Showing 21001 words to 24000 words out of 76784 words

Chapter 8 - WA ZAI FURTA COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2024

15127

kullum Ina hangen abinda gaba zatayi. Ban wuri in wuce jiya Kuma Kai ta shafa bani ba.
Amma ai na Baki hakuri ko?
Ikon Allah nace ban hakura bane? To idan kin hakura ki zauna mu Kara abinda muka Fara jiyan.....tayi murmushi Mai Kama da kuka Allah ya albarkaci abinda mukayi din ya wadatar wallahi bana so na yafe.
Ya kife Kai bisa table....shikai yasan yanda zuciyar sa ke mishi.
Kai nake jira.
Ya dago Kai har Yanzu taki yarda su hada ido, me kike so Yanzu in Miki?
Ka bani wuri in wuce. Ta fada fuska chunkushe.
Anya yarinyar ba zafin kishi ke addabar ta ba? Me yasa bazata fito tace tana sonsa ba kamar yanda sauran Yan Mata keyi Masa?.
Zan Baki wuri ki wuce Amma sai kin mun alkawari Zaki dauki wayata anjima.....banyi ba Kuma bazanyi ba ka bani wuri in wuce Wai Ina dalili?.
Ya Mike tare da say hannu duka biyu aljihu Yana gaba tana bite kamar zata tureshi Yana fita sit din tayi hanyar waje da sauri ya bita da ido har ta yi nisa ta taga.
Sadeeq na can baya kansa bisa littafi kamar Mai karatun gaskiya. Ya ce su tafi library din.
Ita kuwa daki ta koma.
Tana sallar azahar barci yayi awon gaba da ita, sai biyar ma ta wuce ta tashi. Ga wayarta silent missed calls kusan goma shaa biyu. Khausar biyu, mommy biyu, hudu sabuwar lamba sauran Anwar.
Sai da ta Dan watsa ruwa tayi sallah sannan ta bi Kiran, khausar abinci zata Mata tayi, mommy Kuma zata fada Mata gobe zasu shigo Murna tsalle.
Alamar shigowar sako ta gani tana budewa taga wata number.
```i'm guilty I knew, please accept my apologies it will never happen again I promised```
Hmmm, tace kafin ta ci gaba da magana a fili.
Bana iyawa Yan matanka nesa nesan zaifi gaskiya don haka ka gaji ka kyaleni.
Washe gari karfe biyu su daddy sunka iso. Cikin wata Hummer Jeep bullet proof. Duk inda motar ta gitta binta akeyi da kallo. A bakin hanya ta taro su tunda sukayi waya ita da khausar, su Aisha sunje test. Murna, tsalle, da ihu kawai takeyi.
Hankalin Yan compound din ya dawo kansu *lallai Bilkisu ba diyar kananan mutane bace* Nan da Nan kallo ya dawo gunsu musamman lokacin da sukaga irin kayan da ake shiga dasu ciki.
Har dakinta Shima daddy.
Ta rasa inda zata sa kanta tana makale jikin kafar mommy ana shagwaba. Kayan ciye ciye baje na gani na fada. Daman sunce ko ruwan zafi kada ta dafa.
Kawaye aka Fara shigowa da makwabta ana gaisuwa abin ya birge kowa......
Daddy ya kalleta Ina *Anwar* ki kirashi mu gaisa da abokin fadan naki......mutanen dake cikin dakin duk aka Kama dariya.
Gabanta ya Fadi.
Wannan karon fa fadan na gaskene ......mommy tayi karaf, ai dole mu ga Anwar yau Kam maza kirashi a waya kice gamu munzo...........


Ayi hakuri da kadan. Wallahi nayi typing 7 dinnan kawai mistakenly na gogeshi Shi yasa na rasa ta inda Kuma Zan Fara .
AfuwanπŸ˜„πŸ˜„πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ zainab wowo ceπŸ’–βœπŸΌ
🀐 *WA ZAI FURTA?*🀐
0⃣8⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
```wallahi tallahi ban taba ganin maiyi don Allah ba irin ki ya Allah ya Kara Miki lafiya da tsawancin kwana kina Raina Koda yaushe Kuma addu'ar mu in shaa Allah muna rokon Allah ya karba alfarmar fiyayyen halitta SAW```🀲🏼
*Abinda mutane suka kasa ganewa shine, ba daukar kudi ko wata kaddara kaba mutum kadai ne kyautatawa ba, a'a..... Mutuntawa, girmamawa, magana Mai dadi da sakin fuska na daya daga cikin abinda ke saka soyayya, shakuwa da Kuma girmamawa, Amma sai kaga wasu jakkan sun maida mutane banzaye basa daratta kowa kuma suna tunanin dole ayi musu biyayya saboda suna da hannu da shuni....sammmm ba haka abin yake ba, ga Wanda ya San ciwon kansa ka Zama bola daga ranar.* Ya Allah ka wanke Mana zuciyar mu irin ta *Aunty Rabi* ya hana mu kyama da wulakanta Wanda bashi dashi amin.


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Ke ce uwar gida Kuma Amarya in shaa Allah Alawiyya Nasir, matar Daddy uwar maamah da sofy, aminyar gaje Abu kawar Yar hareez Ina godiya ga namjij kokarin Samar mini Yar aiki na gode my disturber πŸ™„. Gaje Abu ga taki πŸ‘‰πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ’– na gode Allah yabar tare*

*****************
*KADUNA RIGASA*
```Wuya makarantar kare``` sunan wani littafin ```ZeeDee```
Ummi ta bala'in shiga hankalinta.
Ranar yabar gidanta, tun la'asar ya mata sallama kagare yake magariba tayi don Yana son Zama da Amira itama.
Gidan ya dauki kamshi tana ta soye soye da gashe/gashe,
Sai dai taga mutum bayan ta. Zabura tayi cikin tsoro.
Ta turbune fuska wallahi ka bani tsoro.
Ai gara haka, Ni jiya ba korata kikayi ba na kwana masallaci......Kai kajiyo. Ta katseshi.
Eh nasan cewa kishi ne yasa kikayi mun haka ....Ni na jiyo tunda na Kara Aure ko?........
Bana son irin wadannan maganganun ya kamata zuwa yanzu ka fahimceni.......naji...naji, shikenan.
Yanzu dai kawon abinda ya samu yunwa nake ji ....ya juya zuwa falo.
Dambun naman kaji, meat pie, doughnuts, da lemun kwakwa ta Fara kawo mishi. Yana Gama ci ya tafi isha'i, lokacin da ya dawo ya tarar da farfesun hanta, hunhu, Koda da tunbi.
Yana son sa sosai, saboda yanayin yanda takeyin sa:
*Farfesun hanta,hunhu,Koda da tumbi*
Bayan ta wanke su da kyau ta zuba a tukunya sai ta kawo albasa Mai yawa (musamman Mai lawashi), tafarnuwa,da citta sannan ta Dan zuba Maggi onga na sachet ( gari ) Shi kadai. Bata zuba ruwa sai ta dora Kan wuta low Yana heating a hankali kamshin kayan zai dakesu sosai ya danyi dry sannan sai ta zuba jajjagen tarugu da albasa again ta tsaida ruwa ta rufe.
Lokacin da ya dauko dahuwa ne ta zuba sauran Maggi da Dan gishiri to taste tare da curry kadan. Idan ya hade sai maganar ci.
Tana zaune gefen sa, suna ci tare, Ahmad ne ya shigo da gudu anyo mishi wanka,
Kai lafiya?
Abba gobe Aunty tace kowa yaci gayu zamuyi class picture.....
Shine zaka fado haka ba sallama daga Kai sai boxers? Ta fada tare da balla mishi harara....sim sim sim ya juya zai koma.
Ya kalleshi naji Ahmad in shaa Allah gobe gayu zakuci je hassu ta baku abinci kaji ko?
Yace toh ya juya.
Kin cika zafi yaran nan yanda suke tsoron ki koni basa tsoro haka meye abin fada ga shekaru irin nasa ma abinda yafi haka yi zaiyi.
Hmmm, kawai tace.
Ya finciko ta......zo in koya Miki yanda ake ba miji amsa idan yayi magana ba hmmm ake cewa ba.........dai dai ita Kuma ta turo kofa ashe bude yabarta lokacin da ya shigo.
Yana kokarin Kai bakinsa ga nata sukaji an turo kofa itace tayi saurin zamewa tunanin ta ma ko Yan aiki ne.
Tuni idanun ta sun gane Mata.....me ya kawo ni?
Wace kaddara ta aikeni?
Na gano ma kaina Ni Ummi........gabanta ya dinga halbawa da karfi da karfi.
Ita Bata karaso ba, Bata Kuma juya ta koma ba.
Gashi ya rike Amirar gammmm yaki saki, sai kichiniya takeyi amma ya riketa tamau . Dole ta hakura ta kalleta, ki karaso daga ciki Mana Kika yi tsaye bakin kofa.
Bai dago Kai ba Yana ta wasa da hannun Amirar yace idan wani abu kike bukata me zai hana ki Kira waya?
Shiru dai tayi har ta zauna bisa kujera tana facing dinsu amma ta kasa Kara maida idanu ta kalli takaici.
Tayi shiruuuuuuuuu, sai Kuma kwallah sharrrr, duk motsin da takeyi idon Amira na kanta saboda tana ta mamakin zuwan nata.
Ganin zubowar kwallah yasa ta zunguro shi,
Ya maida Kai gefe Ummi lafiya dai ko?
Ita kanta tasan kukan da biyu takeyin sa, kasa ta sauko ta Fara magana a hankali,
Aunty Amira kiyi hakuri Dan Allah Akan abubuwan da suka faru sharrin shaidan ne, in shaa Allah hakan bazai Kuma faruwa ba......Ayya Ummi ba komai ya wuce.
Ta fizge hannun ta bari in zubo Miki abinci......um um na gode ta mike.
Ina zakije toh? Ki zauna muyi fira.......ya Kara hade fuska ya tsuke.
Ta Dan tabe baki , a'a barci nakeji da wuri sai ko zuwa gobe haka.
Har kofa ta taraka, kafin taja kofar.
......... Gaskiya abinda kakeyi ko kayi Abban Ahmad wallahi baka kyauta ba, Shi ido ba mudu ba yasan kima.
Ka rikeni gaban Ummi ai wannan cin fuska ne.
Ya kalleta sosai.......makaho idan Yana Kashi in har ba'a zungureshi ba to bazai gane ana kallonsa ba.
Yarinyar can abinda take nuna mun tun kafin in aureta dole in bita in Mata yanda takeso ita bazata bi ra'ayi na ba.
To Ni da ita wake auren wani?......duk da haka Yanzu kaga.....kiranta mukayi?.
Inba kilibibi da tsugudidi ba me ya kawota Yanzu?
Ba a haka......ke naji.
Tayi murmushi.... Ita Amarya ai Bata laifi.
To wannan dai tanayi.
Naji dadin zuwan ta yau din wata kilan ta Dan Sami darasin kula da miji idan ita din Mai hankali ce.
Ya Mike idan kin Gama sallamar Yara Ina jiranki.

*Ummi* taci kuka kamar ranta zai fita, tabbas ya kamata tayiwa kanta karatun ta natsu. Ashe ita sunan tana Aure Amma har Yanzu Bata San meye Jin dadin Aure ba, ta goge hawayen da ke shatatowa, dole in kwantar da kaina inci arziki in barshi inda yake saboda tabbas idan naki abinda yake so nice Masha wuya.............

******************
*Federal University dutsinma*
Shigowar su Aisha ya bata damar neman mafita.
Ita kanta ma tana son ya zo su gaisa amma bazata iya kiransa ba.
Text ta tura mishi.
_Kaxo ku gaisa da su daddy yanzu_.
Wayar na hannun sa Yana kallon film.
Zaune ya tashi zumbur.
Sadeeq ya kalleshi lafiya?
Ya jefa mishi wayar.
Anzo wurin Dan ubanka sai kaje ka gabatar da kanka.
Munafukan banza Kun tsaya sai ba juna wahala kukeyi.....mtsew malam ban wayata.
Ya jefa mishi.
Wani text din ya Kara shigowa ... _zasu tafi in d next 30 minutes so hurry up and come_
Kara jefa ma sadeeq wayar yayi.
Kai seriously fa ...ya fada Yana zaro ido.
Ya tuntsire da dariya sai ka tashi ka tafi.
Ku dai tashi mu tafi wallahi bazanje Ni kadai ba. Kasan dai rashin zuwan Nan kuma wani problem din ne.
Anas ya Mike zumbur Tabb ku tashi mu tafi rigima dame ta cimma kurege.
........ Ya kallesu sai faman canza Kaya sukeyi, yayi murmushi wallahi Yan iska ne ku.
Kaman zakuje biki?
Sadeeq ya jefo mishi wani farin boyal malam saka mu tafi...
Ya Mike idan Kun Gama mu je banson shirme.
Duk sukayo mishi chaaaaaa wallahi sai ka canza Kaya Dan ubanka da wannan hug din zaka je?
To meye aciki?
Kana hauka ne?
Ku daine mahaukata, Kun zauna Kuna ta faman wata kwalliya kamar zakuje daurin Aure.
Yayi hanyar waje.
Anas ya finciko Shi, kasa manyan kayan nan kada muci ubanka.....kici kici suka Fara kokawar cire mishi riga. Ba arziki ya cire su.
Sukayi juyin duniya yasa hula kube yakiya dole suka hakura sai dariya yakeyi masu duk sun Sha huluna.
Daddy ya Fara mikewa Zan jiraku waje ku karasa kada muyi dare....... Tuni su Aisha sun rufo mishi baya don barin Bilkisu ta gana da mommy.
Mashin din muhseen roba roba suka amso.
Sadeeq ne driver, Anas tsakiya Anwar karshe.
Suna shawo kwana sadeeq ya kurma zagi ashar, wancen muguwar motar fa?
Dai dai su daddy na kunno Kai sai dai ji sukayi Anwar ya dire da yake ba gudu sukeyi ba.
Ga Anwar nan kuwa inji Aisha.
Murmushi daddy yayi, nesa kadan sukayi parking.
Tare suka jero su uku.
Wata irin faduwar gaba yakeji wacce bai taba Jin irinta ba, duk suna durkushe lokacin da suka karaso.....Barka da rana.
Idanu su Aisha suka bude duk girman Kan su?
Ya fadada fara'ar sa ya Mika musu hannu, Assalamu alaikum duk Wanda suka gaisa sai ya dago hannun alamar ya Mike tsaye har yakai ga Anwar,
Wani shocking yaji duk illahirin jikinsa ya dauka dai dai lokacin ne Kuma Bilkisu da mommy suka fito.
Ta danyi dariya to mommy ga Anwar can .
Da sauri ta Fara waige waige Yana Ina?
Gashi can daddy ya rike hannun sa.
Tunda ya dago daddy bai saki hannun sa ba, ya rikeshi gamm suna Yar tafiya hakan yasan su sadeeq da Aisha stepping back kadan suna bin bayan su.
Sai murmushi yakeyi Yana sunsunne Kai.
Daddy ya kula dashi tsaf!, ( Abinda bai sani ba yasa an kishi bincike kaf akansa tun lokacin da Bilkisu tace wurin Shi take daukar karatu ).
Ya karatu?
Alhamdulillah! Ya fada,
Kana fama da rigimar Bilkisu ko?
Yar dariya kawai yayi, har lokacin yaki yarda su hada ido dashi.
Ai kullum labarinta Anwar, ko an Kara wani fadan ne?
A'a ya fada Yana murmushi.
Ta ce Kai Dan Kano ne ko?
Eh, ya ce har lokacin fuskarsa ta kasa daina murmushi.
Me yasa baka jituwa da malamai?
Lokacin ne ya Dan saci kallon daddyn ta gefen fuska....
Ya kasa amsa tambayar.
Ganin haka yasa yaci gaba da cewa, mutunta malamai akeyi ana gaishesu, wasu akasin hakan duk kokarin ka sai sunyi maka mugunta.
Haka ne!, Anwar din ya fada a hankali.
Sai a kiyaye kaji ko?
In shaa Allah. Yace.
A bakin mota suka tsaya.
..........ga Anwar ga Anwar , tun daga nesa mommy ke fada tana dariya.
( Na shiga uku ni Hamza ). Ya fada cikin zuciya.
Duk su sadeeq suka gaisheta Bilkisu na gabatar dasu.
Ya yunkura zai zukunna don gaisheta daddy ya rikeshi, ku gaisa a tsaye kamar yanda sunna ta koyar.
......ya akayi Kika gane shine Anwar? Daddy ya tambayeta Yana murmushi.
Balky ta nuno min Shi lokacin da mun fitto.
Idanun ta na kansa Shima Yana son kallonta Amma ya kasa.
Su Aisha sukayi bankwana suka juya, Shima ya saci kallon su Anas alamarr su ware lokacin dasu daddyn kema su Aishar bankwana da nasiha.
Sai dariya sukeyi mishi daga nesa. Daman tun da suka taho da daddy din suke mishi dariya ganin duk yanda ya dabarbarce.
Anas yace munafuki kaga duk rashin kunyarsa yaki sakewa Kuma don sun dauki mutane Yan iska Basu so a gane suna son juna.
Anas ne ya matso ya Dan rusuna zamu koma hostel Allah ya tsare hanya...... Amin Amin ya zaro envelope ya Mika musu. Har lokacin hannun daddy na cikin na Anwar.
Ya kalli Anwar tafiyar ku daban ko?
Ya Dan sunkuyar da Kai tare muka zo.
Ohhh, to su tafi sai mu ajiyeka...... Ba Anwar din ba ita kanta Bilkisu tayi mamakin hakan.
Ya kalli Bilkisu ba abinda kike bukata Kuma?
Tace eh. Okay muje kada dare yayi suka bude mota.
Lokacin ne ya Sami hada ido da ita.
Ya sakar mata murmushi sai kawai ta harareshi ta juya.
Gaba ya shiga Yana nuna hanya.
Allah dai ya baku sa'ar karatu ya kareku daga dukkan sharri.
Yace Amin
Dan Allah kusa tsoron Allah ga dukkan al'amuran ku Anwar kada kuci amanar iyayenku, kaji ko ?
In shaa Allah mommy. Ya fada.
Yayi matukar godiya lokacin da suka ajiye Shi daddy ya umurci driver ya sauke mishi sauran kayan dake boot , sannan ya Mika mishi envelope Mai kauri.
Yayi godiya sosai. Aka Fara sauke Kaya, cartons din lemuka , ruwan roba, carton din indomie, oat,Madara family size 3, corn flakes, biscuits kala kala,Dan kalin turawa cikin buhu, plaintain, kwai Crete hudu,fresh milki, gasassun kaji, kilishi, soyayyar miyar naman rago, dambun Daman kaji, fanka Mai chargy ( Daman Yana da ita ), sabon carpet kato Mai laushi da turaruka.
Cikin kwalaye aka jero kayan.
Yabi kayan da kallo kafin ya Kara komawa bakin tagar motar yadan rusuna, Angode Allah ya Kara arziki Mai albarka ya bada lafiya da tsawancin kwana. Duk suka amsa Amin Amin.
Ya daga musu hannu Allah ya kiyaye lokacin da driver yaja mota, gaban hostel din cike da mutane Shi kawai ake kallo saboda motar da ta janyo hankalin kowa.
Da gudu su sadeeq suka karaso.
Ya kallesu ku shiga da kayan Nan zanje in ga Bilkisu......kawai ya tsaida mashin ya koma..............Tana ta faman shirya kayan Jennifer ta shigo, Bilkisu Anwar want you......ta kalleta da sauri Anwar?
Yah, he's out side...... Tana fadar haka ta fice abinta.
Ikon Allah, lallai ni ta bance , duk FUDMA kuwa akwai macen dake juya Anwar kamar Ni?.
Wallahi Bata taba tunanin zaizo ba lokacin da tayi mishi text despite fushi da rashin daukar wayarsa, Wai me yasa Baya mata fushi da gadara da Kuma wulakanci kamar yanda ya Raina kowa?.
Hijabi ta saka ta janyo dakin.
Yana tsaye ya harde hannu duka biyu a kirji.
Manyan Kaya na mishi kyau matuka, ya Kura Mata ido kamar zai cinyeta.
Ta karaso kanta kasa, Ina wuni.....ban amsawa.
Wai Bilkisu me kike nufi ne?
Me Kika fadawa su daddy akaina?
Ta dago Kai me fa, wani abu ya faru?
Komai ma ya faru gashi kince dole nazo mu gaisa ya Mika Mata kudi Kinga bayan Wanda aka ba su sadeeq ga nawa Kaya Kuma nacan an ajiye mun kamar.....to meye ne ba kyauta bace?
Ya kalleta, Kuma only me?
Ta daure fuska Ni ban gane abinda kake nufi ba...... Meye Kika fada ma iyayenki a kaina? Simple question.
Ta gyara tsayuwa, sun San cewa Kaine kake koya mun karatu Kuma Koda yaushe Ina Basu labarin karatun da mukayi.....ya akayi daddy yasan bana shiri da malamai?
Ta zaro ido wallahi bamuyi wannan maganar ba.
Kin tabbatar?
Ta balla mishi harara na maka ta kudin ka.
Ya kyalkyace da dariya, to ai abun ne ya bani tsoro,
Mtsew ....tayi tsoki.
Mun shirya ko? Tunda na amsa Kira na Kuma bada hakuri Nima ayi hakuri na gaji da fadan Nan wallahi.
Mun shirya ko? Ya Kara maimaitawa Yana murmushi,
Ta yi Yar dariya eh,
Good, Dan Allah kiyi mun godiya sosai na gode.
Ba komai. Sai gobe.
Korata kikeyi?
A'a bana son dai a Kira magriba kana Nan ko?
Hmmm, kawai kin koreni sai anjima ya Dan juya kamar yayi fushi.
Allah ya baka hakuri ka dawo ban koreka ba.....ya juyo Yana murmushi tunda kin bada hakuri kin tsira.
Zan kiraki please.
Ta juya.
Kinji?
Na ce toh.
Tuni magana ta Game ko'ina akan zuwan iyayen Bilkisu Kuma anga Anwar a wurin.
Hankalin mufeeda yayi mugun tashi ta dunga bala'i a daki. Tare da Shan alwashin dole ta gyarawa Bilkisu Zama ta Kuma ja mata kunne akan Anwar.
Sha daya da kwata na dare ya kirata. Labarin kayan da aka kawo mishi da makudan kudin da aka bashi yake lissafa Mata sanannan yadanyi Mata bayanin course din da zasuyi gobe.
Sha biyu ta wuce suka ajiye.
Su sadeeq sunyi sunyi yayi confessing akan Bilkisu Amma amsar kamar kullum itace, *baku da hankali*
Kowa yayi mamakin ganin su rumi rumi.
Sai karfe hudu suka gama lecture.
Duk ta gaji tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login