsohon tarihi?" Umaima ta gyaɗa masa kai. "Mai martaba na gama mu'amala da ita ki tabbatar kin ɗebi najasar jikinsu sai ki shafa ta akan saman murfin take murfin zai buɗe, ki zura Maimuna cikin rijiya ki koma gefe su zuba ido zai koma ya rufe kamar yadda yake da farko. Maruƙar kika aiwatar da komai yadda ya kamata za ki sha gaban duk wata hallita da ke cikin ƙasar Huddam, kwarjini da tsoronki zai mamaye zuƙatansu ta yadda kina faɗar maganar za a aiwatar miki. Sai dai akwai sharaɗi duk ranar da aka fito da Maimuna daga cikin wannan rijiyar wannan asirin ya karye, amma kuma abu ne da kamar wuya gurguwa da auren nesa domin yanzu haka rabon da a buɗe rijiyar yau kimanin shekara ɗari da hamsin kenan." Umaima ta sauke ajiyar zuciya. "
Duk wannan ban ɗauke shi abu mai wahala ba, shin ya za a yi na wuce da Maimuna har turakar Takawa ba tare da wani ya gan ni ba, kuma na sa shi ya yi mu'amala da ita?"
"Umaima a kullin kin fi son a yi miki ciki a yi miki goyo, za ki saka hannu ki ƙwaƙwalo ƙwayar idonta ki jefa a cikin wancen sihirtaccan ruwan, yadda za ta makance ta daina gani haka za ki ci karenki babu babbaka ba tare da wani ya kawo miki cikas ba. Kuma daga wannan lokacin hatta uwar da ta kawo ta duniya ba za ta sake tambayarta ba, yadda matacce ke mantawa da rayuwar baya haka duk wanda ya santa zai manta da shafinta." Umaima ta yi masa jinjina da hannu. "Na gode sosai Bamaguje faɗi kowanne irin tukwici kake buƙata." Bamaguje ya saki murmushi, "Ki je Umaima zan fanshi aikina a cikin masarautarku." Umaima na gama sauraronsa ta miƙe ta ƙarasa gaban Maimuna da ke zaune kamar butum-butumi, ƙaramar wuƙa ta saka ta ƙwaƙwalo idanunta ta watsa cikin wani koren ruwa kamar yadda Bamaguje ya faɗa mata. Ta koma gabansa ta yi masa sallama da faɗin duk abin da ake ciki za ta sake ziyartarsa. Ta rungume littafin a jikinta hannunta ɗaya riƙe da Maimuna na biye da ita kamar raƙumi da akala. Duk wani abu da take gudanarwa na siddabaru sai da ta gudanar babu jimawa sai ga su a cikin ɗakinta a tsaye. Kai tsaye uwar ɗakinta ta wuce da Maimanuna ta buɗe wani akwatinta na ƙarfe da take ajiyar abubuwanta na sirri ta ajiye littafin, sannan ta koma falo ta zauna tana ta zuba murmushi don gani take ƙiris ya rage haƙonta ya kai ga cim ma ruwa.
Bayan fitar Fulani Umaima daga sashen Fulani babba, Jakadiya da kanta ta ɗan tattara wurin. Ta leƙa madafa tana tambayar su Baraka ko ruwan zafin ya tafasa, a daidai lokacin ta same su sun fara kwashe ruwan. Bayan an zuba aka kai banɗakin Fulani babba, shi kuma jaririn Jakadiya ta zauna ta sulle shi tas. Sai da gari ya waye tangararan sanna