Showing 27001 words to 30000 words out of 42008 words
da ita?" Uwar tuwo ta furta. Zuciyar Mai gado ta yi ƙal ta ƙarasa wurin Baiwa Zinaru da ke goyon ɗanta mai kimanin shekara guda. Take Zinaru ta amsa ba ta musa ba, sai dai tana ɗaukar Jawahir ɗanta da ke gefenta ya ƙanƙame mahaifiyarsa yana tsanyare wa da matsanancin kuka haɗe da cusa kansa cikin jikin mahaifiyarsa. A lokacin babu wanda ya kawo komai a ransa don a tunaninsu ma kishine irin na yara yake yi don ya ga an ɗauki wata yarinyar, kai tsaye Zinaru ta rungume Jawahir ta fara shayar da ita, wani irin zuuu! Zinaru ta ji tamkar wacce aka kafa wa shocking har tsakiyar kanta. Ga wata irin zuƙa da take ji Jawahir na yi kamar za ta fige maman jikinta, suna nan tsaitsaye ruwan nono ya fara dawo wa Jawahir ta hanci da kunnuwanta. Wannan yanayin da ta shiga ya sake faɗar da gaban mutanen wurin, cikin masifa Jakadiya ta fara magana. "Wannan wacce irin masifa aka kawo mana saboda Allah, yarinyar tun da aka kawo ku sai faɗar mana da gaba kike yi." Mai gado jiki a sabule ta karɓi Jawahir ta fita zuwa bakin wata bishiya ta zauna cikin sarewa ta fara zubar da ƙwallah. Jawahir ta jima a haka sannan nonon da ke fita daga jikinta ya dakata da zuba, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta sake goge mata haɗe da saka ta a baya ta goya ta. A ranar kusan kwanan zaune mai gado ta yi cike da rashin sabo da zaman baƙunta, uwa-uba rashin kyakkayawan makwancin saɓanin wanda suka saɓa kwana a ciki.
Cikin Dare.
Wata doguwar hanyar ya bi samɓal yana tafiya wacce babu komai sai dogayan bishiyu, tsawo da girmansu ya haddasa wa wurin duhu mai ban tsoro. Daga bayansa ya ji kamar ana bibiyarsa don haka ya yi saurin waigawa cikin tsoro da tashin hankali, wata baƙar mage mai ratsin fari ya gani tana tafe tana shinshina sawunsa. Tun bai yi wayo ba yake ƙaunar kyanwa don haka ya tsugunna da niyyar kai hannu kanta, da sauri ya ji an fisge shi gefe waɗansu surutai na tashi sama-sama a cikin kunnuwansa. Waigawa ya yi bai sake ganinta ba, ya ci gaba da tafiya. A jikin wata murgujejiyar bishiyar kuka ya hangi wata rantsatstsiyar karaga, "Je ka ƙarasa kan karagarka." Ya ji an furta masa. Wani irin sanyi ya ji yana ratsa shi, jiki a sanyaye ya fara takawa da niyyar hawa kan shimfiɗar da ke ɗauke da karagar, ga mamakinsa sai ji ya yi wannan baƙar magen ta hankaɗa shi gefe ɗaya. Ta ɗora wani mulmulallan abu mai kama da ƙawai a kan karagar, sannan ta fara zagaye karagar cikin ƙasaita. A can ƙasa ya faɗi kansa ya bugu da wani farin dutse take jini ya fara ɗiga, dafa wurin ya yi cikin azaba sai gani ya yi magen ta ƙaraso tana lasar jinin da ke zuba daga goshinsa. Ta fara ɗaga kanta tana da alamar tana son kai wa kansa farmaki wurin da ragowar jinin yake ɗiga. Ganin ta dumfaro shi ya sa ya ci gaba da ja baya zuciyarsa na dakan luguje, ganin haka ya sa magen ta fara wata irin dariya fiƙoƙinta na zubowa ƙasa ɗaya bayan ɗaya. Duk wurin da fiƙar ta faɗa sai ƙasar wurin ta rufta har ta yi tsalle za ta damƙi saman goshinsa. Firgigit Kamalu ya tashi cikin matsanancin tsoro, firgici da tashin hankali. A lokacin dare ya tsala sosai, ban da munsharin mutanen ɗakin da kukan tsuntsaye babu abin da yake tashi. Jin abu na gangaro masa a goshi ya sa ya kai hannunsa ga mamakinsa ya ji ya taɓa abu, da sauri ya yunƙura zuwa wurin aci-balbal ɗin da ke kunne a gefen ɗakin ya haske. Rass! Gabansa ya faɗi, jikinsa ya ɗauki karkarwa kamar mazari.
"Jini!" Ya furta a kiɗime.
Yana shirin komawa ya tashi Baffajo ya sanar da shi abin da faru ya ji an dafa kafaɗarsa.
"Wannan gidan ba irin kowanne gida ba ne, sai ka ɗaura ɗamarar juriya da jajircewa. Gadon gidanku ba a sansu da sarewa ba, ka zama jarumi mara tsoro a haka ne za ka ƙwaci kanka. Ka gode wa Allah da ba ta yi nasarar yagar naman jikinka ba, kuma kada ka ɗauka za ta haƙuri. Wannan daɗɗaɗiyar mummunar manufa ca tunkafin haihuwarka, zan yi takaici ƙwarai matuƙar ta yi nasara a kanka kamar yadda ta ci galaba a kan mahaifiyar..." Sam Kamalu baya fahimtar kalaman da farin dattijon ke gaya masa, cike da damuwa ya katse shi. "Don Allah wane ne kai? Ya aka yi ka san mafarkin da na yi?" Murmushi Dattijon ya yi, "Yaro man kaza! Da sannu za ka fahimci turbar da nake son ɗora ka, izza da ƙasaitar jinin Sarki Muhammad Safwan ba za ta tashi a banza ba. Ba ni zan bayyana wa duniya waye kai ba, izza da tasirin jinin sarautar da ke jikinka ne zai bayyana wane ne kai. Ni Aminin Kakankakanka ne, ina bibiyar al'amarinka saboda waɗansu muhimman abubuwa da tasirinsu. Ta so mu je ka wanke ciwonka a wancan rafin, idan gari ya waye kada ka sanar da kowa mummunan mafarkinka hatta Baffajo da Inna wuro, domin wannan gidan sarautar cike yake da idanu mabanbanta."
Tamkar raƙumi da akaɗa haka Kamalu ya bi bayan tsohon yana gaba shi kuma yana biye da shi, lokacin da suka ƙarasa bakin rafin wani irin sanyi ne ya fara ratsa shi har sai da jikinsa ya ɗauki rawar ɗari. Kaf kaf kaf haƙoransa suka fara rawa, ga wata irin juwa da take ƙoƙarin fisgar shi ko ta halin ƙaƙa, ɗagowa ya yi a wahalce ya furta. "Ba zan iya ba, ba zan iya zuwa ba sanyi nake ji." Rufe bakin Kamalu sai dajjijon ya sa hannunsa a tsakiyar goshinsa, a hankali ya ji sanyin da yake ji yana raguwa, "Ba na jin daɗi a duk lokacin da ga karaya a ƙwayar idonka, daga yau kada na sake jin ka furta kalmar gazawa. Tabbas za ka iya domin duk tsawon lokacin da muka ɗauka lokacinka muke jira, mu je ka aiwatar da abin da yake gabanka." Dattijon ya faɗa yana kama hannun Kamalu ya sanya ƙafarsa ta dama a cikin rafin, wani irin zuuu! Ya ji har cikin kwanyarsa. Gabansa na faɗuwa ya tsugunna a ɗebi ruwan ya wanke ciwonsa kamar yadda tsohon yake ba shi umarni, yana gamawa ya sake ba shi umarnin wanke fuskarsa ya ɗura masa ruwan a cikin kunnuwansa. Ruwan ya gani ya fara kaɗawa a hankali, daga baya kuma ya ga igiyar ruwan tana katantanwa da su. Yana shirin guduwa tsohon ya riƙe shi tsam a jikinsa, ganin a kowanne lokaci yana iya halaka ya sa Kamalu runtse idonsa. Sannu a hankali ya ji komai yana lafawa, hakan ya sa shi buɗe idonsa suka fara takowa suka fito daga ciki. Wani irin sauti yake ji cikin sigar kururuwa da neman ɗauki, lokaci ɗaya ya ji zuciyarsa na fisgar gangar jikinsa. Tafiya yake yi ba tare da ya san wurin da yake jefa ƙafafuwansa ba har ya zagaya wurin da yake jin ƙarajin sautin na kusantarsa a bayan ɗakin Mai martaba. A saitin kusurwar yamma ya hangi wani mulmulallan abu baƙi saboda duhu bai tantance takamaiman mene ne ba. Cikin dakiya da ƙarfin zucuya ya sa ka hannu da niyyar tonowa take zoben hannunsa ya mamaye wurin da haske, a nan ya yi tozali da wani abu mai tsananin wari da siffar jarirai har sai da ya ji tamkar ya amayar da kayan cikinsa. Tsaki ya yi cike da jin haushin abin da ya aikata, shi kansa bai san dalilin da ya sa shi aikata haka ba, ya dai ji ba za iya haƙura ba har sai ya taimaki abin da yake cikin ƙarƙashin ƙasar. Koda ya koma sama da ƙasa ya nemi Dattijon ya rasa, a bakin ƙofar ɗakinsu ya hangi Baffajo yana kai wa da kawowa yana ganin Kamalu ya ƙarasa yana tambayarsa inda ya je.
"Baffajo fitsari ne ya tashe ni, na ga kana bacci shi ya sa ban tashe ka ba." Ya tsinci kansa da ƙin faɗa wa Baffajo gaskiyar abin da ya faru. Riƙo hannunsa Baffajo ya yi tsam kamar wani zai ƙwace shi suka ƙarasa cikin ɗakin, ƙwallah ce ta ciko idanun Baffajo ya furta. "A wannan farautar da aka yi mana mun rasa Salele Kamalu yanzu haka ban san duniyar da ya nufa ba, don Allah kada ka yi yunƙurin abin da zai raba ni da kai, ka ga wancan rafin dai an ce hallaka mutane yake don Allah koda wasa kada na ga gilmawarka a wurin." Kamalu ya jinjina kai sannan ya koma ya kwanta cike da tausayin mahaifinsa.
Tun da asubar fari aka tashi duka Bayin da ke sashen kamar yadda aka sunnanta musu, bayan sun idar da sallar asuba Uwar Bayi ta shiga raba wa sababbin Bayi aikin da za su gudanar, waɗanda suka san aikinsu kuwa suka ci gaba ɗorawa daga inda suka tsaya. Sai da rana ta fara fitowa sannan suka samu zarafin kai abinci cikin bakunansu, Mai gado ita da Inna wuro kusan ɗura suka yi wa kansu da sauran baƙin Bayin da aka kawo su rana ɗaya. Baiwa Fatsim na ganin yadda suke cin abinci ta saki shewa tana yi musu kallon sheƙeƙe ta furta. "Ahayye! Allah na dawo inji kishiyar mai yaji, duk wannan feleƙen da kuke yi gumi ce ba ta yi gumi ba. Amma da sannu za ku gane karatuna." Gabaɗaya babu wanda ya tanka musu, wata Dattijuwa da suka ji ana jira da Uwar tuwo ta ƙarasa wurin ta ce, "Tun wuri ku cire kawaici da kara ku fara ƙwatar wa kanku 'yanci idan ba haka ba kowa takaku zai yi kamar takalmin sawarsa. Wannan gidan yana da matuƙar bambamci da wuraren da kuka fito..." Sallamar Jakadiya ta katse ta, fuska a haɗe ta dube su ɗaya bayan ɗaya. "Zan ɗebi sababbin Bayi gabaɗayanku zan kai ku sashen Fulani Umaima tana son zaɓar waɗanda suka yi mata domin tana buƙatar ƙarin masu yi mata hidima." Jin babu wanda ya tanka mata ya sa ta buga musu tsawa, jiki na rawa duka suka miƙe sai Inna wuro da ke faman jera loma da sauri don ita idan tana cin abinci tana tashi duk daɗin abinci ba ta iya cinsa, ballantana a nan da abincin dare da suka ci ko kaɗan bai ishe su. Jakadiya ta leƙa ganin Inna wuro na zaune. "Ke ce shafaffiya da mai ba ki ji abin da na ce ba?" Baki na rawa Inna wuro ta sanar da ita uzurinta, ai kuwa lokaci ɗaya ta ji an kwashe mata da dariya.
"Ke a tsammaninki tun da kika shigo masarautar nan kina da sauran ikon da kanki? Ko kin manta matsayinki na Baiwa ne? Idan ba ki sani ba ki sani a yadda kika a cikin gidan nan sai yadda aka yi da ke, idan aka so ki kwana a tsaye dole ki kwana, gara tun wuri ki yakicewa kanki ɗan guntun 'yancin da kike taƙama da shi." A sanyaye Inna wuro ta tashi, idanunta suka ciko da ƙwalla. A duniya babu abin da ta tsana sama da yarfi da tozartawa. Babu yadda suka iya haka suka bi bayan Jakadiya haka kawai Mai gado ta tsinci gabanta na matsanancin faɗuwa, tun da suka nufi sashen Fulani Umaima Jawahir ke wani irin mutsu-mutsu har zuwa lokacin da Jakadiya ta sa suka jeru ɗaya bayan ɗaya. A hankali ta fara bin Bayin tana duba su a wulaƙance cikin yarfi da ƙasƙantarwa. Tana zuwa daidai kan Mai gado gabanta ya yanke ya faɗi, ta dube ta a yamutse. "A sauko da wannan jaririyar." Ba musu Mai gado ta kunto Jawahir da jikinta ya yi wani irin sanyi kamar wacce aka ciro daga ƙanƙara. Sauke idanun Fulani Umaima a kan ƙwayar idon Jawahir ya haddasa mata matsananciyar faɗuwar gaba, kalaman Bamaguje suka faɗo mata. Ba ta sake tsinkewa da lamarin ba sai da ta yi tozali da goshinta.
😁😁 Yanzu ne za a fara buga wasan, Shin me yake shirin faruwa tsakanin Fulani Umaima da Jawahir. Wai ma wace ce Jawahir ɗin nan kuma mutum ce ko Aljan?
Ina Dattijon nan kuma me ye alaƙarsa da Shu'umar Masarauta, wai ma me ye silar wannan abubuwan da ke faruwa? Akwai ɓoyayyan sirri mai ƙarfi da Dattijon nan ya sani mai ya sa bai aiwatar da komai ba sai da Kamalu ya zo. Wai shin Bayin Masarautar da shi Kansa Sarki Abdul'aziz za su gane shi ɗin jinin masarauta ne? Idan Fulani Umaima ta fahimta me kuke tunanin za ta aiwatar? Ina labarin Abubakar zai warke a nan gaba ko a'a?😢 Fulani babba tana warkewa daga cutar fitsari ko bata warkewa?
Maza hanzarta kada ki bari a yi babu ke, salon labarin daban yake. Namu ba irin nasu ba ne💃🏼💃🏼💃🏼 na san ba ku manta da BAƘAR DAULA ko AN YA BAIWA CE da ZAUJATU JINNUL-ASHIQ ba. Kar ki bari a yi babu ke wannan kafcan.🥳🥳🥳💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
[8/20, 7:22 PM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️
1
A duk lokacin da Allah (S.W.A) ya ƙaddara wanzuwar hallitar Ɗan adam a doran ƙasa, ko ya ƙi ko ya so akwai waɗansu abubuwa da suke yin jerin gwano a gangar jiki da ruhinsa. Inuwa! Wata aba ce da Ubangiji ya ke ƙaddara wanzuwarta manne a jikin kowanne abu, walau mai rai ko akasin haka. A kodayaushe tana bibiye da su matuƙar bawa zai zuba maganansa zai lura da haka. Kalmar ƙaddara! Kalma ce mai ɗauke da rassa biyu walau ƙaddara mai kyau ko kishiyarta. Ƙaddara abokiyar tagwaitakar inuwa ce domin bawa ba ya taɓa shallake wa ƙaddararsa, sanin haka ya sa na fahimci karin maganar Malam bahaushe ta: 'Tun ran gini tun ran zane." ta zauna ɗaram kwatankwacin yadda ake ɗora ƙwarya a gurbinta.
10/06/1022
Shekara Dubu Ɗaya baya.
Hankalinsa ya fi na kowanne lokaci kai wa matuƙar ƙolokuwar tashi, yana tafe yana taku da sandarsa Waziri da sauran muƙarraban cikin daular suna take masa baya. Tamkar waɗanda saƙon mutuwa ya dirar wa haka fuskokinsu suka fasalta saƙon da ke ƙunshe cikin birnin zuciyoyinsu. Sarki Damina yana kai ɗora ƙafarsa kan jan dutsen da ke a matsayin matattakalar benen hawa tsauni tsidik! Wani gajiyayyan talakansan ya dira a gabansa cikin firgice da tashin hankali, kuka yake tamkar hawayen idanunsa za su ƙare. Ya ruƙo ƙafafuwan Sarki Damina a ɗimauce yana faɗin, "Ya kai babban Sarki, Sarkin sarkunan duniya bakiɗaya sarkin da yake share mana hawaye. Ka taimaka ka roƙar mana afuwa wurin Sarauniya Sha-kundum, yanzu haka ɗana Rabo yana can yana aman jini ta hanci ta baki don mai ɗakina naƙuda take jini ya ɓalle mata tana gangarar..." Tun bai rufe baki ba Sarki Damina ya daka masa razananniyar ƙarar da sai da hantar cikinsa ta kaɗa, yana shirin sake magana Sarki ya fisgi takobin da ke maƙale a kafaɗar Waziri kafin Bawan ya yi wani yunƙuri tuni ya sauke kansa ƙasa. Da sauri wasu ƙaratan Dogarai suka ƙarasa wurin suka zube suna yi wa Sarki godiya, "Godiya muke Sarki Damina mai masoya da yawa, Sarauniya Sha-kunduma ta yi ruƙo da hannayenka. Haushin zuciyarta ya gushe domin ta faɗa mana hanyar maganin samun lafiyar Yarima, idan wannan bai wadatar da kai ba ka yi mana umarni mu kawo maka wani ko da a cikin mu ne ka sake datse rayuwarsa matuƙar zai sanyaya zuciyarka" Bai tanka musu ba ya miƙa wa Waziri takobin da ke ɗigar da jini, har sun cicciɓi gawar bawan da kansa tuni ta samu mutsuguni a gefen wata bishiya, Sarki ya dube su yana cewa. "A gaggauta ƙone gangar jikinsa tare da yaron nasa da ba shi da lafiya. Ita kuma mai ɗakinsa a zaro jaririn cikinta a kai wa babban dodo sannan a salwantar da gangar jikinta" Yana gama magana ya haye kan tsibirin maƙarrabansa suna biye da shi a baya.
Kamar yadda yake farillah a wurinsu duk lokacin da za su shiga cikin kogon dutsen a yanzu ma sai da suka aiwatar, sai da kowannensu ya saka ƙanƙanuwar aska ya yanki gefen ɗan yatsan hannunsa suka yarfar da jinin a jikin wani sassaƙaƙƙaen gunki, hannun gunki ɗauke yake da kwari da baka daga bayansa an jingina masa takobi a jiki. Kansa a sunkuye yake alamar ƙasƙantar da kai ga wani dungulmin kan mace da suka ɗora masa a gadon bayansa. Sarki Damina ne ya fara yin gaba sannan su Waziri suka rufa masa baya, daga bakin shiga dutsen suka tsaitsaya don sun san ko karan hauka ne ya cije su ba za su taɓa haure bakin ƙofar dutsen ba. Kai tsaye Sarki Damina ya kutsa ciki sandarsa ta zame masa abokiyar tafiya. Daga tsakiyar kogon dutsen ya hangi Boka Mai zamani zaune da wasu ƙanana tukwane a gabansa, daga shi sai ganyen ayaba wanda ya yi makari don rufe al'aurarsa.
"Yau ba ranar zuwan ka ba ce kamar yadda yake a bisa al'ada, me yake tafe da kai don na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa." Boka mai zamani ya faɗa yana karkatar da hankalinsa wurin Sarki Damina. Duk tsananin izza da taƙama irinta Sarki yau ya sauke ta a gefe ya fusakanci Boka yana mai bayyana damuwarsa, Sarki Damina ya zube gwiwowinsa kamar wanda ya aikata wani mummunan zunubin da yake neman gafara. Murya ɗauke da damuwa ya furta, "Ya kai Boka Mai zamani lamarin halin da talakawanmu suke ciki tabbas tura ta fara kai bango. A yau mun wayi gari da samun ɓillar annobar haɓo a cikin gari fiye da tsammani, babban abin da ya ɗugunzuma hankalina