Showing 30001 words to 33000 words out of 42008 words

Chapter 11 - SHUUMAR MASARAUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Apr 2025

3357

abin bai tsaya iya waje ba hatta ahalina na fuskantar wannan barazanar, a taimaka a roki Sarauniya Sha-kundum ta yafe mana tun da laifin wani ba ya taɓa shafar wani." Boka mai zamani ya miƙa masa busasshen hannunsa mai ɗauke da zaƙwa-zaƙwan farata, taurin hannunsa tamkar busasshen katako sannan ya ce, "Ina tukwicin ziyarar Sarauniya Gunki Sha-kundum kafin na san abin yi? Domin sanin kanka ne tuni bakin alƙami ya riga da ya bushe." Sai a lokacin Sarki Damina ya tuna da ƙoƙon tukwicin ziyara, cikin sake ƙanƙan da kai ya furta. "Sha-kundum ta dafa aikinka ta shiga lamuranka boka mai dogon zamani. Ka ga taka ka ga ta kakanninmu, iyayenmu duka sun wuce sun barka. Ya kai wannan boka mai dauwamamman ruhi da dogon zamani a yi mini afuwa bisa mantuwar da na yi, amma duk wani hukunci da Sha-kundum za ta yanke ni mai biyayya ne." Boka na gama jin haka ya miƙe ya tunkari bakin wata rijiya wacce faɗinta ya fi girman ƙaramin ɗakin, yana zuwa ya fara taka matattakalar da ke cikinta ya shige. Shigarsa ke da wuya bakin rijiyar ya shafe tamkar ba a taɓa wanzar da komai a wurin ba. Yana shiga kai tsaye ya tunkari gunkin wata mace da ke tsaye da tulelen tsohon ciki a jikinta, hannunta ɗaya tallafe da tsohon cikin ɗayan kuma yana riƙe da garkuwa alamun ta kare kanta da shi. Sai da ya sunkuya ya miƙa gaisuwa sannan ya furta, "Ya ke Sarauniya sha-kundum! Ya ke mammallakiyar wannan Daular a yau ma na sake dawowa da neman yafiyar al'ummarki.Na tabbata kina saurarena kamar yadda kika daɗe kina jina. Haƙiƙa talakawanki sun dawo da wata buƙata domin a yau sun wayi gari da samun annobar haɓo shin wane taimako za ki yi musu?" Hawayen ne ya ziraro daga cikin idanun gunkin, boka ya ƙarasa ya kanga kunnensa a jikin ƙirjinta. Ya jima a haka sannan ya ɗago cike da girmamawa ya ce, "Tabbas zan isar musu kamar yadda kika buƙata, ki ƙara haƙuri nan ba da jimawa ba za ki dawo cikin ainihin hallitarki ta zahiri. Za ki ci gaba da mulkar al'ummarki kamar yadda kika mulke su a ɗaruruwan shekarun da suka gabata. Komai ya zo ƙarshe tun da ke kika tabbatar min da haka, sarauta da izzar mulki na baibaye da rayuwarki. Taɓewa da hallaka tana ga Maharba da Mafarauta har ƙarshen rayuwarsa." Yana gama maganar ya juya jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da gishiri, yana taka matattakalar bene ɗaya rijiyar ta fara dawowa kamar yadda take da farko a wurin.

Kan shimfiɗarsa ta farko ya koma ya zauna ya dubi Sarki Balarabe yana faɗin, "Ta faru ta ƙare..." Da sauri Sarki ya katse shi da cewar, "Allah sa ba laifinmu ne ya sake hauhawa ba."

"Ka buɗe kunnenka da kyau ka saurari abin da Sha-kundum ta gaya min game da ku." Boka mai zamani ya faɗa fuska babu walawa. Shiru Sarki ya yi yana sauraron Boka. "Tabbas Sarauniyarmu Sha-kundum ta sake dawo wa kamar yadda ta faɗa a lokacin da numfashin zai ɗauke..." Baki na rawa Sarki ya katse boka da cewar, "A ina aka wanzar da ruhinta? A wane yanki ne mu sa a kawo mana ita? Idan ta kai bangon duniya na rantse da hatsabibanci Sarauniya da izzar mulkina sai na sa an ɗaukota a faɗin duniya." Boka ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya har yana birgima a ƙasa tamkar jakin da yake birgima a cikin sahara. Sarki sai da ya fusata ya doki ƙasa da tafin hannunsa sannan Boka mai zamani ya koma kan buzunsa  ya furta, "Haba Sarki Damina ai duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu, haka duk mai niyyar yin sammako ya bari duhun dare ya gifta. Sarki Damina a kwai gaggarumar matsala, kamar yadda duk faɗin garin nan babu wanda ya taɓa gani ko jin sautin Sarauniya Sha-kundum sai ni, to tabbas a wannan karon ko ni ba ni da masaniyar a ɓangaren da wannan sabuwar sarauniyar take. Babban abin baƙincikin ma waɗanda suka sulwantar mana da ruhinta a cikinsu halitar Saruniya ta sake wanzuwa..." Tun bai ƙarasa magana ba jikin Sarki Balarabe ya fara rawa kamar wanda ake kaɗa wa gangi, a fusace ya miƙe tsaye yana huci tamkar kumurcin macijin da ke tsaka da fusata. A fusace ya furta, "Boka mai zamani ka na nufin Sarauniyarmu ta ɓullo daga cikin zuri'ar maharba da mafarauta ne?" Boka ya jinjina kai yana faɗin, "Ba harsashe ba ne Damina domin Sha-kundum ta tabbatar mini kuma kai shaida ne bata taɓa yin ƙarya, ta ba ni muhimmin saƙo gare ku na farautar Maharba a ko ina suke a faɗin duniya. Sai dai babban tashin hankalin ta yi alƙawarin ba za ta sake magana ba har sai na sada da ta da ainihin ruhinta. A sanyaye Sarki Damina ya furta, "Tirƙashi! Ana dara ga dare ya yi. Bayan wannan ina tafe akan buƙatar Yarima Nomau, babban boka lamarin ciwon yaron nan a kullin ƙara ta'azzara yake. A da muna haɗa shi da ƴan mata ɗaya zuwa biyu a rana amma yanzu har ta kai ga mata biyu ba sa iya gamsar da shi, kafi kowa sanin shi kaɗai na mallaka kuma har abada ba zan sake haihuwa ba. Idan na tuna ba ni da magaji lamarin na sake ɗugunzuma hankalina." Boka mai zamani ya hura ƙasar gabansa nan take wata ƴar ƙorama ta bayyana a wurin, sai da ya barbada wani garin magani sannan ya zura hannunsa ya warasu haɗe da runtse idanunsa tare da fara karanta waɗansu irin ɗalasuman tsafi, ƙirjin Sarki Damina ban da bugawa babu abin da yake yi saboda fargabar abin da Boka zai sanar da shi. Boka mai zamani ya jima a haka sannan ya buɗe idonsa yana kallon Sarki Damina haɗe da furta, "A kodayaushe maganar ɗaya ce! Kamar yadda na sanar maka Yarima Nomau ba zai taɓa warkewa ba matuƙar bai sadu da da inuwar wannan macen da nake gani a tattare da shi ba. Tabbas zai warke sai dai bazan taɓa ce maka ga wa'adin lokacin da zai ɗauka cikin wannan tuburewar ba. Na ga haske jingine da su daga inuwar yarinyar nan na ga akwai rabo a tsakani, sai dai ka fi kowa sanin yadda aka yi aka samu Yarima Nomau don haka idan har ya samu rabo da wannan yarinyar Ɗa ko Ƴar da za su haifa dole zai zama mallakin Babban dodo ne, idan ba haka ba duk daren daɗewa za su zama masifa a daular nan. Kuma wannan hasken ba komai yake bayyana mini ba illa kusantowar warakarsa, don na lura akwai yuwuwar samun waraka nan ba da jima wa ba." Ajiyar zuciya Sarki ya yi don tun da yake zuwa wannan kogon bai taɓa jin labarin da ya faranta ransa kamar na wanan ranar ba  Ya dubi Boka fuska ɗauke da murmushi ya furta, "Ya kai babban malamin madogararmu shin zan iya sanin wacece yarinyar nan kuma a wane yanki take?" Boka Mai zamani ya girgiza kai yana cewa, "Lamarin Yarima Nomau ya wuce duk yadda kake tsammani, daga ni har bokayen duniya babu wanda yake da wannan amsar don haka ina mai baka shawara kar ka wahalar da gangar jiki da ruhinka akan abin da babu takamaimar amsa. Wani hanzari ba gudu ba, daga bayan wannan inuwar na hango wata baƙar ƙura wacce ta lulluɓe sarararin samaniya sai dai ni kaina ban fahimci wacce irin ƙura ba ce koma dai wacce iri ce ina fatan za ta zame mana alkairi." Sarki Damina ya miƙe ya fara zagaye cikin kogon dutsen sai da ya zagaye boka mai zamani sannan ya ce, "Wannan ba zai zame mana matsala ba domin mun dogara da Sarauniya Sha-kundum da babban dodo na tabbata su za su kawo mana waraka a rayuwa. Yanzu wanne irin magani ta ba mu wanda za mu aiwatar mu da al'umnarmu?"

Boka mai zamani ya miƙe ya ƙarasa bakin rijiyar ya miƙa hannu ciki nan take ruwan cikinta ta kawo har sama sannan ya ɗebi ruwan da ƙoƙo ya miƙa wa Sarki Damina yana faɗin, "Wannan ruwan a je a zuba shi cikin kogon Ɗanbille duk wanda wannan annobar ta same shi ya ɗauka ya sha kai koda bata kama mutum ba zai iya wanka domin yin rigakafi. Wannan ce iya maganar da ta umarce ni na sanar da ku don haka za ka iya tafiya ya sarkin sarakunan duniya." Sanin ƙa'ida da dokar Sarauniya ya sa Sarki bai musa ba ya miƙe ba tare da ya furta koda kalma ɗaya ba, har ya je bakin ƙofa ya ji muryar Boka yana faɗin, "Ka da ka manta a kai wa Babban dodo Mai tsohon ciki biyu da idanun dattijai biyu." Gyaɗa kai kawai Sarki ya fice daga kogon dutsen.

Garin Dabur

   Daga cikin bukkar da nake kwance ina bacci na fara jin hayaniya sama-sama, ina yunƙuri tashin na ji muryar mahaifiyata ta karaɗe majiyar sautina da cewar, "Yau wacce baƙar rana muke gani da yammacin haka? Ya abar bauta kada ki yi fushi da wannan mummunan zunubin domin ba mu da sa hannu a ciki, ka hukunta masu wannan zunubin da gaggawa don sun cutar da ƴar tsintuwar da bata ji ba bata gani ba." Ihun da Kandala take jerawa ne ya sa ni fito wa saboda duk wanda ya ji kukan nata ya san ba na lafiya ba ne. Jikina ne ya ɗauki tsuma sakamakon ganin halin da take ciki kace-kace da jini, a gefe ɗaya mutane daga jinsin maza da mata sun yi carko-carko a kanta suna kallon halin da take ciki. A gabanta na tsugunna raina ya kai ƙololuwar ɓaci, na dube ta fuska babu walwala na furta "Waye ya yi miki haka Kadala?" Ilahirin jikinta rawa ya ke don haka na kama hannunta na haɗa su da nawa na sake furta, "Babu abin da zai faru da ke ki gaya min waye ya yi miki haka?" Cikin yanayin azaba ta furta, "Ban san sunansa ba amma na ji wasu suna ce masa Barde." Ban jira ragowar maganar ta ba saboda tun farkon ganin halin da take ciki shi ne mutum ba farko da ya fara faɗo min a rai, saboda sanin hali ya fi sanin kama. Barde riƙaƙƙen ɗan akuya ne baya iya kwana biyu ba tare da ya kusanci wala macen bil'adam ko dabba ba. 

Ina miƙe wa na riski muryar Goga ya fara fito yana busa ƙaho wanda yake alamtawa sauran ƴan uwa na nesa da na kusa akwai fita ta gaggawa. Kafin ya gama busar da yake tuni gidanmu ya cika damƙam da sauran ƴan uwa maharba da mafarauta kowanne yana tafe cikin shirin dawa, ɗaya bayan ɗaya na kalle su kowannen su yana jiran umarnin da zan bayar. Jin na yi shiru ya sa Goje  ya ɗaga gorarsa sama da hannun ɗaya, ɗayan hannun mai riƙe da kwari da baka ya sauke ya fara zabga mini kirari. "Burugu ce da kanta ba aike ba mace mai kamar maza ko cikin maza sai an tona. Cau cau cau cau ƙurungu mugun kifi sa'a a dawa sa'a a cikin gari wani aiki sai jan wuya makutsa daji, a lafiya uwar gidan kere amanar kura kyaci da gashi. Dawa dai, dawa gidan maza tsanani yana dajin Gurɓu ku bar faɗa musu wahalar sanar da su daɗin maza na cikin dawa mata na gida suna yin girki, wuya a dajin gwiɓau wuya a dajin fatalaki wuya ta ƙare a kan Barde yau ya taɓo ajalinsa." Ilahirin jikina ban da rawa babu abin da yake yi saboda tsumin da ya tayar min har nake jin da ace Barde na gabana babu abin da zai hana ban tsarge ruhinsa gida biyu ba, duk da kowa ya san Barde a cikin garinmu ba kanwar lasa ba ne.

  Da sauri na faɗa bukkarmu na ɗabo gurun damatsan hannuwana da wuya, na kunce fatar mesar da ke ɗaure a ƙuguna na ɗaura ta damisa sannan na ɗauko kwari da baka haɗe da zabgegiyar adda na fito wurin da su Goga suke tsaitsaye. Suna ganina suka yi yunƙurin saka kai a hanzarce na dakatar da cewar, "Wannan fitar ba taku ba ce saboda Barde gidanmu ya taɓo ba ku ba, na yi rantsuwa da abar bauta ba zan dawo gida ba sai na sauke kan Barde daga gangar jikinsa, weeeehuuuuhuuuuu sai ni sarauniyar baka jikar marigayi Baushe amanar kura kawanciyarka ka huta muna tafe idan dabbobi sun ƙare. Sai ni yaƙi ban san wasa ba Abar bauta ta buɗa mana matuƙar na saka kai ko yau ko yanzu ban san namiji ba sai na ga tabo a jikinsa, wahala a hanyar tugu wuya a hanyar badake wuya ko da magani babu daɗi ko ana ha maza ha mata sai na dawo da kan Barde a hannuna." Ina gama zabga kirari cikin haɗin baki tawagar da ke wurin suka furta, "Dawa dai Sarauniyar kwari da baka, Abar bauta ta buɗa miki a dajin Gurɓu." Har na saka kai zan fita na dawo wurin Mahaifiyata na russuna saitin kunnenta ina faɗin, "Ki roƙar mini abar bauta da ta rinjayi ɗayan ruhin kar ya ziyarce ni ina tsoron kada Barde ya yi nasara akaina." Cike da ƙwarin gwiwa ta furta min, "Sa'a dai Sarauniya abar bauta ta buɗa miki ɓoyayyan ruhi ba zai ƙara ziyartar ki ba." Ina gama sauraronta na fice daga cikin gidan cike da ƙwarin gwiwa na nufi wurin da na tabbatar Barde na zama da ƴan koronsa.

Daular Sarki Damina.

   Daga kogon boka mai zamani ya so kai ziyara bukkar babban dodo amma sai ya ga mafi dacewa ya fara zuwa wurin al'ummarsa ya umarci rundunar mayaƙansa da su fita yi masa farautar duk wata halitar bil'adam, musamman daga tsagin maharba da mafarauta kamar yadda suka saba yi a baya. A tsaitsaye suke dubbanin mutanen daular don a zatonsu maganin warakar annobar da ke damunsu aka kawo musu, Waziri ne ya yi gyaran murya sannan ya furta, "Ya ku waɗannan jama'a ya kamata kowa ya nutsu don jin saƙon da Sarauniya sha-kundum ta aiko." Tamkar ɗaukewar ruwan sama haka wurin ya yi tsit, Sarki Damina ya yi gyaran murya sannan ya dube su ɗaya bayan ɗaya  ya sanar da su duk yadda suka yi da boka Mai zamani sannan ya ɗora da cewa, "Ina umartar manyan mayaƙan dakarun daular nan da su hanzarta fita cikin gaggauwa don yi mana farautar bayi kamar yadda suka saba a baya, kuma su yi sani cewa ya zama wajibi su farmako mana La'anannun hallitar can ta maharba da mafarauta a ko ina suke a faɗin duniya. Wannan umarni ne daga Sarauniya sha-kundum idan ba haka ba bala'in da muka shiga da wanda muke ciki a yanzu shafar mai ne akan abin da zai faru da mu a gaba." Yana rufe baki zaratan dakarun mayaƙan suka fara fita a guje zuwa mahallansu kowanne na fito wa da manyan makamai, runduna guda suka yi tsaya a gaban sarki Damina. Sai da ya ƙare musu kallo sannan ya kasa su gida huɗu, manyan zaratan mayaƙan ya ce su bi gabas hanyar da za ta sada su da ƙasar Dabur. Runduna ta biyu ya ce su bi Yamma hanyar da za ta sada su da ƙasar Baƙasud, runduna ta uku ya ce su bi kudu hanyar da za ta sada su da ƙasar Mubali sai tawaga ta huɗu da ya umarce su da Arewa wacce za su isa da Ƙasar Surima. Lokaci ɗaya suka bazama a yunwace da farauto kowanne irin bil'adam kamar yadda Sarkin da yake mulkarsu ya ba su umarni.

*KU MATSO KU TAHO*💃🏼

Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananjn ban tausayi😰  ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼

Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰
Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
[8/20, 7:26 PM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*

      ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
 
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

                  2

Fita ta ke da wuya na ci karo da Mahaifina da ya sawo kai ciki kafaɗarsa maƙale da barewa da ingarman zaki, ganin yanayina ya tabbatarsa masa akwai wani abu da yake faruwa don ya san fitarsa ban yi da shi zan shiga dawa ba. Cike da ladabi na miƙa masa gaisuwa irin tamu ta maharba ina faɗin, "Dawa dai Sarkin sarakuna uban dawa ga tsini ga mashi, ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login