Showing 27001 words to 30000 words out of 76784 words
kurma ihu.
Malami ya shigo yace ku fita zamuyi darasi......
Haka suka fito tare da jingina jikin icce ita da sadeeq har lokacin hotuna sukeyi ko kallon inda take baiyi ba.
Sadeeq ko zamu je ka nuna mun Dan Allah? Ta fada Rai bace........ A 'a ki jira ya Gama kinsan halin mutumin....wallahi yau Kam bana so ko da kuwa yazo.
Tohhhh..... sadeeq yace kafin ya Kara magana sai ga Anwar din.
Bilkisu muje.
Ta kalleshi kallon da ya gwammace bugu dashi sannan tace bana so kaje kawai.......
Duk akayo musu ratai da ido.
Nan da Nan ya hasala don yasan a rina iyakar rainin wayo yarinyar nan ta daukeshi sakarai,
Saboda me Baki so? Ya bukata a hasale....
Ina ce hoto ne a gabanka, ko? Ina jiranka mintuna kusan talatin.....Kai ma abokina meye haka.
Zanci ubanka sadeeq...ya daka mishi tsawa.
Kada Allah yasa taso waya rasa?
Don kinga Ina lallabaki naje nayi hoton me ya hana kizo ayi dake?
Ko Zaki hanani ne?
Sadeeq zai Kara magana ya nuna Shi da yatsa a hostel zamu hadu zanga ubanda ya tsaya maka kaima......duk suka zaro ido lallai fa da gaske yake. Sannan ya kalleta kada Allah yasa kiso ke Kika rasa........ Ya wuce fuuuuu ya fada wani class ya zauna Rai bace kamar zaiyi hauka idanun sa sunyi jawur.
Bilkisu ta rasa inda zata Sanya kanta, kuka zatayi ihu zatayi, itama nata idanun sukayi ja tare da kawo ruwa kamar zatayi kuka abin yazo kaina?
Hakan take ta nanatawa cikin zuciya.
Sadeeq ya kalleta hankali tashi, wallahi fada zamuyi dashi tunda Kika ji ya rantse....... Ta zaro ido fada?
Hmmmmm Baki San halin Anwar ba..... Sai akwai tabar Shi nan ta wuce class din da taga ya shiga....
Yana zaune ya hade Kai da table. Ta zauna kujerar gabansa, ta Kira sunan sa,
Anwar!..
Ya dago da sauri sai da gabanta ya Fadi ganin yanayinsa.
Ta daure ta Kura mishi ido zuciyarta kamar zata fito amma ta daure kada tayi sanadin raba abokai . Ta Fara magana a hankali.....
Ba ruwan sadeeq cikin maganar nan, kada laifina ya shafeshi duk abinda zakayi mishi kayi mun Amma kada ka Sanya Shi ciki kayi hakuri ka kyaleshi .......bazanyi hakurin ba. Ya fada kamar zai mareta.
Duk ajin akayi shiru ana kallonsu,
Ya daga murya, ke har Zaki ce na Bata lokaci Baki so na koya miki? Ni idan naje wurin malamai su koya mun korata sukeyi wani lokacin sai na kwashe fiye da awa daya sannan suce in tafi in Basu wuri, bana zuciya gobe sai na koma sai ke daga Yan mintoci Zaki nemi kiyi mun wulakanci cikin jama'a?...... Naji kayi hakuri,......
Bazanyi ba nace ki tashi ki bani wuri.....gabanta ya Fadi.
Ta daure ta hadiye kwallan dake son taruwa a idonta tace sadeeq nake nufi kayi....... Bazanyi hakurin ba ya Mike, idan ke bazaki tashi ba ni na tafi.....kawai yabarta wurin.
Na shiga uku ni Bilkisu ta fada.
Tashi tayi tabar class din don kwallar sun kasa tsaiduwa.
Ni Anwar zaiyi ma wannan wulakancin? Ni Anwar zai dizga?
Ni Anwar zaiyi ma gorin karatu?
Me yasa tun farko na bashi fuska?
Idan sai Anwar ya koya mun karatu zanci jarabawa billahil azim na hakura da degree har abada. Biji biji take ganin hanya....ba abinda kanta keyi sai sarawa, kaicho na ni Bilkisu na kyale Anwar har abada tallahi ko kallonsa bazan karayi ba.....ta bude daki ta fada bisa katifa sai kuka.........
Hankalin sa yafi nata tashi, kamar mahaukaci ya Isa daki Anas ne kwance ya fada bisa katifa Anas na shiga uku nayiwa Bilkisu wulakanci.
Ya zaro ido me ya faru.?
Yarinyar nan kureni tayi yau, na rasa ta inda Zan bullo mata.....naji me ya faru.
Ya Mike kamar mahaukaci.......laifinta ne nasan gobe zata Kara bani hakuri. Zamu shirya .....ya fice dakin.
Duk duniya Yanzu Babu Wanda takejin tsanar say ranta irin Anwar ko sunan sa Bata so a fada ta fita batunsa Amma kullum cikin kuka take.
Kwananta biyu daki kwance ta kasa zuwa lecture saboda Bata kaunar Kara ganin sa.
Shi Kuma jira kawai yakeyi tazo ta Kara bashi hakuri su dai dai gashi Yana ganin ya zubda ma kanshi class matukar ya kirata a waya, abinda bai sani ba har ta goge no. Sa cikin wayarta.
Abu kamar wasa kusan sati Bata zo school ba, sai dai kullum tabi dakuna ta karbi note tayi.
Ranar laraba ta Kama kwananta tara rabonta da school Shima tazo ne dole saboda za'ayi C.A Kuma course din da tafi tsoro.
Dadi ya kamashi yasan dole yau ta nemeshi.
Yana zaune Yana koya masu Helen ta shigo gabansa ya Fadi ganin irin ramar da tayi though Shima ya Dan fada.
Layin da yake Bata kalla ba ta Isa can baya, Damian please help me here ta fada a hankali..... Ashe bai iya uwar komai ba nan da Nan hankalin Anwar ya tashi ganin ana koya Mata wrong.
Helen ta zungureshi ga fa Bilkisu..... Eh na ganta, tana fushi dani ne Kinga taje Damian na koya Mata hauka. Mtsew ya buga tsoki.
Ya kasa ci gaba da koya ma Helen din.
Damian na gamawa tabar class din sai lokacin test ta dawo.
Tana shigowa ta hango sadeeq ta Isa wurin Shi....... Alhamdulillah dama Ina ta addu'ar kada a riga ni.
Yayi murmushi kawai, tare suka zauna ya Bata ta kwashe hankalin Anwar na kansu kamar zai haukace.
Tana gamawa taje tayi submitting tayi tafiyarta daki Koda Anwar din ya fito bai ganta ba ya Kara hasala....... Sadeeq na fitowa ya Fara surma mishi Zaki har Yana yunkurin dukansa Wai ya zauna tare da Bilkisu test.......🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Tirkashi.
Ayi hakuri da kadan...✍🏼. Zainab wowo ce💖😄
Juma@ mubarak don't forget to receive suratul kahfi👏🏼
🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣0⃣
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
************
*KADUNA RIGASA*
Tun daga bakin gate yake jiyo kamshi, mamaki ya cika Shi, shin ko yayi batan lissafi ne gidan Amira yake ba Ummi ba?
Tana tsaye cikin Riga da skirt na leshi tasha ado ya shigo.
Da gudu ta rungumeshi yaji wani tsammmmmmm...... Anya Ummi ce?
Nan danan ta Fara sabon salo. Shigowa yayi kawai ya ajiye jaka ya wuce wurin Amira sannan ya dawo Amma inaaaa tuni hankalin ya karkata........ Bayan yayi wanka, ta zauna tana bashi abinci kamar yaron goye tun a daki da ya motsa sai ta bashi hakuri yanzun ma tana bashi abincin tana Kara lallashi duk ya sukukunce ya rikice.
Ya kalleta wallahi Ummi Ina sonki, kawai halayenki ne suka Sanya mun ko kwanto a zuciya Shi.......ta rufe bakin da chokaci ta debo peppé soup, sorry my love zaka ga changi I promise...... Ai na ga changi wallahi please keep it up.......
Amira Bata Sanya Shi ido ba sai bayan isha'i ta gama kulewa ta Kai karshe.........
**************
*Federal University dutsinma*
Kowa yasan sadeeq baida fitina, murmushi kawai yayi yabarshi a wurin yana babatu.
Sai kawai ya Fara fushi dashi.
Cikin bacin rai sadeeq ya samu Anas, Yana fada mishi abinda Anwar din yayi mishi Kashi na biyu akan Bilkisu.
Yaja guntun tsaki, kayi hakuri sadeeq wallahi *So* ke wahalar dasu duka for now ka bashi time zai nemeka.
Tun daga ranar Bilkisu ta koma sadeeq ke nuna mata, sun kyale Anwar.
Hankalin Anwar yayi matukar tashi ga exams na karatowa, hanya ma idan ta hango shi canzawa takeyi.
Ya rasa inda zai saka ransa.
Ko kallo bai isheta ba. Idan ta zo school amma tana komawa daki zata ci kukan ta tayi ma'ishi.
Yanzu fa kowa ya fahimci an bata Bilkisu da Anwar. Tsalle da Murna mufeeda ta ringa yi.
Tana zaune class za'a yi lecture ya shigo.
Yana ganin ta yayi saurin shiga sit din zai zauna kusa da ita...... Sai da ya karaso gaf! Daman can karshe take sai kawai ta kwashi kayanta ta dora waya a kunne , helllooo....yes inajinki.
Tayi waje kamar me amsa wayar gaske.
Tana fita tayi jimmm sannan ta dawo tare da canza layi ma gaba daya.
Ransa ya baci, hankalin sa ya Kara tashi, kowa ya fahimci abinda tayi.
Sam ta rage fara'a in kaga tana dariya to tare take da Suleiman.
Ana gama lecture ya tsaya bakin kofa yasa hannu duk Wanda zai fita sai ya mishi magana, tana ganin haka ta yi zamanta, Shima ya ayyana a ransa wallahi yau Kam sai dai su kwana haka.
Masu shigowa da masu fita kowa sai ya mishi magana sannan.
Ta dawo gaban sit suna magana da chinyere, tayi sa'a ya juya suna magana da wani dan aji daya da alama bayani yakeyi mishi har ya manta ya saki hannu Yana magana cikin nuni da hannu....tayi wuf, ta wuce ko alama bai lura ba sai da tayi nisa ya waiga class din da sauri ya tabbatar lallai ita ce.........wani mugun tsoki yaja tare da dunkule hannu ya daki bango har yaron ya tsorata.
Cikin tsawa yace yaron ya bace mishi da gani.....
Daki ya tarar da sadeeq nacin abinci. Yasa chokali kawai Shima, ya kalleshi malam zaka Sanya mun Rani.....dama jira yakeyi yayi magana ko sa shirya.
Anje an Sanya.
Ya Galla mishi harara kawai.
Anwar din ya rike kunnuwa biyu am sorry my friend pls sorry.
Murmushi sadeeq din yayi kawai.
Ya Fara magiya, har Anas ya shigo yasa baki.
Nan da nan aka koma normal.
Ya kallesu kamar zaiyi kuka. Dan Allah ku shiryani da Bilkisu yarinyar nan tayi fushi dani sosai.
Wallahi nayi tunanin bayan kwana biyu zata bani hakuri shikenan komai ya wuce ashe ita zafin nata yafi nawa......
Anas ya harareshi, kunfi kusa, a da idan kunyi fadan ku waye ke shirya ki?
Wallahi tsoronta nake yanzu, bana iya tunkarar ta ku taimaka ku shirya mu....
Zamu jaraba gobe....inji sadeeq.
Duk an Fara covering ana shirye shiryen tafiya sallah break ( babbar sallah ), da andawo Kuma da sati za'a Fara exam.
Tana zaune can baya sadeeq ya sameta.
Bayan sun gama gaisawa ya kalleta.
Bilkisu ya kamata ku shirya keda Anwar fadan ya Isa hakanan Dan Allah Kinga....... Mikewa tayi tsaye, tace, sadeeq Ina ganin kimarka da mutunci wallahi duk ranar da ka Kara mun maganar Anwar kaima Zan daina magana dakai har nabar makarantar Nan.........ta kwashi books dinta lecture din da bata dauka ba kenan ranar.
Gaban Anwar sai faduwa yakeyi...... Tana fita ya koma inda ta tashi... Yaya?
Sadeeq din ya bata rai tare da fada mishi abinda tace, sai kawai ya dora Kai bisa table yayi shiruuuu!
Ya dan sunkuya da Kai Anwar idan kana son yarinyar nan ka sameta ku daidaita........mtseww Shima ya figi takardu yayi waje....ya bishi da ido yace ikon Allah!
Anas ya taso Yana dariya...... sadeeq ma ya kyalkyace da dariya suka tafa.
Ni naga karshen wannan girman Kan nasu, ko wane ta ciki na ciki sai wahalar da juna ake....
Laifin Anwar ne kasan Allah sadeeq maganinsa Bilkisu.
Bashi da aiki sai dai ya dauko waya yayi ma sunan ta zuruu Yana kallo. Text din da ta mishi na birthday ya Zama tamkar paracetamol ga Mai ciwon Kai.
Kwance yake ruf da ciki suka iso, Anas ya tabo Shi ...abokina barci kakeyi?
Ya tashi firgigi yace no, Ina jinku kawai na kwanta ne na huta Yaya?
Ya Mika mishi littafi exercise question din nan zaka solver Mana please...... Wallahi tallahi bazan kara koya ma kowa ba school din nan inbaku shiryani da Bilkisu ba.....hada rantsuwa sadeeq ya zaro ido.
Kana wasa ko?
Ya Kara Bata rai try me and see. Ya koma ya kife a katifa.
Nan da nan suka shiga damuwa, Anas ya kalli sadeeq lallai abun nan ya girmama.
Sadeeq ya nisaaa, kagane kamata yayi mu Sami Suleiman da Helen muje mu Kara bata hakuri kasan Dan iskan yaron nan fa zai Kira Mana ruwa mu shiga uku.
Yana zaune ya ajiye littafi alamar ita ya ajiyewa sit sakamakon ita ce lecture karshe kowa yayi covering shine yayi saura.
Suka Mika mishi hannuwa ya bisu da ido Yana mamaki saboda yasan clique din su basu daukeshi bakin komai ba har gara gara sadeeq suna gaisawa jefi jefi idan Yana tare da Bilkisu.
Suleiman wannan zuwan naka ne,
Toh, gani lafiya dai ko?
Da sauki gaskiya, akan Anwar ne da Bilkisu ya rantse cewa duk semester din Nan ba Wanda zai karu dashi matukar ba'a shirya su da ita ba Kuma wallahi ni dana Mata magana cewa tayi na Kara Nima zata daina mun magana.
Murmushi kawai yayi.
Anas yayi karaf! Yace, shine muka yanke shawara mu sameka Dan Allah kasa Baki muje mu Bata hakuri.
Ya Kara murmushi okay ba damuwa.
Har aka tashi class bata zo ba,kawai suka yanke shawarar zuwa gida su sameta .
Aisha ta Fara haduwa dasu ta fito da alama garin zata bari take shaida masu ai tun karfe bakwai Bilkisun ta tafi Kano zata hau jirgi ta tafi Abuja..........
Kofin dake hannun Anwar ya Fadi ji kake tartsatsatsa...... Lokacin da Anas ke Mata bayani.
Ya kallesu asanyaye... shikenan tunda ta tafi.
Washe gari Shima suka tafi.
Abinda yafi komai bata mishi rai shine bata chatting, ya Kira duk wadanda suke tare ko tana da wani layin na daban Amma sunce layinta daya ne kwal!
Ba abinda ta boye ma mommy hada kukanta.
Yar dariya kawai tayi tace zaku shirya karatu ya gaji haka.......zumburar baki tayi kawai ta wuce ciki.
Shima ya kasa sukuni, ya gama ayyana ma ransa dole ya kirata ranar sallah ya Mata Barka da sallah tunda ranar kowa na cikin farinciki yasan dole ta saurareshi Kuma ta sauko.
Hakan kuwa akayi, misalin Sha daya na safe taci kwalliya tana tsaye kitchen tana zuba gasassar hanta a plate Kiran ya shigo.....
*Anwar* shine abinda true caller ta nuna Mata, kamar zata ki dauka sai Kuma ta tuna gara ta dauka ya gane cewar ko number sa bata dashi ........
Assalamu alaikum. Ta fada a hankali.......luuuuu ya tafi tare da lumshe ido kafin yace wa'alaiki Salam *Barka da sallah*....... Wake magana?
Ta bukata a dake,
Ya zaro ido kamar tana kallonsa.... Bilkisu kin goge number ta?
Tayi shiru kwalla sun taru idonta....
Kinji? Na ce kin goge number ta awayarki?
Kwallah suka shatato Mata tayi tsoki kawai ta kashe wayar......yace what???
Ya Kara Kira.
Tana kallo taki dauka sai da yayi missed call biyar amma Bata dauka ba.
Ya dankara wayar a kasa ta tarwatse sannan ya dafe Kai saboda juya mishi da yakeyi.
Ita kuwa sadadawa tayi zuwa dakinta taci kuka Mai isar ta tukun sai bayan azahar ta fito Shima fa'iza ce ta kirawo ta su fito zasu tafi millennium Park duka gidan.
Tambayar duniya gida Anyi ma Anwar cewar meke damunsa amma yace ba komai fargabar jarabawa ce .
Sati daya ya koma school ita kuwa sai ana gobe jarabawa sannan.
Don haka basu hadu ba sai dakin jarabawa, ya hangota can gaba, tun kafin su shiga sadeeq ya fada ma Suleiman ya tsaidata ko ta gama don su ganta.
Sai gashi ma duk sun rigata fitowa har Anwar din.
Ya tafi can nesa bakin bedi ya tsaya su Kuma suna gaban class suna jiranta.
Suleiman man ya Fara tarar ta sannan sauran suka matso aka Mata zobe .
Ya kalli kowa, sannan ya kalleta wannan zuwan naki ne fa, Dan Allah kiyi hakuri ku shirya da Anwar haka nan kinji yace matukar ba'a shirya ku ba ya gama koya ma kowa karatu........and then?
Sai su dage su koya da kansu Shima ba da iyawa aka haifeshi ba, Suleiman ka fita maganar Nan ba huruminka bane.......ta juya tayi tafiyar ta.
Anas ya zaro ido.... Suleiman ya kallesu Yana murmushi ku Kyaleta Zan lallabeta zasu shirya...... please try your best Dan Allah sadeeq ya fada tana wucewa Anwar ya karaso. Yaya?
Anas ya dankara mishi harara yayi gaba kawai.
Hankalin sa ya Kara tashi jin ba wata nasara. Amma Suleiman din ya masu alkawarin zai shawo kanta.Hankalin kowa a tashe yake cikin department ganin da gaske Anwar yake bazai koya ma kowa ba matukar bai shirya da Bilkisu ba.
Ya daina ma kowa dariya tun su sadeeq na daukar abin wasa har suka ga lallai da gasken gaske yake fa.
Ba Wanda ke iya tunkarar sa, idanun sa cikin facing cap yake shigowa Yana rubuta jarabawar za a nemeshi a rasa.
Courses din ana Shan wahalar su, Bilkisu kuwa tuni ta sadakas, idan tana ta exam 3 tun 7 take shiga library sallah kawai ke fiddo ta. A cewar ta in kaji maraya raggo.
Bai taba tunanin Bilkisu zatayi wannan zuciyar ba Yana tunanin yanda ta Saba da tutorial din sa bazata taba karatu babu Shi ba.
Sun Sami interval na kwana daya, da marece tana class tana karatu Suleiman yazo.
Suka Fara karatun tare...... Wani wuri ya Dan kakare masu.
Yayi murmushi Kinga da kin huce da duk wannan wahalar bamu Sha ta gashi kinja ma kowa, Anwar...... Suleiman ka kasa ganewa na fada maka wallahi ko sunan Anwar bana son inji an fada.....
Saboda me?
Ni bakiyi mun adalci ba wallahi sai nake ganin kamar bani da kima ko mutunci a idon ki, tunda ya Baki hakuri Nima na Baki sai ki......yaushe ya bani hakuri? Wallahi bai bani hakuri ba.
Mutane nawa ya Aiko Miki?
To ai mutane kace Shi in person baizo ba ta Yaya Zan San cewar ya gane kuskuren sa?
...... Yanzu idan yazo da kansa ya Baki hakuri Zaki hakura ku koma normal?......
Tayi shiruuuuu.... Me yasa Suleiman zai Sanya ta kwana.
Kinji? Dan Allah Ina son Anwar yaci albarkaci na ki yi hakuri Kinga Yanzu idan ya dauke hannunsa ga kowa tabbas an Sami matsala Kuma kece sila...... Ni?
Yayi murmushi, kiyi hakuri Bilkisu Yanzu dai, Dan Allah kiyi hakuri.
Ya Gama daureta ta ko'ina, tafi mintuna hudu bata ce komai ba.
Ya Kara kallon ta, Ni zakiyi ma wannan alfarmar ba kowa ba kiyi hakuri.
Kwalla suka suka zuba Mata...... Ta mayar dasu da karfin tsiya sannan ta ce shikenan ya wuce...... Ya zaburo, kin hakura?
Eh, amma ka sani saboda Kai...... Na sani wallahi. Na sani Bilkisu na gode na gode words cannot express my gratitude.
Suka jero tare ya rakata har bakin gida sannan ya tafi.
Hostel yayi ma tsinke, kamar daga sama suka ganshi karon farko da