Showing 15001 words to 18000 words out of 42008 words

Chapter 6 - SHUUMAR MASARAUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Apr 2025

3356

nake ji ta fara rikiɗa zuwa muryar da nake jin tamkar na taɓa sanin mamallakiyar muryar.

"Barka da zuwa Sarauniya."
Na ji an furta. Waige na fara yi amma ban ga kowa ba, na riƙa jin busar sarewa a tsakar kaina ba tare da na ga masu yi mini ba. Ina nan tsaye na ji Uwar Bayi na faɗin.

"Ku yi hanzari kada ku fusata Fulani kuke tafe laƙai-laƙai kamar marasa laka a jiki." Da sauri na ci gaba da tafiya har muka ƙarasa babban rufar Fulani da ta ƙayatu da kayan alatu kala-kala. Kaina na ji ya yi girma wata irin ƙasaita, isa da tsantsar izzar mulki na ratsa ni, da ƙyar nake taku cikin ƙasaita. Uwar Bayi da sauran Bayin da muka taho tare suka tsaya cak a bakin wata mashinfiɗa wacce bayi suke tsayawa idan sun shiga wurin Fulani Hauwa kulu. Ban kalle su ba na zarce kan ƙasaitacciyar karagar da ke cikin falon, na zauna ina kallon su Uwar Bayi ɗaiɗai. Da zamana na ji wani abu ɗau! Yana zagaye ƙoƙon kaina. Uwar Bayi kusan mutuwar tsaye ta yi ganin ɗanyan aikin da na aikata, bakinta na rawa ta furta mini.

"Hidaya...hankalinki ɗaya kuwa? Kin san a fadar wacce kike?"

"Ya kamata ki gyara linzamin harshenki, idan ba haka ba sai na sa an datse shi nan take. Wannan fadata ce..." Ashar ɗin da Fulani Hauwa kulu ta saki ya katse kalamaina, na dube ta cikin tsadaddiyar shigarta ina ƙare mata kallo.

"Uban waye ya halatta wa wannan ƙasƙantaciyyar zama a karagata?" Cikin isa da ƙasaita na ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, kamar ba zan amsa ba na ɗago ina kallonta a wulaƙance. "Wannan karagar iyaye da kakannina ce don haka ki gyara kalamanki."

Na lura da razani a saman fuskarta, ɗan yatsanta na rawa ta nuna ni. "Ta tabbata ke ce Hidaya ko?" Na jingina da jikin kujerar na furta. "Ba tsammani ba ne ni ce Gimbiya Hidaya." Wata gwauruwar ajiyar zuciya na ji ta sauke. "Tabbas da alama tarihi zai kuma maimaita kansa.

"Tarihi tuni ya sake maimaita kansa tun da gani na wanzu a gabanki."

Fulani Umaima ta rufe littafin tana jin kanta na sarawa don a kullin labarin Hidaya ƙara hargitsa kwanyarta yake. Ta wurga shi cikin akwatinta tana sakin tsaki a fili don ba ta jin za ta sake ci gaba da karanta wannan rikitaccan labarin.

Komawar su Yaya Halima Masarautarsu da kwana ɗaya labari ya dawo wa Fulani Babba na sabuwar lalurar da ta afka wa Yaya Halima na kurumcewa da makanta, hankalin Fulani Babba ba ƙaramim tashi ya yi ba. Da yake jego take yi babu damar ta tafi dubiya haka ta zauna ta ci kukanta a cikin ɗaki, ta sake ayyanawa zuciyarta ko da wasa ba za ta sanarwa da mahaifiyarta halin da take ciki ba don kar damuwa ta yi mata yawa.

BAYAN SHEKARA GOMA

Tafe suke a cikin wani baƙin ƙasurgumin daji mai matuƙar hatsarin gaske, su kansu sukan yi takatsantsan wurin shiga irin waɗannan dajijjikan sakamakon miyagun hallitu da iskokin da ke cikinsa.

"Mai gado wai ni kam kin taho mini da baƙar bakata?" Umaru ya faɗa yana sake leƙen wani koren maciji da ke saƙale da wata koriyar bishiya. "A'a Malam tsakani da Allah ni kam na manta ka san sai da na ce idan za mu fito ka tuna mini." Da sauri ya ciro wata ƙanƙanuwar kwari da baka daga cikin ƙugunsa, bai cika harbi da ita ba don haka ya so Mai gado ta taho mata da farar bakar wurinta. Ya kalli macijin haɗe da matsa wata laya da ke saƙale a wuyansa, ya sakar wa macijin harbi nan take ya tsire shi wani koren ruwa mai kauri ya fara fita daga jikinsa. Yana shirin miƙa hannu ya ciro kibiyar daga can gefensu suka fara jiyo numfarfashi, Mai gado da sauri ta fara matsawa don tabbatar da zarginta.

"Wash wayyo! Ku taimaka mini, ku kawo mini ɗauki tsafi zai taimake ku. Tsafi zai shiga lamarinku, ku taimaka mini kada na mutu idan na mutu tsafi zai yi fushi da ku." Gaban Mai gado ya faɗi ganin wata matashiyar mace mai tsohon ciki tsugunne babu kaya a jikinta, ƙugunta ne kaɗai ɗaure da ganye sai saman ƙirjinta. Kanta da wani irin cukurkuɗaɗɗan gashi ya zubo har ƙirjinta.

"Malam zo ka ga."

"Kada ki taɓa komai Mai gado, har yanzu ba ki gama sanin sharrin daji ba. Wannan ba kamar sauran dajijjika ba ne, ki yi takatsantsan." Yana ƙarasawa idanunsa suka yi tozali da matar, ta galabaita da alama naƙuda take duba da yadda jikinta ya ɓaci kace-kace. Mai gado ji ta yi ba za ta iya daurewa ba don haka ta ƙarasa ta ruƙo ta tana faɗin.

"Baiwar Allah me ya kawo ki naƙuda cikin dokar dajin nan?" Wani irin nishi suka ji ta yi cikin galabaita da fita hayyaci tana faɗin.

"Tsafi, tsafi ka dafa mini. Abin bauta ka tserar da jinina ko ɗon ta gagara magautana, tsafi ka taimaka mini." Rufe bakinta babu jimawa suka ji ta ƙwalla ƙara nan take ta haifo jaririyar 'yarta mai tsananin kama da ita. Mai gado na shirin taɓa jaririyar da sauri matar ta dakatar da ita, ta hanyar ture hannunta tana girgiza mata kai.

"Zuri'ar RUMZU daban take da sauran al'umma, idan muka haihu tashin farko jinin wata al'umma ba ta isa ta taɓa mana 'ya'ya ba har sai mun gama da 'ya'yanmu ake taɓa mana su. Idan ba haka ba yanzu za ki mutu, abin bauta zai hallaka ki." Mai gado ta ɗan zaro idanu cikin tsananin mamaki. Umaru da ya juya bayansa ya jinjina kai yana taɓe baki.

Hannu ta sa a ƙugunta ta ciro wata ƙaramar baƙar aska ta yanke wa jaririyar cibiya, ta sa wata siririyar fata ta ɗaure cibiyar tamau. Hannunta ta saka ta lakuto jinin da ke fita daga ƙasanta ta shafa a saman goshin jaririyar lokaci ɗaya jaririyar ta tsanyare da wani irin matsanancin kuka, jinin da ta lakata mata a goshi ya shiga wata irin tafarfasa a kan goshin jaririyar. Wani irin baƙin jini ya fara zuba daga cikin hancin jaririyar, kunnuwanta da ƙasanta. Mai gado tana tsaye tana kallon abin da matar take yi cikin al'ajabi da tsananin mamaki har sai da tsoro ya fara kamata. Ganin jinin ya zarce ƙa'ida ya sa matar ta saka bakinta ta zuƙo shi sannan ta fesar a gefe, take ciyawar wurin ta ƙone ƙurmus. Ta jima tana zuƙe jinin jikin jaririyar tana ɗiban jinin gabanta tana zubawa a goshinta, idan ya tafasa sai ya shige jikin jaririyar.

Sai da matar ta gama ta ɗago ta dubi Mai gado cikin karyewar zuciyata tana faɗin, "Ban san ku su waye ba, amma na tabbata daga yanayinku ku masu karamci ne kuma tsafi zai shiga lamuranku ya dafa muku..."

Da sauri Umaru ya waigo ya katse ta. "Baiwar Allah mu ba mu dogara da tsafi da sihiri ba, mun dai dogara da Ubangijin sammai da ƙassai." Jinjina kai ta yi tana murmushi ta furta.

"Koma da wa kuka dogara ban damu da na sani ba, zan bar muku amanar 'yata domin na san dangina ba za su bar ni ba mutuwa zan yi, don na hangi tsinin mashin tsafin da Mahaifina ya wurgo min, idan ban damƙa muku ita ba tabbas har ita za su hallaka mu. Ba a nan doron ƙasa ba, ko ƙarƙashin ƙasa na nutse matuƙar ina numfashin na tabbata zuri'ata ta Rumzu ba za su bar ni ba." A firgice suke kallonta.

"Wace ce ke? Mutum ce ko aljan?" Mai gado ta wurga mata tambaya a tsorace.

"Sanin matsayin hallitata ba shi ne mafita ba, domin a yanzu ba lallai ya amfane ku da komai ba. Ga amana zan bar muku ku dubi darajar abin bautarku ku riƙe ta amana, na so a sanya mata suna HAIZAT amma dalilin mahaifinta ya nunke nawa don haka ya ce mini ya fi son a saka mata sunan JAWAHIR, ban san ma'anar sunan ba don ba ya daga cikin sunan zuri'ata. Sai dai na tabbata wannan sunan zai amfane ta zuwa nan gaba, idan ta isa zama budurwa ku ɗauke zuwa bakin kowacce irin bishiyar kuka akwai ajiyar da mahaifinta ya taɓa yi wanda ita za ta tono gadon da zai bayyanar da ita jininsa ce da hannunta. Wannan jaririyar ita za ta sanar da ku asalin wace ce ni har zuwa zuri'ata ta Rumzu, tun daga zubin hallita har zuwa tushenta. Na san dangina da bibiya, kafiya da matsanancin ruƙo duk rintsi kada ku bayyana ba kune asalin iyayenta ba matuƙar za ku shiga baƙon wuri ko al'umma, wataƙila ta iya tsira da rayuwarta daga kaidinsu." Tana gama maganar ta ɗora jaririyar a kan saman wani ƙaton gidan tururuwa, ta damƙi ƙasar gidan tururuwar tana runtse idanunta haɗe da furta waɗansu irin kalaman tsafi da su Mai gado ba su taɓa ji ba, tana gamawa ta shafa a jikin jaririyar gabaɗaya, take jinin da ke saman goshin jaririyar ya ɓace ɓat. Ta sunkuya saitin kunnen jaririyar tana yi mata raɗa, lokaci ɗaya jaririyar ta yi shiru tamkar wacce take sauraron kalaman mahaifiyarta. Wani irin jini ne ya ɓalle wa mahaifiyarta amma duk da haka cike da ƙwarin gwiwa da dakiyar zuciya ta ɗauki jaririyar ta fara takawa har zuwa bakin ramin kwarmin bishiyar kukar da ke gefenta ta ɗora jaririya a ciki, ta saka hannu ta dafa saman goshinta nan take suka ga ta fara wata irin jijjiga, idanunta suka firfito numfashinta ya ɗauke rai ya yi halinsa.

Daga Umaru har Mai gado kusan mutuwar tsaye suka yi saboda al'ajabi don tun da suke a duniya ba su taɓa ganin makamancin irin wannan lamarin ya faru a gabansu ba. Mai gado ce ta iya motsawa ta ƙarasa ta ɗauki jaririyar da mamaki ta kalli Umaru jin jikin jaririyar ya yi wani irin sanyi kamar ƙanƙara.

"Malam yanzu ya zamu yi da wannan gawar?" Ajiyar zuciya ya sauke yana shirin yin magana suka ga gawar matar na matsawa haɗe da nutsewa cikin bishiyar kukar da take jigine a jikinta. Cikin tsoro suka ja da baya suna kallo, kafin wani lokaci babu gawar babu alamarta ta nutsa cikin bishiyar kukar sai shatin jinin da ke manne a jikin bishiyar.

Jiki na karkarwa Mai gado ta ajiye jaririyar a ƙasa tana ja da baya ta furta. "Mai gida Allah ya sani ba zan iya riƙon wannan abin ba, domin ba na ko tantama mahaifiyar yarinyar aljana ce ita kanta yarinyar dubi irin siddabarun da mahaifiyarta ta yi mata kafin ta mutu." Cike da gamsuwa Umaru ya ɗago zai yi mata magana, gabansa ne ya yanke ya faɗi sakamakon mugun gamon da ƙwayar idonsa ta yi. Da sauri ya ja hannun Mai gado suka faɗi can gefe haɗe da kurma ihun neman taimako.


_Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚
07062062624
[10/4, 11:49 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA*


©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.


SHAFI NA BAKWAI


Koren macijin da Umaru ya kashe tun kafin haihuwar matar nan suka hango ya sulalo ya kafe su da ido yana kallo tamkar zai far musu da sara, suna nan cikin tsinkewar zuciya suka ga ya ƙarasa wurin jaririyar ya kanannaɗe ta, suna daga wurin da suke a gefen Umaru ya ce. "Mai gado an ya yau mun shigo dawa a sa'a kuwa?" Da sauri ta girgiza masa kai. "Tun wuri mu kama hanyar gida." Cikin sanɗa suka miƙe da niyyar tafiya sai dai bisa ga mamakinsu babu macijin babu alamarsa, don haka suka nufi hanya da niyyar tafiya.

Cak Mai gado ta tsaya tana waige. "Tsayawar me kika yi Mai gado?"

"Mai gida zuciyata ta karaya, ba zan iya tafiya na bar yarinyar can ba. Ka dubi yadda mahaifiyarta ta aminta har ta damƙa mana amanarta. Ba mu sani ba wataƙila samunta babbar rahama ne a tattare da mu, ta wani fannin ma gani nake Allah ne ya azurta mu da samunta ka duba ka gani haihuwata huɗu duk yanzu babu rayayye, idan muka bar ta a wannan ƙungurmin dajin ba mu san wacce irin rayuwa za ta gudanar ba." Jikin Umaru ya yi sanyi ya waiga yana hango jaririyar da ke tsala matsanancin kuka. "Mu je na ɗauko ta In Shaa Allah, Allah zai kare mu tun da ya ga kyakkyawar niyyarmu." Da haka suka rankaya suka wuce har gaban jaririyar suka ɗaukota, Mai gado ta kunto ɗankwalinta ta nannaɗe ta a ciki sannan suka nufi hanyar da za ta sada su da gida. Sai da fargabar da Umaru yake ciki ba wuce irin tarbar da mutanen ƙauyensu za su yi musu ba, musamman idan aka samu akasi wani al'amarin almara ya faru kamar yadda suka gani daga wurin mahaifiyarta. Sai dai sun ɗaukar wa kansu alƙwari babu wanda za su furtawa silar samuwar yarinyar don kada ta taso cikin tsangwama da ƙyara.

Masarautar Huddam

Ɗan matashin ne mai kimanin shekara goma zaune a cikin fadar Sarki Abdul'aziz a kan shimfiɗaɗɗiyar shimfiɗar alfarma yana sanye da rantsattsiyar alkyabba. Kallon mutane yake yi ɗaiɗai fuska a murtuke babu walwala, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da mulkin gadarsa ya yi ba taka-haye ba. Gajiyar da ya yi da zaman cikin fadar ya sa ya miƙe cike da izza yana taku kamar ba zai taka ƙasar ba.

"Takawarka lafiya Yariman masarauta, a huta lafiya sarkin gobe da yardar Allah."

Fadawa suka ɗauka a lokacin da suka lura Muhsin ya miƙe da niyyar fita daga fadar, wasu daga ciki suka ƙarasa suna take masa ba. Hannu ya ɗaga haɗe da tsayawa wuri ɗaya cak, ya kusa minti ɗaya a haka sannan ya furta. "Ba na buƙatar rakiya." Lokaci ɗaya suka ja da baya sannan ya ci gaba da taku, duk hanyar da ya bi haka bayi da fadawa suke zubewa suna kwasar gaisuwa amma ko kallansu ba ya yi ballanta su saka ran zai tanka musu. Yana gab da shiga sashen mahaifiyarsa bisa tsautsayi wata baiwa ta fito da sauri don isar da saƙon Fulani Umaima, a rashin sani ta bangaje shi har sandar hannunsa ta faɗi ƙasa. Jiki na karkarwa ta zube ƙasa.

"Tuba nake shugabana, a gafarce ni uban gidana ni mai laifi ce ba tare da..." Marin da ya ɗauke kuncinta da shi ya sa haƙoranta suka datse harshenta har sai da bakinta ya fashe, idanunta suka fara zubar da ƙwalla ta sake zube wa a ƙasa tana faɗin. "Godiya nake Sarkin gobe." Ɗaga kansa ya yi ya hango wani Bafade hannunsa ɗauke da murtukekiyar bulala ya furta, "A hora ta na tsawon wuni guda da alama ba ta gama sanin a gidan masarauta take rayuwa ba tun da ba ta san aikinta ba." Yana gama maganar ya wuce ba tare da ya jira cewarsu ba.

A kishingiɗe ya tarar da mahaifiyarsa tana huatawa, wasu 'yan matan Bayi na tsugunne wurin ƙafarta suna yi mata tausa. Ganin yanayinsa ya sa ta tashi zaune haɗe da sallamarsu.

"Wa ya ɓata ranka Muhsin?" Fulani Umaima ta tambaye shi.

Bai tanka mata ba sai da ya zauna. "Wata baiwarki ce ta ɓata mini rai amma komai ya wuce."

"Wace ce ita na sa a hukuntata?" Muhsin ya fara rage kayan jikinsa. "Na sa a hukuntata, ina Ruƙayya ban ganta ba?" Fulani Umaima ta yamutsa fuska, "Za ta wuce sashen Fulani babba ne, yarinya sai baƙin nacin tsiya kamar tsohuwar mayya." Take idanunsa suka yi jawur rai a matuƙar ɓace ya saki guntun tsaki, ba tare da furta komai ba.

Ihun da Ruƙayya ke ƙwallawa ne ya ja hankalin Fulani babba da sauran bayin da ke harabar gidan, turus bayin suka yi suna kallon juna duk da ba yau ce rana ta farko da suka ga Abubakar na kama gashin duk wani mutum da ya kusance shi ba ciki kuwa har da mahaifiyarsa. Ruƙayya ƙanwar Muhsin ce ita take binsa shekararta bakwai a duniya, Allah ya haɗa jininta da Abubakar ba ta iya wuni guda cir ba tare da je sashen Fulani babba ta shiga ɗakin Abubakar ta tsaya yana yi mata gwaranci tana mayar masa ba. Babbar matsalar da ke damun Fulani Babba bai wuce yadda Abubakar yake cizgar gashin kansa yana ci ba, idan na kansa ya ƙare kuma duk wanda yake da tsautsayi idan ya damƙe ka haka zai dinga cizga har sai an kwace ka. Abubakar ya shiga shekara ta goma sha ɗaya, sai dai har lokacin a zaune yake ko motsi ba ya iya yi komai sai an yi masa. Fari ne sol kamar mahafiyarsa sai dai kammaninsa sak da Sarki Abdul'aziz, tun da ya taso ba ya iya magana sai dai gwaranci kuma har kawo lokacin yawu na dalala daga bakinsa. Idanunwansa duka biyun a juye suke, hannuwa da ƙafafuwansa suma a shanye suke babu abin da yake iya aikatawa hatta wanka da tsarki yi masa ake yi.

Fulani Babba da sauri ta ƙarasa gaban Abubakar ta sa hannu cike da ƙunan rai ta ɗauke fuskarsa da mari, wannan ne karo na farko da ta taɓa sanya hannu a jikinsa da sunan duka. Zafin marin ya ratsa shi hakan ya sa ya ƙarasa cizge kitson kan Ruƙayya da ke bakinsa, sai kuma ya fashe da kuka yana gwara kansa da ƙasa. Cikin azaba ta sake ƙwalla ƙara take numfashinta ya ɗauke ta sume a wurin. Tamkar mayuwancin zakin da ya samu nama haka Abubakar ya tura sillin jelar kitson kan Ruƙayya da ya cizge cikin bakinsa ya fara tauna kafin wani lokaci ya haɗiye shi gabaɗaya. A firgice Fulani Babba ta shiga yayyafa wa Ruƙayya ruwa ta jima a kanta sannan ta sauke ajiyar zuciya a galabaice, ganin ta buɗe ido ya sa Fulani Babba ta ji farinciki har cikin ranta sai dai kuma wurin da ya ɗaye mata kitson tuni gefen kan ya kumbura suntum. Wani irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login