Showing 9001 words to 12000 words out of 42008 words

Chapter 4 - SHUUMAR MASARAUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Apr 2025

3358

Jakadiya ta ɗauki Yarima ta wuce da shi turakar Mai martaba. Farinciki fal fuskarsa ya karɓi jaririn yana jin son shi a zuciyarsa don ya jima yana mafarkin samu ɗa namiji. Huɗuba ya yi masa da suna Abubakar sannan ya ba wa Jakadiya ta mayar da shi, Jakadiya na mayar da shi Fulani ta rungume jaririnta suka kwanta bacci. Jakadiya da kanta ta sanar da Baiwa Zainaba a kan duk wanda ya zo mata barka a ce masa tana hutawa. Sai a lokacin ita ma Jakadiya ta wuce can sashensu na Bayi ta samu ta yada haƙarƙarinta don ta yi ramuwar baccin daren da ba ta yi ba.

Fulani Umaima tun da ta dawo ta kasa zaune ta kasa tsaye don burinta bai wuce ta ga ta aiwatar da abin da Bamaguje ya umarce ta ba. A yadda ta jingine Baiwa Maimuna a haka ta same ta a bayan ƙofa, bayan ta idar da sallar asuba ta riƙo hannun Maimuna tana faɗin, "Wuce mu je sashen Mai martaba." Babu musu Maimuna ta fara tafiya tana biye da Fulani. Duk da ta aminta ɗari bisa ɗari da hatsabibancin Bamaguje, a lokacin da ta fita harabar da Bayi suke kai wa da kawowa sai da gabanta ya faɗi, jikinta ya ɗauki rawa tana tsoron kada su ankara da Maimuna wacce take tafe da ƙwaƙwulallun idanuwa asirinta ya tonu. Amma ga mamakinta duk wurin da ta gifta sai dai Bayi su riƙa zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa. Cike da izza, ɗagawa, faɗin rai da alfari Fulani Umaima ta ci gaba da taku ɗaiɗai tana kallonsu a banzace ba tare da ta amsa ba ta wuce. Ba su yi mamaki ba domin ba wannan ne karo na farko da ta saba yi musu haka, wulaƙanci da tozarta na ƙasa da ita kamar a jininta yake don haka kowannensu ya sake shiga taitayinsa. Lokacin da ta isa sashen Sarki Abdul-aziz shiru ta ji wanda hakan ya alamta mata baya nan, can gefen gadon sa ta zaunar da Maimuna sannan ta fara jiyo motsi daga jikin windonsa. Tana leƙawa ta hango Takawa a cikin lambun shaƙatawarsa zaune a kujera a gefensa ɗawisu ne da ƙananan tsuntsaye suke ta kaiwa da kawowa. Har ta nufi ƙofar da za ta sada ta da lambun ta tuna ba ta ɗauko sihirtaccen turarenta, da sauri ta fice don kar Sarki Abdul'aziz ya dawo ba tare da ta kammala shirinta ba. Da fitarta ba a ɗauki minti biyar ba Sarki Abdul'aziz ya taso kai tsaye ya nufo cikin turakarsa, gabansa ya ji ya yanke ya faɗi ƙwarin gwiwar da ke tattare da shi ta tarwatse. A razane yake bin kan gadonsa da kallo, sakamakon ƙwaɗayin idanunsa da suka hango masa abin da ba yi tsammani ba.

Fulani Umaima na zuwa ta wuce ta zaro akwatinta da ke ƙarƙashin gado, ta buɗe ta da niyyar ɗaukon turaren amma zuciyarta ta fara kwaɗaita mata son sanin abin da yake ƙunshe a cikin littafin da Bamaguje ya damƙa mata. Ta sake tuna matuƙar ta rasa karatunsa a wannan ranar sai dai ta bari zuwa wani makon mai zuwa. Ɗaukan littafin ta yi ta koma gefen gado ta zauna, za ta sa hannu ta buɗe ta tashi da sauri ta je ta saka kuba a ƙofarta ta rufe sannan ta sake komawa ta buɗe shafin farko daga cikin littafin, ƙwayar idonta ta sauka a kan jimlar farko da aka yi rubutunta da ajami.

BAN SAN KAINA BA

Da mamaki ta sake furtawa da bakinta, "Ban san kaina ba! Me hakan yake nufi?" Duk harsashen kwanyarta ta gagara lalubo mata amsar tambayarta don haka ta sake mayar da kanta ta ci gaba da karatun.

Ban san mizanin tubalin ginin da ya dace na jingine rayuwata ba, balle na san kaina da abin da rayuwata ta ƙunsa, abu ɗaya na sani ban san kaina ba. Ban san wace ce ni ba domin kuwa wata hallita ce ke sarrafa zuciya da ruhin gangar jikina. Ban san asalina ba ballantana na binciki dangina, hasali ma kusan duk wani Bawa ko Baiwa da za ka gani a cikin masararutar Kabbab kusan kowa akwai tushe da asalin yankin da ya fito, nawa asalin ya yi rauni dalilin da ya sa ko a cikin Bayi na kasance ƙasƙantacciyar baiwa. Wacce take fuskantar tsangwama, kyara da duk wani nau'in cin zarafi saboda babu mutum ɗaya da zan kalla da sunan dangina. Har ya zame mana jiki a kowacce rana idan rana ta take muna karkasuwa ɓangare-ɓangare domin gudanar da ayyuka daban-daban. Ni da su Dije muna ɓangaren bangon yamma muna sirfen geron da za a yi wa su Fulani fura da shi, a lokacin rana ta take sosai daga bayana na ji an saka hannu an dafa kafaɗata wacce na ke kai taɓarya ina yin surfe da ita. A hankali na waiga ƙwayar idona ta sauka a kansa, cike da fargaba da sake waro idanuna haɗe da tattaɓa gefen fuskarsa don tabbatar da ƙwayar idona ba yaudarata take ba. Tun ban fi shekara biyar a duniya ba nake mafarkinsa ba dare babu rana, domin a duk lokacin da zan yada haƙarƙarina gangar jikina ta samu hutu bacci ya yi awon gaba da ni sai na yi mafarki da wannan hallitar. "Ki taya ni murna da farinciki domin na samu 'yancina, na zama kamar kowa mai ɗauke da rayuwar gashin kai. Na yi miki alƙawarin sai na karɓo miki karagarki, a kullin Kaka na sake jadadda mini mu tabbatar da mun ba wa alƙawari muhimmanci kuma mun cika shi, wannan zai dawo da ƙima da martabar ahalinmu, wacce zuri'armu ta tarwatse silar cin amanar da aka yi mana." Kalamansa suka mamaye masarrafar jina, mamakina ya ninku dalilin ganin ƙwalla na zuba daga ƙwayar idonsa.

"Ke Hidaya kar ki raina wa kanki hankali, kina nufin mu za mu ci gaba da surfen kina can kina kalle-kalle banza da wofi? Wallahi kika bari muka surfe na cikin turmin nan sai dai ki surfe wannan kwano ukun ke kaɗai." Kalaman Safare suka katse ni, da sauri na waiga wurinsu kowaccensu ta sakar mini harara kamar idanunsu zai faɗo. A zuciyata na furta. "Ko dai su Safare ba sa ganin wannan saurayin?" Daga bayana na ji ya sake taɓo ni. "Ba za su taɓa ganina ba, saboda wasu muhimman abubuwa. Ke ma akwai dalilin da ya sa kike rayuwa a cikin Masarautar nan har kike mu'amala da su. Ki ci gaba da haƙuri kin san idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi." Yana gama furta mini waɗannan kalaman na neme shi na rasa. Wata irin azaba ta riyarci ƙafata sakamakon wurgo mini taɓarya da su Safare suka yi, na sunkuya cike da azaba ina matsa ƙafata. "Ga shi nan ki yi ki surfa ragowar, kuma kin fi kowa sanin halin Uwar tuwo matuƙar aka gama surfen aka bar ki a baya za ki yaba wa aya zaƙinta."

Idanuwana na kai kan ƙwaryar da ke cike da gero har kusan kwano uku, tausayin irin wuyar sirfen da zan sha ya mamaye ni. Dole ƙanwar na ƙi, na sunkuya na ɗauko taɓarya kafin na ɗago na ji saukar bulala a tsakiyar bayana, azaba ta sa na wurgar da taɓaryar ina ihu haɗe da soshe-soshe. Ragowar mutanen da ke wurin babu wanda ya motsa ballentana na saka ran wani daga cikinsu zai kawo mini ɗauki, sai da Uwar tuwo ta gaji da dukana don kanta sannan ta nuna ni da murtukekiyar dorina.

"Ki yi gaggawar ƙarasa surfen gabanki idan ba haka ba wallahi sai na sa Balele ya kai ki ɗakin duhu, shegiyar yarinya da idanu kamar na ƙwanƙwamai." Tun ba ta ƙarasa zagina ba na suri taɓaryar da a tsaye ta kusan tsayina, jiki na karkarwa na fara daka cike da tashin hankali. Ganin haka ya sa Uwar tuwo ta yi gaba tana buga wa sauran Bayin da ke tsaitsaye tsawa, da tafiyarta babu jimawa waɗansu zaratan samari biyu suka kewaye ni.

"Shugaba wannan ba aikinki ba ne." Mamaki ya lulluɓe ni domin ko a mafarki ban taɓa cin karo da su ba, haka kuma suturun jikinsu bai yi kama da kayanmu na bayi ba. Na sake mamakin kalamansu da suke kirana da shugaba. Tsaye na yi ina bin bayan Uwar tuwo da kallo samakon har lokacin ina hango ta sai da ta ɗan yi nisa da ni, takaicin dukan da ta yi mini ya mamaye ni na fara ayyana da ina da hali sai na karɓi doriyar hannunta na zane ta ita ma ta ji irin abin da muke ji. Ihun da na ji Uwar tuwo na yi ne ya dawo da ni hayyacina, na kai ƙwayar idona wurin cikin mamaki nake bin ta da kallo. Kamar yadda na ayyana haka Uwar tuwo ke tsalle tana ihu, hatta ni da nake nesa da ita haka na riƙa jiyo sautin saukar dukan da ake yi mata.Ta jima cikin wannan halin sannan ta faɗa gefe ɗaya tana sauke ajiyar zuciya, kamar wacce aka ce na waiga ina juyawa wurin turmin na yi tozali da abin da ya daskarar da ni. Gabaɗaya geron da ke wurin an surfe shi an dake mini tas, tsoro ya mamaye ni da ganin wannan lamarin. Duk da ba sabon abu bane a wurina na ji kalamai daga cikin zuciya, amma a wannan karon na razana, "Kada ki tsoro ta Shugaba domin firgici ba hali ko ɗabi'ar ahalinku ba ne." Jin haka ya ƙara mini ƙwarin gwiwa na ɗauki ƙatuwar ƙwaryar na ɗora ta a kaina da ƙyar, kafin na ƙarasa wurin da Uwar tuwo ke kwance tuni Bayi suka taimaka mata aka kai ta can ɓangarenmu na Bayi. Kallo ɗaya za ka yi wa Bayin da ke wurin ka fahimci kowa ya sha jinin jikinsa, don babu hayani tsit wurin ya yi kamar an yi mutuwa.

Kamar kullin idan kowannenmu ya dawo daga sashen da yake yi wa hidima, mukan taru a sashenmu na Bayi. Zaune muke gabaɗaya a tsakar gida, wasu daga cikinmu na zaune kusa da yayyansu suna wasa. Waɗanda suke da ƙanƙarta shekaru kamar nawa da ba su wuce sha uku ba suna kwance a jikin iyayensu, idanuwana suka ciko da ƙwalla sakamakon ganin ni kaɗai ce wari ɗaya ba ni da makusanci. Ko da ba ni da iyaye ya kamata wasu su tausaya mini su ƙaunace ni kamar yadda na ga wasu Bayin da aka samo marasa iyaye ake kula da su, me ya sa na kasance mai baƙin jini kowa ba ya ƙaunata?" Ba zato daga gefen kunnuwana na ji an furta mini.

"Ke kike da kowa Hidaya! Kada ki karaya domin lokacin na nan da za ki tabbatar da haka." Abin ka da mai shirin kuka an jefe shi da kashi awaki nan take hawaye ya fara kai-kawo a ƙwayar idona. Jiki a sanyaye na miƙa zuwa gaban Jakadiya na tsugunna, da mamaki gabaɗaya suka juyo suna kallona. Ban damu da irin ƙalubalen da zan fuskanta ba, babban burina bai wuce ni ma na san wace ce ba.

"Lafiya kika zo kika saka ni a gaba kamar tsohuwar mayya?" Gabana na dakan lugude na tattaro kalaman bakina da na guntso na fesa mata. "Don Allah Jakadiya su waye iyayena?" Kamar haɗin baki haka na ji sun tuntsire da dariya, sai da suka yi mai isar su sannan Jakadiya ta nuna wurin da Uwar Bayi ke zaune. "Akwai tarin bayanai dangane da samuwarki, ki tafi wurin Uwar Bayi za ta warware miki zare da abawa." Cike da ƙwarin gwiwa na miƙe cikin sassarfa na isa gaban Uwar Bayi, na baje tagwayen kunnuwana ina sauraron makoma da tushena.

Ajiyar zuciya Fulani Umaima ta sauke ta kai hannu ta rufe shafin littafin ba don ta gaji da karatun wannan hargitsattsan labarin mai cike da rikitar da kwanyar mai karatu ba. Mayar da littafin ta yi cikin akwatinta sannan ta ɗauko turaren da take amfani da shi a duk lokacin da za su yi wata mu'amala da Mai martaba. A cikinta ta soke shi sannan ta rufe ɗakinta ta fice kai tsaye ta wuce sashen sarki Abdul'aziz, haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa ba tare da ta san dalili. Babban tashin hankalinta bai wuce kada laƙanin jikin Takawa ya wargaza mata shiryayyan shirin ta a kan Maimuna ba.

_Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚
07062062624.
[10/4, 11:48 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA*


©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.

SHAFI NA BIYAR


Cikin mugun yanayin ta kafe shi da ƙwalaƙwalan idanuwanta masu razana duk wanda ya yi tozali da ita, a hankali Sarki Abdul'aziz ya fara ja da baya jikinsa na karkarwa. Bai yi tsammani ba ya ji bayansa ya bugu da bangon ɗakin, cikin tsinkewar zuciya yake sauke ajiyar zuwa. Da wata irin sanɗa ta taso daga kan gadon tana durfafo wurin da yake tsaye, ganin tana gabda cin masa ya sa ya fice da sauri daga cikin ɗakin ya ƙarasa wurin dogaran da ke tsaron sashensa. Yanayinsa kaɗai ne ya tabbatar musu da tabbas Takawa yana cikin damuwa, tun bai ƙarasa wurinsu ba suka zube cikin girmamawa. "Allah ya taimake ka ya ƙara lafiya da nisan kwana, ɗawisu sarkin ado mai taƙama da ikon Allah..."

"Ya aka yi kuka bar waccan hallitar ta shiga har cikin turakata?" Mai martaba ya katse su fuska a tamke babu ɗigon fara'a.

"Tuba muke ranka shi daɗe, Allah ya huci zuciyar amale a gafarce mu wannan ne na farko na ƙarshe." A daidai lokacin Jakadiya ta ƙarasa ita da Baiwa Saro hannunsu ɗauke da kayan lambun da ake kai wa Sarki Abdul'aziz kamar wannan lokacin. Dogaran ta gani sun nufi turakar Takawa kafin su ƙarasa su ka ga wata baƙar mage ta fito daga cikin turakar idanuwanta jawur kamar gauta tana bin mutanen wurin da wani irin kallo. A zabure Jakadiya ta furta. "Ka gafarce ni uban gidana ka yi mini afuwa, amma ba ni da masaniya game da sakacin Dogaran ƙofa da har suka bar kyanwar nan ta shiga cikin turakarka." Jakadiya ta yi maganar jikinta na karkarwa don ta san a duniya babu abin da Takawa ya fi tsoro sama da mage, wannan ɓoyayyan sirri ne da ba kowa ne ya sani ba saboda gudun kada magauta su fahimci lagonsa. Ita ma Jakadiya abin da ya sa ta sani tun wani lokacin da ta taɓa shiga sashen Mai babban ɗaki (Mahaifiyar Takawa.) wata mage ta shiga har suma ya yi a wurin, kuma ko da ta ga haka sai da Mai babban ɗaki ta tsawatar mata a kan wannan sirrin.

"A kiyaye gaba, ba na buƙatar sake ganin kowacce hallita a sashena." Gabaɗaya suka amsa masa cikin girmamawa. Jakadiya da kanta ta shiga ta jera kayan lambun kamar kullin sannan suka fice bayan ta tambayi Takawa ko akwai wani abin da yake da buƙata, ya ba ta amsa fuska babu walwala. Har bayan wani lokaci Sarki Abdul'aziz bai saki jikinsa ba, ganin bai sake jin motsin komai ba ya sa ya ɗan saki jikinsa.

Cike da ƙwarin gwiwa Fulani Umaima ta ƙarasa cikin turakar Mai martaba, ganinsa zaune a gefen gado kusa da baiwa Maimuna ya sa ta zaro idanu cikin fargaba har sai da ya fahimci ruɗewar da take ciki.

"Lafiyarki Umaima?" Cikin kissa ta daidaita nutsuwarta ta ce, "Dama na yi mamaki ne ganinka shiru, kar dai ka jima kana jirana." Murmushi ya sakar mata haɗe da girgiza kai. Ta ƙarasa wurinsa asirtaccan ƙamshinta ya ratse hancinsa, ya lumshe ido cike da jin daɗin ƙamshinta.

"Ki tabbata kin sa shi ya shiga bayan gida kafin ki saka wa Maimuna turare a gabanta."
Kalaman Boka Bamaguje ya dawo mata raɗau a cikin kunnuwanta. Miƙe wa ta yi ta furta. "Sarkina bari na haɗa mana ruwa mu ɗan watsa ko?" Ba ta jira cewarsa ba ta nufi banɗaki ta haɗa komai da kanta sannan ta zuba turaren da Bamaguje ya bata, bayan dawowarta ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa sannan suka wuce banɗaki. Da kanta ta ɗebi ruwan ta watsa masa cikin sigar tsokana, sai kuma ta yi farat ta furta. "Na yi mantuwa."

Kallon da ya yi mata ne ya alamta mata yana buƙatar ƙarin bayani daga gare ta.

"Ina zuwa." Kawai ta furta ta fice a gaggauce. Sai da ta tabbatar da ta rufe ƙofar ta baya sannan ta koma turakarsa cikin sauri ta ɗaga doguwar rigar Maimuna ta kwara mata turaren a ƙasanta sannan ta shafa mata a fuskarta, ita ma ta murtsuke jikinta da shi ta rage kayan jikinta ta sake komawa cikin banɗakin. Tana shiga ƙamshinta ya daki hancinsa, take ya ji wani irin yanayi ya tsarga masa. Buƙatar ya kusance ta ta yunƙuro masa, ganin saƙwannin da yake aika mata ya tabbatar mata da haƙonta zai cim ma ruwa, don haka ta fara neman shawarar da za ta yanke wa kanta. A hankali ta yakice shi tana faɗin, "Sarkina a banɗaki muke mu ƙarasa turaka." Bai musa mata ba, ta ƙarasa sheƙa musu ragowar ruwan sannan suka fito hannunta na riƙe da shi, idanuwansa a rufe suka ƙarasa don haka ko da ta zaunar da shi a gefen gado ta ga ya rarumo Baiwa Maimuna da ke zaune kamar gawa. Fulani Umaima ta koma gefe ta zuba masa ido zuciyarta ƙal, tana nan tsaye Takawa ya gama mu'amalarsa da Maimuna ya koma gefe ɗaya sai gani ta yi numfashinsa ya ɗauke. Da sauri ta ƙarasa ta ɗebi najasar jikinsu ta isa bakin rijiyar da tun da take shiga cikin turakar ba ta taɓa taka wurin ba, wata irin kuɗa ta fara ji a cikin kunnuwanta ga wata 'yar juwa-juwa da take ji sama-sama. A haka ta samu ta zuba najasar a kan rijiyar take murfinta ya buɗe, wata baƙar ƙura ta turnuƙe ta. Sai daga baya komai ya washe, ganin haka ya sa Fulani Umaima ta koma ta janyo hannun Baiwa Maimuna sai da suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login