Showing 9001 words to 12000 words out of 26185 words

Chapter 4 - ️YADIN MAGE OUM YASMEEN

29 Jun 2024

3211

haka su zee suna nan suna ca'ca
Hangame baki inna Hajara tayi ganin abba yana ta fiya da kansa ɗan kuka kuwa dafe bango yayi da ɗaya hannunsa ɗayan kuwa yana ƙirjinsa yace


"Laha'ilaha illallahu tofa me zan gani gawa taƙi rami da kanta tana tafiya zancan aurena ya rushe uwar ɗakina Ko,


Abba ne ya haɗe rai cikin rashin saƙin fuska yace


"Daga yau ƙar ku ƙara zuwar min gida duk wanda zai siyi waina ya aiko yaro ku kuma ya nuna su zee ƙar Ku ƙara zuwar min da ba zaku lalatamin gida ba,


Tsalle inna hajara tayi tace


"Billahillazi baka isa ba kai ka gagara nemowa ni na nemo kake min ƙashi sai de muyi wacce zamuyi dan ma na rufama asiri na zauna da kai shine yanzu ka tashi baƙin hali ya dawo ko to wallahi ƙusƙure bakin ka da hypo,

Banza Abba yayi mata ya fita muka shiga a dai daita sahu sai kotu ko da muka je na dauko kuɗi na bawa me babur ƙuɗinsa shiga mukai ciki sai da aka fara wata Shari'a sannan tamu

Wani lauyane ya miƙawa alkhali ta karda ɗan rubuce rubuce yayi ko abba kabiru ban gani ba wani lauyane ya tashi yace


"Ya me Shari'a ni ne lauyan dake kare Alhaji kabiru komawa yayi ya zauna,



ɗaugo alkhali yayi yace



"Ko a kwai lauyan da wanda ake ƙara suka dauka ?,


Girgiza kai abba yayi ganin haka lauyan gwamnati ya tashi yace


"Ni ne wayanda zan kare su ,

Rubutu yayi sannan yace kotu tana neman malam sulaiman


Tashi abba yayi ya shiga wannan wajan lauyan abba Kabiru yace


"Malam sulaiman me zanba cikin aminci kun ƙarɓi hayar gidan Alhaji kabiru rana bakwai ka watan Oktoba ashekara ta dubu biyu da biyar yanzu in Ka kirga shekaru shekara goma sha tara kenan sannan bincike ya nuna sau daya kuka bashi kudin haya daman ce muku yayi ya bar muku.........✍️
*YA ƊIN MGE*



_story and writing_



_by_



*Oum Yasmeen*




*Kar kumanta ga channel ɗina kuyi following*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


*Page 61-63*



Tuninanin abbane ya tsaya na hucin gadi ba zato ba tsammani jayi lauyan yace


"Ya me Shari'a ko da wannan hujja da wanda yake ƙara ya bayar ya kamata a koresu da ga gidan gashi Kuma ya kama kansa ya kasa magana ina ruƙon alkhali ya kori shari'ar nan,


Ganin lauyan Alhaji kabiru ya zauna lauyan su samha ya tashi yace


"Ya me Shari'a duk kanin hujjojin da na tara da shedo sun nuna cewa gidan nan na magada ne ba kowa ta ci gadon nan ba sai malam sulaiman da ƴarta samha alhaji kabiru bashi da gado a gidan dan haka shine ya ke nema ya kwace wa marainiyar Allah gidan ta sannan mahaifiyar samha kasheta akai ya kamata ma abinciken wanda suka haura musu gida suka kashe ta sannan,


Ai kafin ya ƙarasa lauyan Alhaji Kabiru ya tashi yace


"Ya me Shari'a duk wannan ba gaskiya yake faɗi ba yana ƙoƙarin fitar da wanda ake zargi ina neman alfarmar wannan kotu da ta bani ikon gabatar da shedata ta gaba wato malam idi dillali wanda shi ya siyar wa da Alhaji Kabiru gida kuma ya ce a nemo yan haya ya nemo wannan mutumin ya sa shi,


Ɗago wa yayi yace


"Kotu ta baka dama,


Baki abba ya saka ganin aminin sa malam idi dillali duniya ina zaki damu yanzu ya yarda ya goyi bayin ƙarya shiga wannan gun yayi ya tsaya ya dauke ido daga kallon abba yace


"Ni ne malam idi dillali Ni na siyarwa da Alhaji kabiru gida sannan na dauko malam sulaiman ya zauna haya duk shekara sai nazo akan ya bani kuɗin haya sai yace bashi da shi har na gaji da zuwa ganin suna ƙoƙarin cin yemai gida na bashi shawarar ya kai su kotu a karɓar mai gidan sa ,


Alkhali ne yace ya koma sannan ya dubi jama'ar kotu yace zai tafi hutun rabin awaya ya buga gudumar sa


_____________________ *ABUJA*


Cikin sirri aka zo aka dauke shi sai unguwar osokoro abuja lumshe idanuwansa yayi tambas kowa yabar gida gida yabar sa gaban wani tafkeken gida motar ta tsaya tayi horn aikuwa kamar jira ake gate man ɗin ya buɗe mai gate iya haɗuwa gidan ya haɗu gidan shiru ba kaji inhun komai sai na tsuntsaye ga wasu irin flowers masu kyau koraye shar da su A parking space aka sauke shi fitowa yayi yana tako cike da izza gaban wani ƙaton apartment ya tsaya gabaki ɗaya gun glass ne ƙofar tana jin hucin mutum take buɗewa wani haɗadɗan floor ya shiga ga kyau ga tsaruwa ga wasu irin laxury sofa masu kyau assalama wata kyakkyawar matace tafito fara tas da ita fuskarta cike da fara'a tace


"Wa'alaikassalam mu'aruf,



Murmushi ya sakar mata yace


"Ammi na samike lafiya qalau,


Cikin so da kaunar ɗan nata tace


"Wallahi lafiya qalau ya hanya ?,


Zama yayi yace


"Alhmdllh,


Dinning room ta nufa ta ajiye stainless steel flask ɗan gidan vacuum sannan ta fito ta dawo floor ta zauna tace


"Wanka za kai ko kuma zaka tsaya kaci abinci,


Tashi yayi yace


"Ammi bara inyi wanka inna tashi daga bacci naci auta tana makaranta ko ,



Eh wallahi ai sun kusan hutu ta dawo gida


Ma'aruf yace



"Allah ya temaka,



Amin tace




Raƙiba ce ta shigo sanye da abaya shuɗiya yar gidan kahu saminu da nazifa sai hura hanci suke kai kace ya'yan wasu ne shigowa sukai shi kuma har yabi hanyar da zata sada shi da ɓangaransa zama nazifa tayi tace


"Ammi kamar ƙamahin turaren ya jj nashi ya dawo ne ,


Zuba mata ido ammi tayi yawa me karantar wani abun sannan tace


"Eh ya dawo,


Wata irin murna ce ta kamata raƙiba tace


"Amma ammi tun safe baki faɗan ba inmai abincin tarba,


Ammi tace


"Aikin san baya cin ko wanne abinci shi yasa tana kai wannan ta tashi bata fatan ko sau daya mu'aruf ya aure ɗaya daga cikin ya'yan baffaninsa saboda ita ta sani wataran zasu iya harar ransa ba son gaskiya suke mai ba abin hannun sa suke so,

tafi so ya aure wacce bata san waye shi ba


_______________ *kotu*



Alkhali ne ya dawo daga hutun da ya tafi yace



"Duba da irin hujjujin da Alhaji kabiru ya kawo nawa ba malam sulaiman kwana ɗaya tak ya tashi ya bashi gidan sa sannan zai biya shi tarar dubu talatin da hudu,


Jirine yake neman zuwar da abba nima da nake zaune kuka nasa tambas yanzu mutane basa tsoran cin haram wannan wacce kaddara ce haka ɗaga hannu tayi hawaye na bin kuncinta tace



"ya Allah mu bayin kane baka barin kuma zalinci kai me adalci ne Allah ka saka mana ya Allah kazamu gatan mu bamu da gata sai kai,


Wani ne ya juyo ya kalle ta tausayi ta bashi tashi yayi ya zura hannunsa a aljihu yace



"Ungo ku biya tarar da ake bin ku ,



Hannun samha na karkarwa ta amsa tace



"Nagode Allah ya saka da alkhairi ya jikan mahaifa ,



Amin yace ya yatashi ya fita daman ya kan je kotu me gidan sane yake aikensa ya biya tarar wanda yasan bashi da shi......✍️



*YA ƊIN MGE*



_story and writing_



_by_



*Oum Yasmeen*







*Page 64-66*




_addu'arku nake buƙata na maida littafin nan free book 📚 📖 ku tayani da addu'a Allah isa in gama jarabawa lafiya_



*Kar kumanta ga channel ɗina kuyi following*








Bayan sun biya suka fito akafa suka ɗinga tafiya har unguwar su shiga gida sukai zama samha tayi ta zuba tagumi tace



"Abba kar wannan ta tada maka da hankali kai haƙuri komai me huce wane ,



Kujera ya ja ya zauna yace



"Samha wallahi Ubangiji ya yaye min damuwata insha Allahu komai zai dai daita shi kuma yaje shi da Allah bana ko tantama cin hanci suka bawa alkhalin sai dai sun manta da cewa ita dukiyar maraya yaɗin mage ce wataran sai yayi amansa ta saniyar haka ma zata iya cinye arzikinsa ,


Ajiyar zuciya ta saki tace




"Abba yanzu sai mu haɗa kayan mu tafi kan karofi ko ,



Tashi yayi ya ɗebo ruwa sai ayanzu yaga kofar inna hajara a rufe girgiza kai yayi abin hajara ya ishe shi yawa yawa taci kafar kare yace



"Bara hajara ta dawo sai itama ta haɗa kayanta,



Tashi tayi ta shiga ɗaki hawaye ne ke bin fuskarta




Haiye yaraye iye nanaye takun bana yafi nabara saki ɗan yaƙe haƙura naji kina takun kasaita tafiyar bata chanza zani ba shigowa tayi bako sallama turuss tayi ganin malam ya zuba ta gumi tace



"Bar ta gumin nan daga gidan Alhaji kabiru nake yace zai siyar min da gidan nan kaga sana'a tayi zaman banza kuwa ai yanzu anga ribar sa ko ta sheƙe da dariya ta shiga ɗaki a guje ta fito tana gyara daurin zani kan uban can tab yasin in nayar da meta tsina ya dawo duniya wato Ni zubi zata yiwa haka yasin ko ita takawo son kuɗi duniya sai ta bani zanin ta na kuncewa tana ƙara soke shi ta fita tana babbami

Tashi yayi ya shiga ɗaki yace



"Samha haɗo kayan ki mu tafi ban ga alamon Hajara zata biyuni ba we siyan gidan xata yi ,



Tashi tayi tace



"To, har hada kayan suka shiga yi ya dau wasu samha ta dau wasu suka fara tafiya daman ba wani shirgene da suba



______________________




Ma'ruf na yarda Allah ya baka sa'a



Amin yace ya tashi ya fita a floor ya tarda raƙiba da nazeefa ko wacce harkar gaban ta take har ƙasa suka durƙusa suna gai da shi ciki ciki ya amsa ya fita yana fita ya samu wanda zai kai shi airport yana jiranshi shiga yayi ya zauna a kujerar me zaman banza aiki yake a system ɗin sa har suka isa be gama ba rufewa yayi ya fito baya tafiya tare da mutane ba shi yasa kowane ya san sa ba sai de sunan sa da ya karaɗe duniya baya yarda yan jarida suyi hira da shi picture ɗinsa ma ba ya yarda ya shiga media ba we baya yi bane a'a yana hi yana kallo meke wakana

Akwai ma wani hira da ya gani ana hira da yan makaranta ana tambayarsu we in jj ya baka dama ka rubuta adadin kuɗin da ake son nawa zaka rubuta sosai yayi dariya har da mece wa gabaki daya kuɗin dake account ɗinsa zan rubuta kayan sa wani ya zo ya karɓa sosai son duniyar mutane ke bashi mamaki Basu san ya akai ya sami kuɗinsa ba basu san wahalar da yasha ba kawai dukiyar suke hange



tafiya yake yana bin bayansa kai tsaye reception ya nufa bayan ya ɗan wani rubuce rubuce ya ɗauko dalar America besan iya adadinsa ba ya basu su rabawa duk wanda ke airport ɗin ya shiga jirgi nan fa yan jaridu sukai dirar mikiya kas sai de daukar pictures ɗin jirginsa sukai nan fa wani dan jaridar c.r.l yace



"Ayau munyi rashin sa'a ba mu tarar da j.j ba amma zaku ga photo jirgin da ya hau munyi ƙoƙarin jin ta baki detractor manager na airport amma be fada mana inda yaje ba assali ma yace we besan da zuwansa ba shin me zaku ce da j.j ,



Nan fa labare suka karaɗe duniya kowa na fadin albarkacin bakin sa wasu ma cewa suke ba mutun bane wasu suce kawe bashi da kyakkyawar kamane wasu cewa suke wasa yake da hankali mutane akai kuma masu fatan alkhari



*Nikwa nace lol nagan sa Nima na karɓi nawa kuɗin😁😁💵💵💵*


*YA ƊIN MGE*



_story and writing_



_by_



*Oum Yasmeen*







*Page 68-70*




_addu'arku nake buƙata na maida littafin nan free book 📚 📖 ku tayani da addu'a Allah isa in gama jarabawa lafiya_



*Kar kumanta ga channel ɗina kuyi following*



https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k




*Previous for last page 📄 📃*


Nan fa labare suka karaɗe duniya kowa na fadin albarkacin bakin sa wasu ma cewa suke ba mutun bane wasu suce kawe bashi da kyakkyawar kamane wasu cewa suke wasa yake da hankali mutane akai kuma masu fatan alkhari




*Continue*


*KANO TA DABO TUNBIN GIWA*


Karfe shidda na yammaci jirgin sa yayi durar mikiya a filin tashi da sauka na malam aminu kano international airport fitowa yayi ruƙe da briefcase ɗinsa tsaya wa yayi wani matashi ne ya matso kusa da shi ya karɓi kayan sa yace


"Barka da zuwa sir,


Amsa wa yayi yayi gaba buɗemai mota yayi yashiga tuƙi ya fara matashin yace



"Yanzu ina za'a kai ka ,



Glass ɗinsa ya zare yace



"Kai ni tahir guest place Tahir ,




to yashi kai shi yayi yace



"Tsaya in fito sai muje gidan naku,


Okay sir yace


Kayan sa ya ajiye yasa wasu kayan fitowa yayi cikin sauri matashinnan yafito yana sakar baki yana kallonsa ganinsa yayi yawa be taɓa sanin dadin kuɗi ba ko shi yafi shi kyan gani kayan nan sun ƙoɗe duk sunbi sun ɓole ga sumar sa duk ta cukurkuɗe wandon ma ya ɗage mai ga wani matatcan takalmi yawa kofato yace



"Wallahi oga ban gane ka ba,


Murmushi yayi ya shiga ba tare da yayi mai magana ba shima be damuba sanin da yayi shi ba me magana bane wata matatciyar waya ya ɗauko ya sa wani lahi duk an ɗaureta da ƙyeuro ya ɓoye babbar wayar sa ajikin sa yace



"gobe sai ka kaine inda zan dauki hayar adaidai ta sahu ,



To yake gidan su dake jakara ya kai shi Assalam sukai har ƙasa ya ɗurƙusa ya gaishe da mahaifan sagir masawa sukai cikin mutunci ni'ima ce ta shigo sanye da doguwar riga da mayafi Zata kai shekara ashirin da daya gaidashi tayi tana ya mutsa fuska yawa taga kashi sagir yace



"Inno ga Ma'aruf zai zauna a shagona kafin yasa mi kuɗin kama shago daman tun sauran sati zuwansa na faɗa muku,



Yaya ne ya washe baki da yake haka suke kiran mahaifin nasu yace



"Ba matsala Allah ya kai mu lafiya yaro a kula aruƙe gaskiya da amana insha Allah zakaga ancin ma gaci komai zai zamo tahiri kaga abin da ke hana mutanen mu ci gaba rashin riƙe gaskiya da amana suna hima babbar illar dan Allah kuma a ruƙe imani kar ka ga ba kowa naka kace za kai abin da kaga dama Allah yana ko ina ko dan mutuncin kan mu ya kamata mu tsare imanin mu ,




Sosai yaji dadin nasiyar mahaifin sagir daman har yanzu akwai irin mutanen nan ya yar da cewa na Allah basa ƙarewa yace



"Insha Allah zan ruƙe zaka sameni ma fiye da harda bakai tsammani ba Nagode sosai,



Ita kuwa mama tana zaune tana taɓe baki shi wannan mutumin ma talaucin sa har yafi na ɗanta ga kayansa yawa wani mahaukaci yaya ne ya tashi ya shiga ɗaki ganin daga shi sai wani buhun babko alamu ma kaya ɗayane a cikin amma yana mamakin kyan fatarsa duk da yayi mata fenti ta koma me dan duhu amma a kwai hasƙen ka ɗan da alama bafilatani ne haka ya raya a ransa fito wa yayi ɗauke da kaya ya miƙo mai yace



"Ɗana gashi ahi haƙuri komai na rayuwa me hucewa ne ,



Ɗagowa yayi ya faɗaɗa murmushinsa tambasyana jin yaya kamar mahaifinsa yace



"Nagode da karamcin ku ,


dariya yaya yayi yace



"Ɗana Allah ne abin godiya wallahi ina jinka kamar abokina da narasa shekara da shekaru Allah yayi masa rasuwa tare muke faɗi tashi wallahi ciwon hinwane ya kasheshi wallahi a lokacin yana tsananin rayuwa nima haka daga haka da ya mutu ya'yansa suka bar unguwar nan wallahi kamar ku daya da shi nayi neman su har nagaji,


Ƙasa yayi da kansa kwalla ta tarar mai tambas mahaifin sa yake nufi yace



"Allah ya jikansa,


Amin ya Allah yace inno ce ta tashi ta ja dogon tsaki ta shige ɗaki

Ni'ima ce ta fito ko kallon sa batayi ba inta kalle sa zuciyar ta tashi take Allah yayi mata ƙamatar talaka gashi bawani kuɗine na kuzo a gani da suba amma bata kaunar haɗa hanya da talauci kullum bata da zance sai tace yaya sagir dan Allah ka haɗani da me gidan ka jj ko number ka bani sai dai yace mata ni ƙaramin ma aikaci ne bani da iƙon ganin sa ko samin number sa har inno ce kesa baki tace



"Kai baka da kishin kanka ka shigewa mana manyan ma aikatan nasa kasamo mana muma mu warke,


Saide ya ce musu inno kenan to baya zama a ƙasar nan fa kullum yana kasar waje har karsuwancin sa amma yana gab da zuwa kano


________________________



Kai kai kaiyasa butar uwarnan sule kai ka dawomin bayan na aurar da kai ina ma laifin ka dawo kai ka ɗe har da ƙari



Ƙasa yayi da kansa yace



"Innna wallahi haka jarabawar rayuwa tayi dani nasame ki lafiya,



Zama tayi ta ɗaura hijabin sallarta a kai kai kace gwawgwaro ta ɗaura tace



"Uhmmm gaskiya ne ta ƙutsiri goro ta fara taunawa,


Tashi yayi ya gyara tsohon ɗakin sa ya zuba kayansa ya dubi samha yace



"Jiki ɗakin yaya isah ki zauna a can ,



Tashi tayi ta kwashi kayanta sosai nuratu tayi murna da ganinta inna zenaru ta jajanta musu hamziyyah ce ta shigo tana dadɗaga kai sama ta girmin samha da shekara biyu yanzu ita na sha tara ita sha bakwai ko kallon inda samha take batayi bace



"Nuratu aramin wayar ki in dau number anty salma,


Miƙo mata tayi zama tayi tana wani daddauke kai we ita ala dole bata harka da kananan yara sai manyan kai wayar hannunta me tsada ce iPhone 7 CE gamawa tayi ta tashi ta fita ta zo ƙofar fita ta takewa samha kafa da sauri ta janye ta rasa wacce irin tsana hamziyya take mata nuratu ce tace


"Hmmm samha sabeereen fa ta zo gidan nan nan fa ta kwashe komai ta fada mata ,


Mamaki

25, December 2024
Amal

Mage

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login