Showing 18001 words to 21000 words out of 26185 words

Chapter 7 - ️YADIN MAGE OUM YASMEEN

29 Jun 2024

3209

sallama,


Dariya salma tayi tace


"Inna zulailaya gidan dadi bayan sallamar da nayi sai na kara ta biyu?,

Banza tayi mata anty salma tace


"Zan dauƙi samha in mata gyaran jiki,


Kutt ta haɗiye ta kora lemo tace


"Sai kun dawo da dai hamziyyah me ƙashin arziki zaki dauke bazan yar daba yasin,


Dariya salma tayi tace


"Allah ya barmu da ke zulailaya gidan dadi samha haɗo kayan ki,


To tace mata ta haɗo a cikin leda viva da yake bata da wasu kaya


__________________

Tafiya yake a titin sharada rukunin masana'antun dake sharada wani lahi yashiga wani uban tamƙameman Company ne kai kace kana turaine dare ne amma gun yawa rana parking yayi jin wayar sa na ringing sakar baki nayi domin tunda nake ban taɓa ganin me kyau irinsa ba farine tas yawa ka taɓa jini ya fito ga wasu irin golding eyes masu dakar hankali sumar nan kwance lublub p-cap ya cire tuni kyakkyawan sumarshi ta bayyana kallo daya za kai ma kasan hutu da jindadi sun ratsa shi hannusa yasa ya dauki wayar da yar yanzu me kira be gaji ba ganin wacce take kira cikin sauri ya ɗaga yace



"Assalamu alaikum suhailah,


Cikin shagwaɓatace


"Big brother wallahi nayi fushi in na sky line university amma kana kano Ka kasa zuwar min,


Ma'aruf yace


"Sorry sister wallahi abubuwa ne sukai min yawa kin gani yanzu zanje in duba yar da a ke tafiyar da sabon reshan na abuja Company na j&j rice 🍚 🌾 ,


Dariya ta saki tace


"Big brother duk hanyar neman kuɗi ka iya ta to Allah ya temaka,


Amin yace

Suhaila tace


"Big brother Ammi ta faɗamin ankai kuɗin ka amma baka ban number aunty tawa ba,


Dariya ta bashi suhaila ta iya taƙalan rigima yace


"Aunty bata da waya,


Dariya tayi tace


"Really big bro?,


Uhmm yace



"Kinsan bani da kudin siya mata amma ke inki na dashi zaki iya siya mata,


Tsalle ta duka yawa tana gaban sa tace


"Wallahi ina dashi daga kan ta dubu dari zuwa ta one million,



Mamaki yayi yace


"Ke ina kika sami kuɗi haka ko har yanzu shagon saloon ɗin naki yana nan?,


Zama ta gyara tace


"Eh na buɗe a nan zoo road ranar da ba makaranta ina zuwa na zuba ma aikata last year bana tambaye ka jari ba ai shago na buɗe,


Tambas suhaila akwai son kuɗi yanzu shi yazata ma abin ya rushe garin da ba garin kuma ta bude shago ba ma kusa da makarantar su ba yace



"Suhaila ai nayi zaton kin cinye,


Kwanciya tayi tace


"A'a ta nawa zan siya mata a matsayin gift ɗina na Engagement naku,


lumshe idanunsa yayi yace


"Suhaila barshi zan siya mata ki cigaba da kasuwancin ki Allah ya ƙara buɗ a buɗe mana a abuja J&J palace,


Kasan big bro saboda nasa sunan nan yasa wasu ke zuwa guna sau dadama har tambayar number kake sai ince kawai sunan ne yayi min ban san kaba


Murmushi yasaki yace


"Okay bye,


Bye tace mai katsai wayar yayi sai ya tuna lokacin da yake tambayar samha kinsan JJ wannan me kuɗi amsar da ta bashi ita ce wallahi ban sansa ba sau daya na taɓa jin sunan gun ali wai yana son sa tada motar shi yayi horn yayi me gadin ya buɗe mai parking space ya ajiye ta ya fito sanye da facemask hannunsa ya zuba a ajjihu yana tafiya cike da izza kai tsaye office ɗinsa ya nufa


Key ya dauko ya buɗe ya shirya rufe tulin files ya tarar kunna system ɗinsa yayi ya fara aiki sosai ya shiga aiki kallon office ɗin na tsaya yi komai ya haɗo tsaya a faɗi kyansa ɓata lokaci ne wayar sa ce tayi ruri da sauri ya dauka dan yana da tabbacin samha ce ita kadai take kiransa da wayar da kƴar ya iya danna wa saboda lalacewar wayar ta yayi sallama yace


"Sweetheart barka da dare,


Amsa sallamar sa tayi ta gyara kwanciyar ta tace


"Wa'alaikassalma ina hini,


Cikin deep voice ɗinsa yace


"Lafiya qalau ki haƙuri bansan ke bace sai da naji muryar ki da ko bashi naci na kiraki to wallahi kuɗin da zan kama haya nake tarawa,

( 🤔😠Kai readers kunji fa wani rainin hankali anya kuwa samha zata so shi inta gane ga yar da yake ya raina mata hankali )



Cikin sanyin murya yawa ana busa sarewa tace


"Wallahi bakomai wayar aunty salma ce daman zance maka nakoma gidan ta,


Wayar ya maƙale a kagaɗa ya ci gaba da aiki yace


"To namayi tafi ya sai ana i gobe ɗaurin aure zan dawo nasami wata motane akori kura na fara dako yanzu ma haka ina Lagos,


Murna tayi jin ci gaban da aka samu tace


"To Allah ya tsare hanya ya dafa maka,


Jin dadin addu'ar da tayi mai yayi yace


"Amin ki toromin da size ɗin kayan ki kar a haɗa laife kuma zo ana yayi yawa ko kaɗan,


Kunya ce ta kamata tace



"To, sai anjima,



Dariya ce ta kusan kubce mai yace



"Har kin gaji da jin muryata?,

Samha tace


"A'a kar incinyewa aunty salma kuɗinta




Ajiye biro ɗin hannunsa yayi yace



"Hakane sai da safe,



Samha tace



"Allah ya tashimu lafiya,


Amin yace ya kashe wayar aiki ya ci gaba dahi misalin 11:30 sai ga headline ɗinsa ta fara ringing dauka yayi cikin bada umurni yace


"Okay ya shigo,


Ya ajiye ya cigaba da operating system ɗinsa alamar buɗe kofa yaji ta gefen ido ya kalli me shigowa sallama yayi cikin fara'a yace mai


"Wa'alaikaslam babban barrister baku yawo da rana sai dare,


Hannu barrister kamal ya miƙa mai yace



"Uhmm wato wannan maganar da kanka kake saboda ku manyane bakwa yawo da rana sai dare,


Miƙa mai yayi suka gaisa yace


"Bisimillah barrister kamal,


Zama yayi yace



"Bayan shekaru goma sai gashi Ubangiji ya sake haɗamu,


Kujerar office ɗin sa ya ja baya yace



"hakane a wannan haɗa mu da yayi zamu tarwatsa a zalumai ne duk da an gargaɗini amma ina ƙoƙarin sakin duk wasu bayanai insha'Allah bayan na gama haɗa su zan yaye fatar akuyar da suka sa infito da ainiyin suffar su,



File barrister kamal ya miƙa mai yace



"Da a lama alkhali nasir m taura a wannan lokacin yayi shari'a bisa son ransa ko da nayi binkice yaso ya aiwatar da gaskiya amma daga sama akace inhar be abin da ake so ba zai rasa aikin sa ba fansho ba garatuti yau kwana uku da hin rutayar sa nasa d.a.s.s suyimin binkice akan alhaji kabir tamburawa to alhmdllh mun sami abin da muke so shi tsohon me laifini kuma ana zargin sa da kashe yar uwar sa sai kuma yana ƙungiyar Nan ta shanjini wato b.k.o wanda ta haɗa da manyan kasa kai harda sa hannun turai a cikin ta a gaskiya in mukai hin ƙurin ta ɓata sunan mu race in peace amma za mu gwada jan hali Insha Allah ganin mun kawo ƙarshan ta abin ta kaici inyamurai suna ɗiban ya'yan mu ba me magana anzuba ido wai shin shugaban arewa muna da kishi kuwa anabi ana kashe mu Yawa kiyashi anzuba ido wallahi a rana daya aka so fitowa da wayan suke wannan abun sai anji kunya mu kuma al'umma munzama mahaukata matasan mu basu da aiki sai charting dai dai da rana daya ba zai amfane mu ba ana kashe mu ana diɓan dukiyar mu dama iya arzuƙin ƙasa suke kashewa da sauki to har sai an kashe mutum mata sun zama zaurawa ya'ya sun zama marayu ya'ya mata ana binsu yawa dabbobi ana yi musu fyaɗe ƙunsan adadin yaran da suka rasa ahalin su amma duk ba wannan ne agaban mu ba munfi mai da hankali kan social media gaskiya ma'aruf dambu inyayi yawa baya jin mai mu kaɗai ba za yuhuba mu kawar da wannan saboda wallahi ba mu da kishin kai kana ɗauko wannan file ɗin zakaga tsoro ya hana mutanan magana wasu ma zu zare su je su faɗa kaga an bimu har gida ankashe mu domin da ɗan gari akanci gari ko ta hanya sadarwa ita kadai wallahi sai mun gano masu ta'asar nan amma ba wannan ce agaban muba dalibai basu da kwanciyar hankali ko wann lokaci za'a iya zuwa a farmusu,


Ajiyar zuciya ma'aruf yayi yace



"Tambas nima nayi tunanin haka amma barrister rai daya ne sannan Ni na yarda in mutu al'umma su rayu cikin dadi da salama komai yayi tsa yau gwamnati taga daba wallahi zata dai daita farashin yan kasuwa akwai abinci ba babu ba daga nan fita ake dashi turai dan me na zamu daidaita farashin mu ya zama kai daya mu saukaƙawa al'ummar musulmi kaga manfetur muna dashi harta gold muna da shi ruba akayan masarufi duk ƙasar mu arewa na dashi to mene matsalar tattalin arziki me yana komai sauko wa ?,


dariya barrister kamal yayi yace



"Gwarzo jarumi yanayin ƙarfin gwuiwar ka yana kama da na AFIF( my first novel AFIF duk wanda be karanta ba ambarshi a baya) ,



Murmushi ya saki yace


"Tambas shima gwarzon namiji ne ya tsaya ya kawowa ƙasar sa yanci ya tarwatsa azalumai ya binciko asirin maƙiya Allah.......✍️



_Ƙar ku matan banyi littafin nan ba da nufin tuzarta wani ko wata assalima ƙirƙirarran labari ne duk wanda ya ga yayi dai dai da rayuwar sa to ya ɗauka arashi ne ina bawa kowa da kowa haƙuri da na dagata da rubuta shi to ganin zai amfani al'umma yasa na dawo da shi mu gyara halayen mu muyi addu'a insha'Allahu ƙasar mu zata gyaru kar ku manta ba duka a ka taru aka zama ɗaya akwai na Allah tambas shuwagabannin suna ƙoƙari suma fin ƙarfinsu akai_





*YA ƊIN MGE*



_story and writing_



_by_



*Oum Yasmeen*







_addu'arku nake buƙata na maida littafin nan free book 📚 📖 ku tayani da addu'a Allah isa in gama jarabawa lafiya_



*Kar kumanta ga channel ɗina kuyi following*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


*Page 92-93*




_Previous for last page 📄📃_


_Tambas shima gwarzon namiji ne ya tsaya ya kawowa ƙasar sa yanci ya tarwatsa azalumai ya binciko asirin maƙiya Allah_



*Continue*



Dariya barrister kamal yayi yace



"Abin mamaki shine mufa muke bawa wasu ƙasashen hutar lantarki amma mu bamu da tsayar yiyar huta duk wani jin dadi na talaka yana garewa ,



Tissue board ya ɗauko ya zaro ya goge fuskarsa yace



"Yanzu akwai copy na Shari'ar a cikin nan?,




Wani File ya buɗe briefcase ɗinsa ya zaro yace



"Gaka gwara da kayi tambayar nan namijin duniya sa baka dariya sai hamma kana lura da komai ka iya taƙunka,


Amma yayi yace



"Barrister kamal kinan kasar nan sai da haka gobe ma zanyi tafiya zuwa Turkiyya,



Tashi yayi yace


" Safe journey sai munyi waya,



Mu'aruf yace


"Amin okay thanks,

Buɗe ƙofa yayi ya fita aiki ya ci gaba yayi daman be yi zaton cewa wai zata toromai ba ƙarfe 2:00 ya tashi fito wa yayi kai ka rantsai safiya yace wayar shi ce tayi ringing ɗauka yayi bata re da yayi magana ba yayi shiru



Sa'eed yace



"Hy rich man ƙar kafita bayanai sun nuna yanzu Company ɗin da kake ciki kwai wasu mutane jiran fitowar ka suke amma don't worry about it now insha'Allahu I solve the problem ,



Ai ƙarar harbi yaji da sauri ya ja da baya ya shiga cikin Company sauke wayar yayi to wai duk wanda yace zai maganci matsalar cin hanci da rashawa yana cikin matsala ransane ya ɓaci ya shiga cikin office ɗinsa wata system ɗinsa ya ɗauko sai da ya buɗe wani box ya ɗanna password sannan ta buɗe wani flash ya ɗauko ya zura danne danne ya shiga yayi ransa aɓace yake lokaci yayi da al'ummar ƙasa zasu san kowane shi yau zai fasa ƙwai saƙin video yayi ya rufe lumshe ido yayi wasu siraran hawaye suka zobo mai tambas wannan shine dalilin da yasa ya shiga jarida jinin Mahmud ba zai tafi a banza ba duk wani abu da yazama sularsa ne komai yazama Mahmud sanadi tun da akazo akai salama dashi har yau ba asan inda yake ba a binciken da yayi ya gano ankashe shi wayar da ce tayi ruru prevent number ce ta ƙirashi be dauka ba anki ra yafi sau dari can sai ga text message kamar haka


_wato kai bakaji ko mun gargaɗi ka akan ƙarka saki sai da ka saki to wallahi ka saki jinin ƙanwar ka suhaila yau zamu shanye mata jini_


Dasauri ya miƙi wayar barrister kamal ya gani da sauri ya dauka yace ga suhaila aguna da na fita naganta tafito daga makaranta tana gudu so na ɗauke ta tana gun momiyo wato Mahaifiyarsa ƙar ka damu da duk text message ɗin da za a turomaka insha'Allahu ba zasu yi nasara ba


Hamdalah yayi yace



"Okay thanks,

Kashe wayar yayi tun dare fusatattun matasa sun yiwa gidan honourable kabir tsinke zasu ƙonashi ashe da sa hannun sa ake sace musu ya'ya jami'an tsaron sukayi durar mikiya suka fito dashi domin ayi binkice kafin su zartar da hukunci



___________________


Iya gyara samha na sha tayi kyau kyahunta ya ƙara fitowa abba ma ya dawo daga gun aiki sosai yaji dadin yar da yaga yar tasa tana samin kulawa abin da ya ƙara faranta mai jin an kama kabiru sosai yake cikin nishaɗi ko ba komai za ayi maganin zalincin sa


Samha kuwa hankalin ta ya tashi yau four days kenan tana buga layin ma'aruf amma a kashe gashi tun da tazo be taɓa zuwa ba kwanciya tayi ta rungume pillow salamar nuratu taji da sauri ta fito daman abokiyar shawara take nema tace


Aunty salma bata nan sai ni kaɗaice

Dariya nuratu ta saki tace



"A'a kaga amarya jiki duk ya ɗau harami,


Ƙunyace ta kamata tace


"Uhmm shi go ,


Shigowa tayi ta zauna tace


"Kƴa gama uhmm ɗinki washe garin kai ki zaki mana bayani ne,




Zumɓuro baki tayi tace


"Wallahi ku kun wani dameni da magana daya haba Ni Wallahi bana son irin wannan zancan,



Dariya nuratu tayi tace


"Nikuwa ya zo nan ne yaushe yace miki za'a kawo lefen ki ?,


Ƙasa tayi da kanta tana wasa da fingers ɗin ta tace




"Wallahi be zo ba inna buga number sa bata yi na rasa yarda zanyi Allah isa lafiya wayar mu ta ƙarshe yace ya tafi Lagos,




Shiru nuratu tayi tana nazari sannan tace


"To Allah isa lafiya dai gaskiya haka kurum ba zai ƙi zowaba,



Hamziyyah ce ta shigo yawa anjewota ta ɗinga kashewa da dariya ita da surayyah tace



"Kaga amaryar ma'aruf me adaidaita yaushe za akawo lefen naki ne ko ba kuɗin da zai miki,


Baƙin cikin ne ya ishi samha tace


"Ina ruwanki inma be kawo ba wallahi yanzu dai dai nake dake bazan taɓa raga miki ba ke anaki dabbancin kuɗi shine so shiya ga shinan ba tsayayye sai yan yaudara yan ƙarya.......✍️
*YA ƊIN MGE*



_story and writing_



_by_



*Oum Yasmeen*







_addu'arku nake buƙata na maida littafin nan free book 📚 📖 ku tayani da addu'a Allah isa in gama jarabawa lafiya_



*Kar kumanta ga channel ɗina kuyi following*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


*Page 94-95*




_Previous for last page 📄📃_


*Ina ruwanki inma be kawo ba wallahi yanzu dai dai nake dake bazan taɓa raga miki ba ke anaki dabbancin kuɗi shine so shiya ga shinan ba tsayayye sai yan yaudara yan ƙarya*




*Continue*





Nuratu ce ta tashi tace



"Wallahi kukai yunkurin taɓata sai nabuga yarinya da ƙasa wallahi yau ba inna sai na yiwa yarinya targaɗe,



Sanin halin nuratu bata da sauki ko kadan in aka ta bota yasa hamziyya tace



"Au Allah KO gamu lurasaye ba mu da hannun ramawa ai ba karya aka faɗa ba yana da niyar kawo lefen da tun sati biyu da ya huce za a kawo yanzu ba maganar kafi ba wanda yason inda za a kaita tsiyar auran talaka kenan banzaye,



Hijabi nuratu ta cire tace



"Wallahi kika ƙara cewa tak sai na yi ƙasa ƙasa dake ina ruwanki ai wannan ba damuwar ki bace insha'Allahu sai Allah ya shayar da ke mamaki,


Anty salma ce ta shigo hannuta ruƙe da annuwar tace


"A'a lafiya nagan ku kunyi cirko cirko?,


zama nuratu tayi tace



"Wallahi wayan nan basu da mutunci nan ta kashe komai ta faɗa mata ,


Dubansu aunty Salma tayi tace



"Yanzu abin da kukai ya dace samha yar uwar kuce duk wani abu da ya shafi samha ai ku ya shafa uwa ɗaya uba daya ba wasa ba za kuso kuga samha ta shiga wani haline?,



Surayyah tace

"tab ai ni wannan shine farin ciki na suka sa ƙafa suka fice dafe kanta auty salma tayi ta zauna ajiye annuwar tayi ta haɗa mai kayan wasa samha ma zama tayi aunty salma tace


"Samha Allah ya fitar da mu kunya wallahi ko bacci bana iyawa Allah ya kawo mana ɗauki tun wayar da kukai da shi yace yana Lagos ba ku karawa waya ba ko ?,



Wani kunci ne ya mamaye ta tace



"Wallahi ba mu kara ba nayar da da kaddara komai mu kaddarine aunty salma inna ce zansa damuwa a raina zan haɗu ne da wani ciwo kema ki cire ba komai Allah na tare da mu ,


Kai aunty salma ta jinjina tace


"Wallahi hakane samha Allah ya kawo mana mafita,


Amin duk kansu suka ce


_________________________________



Inna zulai ce a kwance a soro sai fifita take yayin da baba hajara ke ta suyar wainar ta daya ke ta dawo yi anan ɗin ba laifi tana samun masu suye amma ba kamar can ba ta kaicine ya ishi inna zulai kullum tare suke zama suya tana ganin ta fito intama

25, December 2024
Amal

Mage

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login