Showing 6001 words to 9000 words out of 26185 words

Chapter 3 - ️YADIN MAGE OUM YASMEEN

29 Jun 2024

3212

💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞
💞💞
💞

*

~yar mutan yakasai~


*Page51-55*

Wallahi yasmin duk ke kika jawa kanki me akai a kayi yi shi da zaki bari har hawayanki mai tsada ya zuba

" Ma'aruf Jafar Jabir ne fa shin kinsan waye jafar kuwa kinsan irin dukiyar da ya tara to daddy yace min lalle inde ina son ya cigaba da kallona a matsayin yar sa to in samo soyayyar ma'aruf jafar jabir shin kinsan dalilin da ya sanya daddy yace in aure shi saboda yana son ya mallake dukiyar sa wannan yana daga cikin plan ɗin mu sannan mu mai da shi abin tausayi

Yasmeen kinsan kowa ba tun yau kike asiri akan ya soki amma abin baya yu huwa dan Allah kiyi haƙuri kizo mutafi

"To, amma wllh JJ dani kake zance sai na ta gayyara rayuwar ka

wannan kenan

lumshe idanuwan shi yayi yashi ga tunani we yau she zai samu matar da zata so shi tsakani da Allah tambas yasan ba alkairi bane ya shigo da Alhji tahir cikin rayuwar sa tuno wa yayi da lokacin da yake talaka yadda yake cimai mutunci har yace ba zai haɗa zuri'a da jinin jafar ba to amma yanzu ya a kai ya toro yar sa domin yana da yaƙinin cewa yasmeen ita ta kwaro mai ruwa lokacin da yaje neman temaƙon kuɗin makaranta bayan mutuwar mahaifinsa hawayene ya cika mai ido ina ma abba kana nan na sami arzuki inama kana nan in wanke maka takaicin ka abba har ka mutu da riga daya ce da kai abba yau gani ina da rigunan sawa ni kai na bansan adadin suba abba lokacin da kana tsaka da cuta sai mu yini mu kwana bamu samu komai ba in ban sami aikin gini ba kaf faɗin unguwarmu ba mai tausaya musu karshe ma sai aka bini da sharri ringing ɗin wayar shini ya katsai mai tunani da sauri ya daga ganin mai kiran cikin girmamawa yawa yana gaban ta yace barka da warhaka ammi

yauwa yanzu nan kahun ka ya ƙirani yana faɗa we ka raina shi baka jin magana yace ka bashi dubu dari zai gyaran gida kaƙi we me yasa kake da ruƙo ne ka mai da komai ba komai ba har yake cewa ni nake hana ka alkairi sai yan uwana

Allah ya huci zuciyar ki ammi amma ni bazan bawa kahu inusa kuɗi na ba kin tuna lokacin ina gidan yari dubu biyar zai bayar a sallameni me yace bashi da shi sai yanzu we ace yan uwan mahaifina su suka kai ni akan laifin da ban aikata ba wannan shi yayi sana diyar mutuwar abba ammi sai ya fashe da kuka muryar sa har rawa take yace

banga gawar mahaifina ba sai kaini akai naga ƙabarinsa wallahi in badan suna cin darajar ki fici kata ba zasuci ba

Ma'aruf ina baka umarni ka tura mai duk wannan ya huce suje su da ubangiji kitta kashe wayar bin wayar yayi da kallo gaban wani ƙatutan gida ya tsaya horn yayi mai gadin gidan ya buɗe masha Allah gida ne madai daici iya tsaruwa ya tsaru ga wasu flowers kala kala dare ne amma yawa rana iya ƙayatuwa ya ƙayatu fitowa yayi ya buɗe wata glass door mai shegen kyau mu kunnin fitula ya kunna tuni haske ya mamaye ɗakin komai na ɗakin farine tas harta sofa itama fara ce da alama jj mai tsabta ne komai kal kal kai tsaye kitchen ya nufa y bude fridge ya dauki ruwa mai sanyi duk kuwa yau an tashi da dusar ƙanƙara amma hakan be hanashi shan ruwan sanyi ba kusan ma ya saba da wannan rayuwa tas ya shanye ruwan sallamar munir ce ta dawo dashi daga tunanin daya shiga

barka da dawo wa big bro ya rumgumai shi tambas so gaman jini yana son dan uwan nashi shiya sa yanzu da ya gama secondry ya kawo shi nan yayi karatu

"ya karatu"

Alhmdllh yaya komai yana tafiya dede

masha Allah

Bara in sama mana abincin da za muci da a ce ammi ta yarda da zaman cikagon ai da mun huta ko auta tayi mana girki

Allah yaya bana so ka koma kano ka barni ka bari in na gama karatuna ka koma

Hmm kanina ammi ta matsa in dawo nima ina so in koma kodan kasuwancina so nake kagama karatu in doraka akai

Wow yayana naji daɗi yaya ashe halima ce yar gidan kahu inusa take mun wannan test haba ni in dunga ganin code ɗin nanjeriya a she ita ce wallahi mutanan nan suna ban mamaki

hmm kai de bari na tafi inyi wanka kafin lokacin sallah yayi

"To, big bro,

wannan kenan

kinga pic ɗin sa

Zaro idu tayi cike da mamaki wannan shi tagani a gidan baba bilyaminu yazo zance gun sabeerin da ta kai mata abinci har ya zube

"kin san sane ?"

nan samha ta kwashe komai ta fada mata

dafe girji yayi tace

"na shiga ukku daman biri yayi kama da mutun yana wankin motocine sai kuma yasami aiki a company JJ na yin taliya ashe daman haka yake dan karya ni yanzu wallahi kaka ce ma tsalata kudi yake bata amma wallahi dole mu rabu

Ni na tafi gida ƙar abba yaji shiru

"To, samha saina zo,

"To, nuratu sai da safe ,

fitowa tayi tayiwa inna zinaro sallama tayiwa inna zulai ban garan kahu isma'il bata shiga ba saboda matarsa bata so wani dan gin miji ya raɓe ta shima baya son ɓacin ranta

Wannan kenan

kai yau mukullin gidan da aka baka kabayar haya shi zaka bani iya daran yau saboda sabeerin zata zo

Sani dillahi ya miƙo mai hannu bani

ni matsala ta dakai wallahi tsohon nan kafiye san kuɗi ka taɓa ganin zan hayi gidan ka ban baka kuɗi ba yawa yau muka saba wannan harƙar

Kajini da yaro nima tawa harƙar zan baje domin yau nace wata mikawo min tallan ƙosai tazo zan bata bashin ta kaga sai in kwashi romo

Dan Allah aa nima ka ajjiye min

saika ƙaran kuɗi

"TO, ungu dubu goma shabiyar na ƙara maka"

wllahi bazan amsaba saika ƙaramin ai ba haka muke da kai na kwanaki da kaiwa wata yarinya fayɗe ai ni ka bari a cikin har alhaji isuhu yana cewa zai kwace gidan sa tunda abin da nake bayarwa anayi kenan da ƙƴar na shawo kansa ya haƙuri dubu a shirin zaka bani

Haba sani dillali jiya fa sai da naje gun D.P.O sabon da aka kawo na bashi cin hanci akan duk ƙarar da aka kawo mai ya koreta akan mu ka daure ka amshi sha takwas dubu goma kuma zanyi dan wani abubuwan da ita

Wanne D.p.o?"

Na kan gaggare mana a she shima namune daman ina tararrabi da ɗayan ya sauka ban san wa za akawo ba ashe dan uwan mune

aa aa lamarin nan yayi min daɗi kaga sai muyi ta sheƙa ayarmu

wallahi kuwa na shega ukku ina zan ɓoya kamar sabeerin nake gani ƙar ta ganni tace daman nu ba ƙanin jj bane me yaka wota gidan su nuratu

yaro kenan ai komu daɗe ko mujima wataran halinka zai bayyana kawe ka mazai

Neman makafa yake amma lahin ba wani lungu da zai boya *…………✍🏼*
*YA ƊIN MAGE*




by


OUM YASMEEN





_duk Kan yabo da godiya sun tabbata ga ubangiji Allah na godemaka da kabani iƙon dawowa da ga dogon hutun da na tafi ya Ubangiji ka bani iƙon rubuta daidai ka hanani rubuta ɓarna_



*Tsokaci*


```wannan labari ƙirƙirarran labari ne ban yi da nufin tozarta wani ko wata duk wanda yaga yayi dai dai da rayuwar sa to ya ɗauka arashi ne bana sannan bana son dogon jawabi duk wanda yaga zai iya karantawa to ya karanta domin wannan labarin ba irin wanda na saba kawo muku bane yasha banban da labaran da na saba kawo muku sannan Please ɗan Allah in ƙinsan ba siyan littafina zaki ba ƙar kimin magana bana hulaƙanci ban yarda ayimin ba ƙar ki batawa ƙanki lokaci ki ɓatamin```





Page 56-60




Iya tashin hankali ya shi ga wani gida ya shiga ya ɓoye yayin da sabireen ta faka motar ta a kofar gidan inna zulai fitowa tayi tana hura hanci domin yau allah ne kaɗe yasan irin tashin hankalin da ta zo da shi cikin gidan kamar anjefota tsayawa tayi ta ruƙe ƙugu na inna zulai ta fito daga banɗaki hannunta ruƙe da buta ɗurƙusawa tayi zata ajiye butar hannunta sukai ido hudu da da sabeerin dafe girji tayi tace


"Yar nema ashe ke ce kika shigo mana ba sallama ko wallahi kin tsoratani?,


Wani ƙallon ƙasƙanci sabeerin ta jefawa inna zulai tace


"Ina zeenaru ?,


Ɗagowa inna tayi domin jikinta yayi sanyi duk masifarta sai yau ta nemeta ta rasa yo ta haɗu da yaran zamani hannunta tasa ta nuna mata ƙofar ɗakin zeenaru


Ya mutsa fuska sabeerin tayi ta kau da kai tace


"Am granny kiramin ita bazan iya shiga wannan gunba namayi ƙoƙarin iya shigowa gidan nan ko ya akai kuke iya rayuwa a gidan nan,


Banza inna zulai tayi mata ɗokin ƙofar ɗakinta ta zauna ta zuba ta gumi wai yau ƴar bilyaminu ce take aiƙenta har tana ƙƴamatar ta kahu isane ya shigo yace


"Aa yau manyan baƙine a gidan namu ,


Wani kallon tara saura kata tayi mai ta saki ƙwai ya bada wani ƙas ƙass tace


"Yauwa isah waccar matar ta nunamin ba tasan inda matarka take ba amma kai nasan zaka iya sani ina neman ta ita da shegiyar yarta me ƙwacan saurayi ,


Kan kahu isane ya kulle duban inna yayi yana jiran yaji me zata ce

Ganin sun zama yawa andasa su ala Dole sabeerin ta ɗaga murya tace


"Zeenaruuu zeenaaaruuu!!,


Jin wannan kiran na mafarauta baba zeenaru da nuratu suka fito baki ta buɗe zatayi magana tace


"Sabeereen ce agidan nan lallai yau muna da manyan baƙi,


wani irin taku take na isa ta ƙarasa gabansu cikin raini da nuna ƙasƙanci sabeereen ta nuna baba zeenaru da yatsa tace


"Ki dahalla rufe min baki daman nazo ne akan ki jawa yarki ƙunne akan saurayi na in taƙi wallahi kumace zata rabamu da ita zan iya ɓatar da ita kuma na ɓatar da banza ,


Cikin mamaki da tashin hankali baba zeenaru tace


"Sabeerin lafiya meke faru wallahi kin sani a duhu wa kike magana haka ?,



Bura'ubancan ni sabeereen yar Alhaji bilyamin nake magana kina cewa baki gane me nake magana akai ba to ina nufin saurayin nuratu


Kamar an dasa kahu isah yana tsaye yana kallon iƙon Allah yace


"Sabeereen muga photon sa iya sani na nuratu bata da saurayi me kuɗi tunda yanzu rayuwar kwarya tabi ƙwaryane ,


Wata harara sabeereen ta watsa mai ta nuna mai zaro ido yayi yace


"We Abdul me wankin mota dan gidan malam shehu me wankin hula to ai nadade da rabasu saboda ba dan arziki bane so yake ya lalatamin yarinya ,


Turusss sabeerin tayi tuni zuciyar ta ta shiga kaiwa da komowa daman ashe ƙarya yake mata biri yayi kama da mutum intace ya nuna mata pic ɗin jj yace ai baya son photo ko saudaya bata taɓa ganin family pic ɗin su ba maganar nuratu ce ta katsai mata tunani tace



"Aunty sabeereen kenan au ke daman baki san waye saurayin naki ba kika zo kina tada jijiyoyin huya ?,



Duban nuratu tayi tace


"Da hallacan matsamin yar marasa tarbiya,


Kahu isa zuciyarsa ta zo iya huya besa lokacin da ya ɗaga hannu ya mari sabeereen ba yace


"Sabeereen Ni ne mara tarbiyya to tarbiyyar da aka bani ita aka bawa mahaifin ki bilyaminu,


Cikin sauri Inna zulai ta tashi tace


"Isah zan ɓatar maka hi haƙuri sabeereen so kake ɗan balangwan nan da ake kawo mini a dina kai da ɗan uwan ka me mutuwar zuciya ba abinda kuke min,


Daman yasan za'a rina we ansaci zanin mahaukaciya yace


"Inna hi haƙuri yabar gidan Ita kuwa sabeereen kuka tasa tana tsinewa baba zeenaru da Kahu isah tabar gidan fuuuuu ta tada motar ta



______________________


Tun asubar fari ta tashi ta gyara gidan wanka tayi tasa wata atamfa brown colour da adon milk duk ta ɗan ji jiki hijabinta tasa ta fita gidan me koko da ƙosai fitowar ta ke nan suka haɗu da Usman yana goge a daidai ta sahunsa da sauri ta ɗauke ƙanta ta shiga gidan me koko ta sami lahi raƙuɓewa tayi tana jiran lahi yazo kanta hankalin ta ya kasu kaso biyu tana tunanin ko abba ya tashi ne ko har yanzu yana bacci ga damuwa da tayi mata yawa

ji tayi me sai da koko da kosai tace


"Na nawa zaki siya,


Kuɗin ta ciro tace



"Kokon hamsin ƙosai dari biyu,


Amsa tayi ta ƙirga mata nanah ce ta shigo tana ganin samha tace


"Inna delah kina da tsakin kuka ki sauri ki zuba a huta tun kafin a lashe miki masu siyan koko da ƙosai dan ni wallahi nafi ƙarfin mace ƙurwata da ɗaci,


Me ƙosai ta yi dariya tace



"Uhmm aikuwa bara in sauri in sallami mutum ,


Hawaye suka taru a idaunta miƙa hannu tayi ta ƙarɓa yau daban ace bata da wasu kuɗin ba da bazata amshi wannan koko da ƙosan ba juyawa tayi ta bar gidan da dan saurinta wani irin ƙuncine ya mamaye zuciyar ta ta rasa in da zata tsoma ranta taji dadi dai daita nutsuwar ta tayi ta shiga gida

Abin mamaki baya ƙarewa inna hajara da ita da abokanan iya shegenta har sun fito ta fara suyar waina kenan ba zata kotun ba kenan ganin bata da me bata amsa tayi sauri ta shiga gida mahaifinta tagani a zaune cikin murna tace


"Abba da kanka ka zauna?,


Murmushi yayi yace


"Samha iƙon Allah yau ji nayi yawa an ƙunce min wani abu a jikina kin ga aikin addu'a ko ina zaune naga wani kadangare ya fito gada ginin can da ya tsage yana ƙoƙarin cizon ƙafata shine na dinga karanto ayoyin neman tsari daga shedanu ko abokin gaba Allah ya bani sa'a na dauki sandar can na buga mai ina muga mai ya mutu ya buɗe bakinsa ga laya can ta fito a bakin sa shine fa na iya tashi har bayi na shiga,

Wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarta tace


"Alhmdllh dukkan wani tsanani baya tabbata face Allah ya yaye shi,

Murmushi yayi yace


"Hakane samha Allah ya kawo mana mafita,


Tashi tayi ta nemo kofi ta zuba koko ta miƙa mai da ƙosai ta dauki nata


_________Hyde park Chicago - America


Yau an tashi da sanyi ga wata irin dusar ƙanƙara da take sauka tafiya yake cikin titin Woodlawn avenue tsayar da motar sa yayi kusa da robie house ya dauki wayar sa yayi yan danne danne ya ƙara a kunne ba adade ba ya dauka cikin harshen Hausa yace


"Assalamu alaikum sa'id nazo kana ciki ne ?,


Daga can akace


"Wa'alaikassalam JJ ina ciki gani nan fito wa ,


Okay yace ya kashe wayarsa ba adade ba sai ga wani magidanci ya fito ba haushe zam motar ya buɗe ya shiga gidan gaba yace


"J.j kaga dan kasuwa yawa wani sarki,


Furzar da iska yayi ya cire facemask ɗin fuskar sa duk da motar sa baƙin glass ne amma ko mene da lilin da yasa ya rufe fuskarsa tambayar da nayi Wa kaina kenan amma ba me bani amsa yace


"Sa'id bazan ɓoye maka damuwata ba kasan yanzu naje shopping naga wasu mutane na bina da alama akwai wanda yake bibiyata sai de ya makaro nan ba kamar Nigeria bace ungo wannan ya dauko wata envelope yace ga number motar nan da picture motar kaimin binkice sannan a yau zani Nigeria zan bar ƙasar Nan ,


Ƙarɓa yayi yace


"Yauwa ma'aruf kenan ka dau shawarata wallahi in ba ta haka ba ba zaka taɓa samin wacce zata soka dan Allah ba wata ma za'a iya hada baki da ita akashe ka tunda kasan su Alhaji Abubakar ashirye suke su ɓatar da dukiyar su akan ka saboda ka fisu yawan masu siyan Kayanka da dilloli,

lips ɗinsa ya cize na ƙasa ya lumshe idanuwansa so nake in ganshi amma ba dama inaso inga wane j.j ɗin nan iya gefin fusƙarsa na gani yace

"Okay ai zalinci baya ɗorewa ina nan ina binkice akan su insha Allah na kusan gano inda ake kai dukiyar talaka abin mamaki shine kasan manfetur ɗin nan a kasar mu ake haƙoshi amma we ga yarda yayi tsada ya kamata shuwagabannin arewa su farka sudena ibarmana kuɗi su kai kashashan waje kasan jiya an kirani anmin gargaɗi in fita daga sabgar su sannan in rufe gidan jaridata in ba haka ba zan gani ,


Iska ya furzar me huce yace


"Amma ma'aruf kasan mutanan basu da imani ina zargin su suka turo yasmeen gunka dole ka ƙara sa ido a kan aeman sosai kasan in basu same damar cutar da kai ba zasu ba iya cutar da shi ,

tissue yasa ya goge fuskarsa ya cire glass ɗin sa yace


"Ni yanzu ma hankali na be kwanta ba da zamanshi a Pilsen nan zai dawo da zama,


Okay no problem


Fita yayi tada motar sa yayi cikin sirri ya nufi international airport ya hau prevent jack sai kano


__________________________


Fita waje tayi ta nemo me a dai dai ta sahu da yake har yanzu jikin sa be yi kwari ba ganin ya sami sauki yace ba sai sunje asibiti ba har ƙofar gida ya zo shiga tayi ta faɗa mai ai kuwa ya shirya da kansa fitowa yayi ɗan kuka ya zauna kusa da inna Hajara sai cin waina yake suna hira

25, December 2024
Amal

Mage

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login