Showing 24001 words to 26185 words out of 26185 words

Chapter 9 - ️YADIN MAGE OUM YASMEEN

29 Jun 2024

3208

hankali yace


"Okay thanks please go out,


Zaro ido tayi tace


"Why?,



Tsayawa yayi ya bude mata kofa yace


"Sick headache,


Tashi tayi tace


"Oh sorry 😔,

Matsa mata yayi ta fita ya rufo gidan sa yau yake ganin ikon Allah shi yasa duk wanda ya fita kasar waje sai wanda Allah ya tsare


Zama yayi ya ɗauki wayar sa number suhaila ya Kira aikuwa yawa jira take ta ɗaga ba ko sallama tace


"Yauwa big bro gani ga aunty samha ina gidan su ,


Zaro ido yayi yace

"Daman dake aka tafi,


Dariya tayi tace


"Eh ,


Gyara kwanciyar sa yayi yace


"Bani ita mu gaisa,


To tace miƙawa samha wayar tayi da duk ta takura da zaman ta agun hira sosai suhaila take kuma sai tayi magana hudu ba hausa amsa tayi cikin sanyin muryar ta kamar ko yau she tayi sallama


Lumshe ido yayi jibi iyanzu ta zama mallakin sa yace


"Wa'alaikissalam sweetheart 💋 😘 nayi kiwar ki Allah isa kema kinyi tawa,



Wani takaici ne ya tokare ta tace


"Lafiya qalau,


Daga jin yarda ta amsa mai yasan tayi fushi duk da daman shi yason me laifi ne yace


"Habibty ki haƙuri wallahi ba dan raina ya so ba nayi haka ina tsoron in auro wacce zata hallaka ni ne shi yasa nayi haka,



A jiyar zuciya tayi tace


"Na fahimce ka ,


Ganin kamar ta gaji yayi mata sallama barrister kamal ne ya zo tafiya da suhaila ba dan ta so ba ta bishi iya jan kunne ma'aruf yayiwa suhaila dan haka kuwa ta fasa party da zatayi ranar juma'a mu'aruf ya dawo ranar kuwa aka yanke wa Alhaji kabir hukunci daurin rai da rai ashe shi ya akashe mahaifiyar samha ankuma da wo musu da gidan su da ya ƙwace ranar kuwa muhibba kwana tayi a gadon asibiti irin wannan ranar take gujewa daddy amma shi be gane ba shalele kuwa ko a jikin sa tun safe yan gano gidan amarya suka shirya inna zulai ma cewa tayi sai taje



Ba yarda suka iya haka akasa ta fiyar da ita har da yan uwan mahaifiyar ta wayan da suke uba daya dan samha ba ta son su ba sai a yanzu suka nemeta duniya ke nan mutane ko kunya basa in suna wani abun ita kuwa hamziyyah sai nan nan take da samha abu kadan samha me za aimiki ita kanta mamakin ta take bayan sallar la'asar jirgin su inna ya tashi da yake baza su dawo ba sai an kawo amarya sun sauka inna sai kalle kalle take motoci biyu ne suka zo ɗiban su wani uban katafaran gida aka kai su inna cewa take wai hajara wannan yawa ba'a duniya nake ba tab daman yarinyar nan ai kallar hutu ce kunji fa ce mata fa take me hatumin talauci kai duniya kenan Allah isa mu dace parking driver ya tsayi amma kafin ya gama inna ta buɗe ta fito kai jama'a sau ran kadan ta waɗi driver yace


"Haba hajiya ai kƴabari in gama ki fito yanzu da kin karye fa,


Haɗa rai tayi tace


"Kai yaron nan kar ka faɗamin ba sugari,

Girgiza kai yayi domin ya gane irin masifaffun tsofaffun nan ne wayan da kaɗan suke jira sauran ma fitowa suka wata hadaddiyar kofa suka nufa sa key yayi ya buɗe musu ya miƙawa inna zenaro yace


"Gashi sai ku ajiye mata,


Amsa tayi shiga suka kai aljannar duniya komai ya tsaru iya taruwa ya kashe dukiya wajan kawata gidan nasa ba inda ba su shiga ba suna zaune sai ga yan aiki sun ka wo musu abinci ai inna ta dinga nada kai kace ta kwana ta hini bata ciba waya ta dauko tace

"Ke hajara kiramin mijin ki,

Hada rai hajara tayi domin abin na inna ya ishe ta tun dazu take ce mata juya ai taga arzikin haihuwa amma sai dai aita ci da ita tana kashi kiransa tayi be wani dau lokaci ba ya ɗaga kuka tasa ta fyece majine tace

"Sule yau gani ina cin arzikin ka sule Allah ya bawa samha ka ganni nan sai cin kaji nake sule wallahi na tausaya maka da akai maka baƙin ciki baka zo ka ci ba ina ci kai nake tunawa ko ka tada komaɗa,


Girgiza kai yayi wato me hali baya fasawa yace


"To inna Allah ya basu zaman lafiya,


Cinya ta ɗauka ta ci tace


"Amin sule sai anjima,

Kashe wayar tayi kafin safiya inna ta shiga toilet yafi sau biyar duk ta fita hayyacin ta yo pepper chicken 🐔 🍗 taci ga taco🌮 ya ci kayan lambu cikin ta ya ɓaci ga uban Attahiru cewa take anya ba dangin mayu suka kawo samha ba ai sunsan baki ne yaushe zasu sa Attahiru a girkin su dariya aka kwashe da ita ganin sun mai da ita yawa mahaukaciya sa ta yi shiru da bakin ta badan ta soba


*RANA BATA ƘARYA*


Cikin wata ɗanyar shadda White colour ya shirya anmai aiki da golding colour hular da yasa me tangaran wacce zata dace da shigar da ga agogo dan gidan rado takalmin da golding colour wani irin kyau yayi na ban mamaki yau ya yarda yan jaridu su ɗauke shi tun daga filin jirgi ake mai video har zuwa masallacin juma'a Na Sheikh isaya rabi'u daurin auran ya samu halattar manya manyan mutane har da farar fata sun zo inda duniya ta sheda ɗaurin auran bilkisu sulaiman (samha) da na ma'aruf jafar jabir wata iriyar kabbara aka saki nan maroka suka shiga wasa shi dun guma akai har kan karofi kamal aeman suna tare da shi hutuna sukai da su kahu isah har kahu Ismail ba abarsa a baya ba abin mamaki baya ƙarewa kahu bilyaminu na gani yana washe baki sai bin abba yake duk inda yasa kafa ƙaguwa yayi yana so ya ga samha

amma ba dama mutane sai hutu na suke da shi ba shi ya sami kansa ba sai bayan la'asar lokaci kuma ya kure ana ƙoƙarin kai ta gidan tane tun safe take kuka ga wani irin ciwon kai da take duk ta rame cikin tane ya murɗa jin ana tayi sauri ta shirya jirgi baya jira da sauri ta tashi tana xare ido ta shiga toilet dariya nuratu ta saki tace


"Samha amarya da ga jin kaiki har da gudawa,


Dariya yan ɗakin suka saki fitowa tayi tayi wani irin fari kai kace wanko fatar ta akai atamfa ce Ingila a jikin ta blue Black ɗinkin riga da zani tayi mata cib yawa an gwada ta aunty salma CE ta shigo tace


"Yauwa zo ,

Jitayi kafarta tayi nauyi da ƙƴar take ɗagata wanka tasa tayi da ruwan turarurruka sannan ta bata leshi onion colour anmai adon flower light pink and blue wata hadaddiyar lufaya tasa bule colour tayi kyau ga sarkar gold a huyan ta sai kamshi take ba aimata wani make'up ba zama tayi hawaye na bin fuskarta anty salma tace

"Oni salma samha yau she zaki bar kukan nan ,


Ƙasa tayi da kanta tana wasa da fingers ɗin ta ya ci lalle ja da baki ya ƙara haskaka fatar ta daman abin ka da fari torowa akai zasu tafi gun abba aka kaita yayi mata fada sannan ƙanwar kakar ta tayi kukan rabuwa da su a hankali jerun motocin da zasu raka ta suka fara tafiya har suka isa airport shiga jirgi sukai da yake duk wanda zashi na kusan tane an siyamai ticket 🎫 to bayan sun sauka kai tsaye bangaran hajiya Sa'a aka kai ta aka danka amanar ta cikin mutunci da karramawa ta amshe su tashi sukai a ka kaita ɗakin ta da kafar dama ta shiga a luxury bed ɗinta ta zauna su nuratu kowa sai hotuna suke barin hamziyyah yar tiktok direct wasu bayan sun gama ganin gida aka dauke su a mota za amai da su kano su nuratu kuwa sai gobe yaye lullubinta tayi ganin gidan yayi tsit ba kowa kallon ko ina take fu tsari take ji tashi tayi ta shiga toilet ɗin dake manne adakin ta

Ta shiga shagala tayi da kallo yawa mutum zai kwanta fitowa tayi ta ɗauro alwala domin tasan yanzu dai anyi isha salla tayi bayan ta idar tayi addi'o in samin zaman lafiya a rayuwar auran ta duk kan wata fitina Allah ya kade musu ninke prayermat tayi ta bi lafiyar gado ta kwanta duk irin tsiyar da suke mata bata kula su ba washe gari da safe jirgin su ya ɗaga samha ruƙo aunty salma tayi tana kuka da kƴar aka kwace ta zama tayi tana kuka bakowa ko breakfast ba su tsaya sun ci ba tun safe ammi ta aiko suhaila da rakiba suka kawo

Akan royal sofa ta zauna ta zuba ta gumi wani irin tsoron gidan take baka jin komai sai kukan tsuntsaye ashe mutum ma rahama ne bataji sallamar da yayi ba sai ji tayi an taɓata zubbur ta tashi gumi na yanko mata dariya yayi yace


"Sarkin tsoro tunanin me kike har na shigo nayi sallama baki jiba?,


Ƙasa tayi da kanta ta durkusa ta dauko mayafin ta da tsoro ya sata ta wadar da shi tace


"Ina kwana,


Dagota yayi ya zauna da ita akan cinyarsa ƙoƙarin sauka take amma be bata dama ba yace


"Ni bana son irin wannan gaisuwar nan nake so ba,



Kunya ce ta kamata ta kautar da kai ganin yana ƙoƙarin kamo bakin ta ganin taƙi ya sauke ta ya ruƙo hannunta yace


"Zo muje muyi breakfast ,

Binsa tayi dining chair ya ja ya zaunar da ita ya ja ta kusa da ita ya zauna abaki ya dinga bata 🍳 tun tana nuƙewa har ta saki sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya tashi ya goge mata baki shima ya goge hannunta ya ruƙe yace


"Muje mu gaishe da ammi,


Bata ƙiba haka ta bishi yana gaba tana baya shammatar ta yayi ya ruƙo hannuta ko da suka zo dai dai kofar ɗakin ammi taso ta kwace amma yaki sallama sukai nazifa da rakiba da suhaila sai ammi duk suna zaune amsa musu sukai har ƙasa ta durkuwa ta gaishe su domin dukka sungir meta hannuta ammi ta kamo tace


"Zonan ya'ta,

Matsawa tayi kusa da ita zuciyar su rakiba ce take suya ashe shi isa yaƙi yarda ya aure su balarabiya zai auro ko ya ko ina tai musu fintin kau ga kana nan shekaru yarinya sharaf da ita tashi yayi yace


"Ni zan fita tun da anmin wariyar launin fata,


Dariya ammi tayi tace


"Kowa na son sabo sai ka dawo yau gani da ƴa'ta Allah ya ,


Murmushi yayi yace


"Amin,


To hira suka fara da suhaila tun bata biye mata har ta fara biye mata bashi ya dawo ba sai bayan magarib be shigo gida ba sai da akai sallar isha tarar da su yayi suna kallo gai shesa suka amsa musu yayi kamar ko da yaushe zama yayi yace


"Ammi barka da dare,


Misfruit da take sha ta dakata tace


"Yauwa ka dawo lafiya?,


afakai ce yake duban inda samha take ta wani rakube yace


Lafiya qalau ya tashi yace sai da safe


Ammi tace


''ba zaka tsaya kayi dinner a nan ba ,


Ƙeya ya sosa yace


"Ammi inna yi wanka naci ko fruit salad 🍓 🍑 ,


Duban inda samha take tace


"To samha tashi kije ki haɗa mai,


Badan ta so ba ta tashi ta bishi tashi raƙiba tayi ta shiga ɗaki ta saki kuka yau zasu kwana tare sai wani kishi ya danni zuciyar ta dole ta bar gidan in kuwa taƙi za adau gawar ta



Bayan shekara ukku samha ce ɗauke da wata kyakkyawar yarinya yar kimanin wata hudu gifen ta ma'aruf ne ruƙe da yara maza masu kama daya fara re tas da su wato arif da irfan arif yaci sunan abba irfan ya ci sunan abbie macan kuma sunan inna tace ana ce mata afnan cikin sallama suka shiga wani tamkeken gida abba nagani da baba hajara sosai sukai murnan zuwansu bayan sun gaisa sun dan taɓa hira suka tashi za su gidan suhaila da kamal fitowa sukai nana ta gani da katon ciki ta zama abar tausayi tace


"Samha,


Samha tace


"Nana,


Kuka tasa tace


"Dan Allah ki yafe min kinga irin yarda rayuwa ta zamar dani ko,


Cikin nuna jimami tace


'allah sarki wallahi na dade da yafe miki,

Usman ne ya fito ya zama babban mutum gaisawa sukai kyauta tayi wa yarsa ta bawa nana itama ba samha ta zama babbar mace dan a yanxu dgree ɗin ta na hudu take yi amfanin economics tana aican shiga mota sukai ganin irin cin maganin da yake tace


"Habibty yau fushi ake da ni,

Kara hada rai yayi yace


"Bana so in ga kuna magana da wani namiji balle wanda kuka taba soyayya,

Dariya tayi ta kwantar da murya tace


"Haba sweetheart 💋 😘 gaisawa mukai muka ai a gaban ka ne ko tunda baka so na daina,


Dariya yayi yace


"Yauwa my lovely 😍 🌹 wife,

Sosai suhaila tayi murna da ganin ta bayan su gaisa suka je gidan nuratu to shima ba su da deba suka fito inda suka hau jirgi domin komawa gida

Alhmdllh alhmdllh alhmdllh Allah na gode maka da kani iƙon gama littafin nan lafiya


Ranar talata 21-5-2024

Ƙarfe 4:27

Na mallakawa king 👑 and queen 👑 writing chamber















7
8
9
25, December 2024
Amal

Mage

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login