Showing 18001 words to 21000 words out of 42008 words
sara ta ji kan yana yi mata a daddafe ta iya miƙewa ganin haka ya sa Fulani ta ba wa Bayin da ke gefe umarnin su ɗauke ta zuwa cikin turakarta. Duk dauriya irin ta Ruƙayya sai da ta dinga zubda ƙwalla sakamakon yadda take jin kanta na sara mata kamar zai tsage gida biyu. Duk yadda Fulani babba ta so zaman Ruƙayya a ɗakin zuwa lokacin da zugin zai sarara mata fir ta ƙi yarda, don haka ta sake saka Bayi suka ɗauke ta tana gaba suna biye da ita a baya har cikin sashen Fulani Umaima.
Ganin a halin da aka shiga da Ruƙayya ya sa Fulani Umaima miƙewa zumbur! Bakinta har rawa yake ta furta. "Me ya faru da ita?"
"Laifi ne yayanta Sadik ya yi mata, wallahi tsatsayi ne Fulani don haka na zo da kaina ba saƙo ba..."
"Dakata Fulani! Hawainiyarki ta kiyayi ramata. Ba tun yau ba na lura da take-takenki dangane da kiranyen da kika yi wa Ruƙayya. Lokaci ɗaya kin sa an lashe kurwar yarinya ba ta ƙaunar zaman wurin mahaifiyarta, wannan fa ba shi ne karo na farko na ji labarin wancen shagirigirbau ɗin ya maƙure ta yana yi mata ƙamshin mutuwa ba. Amma an yi ta yanke ta gille, wannan shi ne karo na farko kuma na ƙarshe da zai sake taɓa kowanne bil'adama a sashenki." Fulani Umaima ta ƙarasa maganar tana kai kallonta wurin bayin da ke riƙe da Ruƙƙaya. "A samu Jakadiya ta gaggauta sanar da Mai martaba ina buƙatar ƙwararrun masu magani, don ban san dafin da haƙoransa suke ɗauke da shi ba." Da sauri suka shimfiɗar da ita suka fice, Fulani Babba ta ƙarasa gabanta ido cike da ƙwalla ta furta. "Wallahi ko a mafarki ban taɓa jin Ruƙayya ba 'yata ba ce, tamkar yadda na ɗauki su Khadija haka nake jin ta, ta ya ina sane zan bari Abubakar ya illatata." Sai da Fulani Umaima ta saki murmushin takaici ta furta, "Me ya sa bai kama Khadija ko Sakina ya illata ba, saboda kina baƙincikin kin haifi sauna, wawa, shashasha shi ne ni ma kike burin ƙarfi da yaji na rasa waɗannan biyun da Allah ya ba ni." Tsoron hukuncin da Fulani Umaima za ta yanke ya sake mamaye Fulani babba, ta tsugunna bisa gwiwoyinta don ta san kome Fulani ta gaya wa Takawa hawa yake ya zauna ɗaram. Ba tun yanzu ba ta jima da dawowa daga rakiyarta, don ta lura sai abin da Fulani Umaima take so Takawa yake zartarwa.
"Tabbas Abubakar bai kyauta ba amma ki dubi girman Allah ki yi haƙuri..."
"Idan ba ki yi gaggawar fita daga sashena ba wallahi sai na shayar da ke ruwan mamaki." Fulani Umaima na gama magana ta yi ciki cike da zafin rai. Fulani babba ta sunkuyar da kanta ƙasa tana zubar da ƙwalla, dama ya ya lafiyar kura ballantana ta yi zawo. Gari banza ma Takawa ba ƙaunar Abubakar yake ba ina ga an ce ya taɓa 'ya'yan gaban goshi. Cike da zullimi ta fara yunƙurin tashi, daga bayanta ta hangi Muhsin na zaune yana aika mata da saƙon harara cikin kallon tsana. A haka ta ƙarasa sashenta gwiwoyinta a sanyaye, ta windo ta leƙa Abubukar da ke zaune yawu na dalala. Sai a lokacin ta samu damar fashe wa da matsanancin kuka duk da tana da tabbacin bayin da ke zagaye da ita suna sauraronta.
"Ya Allah ba don ba ka so ko ƙaunata ka jarabce ni da wannan bawa Naka ba, Ya Ubangiji ina godiya bisa baiwa da wannan ni'imar da ka yi mini domin dubbunaina na buƙatar ko da makamancinsa ne. Ya Allah idan rayuwar wannan bawa naka mai tsayi ce Ubangiji ka yalwace shi da lafiyar ya zama kamar kowa, saɓanin halin da yake ciki. Idan kuma mai gajeren kwana ne Ubangiji ka gaggauta ɗaukar kwanakinsa ko na samu salama a rayuwata..." Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya datse ragowar kalamanta.
"Allah ya sanyaya zuciyar uwar ɗakina Ubangiji ya ƙara wa Yarima lafiya." Baiwa Zainaba ta furta jiki a sanyaye kamar kazar da tono wuƙa.
"Zainaba na ɗauka ko kowa zai furta son ransa ke mai faɗa mini gaskiyar abin da ke cikin zuciyarki ne? A haka kike kiran Abubakar da Yarima kina ga ko a mafarki za a damƙa wa Abubakar karagar mulki ne." Tabbas kalaman Fulani Babba a turba suke domin kowa ya san halin da Abubakar yake ciki kuma ko a garin gaɓa-gaɓa babu wanda zai damƙa masa kujerar sarauta, ina ya san kansa ma balle ya san matsalolin talakawa? Sai da ta ƙara rissinawa ta furta. "Tuba nake ranki shi daɗe, In shaa Allahu Allah zai ba shi lafiya." Fulani babba ta amsa mata sannan ta wuce cikin sashenta.
Ganin har zuwa dare babu wani saƙo ya sa Fulani babba ta ɗan fara sakin zuciyarta, har ta zauna su Khadija na soko mata hira wani ta amsa musu wani kuma ta yi musu shiru. Suna cikin wannan yanayin Jakadiya ta iso da kiran da Maimartaba yake yi mata. Take ƙirjinta ya buga dum! Zuciyarta kamar za ta yi tsalle ta fito daga ƙirjinta, da ƙyar ta tattaro jarumtar haɗa kalmomin da ta iya furta wa Jakadiya. A gurguje ta watsa ruwa ta ɗan gyara jikinta, don saboda yadda lalurar fitsarin da yi mata kamun kazar kuku har ji take haka kawai kamar zarni na tashi a jikinta. Da kwalliyarta fes ta ƙarasa turakar Mai martaba ƙamshi na tashi, haka kawai wani lokacin yake jin kamar yana tauye haƙƙinta ko yana yi mata ba daidai ba, musamman yadda ya ga ta fige ta lalace kamar ba ita ba.
"Barka da hutawa Sarkina." Kalamanta ya ji na sauka a kunnuwansa, wani ɗaci ya ziyarci zuciyarsa kamar wanda ya haɗiyi maɗaci. "Barka!" Daga haka shiru ya biyo baya, ganin yanayin tarbar da Mai martaba ya yi mata ya sa jikinta ya yi sanyi. Cikin sanyin murya ta furta. "Allah ya taimake ka na ji saƙon kana son ganina."
"Wani hukunci muka yanke da muke ganin shi ne mafi alfanu babu cuta babu cutarwa." Mai martaba ya faɗa fuska a haɗe kamar dafaffan kwanannan kunun tsamiya. Ƙirjinta ya hau dakan lugude, gumi ya fara keto mata ta ko ina.
"Don haka ba ma buƙatar jayayya. Abubakar Sadiq zai koma ɗaya daga cikin ɗakunan gidan ajiya da gyaran hali, na sa a ware masa ɗaki guda wanda zai zauna a ciki, idan ya so duk wani abu da yake buƙata a aiwatar masa a can. Mun yanke wannan hukuncin ne domin sama wa lafiyayyun gidan nan mafita, idan yau ya nemi nasaka wannan jibi wancan watarana ina tunanin kaina zai dawo." Kafin dirar kalaman Takawa tuni hawaye ya gama wanke fuskarta. Cikin kuka ta zube a ƙasa hannuwanta biyu a saman cinyarsa ta furta. "Don Allah kada ka yi mini haka ranka shi daɗe, Allah ya sani Abubakar ba shi kaɗai na haifa ba akwai yayyansa Khadija da Zainab amma wallahi babu wanda na ke jin ƙaunarsa har a cikin jinina kamarsa. Wannan ƙasƙanci ne a ce jininka zai ƙare rayuwa a gidan ajiya da gyaran hali saboda ya kasance mai nakasa, in dai a kan Ruƙayya ne na yi maka alƙawari ko inuwarsa ba za ta ƙara gani ba ballanta shi. Don Allah ka..."
Cikin tsawa ya katse ta. "Ba mu san lokacin da raini ya gifta a tsakaninmu ba Fulani, da har ake neman yin jayayya da mu. Mu ba ƙananan mutane ba ne sanin kanki ne ba tun yau ba; ba ma taɓa magana biyu. Tashi ki ba mu wuri, wannan hukuncin ba zai tɓa canzawa ba." Fulani babba duk yadda ta so dakatar da hawayenta abin ya gagara, don haka ta fice daga turakar zuciyarta na tuƙuƙin ɓacin rai. Tana shiga ɗaki ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ganin kukan na ta ba na ƙare ba ne ya sa su Khadija rungume ta suka fashe da matsanancin kuka! Yau ita ce rana ta farko da ta ji zama a cikin gidan ya gama fita daga ranta, ta kuma ji wani abu ya tokare mata maƙoshi game da Fulani Umaima sai dai kuma a ɓangare ɗaya shakka da tsoronta ya hana zuciyarta sanar da ita gaskiyar abin da ke ranta. Sun jima ita da yaran a haka sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Abubakar, ta same shi a kwance kamar yadda ta barci. Sai da ta share ƙwallah sannan fito daga ɗakin.
Washegari tun safe Dogarawa suka cika umarnin Mai martaba, tun lokacin da aka fara jidar kayan Abubakar Fulani Babba take share hawaye don dai ba ta da yadda za ta yi.
"Idan kika matsa mana da magana wallahi ranki zai yi mummunan ɓacin da ba ki taɓa gani ba Fatima." A razane ta dubi Mai martaba, yanayinsa kaɗai ya tabbatar mata babu alamar wasa a tattare da shi. Dole ƙanwar na ƙi ta zubar da makamanta, ta rungumi ƙaddarar da ta afka musu babu sallama.
Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta tuna yadda suka kwashe da Takawa, a daren ranar da ta sake zuwa sashensa tana yi masa magiya a kan ya bar Abubakar ya ci gaba da zama a sashenta. Hawaye ya gangaro mata sakamakon ganin wata irin birgima da Abubakar ya fara yi a cikin jar ƙasar da ke ɗakin saboda ɗakunan kowannensu babu daɓe a ciki. Wata ƙasar ya ci wata kuma ya burtune jikinsa da ita, tana ji tana gani bayan ta gama kallonsa ta fice daga ɗakin. Abin ka da gidan masarauta take labarin kai Abubakar gidan yari ya gama zagaye gidan kowa da abin da yake tofawa, sai dai mafi yawa daga cikin shakkun Fulani Umaima ya hana su faɗar gaskiyar abin da yake cikin zuciyoyinsu.
"Allah ya taimake ki ni fa don kada a ce na saki linzamin harshena amma Allah ya sani na fara ɗora zargi a kan Fulani Umaima. Lamarin zamantakewar da ke tsakaninki da Takawa akwai fa ayar tambaya." Jakadiya ta yi wa Fulani babba maganar tana yin ƙasa da murya. "Jakadiya tafi kanki tsaye ba mu fahimce ki ba." Jakadiya ta sake yin ƙasa da murya.
"Bari na fito miki a mutum Fulani, an ya kuwa Fulani Umaima ba ta bi ta ƙarƙashin ƙasa a kan Takawa ba, duba da yadda take cin karen ta babu babbaka a gidan nan kamar wacce ta wanke masa hannu aka. Yanzu musakin yaron nan Bukari me ya yi da zai fuskanci zama a sashen gidan ajiya da gyaran hali." Jin haka ya sa hawaye ya zubo wa Fulani Babba. A fakaice Jakadiya ta saki murmushin cin nasara, don babban burinta ita ma bai wuce ta samu sanadin dandalar arziƙin da su Fulani suke ci ba a matsayinsu na matan Sarki. "Jakadiya al'amurana a yanzu haka na miƙa su a wurin Ubangiji, duk ma wanda ya nemi ya ƙuntata wa rayuwata Allah ba ya bacci yana sane da abin da yake faruwa." Jakadiya ta taɓe baki a fakaice.
"Amma ya kamata ke ma ki tashi tsaye domin kin san da sanyin safiya ake kama fara." Fulani babba ta ɗan sauya fuska don haka kawai ta ji ba ta aminta da waɗannan shawarwarin na Jakadiya ba.
"Ni fa hatta ciwon yaron nan wallahi na jima da ɗora zargina a kan Umaima, saboda Allah yaro shi ba aljanu ba amma an mayar da shi wani iri. Kwanaki fa har barbaɗe na ga tana yi a turakar Mai martaba wai don ya daina jin ɗanɗanonki." A ɗan razane Fulani babba ta dubi Jakadiya sai kuma ta haɗe fuska. "Jakadiya muna buƙatar hutawa a ba mu wuri." Ganin babu fuska ya sa Jakadiya ta fice tana wurgawa Fulani babba mugun kallo.
"Sakarai da ba ta gaji arziƙi ba kya ƙare a wahale cikin warin jiki da fitsari." Jadiya ta faɗa cikin jin haushin rashin samun nasara a kan Fulani Babba bayan ta fita waje.
Wacce ta shirya biyan kuɗin karatun ci gaban littafin *SHU'UMAR MASARAUTA* Ƙofa buɗe take, za ta iya turowa ta wannan Acc ɗin da ke ƙasa domin free pages na gab da ƙarewa. Waɗanda suka fara biya su min afuwa zuwa lokacin da zan buɗe group bayan na kammala free pages.
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
[10/4, 11:49 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.
*Masu ƙorafe-ƙorafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su ƙare a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400*
SHAFI NA TAKWAS
RIGAR ARƊO
A gajiye tuɓus suka dawo gida sakamakon yawon kiwon da suka je cikin dokar daji, zamansu babu wuya wata farar dattijuwa ta ɗauko ƙorai guda biyu sai da ta fara zuba nono a cikinsu ta miƙa wa mai gidanta Baffajo. Ta jima a tsugunne tana jiran ya karɓa tana ɗagowa ta lura da yadda ya dulmiya cikin kogin tunani, a sanyaye ta kai hannu ta taɓa shi.
"Yanzu Baffajo ba za ka daina wannan tunanin ba? Idan kai kana yi ni kuma sai ƙaƙa?" Ajiyar zuciya ya sauke. "Inna wuro aradun Allah lamarin yaron nan ƙara ci mini tuwo a ƙwarya yake, yanzu a ce ɗan mutum ba shi da abokan rayuwa sai gidan tururuwa da dokar daji? An ya Inna wuro ba za mu kai Kamalu wurin Malamijon farar riga ba?" Inna wuro ta yi jim cike da damuwa sanna ta furta, "Eh to hakan ma wani abu ne amma ni sai na ga kamar har da sabon shiga dawa..."
"Kayya mu ba a dawa muka yi rayuwa tun daga ƙuruciya ba? Kin manta a lokacin baya tsakiyar dare nake tsintoshi a bayan rumfar can wurin shurin da ke gabas da shi." Kamalu ya ɗago fuska a haɗe don jin abin da Iyayensa suke furtawa, motsa baki yake kamar wanda zai yi magana, amma sai ya gimtse ya kawar da kai gefe. "Kamalu kai fa ba yaro ba ne a ƙalla shekarunka sun haure goma, mahaifinku girma ya kama shi ba ka ganin sauran 'yan uwanka ba haka suke ba." Kamalu ya sunkuyar da kai ƙasa ba tare da ya kalle su ba, A'iru da ke gefe ta furta.
"Kwarankwasa dubu rannan har gani na yi yana ɗibar wani abu a kan gidan tururuwa yana sha, dubi wancan zobe." A'iru ta yi maganar tana nuna hannun Kamalu mai ɗauke da wani zoben azurfa mai ɗauke da wani irin zane.
"Da bakinsa ya ce mini tsintarsa ya yi a kan shuri wai gadon Masarautarsu ne." A razane su Inna wuro suka dube shi, Baffajo ya ce. "Kamalu wa ya ba ka wannan zoben?"
"Tsintarsa na yi." Kamalu ya furta kai tsaye ba tare da ɗago ya kalle su ba. Haushi ya fara kama Baffajo don haka ya ce, "Kai Kamalu hai ka shiga taitayinka, ba ka san dawa ba ko?" Kafin Kamalu ta ya ba shi amsa daga sama suka fara jin gudun dawakai da iface-ifacen mutane, kafin su yi wani yunƙuri tuni waɗansu Dogarai da sojojin masarauta suka farmusu cikin shammata suka riƙa taɗe su suna ɗaure su da wasu murtuka-murtukan igiyoyi a jikin manyan itatuwa. Lokaci ɗaya garin ya hautsine ban da ƙura babu abin da yake tashi, waɗanda suke da rabon tsira tuni suka shuɗa daji. Waɗanda aka riga da aka rubuta zanen ƙaddararsu kuma tuni aka damƙe su, a cikin waɗanda suka tsira har da Salele ɗan gida Baffajo. Shi kuwa Kamalu ko da ya ga abin da yake faruwa ko gezau bai yi ba, yana nan zaune wani Dogari ya isa gare shi ya fisgo shi da niyyar taɗe shi, ɗayan hannun nasa ya sa ya bigi gefen hannun Dogari, wata irin azaba ya ji tamkar an zuba masa ruwan dalma. Da kansa ya ƙarasa wurin wasu Dogarawa da ke tsaitsaye suna ɗaure ragowar mutanen da aka kama wanda ko tantama babu sun riga da sun zama bayi. Sai da aka ɗaure Baffajo da waɗansu mutane biyu sannan aka ɗaure Kamalu, a ɓangaren mata kuma tuni aka ɗaure Inna wuro da sauran mutanen da ke cikin rigar. Kafin wani lokaci rigar ta yi fayau sai kukan dabbobi da ƙananan tsuntsaye da ke tashi.
ƘAUYEN GANGARE
Jiki a matuƙar sanyaye suka ƙarasa cikin ƙauyen gangare hannun Mai gado ɗauke da jaririya, tun daga ƙofar gari aka fara jefa musu tambayoyin inda suka samu jaririya sabuwar haihuwa. Sai dai amsa ɗaya suke bayarwa tsintarta suka yi a cikin gona, da haka suka samu suka ƙarasa gida. Da zuwansu babu jimawa gidansu ya cika maƙil da mutane, wasu na taya su murna ya yin da wasu suka fara tsegungumi da ƙananan maganganu. Wani tunani Umaru ya yi take ya sa Mai gado ta ɗauki jaririya har ta ɗora ruwan da za ta yi mata wanka ya dakatar da ita kai tsaye suka wuce gabaɗaya wurin Mai gari. Umaru yana zuwa fadar Mai gari ya zube ya kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da jaririyar hannunsu da mahaifiyarta ta yi mata laƙabi da Jawahir, bayan ya tsahirta ya karɓe ta daga hannun Mai gado ya miƙa wa Mai gari, sanƙira yana raɓe a gefensa. Tun da aka ɗago jaririyar Malam Malmo ya zura mata idanu ko ƙiftawa ba ya ni, wannan ya haddasa fargaba da tashin hankali a zuciyoyin Mai gado da Umaru, sakamakon sanin Malam Malmo sarai da mugun aikinsa. A sakaye Umaru ya ɗan yi gyaran murya ya furta.
"Allah shi ba ka yawan rai yanzu haka Mai gado ta ɗora mata ruwan wankan da za a yi mata wanka da shi." Mai gari ya jinjina kai tare da yi musu nasiha a kan su riƙe ta da riƙon amana. Su Umaru har sun miƙe bayan mutane sun watse yana waigawa ya ga Malam Malmo yana yi wa Mai