Showing 48001 words to 51000 words out of 76784 words

Chapter 17 - WA ZAI FURTA COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2024

15149

shiru.
Fiddo ki ban ya fada tare da kokawa ya kife..... Bata San lokacin da tayi dariya ba ta Mike tare da saka hannu ta janyo ledar sai gogar jikinsa takeyi yaki Kuma gyarawa.
Ta fiddo hollandia biyu milk and strawberry, tashi gashi ta fada tare da fiddo wata leda, katuwar gasassar kaza ce taji cabbage da kayan miya nade a foil paper.
Ta bude ikon Allah dadi za'aci Alhaji Anwar..... Ya dago Yana Yar dariya keni wallahi tuwo nake son ci miyar kuka..... Ta kalleshi ka iya tukawa ko?.
Yayi murmushi Allah da gaske nake Ina son cin tuwo Bilkisu ya langabe Kai.
To ka je ka siyo Mana.
Ke zakiyi mun. Zan siyo semo kiyi mun anjima...... Kam wallahi kada kasa ma ranka abinda bazaka samu ba. Zan samu yau sai naci tuwo Kuma ke zakiyi mun.
Ya bude kazar ya cire wurin cinya ya Fara ci.
Tayi shiru kawai.
Wane kike so milk din ko strawberry?
Kai wane zaka sha?
Bani da choice as long as nidai cikina zai cika..... Ta yi dariya kawai ta dauko milk din ta Fara Sha a hankali.
Zakici kazar ko kunya kike ji?
Ta Kara Yar dariya, na ci abinci na koshi.
Me Kika ci?
Taliya muka dafa.
Zaki mun tuwon?
Zan maka Amma ka Bari sai gobe yau dai marece yayi sosai.
In siyo semo din?
Ina dashi Kar ka damu.
Good.
Ba za kici ba da gaske?
Allah na koshi....... Zan baking baki matukar Baki sa hannu kinci ba..... Rage mun idan naje daki zanci da dare.
Mtsew, Allah ya raba ki da gardama.
Yaci gaba da cin abinsa.
Mamaki kawai takeyi Wai me yasa maza Basu da kunya ?
Kamar ya karanci zuciyar ta ya kalleta...... Ni banjin kunyar ki.
Ta danyi dariya ....yabi kuncinta da kallo....
Kin San cewa kina da kyau kuwa?....... Ta kalleshi da kyau me kace?
Yayi murmushi kina son in maimaita abinda Kika Riga kinji?
Hmm, tace.
Samarin ki nawa?
Zaka Fara ko?
Ana zaman lafiya ka Fara tamabayoyi marassa amfani kuma azo ayi fada ko?
Ba Kya so na sani ne?
Ina ruwanka da samari na an fada maka irin ka ce da kowace jik and jak ...... Ya sa hannu ya buge Mata Baki...... Kai Kai Kai ta rike Baki.... Sai tayi kwal kwal zatayi kuka.
Ya harareta wallahi yau kikayi mun kuka Zan baki mamaki ke baki da aiki sai shagwaba.?
Gaskiya bana son abinda kakeyi mun Anwar..... Gaskiya bana son abinda kake yi mun Anwar ya maimaita Yana kwaikwayonta.
Karfe nawa Zan zo na karbi tuwo gobe.... Zan Aiko maka Dan Allah ba sai kazo ba ko ka turo sadeeq ya karba.... Wani kallo ya jefe ta dashi kafin yace *why are you pushing me away?*
Ba haka bane...... Haka ne.
Bazan zo ba, ki Aiko mun ya Miki ko?
Tayi murmushi eh,
Duk ya kware tsokokin kazar ya tura Mata kasusuwa ga naki..... Ta danyi dariya wallahi kana da ci Anwar...... Ya yunkura zai Kara buge bakin ta tayi baya tana dariya.
Tashi muje kada six tayi na gaji tunda ka gama.
Ki shanye tukun.
Tabbb bazan ya ba.
Shi yasa ba Kya kiba.
Hmm, kawai tace.
Wayarsa tayi Kara Yana dubawa ya Mike please Ina zuwa...... Ta mishi wani kallo ya nuna Mata fuskar wayar Alhaji Abbas ne kin gani?... Ya fice Yana dariya kunya ta Dan Kama ta ganin zai fassara ta.
Ya Dan dade kafin ya dawo tana ta latsa waya taji yayi fit da ita.......
Bani naga suwaye samarinki.......Aka Kara kiransa a waya.
Ya kalla sai kawai yayi tsoki, sai ka bar nan ka kirata ne?...... Sai bani kawai yayi picking yasa handsfree.....
Ya akayi?
Haka ma zaka ce?
Baki bani amsa ba nace ya akayi ne?
Jiya an Kai maka abinci ka dawo dashi, tun jiyan nake kiranka kaki dauka Wai me yasa..... Nace kiyi mun abinci?
Sai kace sannan zaka ci?
Ke idan Baki da abin fada Ina da abinyi ya kashe wayar.
Ya kalleta kin yarda Yanzu ita ce ke damuna bani nake binta ba?.
Kai ji Ni me nace toh?
Sai kince? Rigimar ki ai nasan ta.
Wannan semester din na ganki da wani Kato wallahi sai naci ...... Maganar ta makale ta zaro ido ya Mike da sauri tashi muje na rakaki.
Ka karasa abinda kake son fada?
Yayi murmushi kawai,
Ya daure fuska ta mike ka Isa ka hanani gaisawa da mutanen arziki na?
A matsayin a na wa to da zaka Sanya mun irin wannan dokar?
Ke ya Isa tunda nayi shiru kuma Dan Allah ki kyaleni.
Suka jera suna tafiya.
Suna karyo wata kwana su mufeeda na tahowa ta tsaya gaban sa kutumar uba Wai kana cikin school din Nan............???????✍🏼

*Zainab wowo* 💖💖

Zan kawo muku wani true life story anjima Dan Allah Ina bukatar comments din ku please. Na gode masoyana Ina kaunarku🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐
1⃣7⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

***************
*KADUNA RIGASA*
Duk ina son ganin ku falona da karfe takwas...
Ya tura ma kowace sako.
Duk sun you zugum suna mamakin wannan Kira , abinda bai taba ba.
Ya rage karar TV.
Agurguje ba lokaci maganar zata dauka ba, da farko Ina godiya da Jin dadin yanda ko wace ke kokarin faranta mun da Kuma dagewa wurin kyautatawa, hakika naga canji a gidan Nan. Allah ya saka ma ko wace da mafificin alkhairi.
Magana ta karshe doka ce Zan saka na neman shawara ko neman izini ba.
Daga yau na Hana ko wace ziyarar dakina matukar ba ita ce da girki ba. Sannan daga yau kada wacce ta Kara bina ko ta shiga sashen dayar ku matukar Ina ciki.
Wannan shine.
Ummi kina iya tashi ki tafi sai da safe...... Ya Mike yayi ciki.

***************
*Federal University dutsinma*

Gaban Bilkisu ya fadi ita Kam ta tsani fitina a rayuwar ta, tayi kasa da Kai tare da wucewa a hankali..... Ya chafko hannunta ya rike gammm, ba Bilkisu da mufeedar ba duk wadanda ke wurin sai da suka fiddo idanu waje.
Yasha mur ya Kara janyo facing cap dinsa ya rufe idanun sa Yana kallon kowa kasa kasa sannan ya maida kallon sa ga Bilkisu Yana janyota baya a hankali Yana fadin ```yaya Zaki tafi ki barni bayan kin San...``` Amma Anwar ka maida mayar dani Yar iska. Au daman saboda wannan sillan Karan kake Mana yawo da hankali....tabbas yau na gane ma ido na.....
Sake mun hannu Bilkisu ta fada tana doka mishi harara, yayi kamar baiji ta ba.
Ya kalli mufeeda kin gama mu tafi?...... Na gama ai daman ban tsayar da Kai ba ko?
Ta fada tana huci.... Ya ja hannun Bilkisu suka wuce..... Kwallah suka zubo Mata sharrrrrr ta fizge hannun ta da karfi yayi saurin kallonta cikin hula Yana Mai daga kansa sama..... Kuka again?
Ya fada Yana kallonta.
Ni zaka zubda wa mutunci a gaban bainar jama'a? Ana ganina da kima da mutunci.....ke! Wai me nayi?
Hannu na da ka rike ni muharramarka ce? Ta zaro mishi ido. Yayi murmushi Bilkisu rigima, na lura duk duniya ba abinda Kika fi so da kauna irin na taba ki saboda na fada Miki cewar matukar Ina tare dake ban sallameki ba Kika nemi Bari na ki tafi wallahi ko a gaban waye Zan Kama ki, me yasa ke baki ganewa kiyi mun biyayya?......
Bazanyi biyayyar ba, na ce bazanyi biyayyar ba.... Ta nuna Shi da yatsa jira kaji Anwar na lura da take taken ka kana son mayar dani irin su mufeeda da ke binka suna maka biyayya kana musu yanda kaga dama ko?
Saurara da kyau, bana tsoron ka , bana shakkar ka na gaji da wannan dokokina naka marassa Kan gado.
Ka tafi kaje mufeeda is ready for that not me.....ta hada hannuwa alamar tana rokonsa abeg leave me alone.... Ya rungume hannuwa duka a kirji ya tsareta da ido kawai Yana kallo.
Ta mishi kallon up and down ta wuce tabarshi a tsaye.
Yabita da ido har ya daina ganinta...
Yayi shiruuu, me yasa bazan kyale yarinyar can ba?
Anya Bilkisu ta damu dani kamar yanda nake jinta azuciya?
Me yasa ta fita daban cikin matan jami'ar nan take bani wahala ta kasa gane irin qimar da nake da ita.?
Wai ko wannan haukan da Yan Mata keyi a kaina me yasa ita bazata ringa mun yanda nake so ba don su fahimci tafisu?
Mtsewww yaja dogon tsoki, sannan ya fiddo waya ya kira sadeeq, *zo ka daukeni*
Yanayin muryar sa kawai yaji yasan an Kara kwafsawa .
Kicin kicin ya iskeshi bakin gate ya hau mashin din kawai suka tafi.
Yana zuwa daki ya fada bisa gado yayi ruf da ciki....

A bakin kofa ta hadu da Aisha ta bita da kallo kafin ta rufa Mata baya suka nufi dakin Aishar........ Yau ma kuka?
Kuka Zaki ringa mishi lallai kina da aiki...... Aisha bana son abinda Anwar kemun kawai a gaban su mufeeda ya rikon hannu Kuma ya rikeni yaki saki saboda Allah me zasu daukeni?
Ke yau ai na shiga uku Kinga kallon da kawayenta ke mun da ita kanta....... Ai dole. Kut! Wallahi dole su kalleki, Al'amarin Anwar ya Fara ta'azzara gaskiya Kuma Shi yaki fitowa ya Fadi ainahin abinda ke ransa ...... Yana jiran ni na bishi irin su mufeeda haka na lura amma wallahi ki barshi idan yasan wata bai San wata ba.
Ta wuce dakin ta don ta gabatar da alwalar magriba.
Ta kashe wayarta kada ma ya kirata,
Washe gari tara suke da lecture, akayi sa'a malamin ya zo. Ya bayar da first assignment cikin part of outline din da zasuyi semester din, Anwar na baya can karshe idanun sa na Kan Bilkisu dake tsakiya ita da su Joseph, lokacin da ya fita ne ta karbi littafin Joseph din tana rubuta inda aka wuce ta. Tana gamawa ta mike Anwar ya kwada Mata Kira.....
Bilkisu.... Ta waiga da sauri saboda yanayin yanda ya daga murya duk ya janyo hankalin wadanda Basu Kai ga fita ba.
Zo ki zauna anan ya nuna Mata kujerar dake gefensa ..... Kowa ya tsareta da ido Yana jiran response dinta,
Me Zan maka? Ta fada tare da tsuke fuska.
Kawo mun note dinki zanyi using ...... Bai rufe baki ba ta jefa mishi littafin har ya daki fuskar sa, gashi nan idan ka gama gobe Zan karba Ina sauri ta yi hanyar waje.....da gudu ya fito har ya ba wasu tsoro.
Ita kanta sai da gabanta ya Fadi lokacin da ta wurga mishi book din saboda tasan cewa ta debo ma kanta wutar dafa kanta.
Ta yi sauri ta tsaya tare da rike kugu....... Ni Kika jefa?
Ya fada Yana zaro ido.
Ta mishi kallon up and down kafin tace idan kaji haushi ka maido mun littafi na Mana.... Jeki dauka bana so ya fada Rai bace .
Fine , ta fada tare da wuce Shi ta koma class din.
Duk aka kawar da fuska ganin ya biyo bayanta, samm bata lura ba Bata Kuma ji takunsa ba.
Littafin ya fada can karkashin desk ta kutsa can ciki ta Kuma duka tana kokarin dauko Shi, ya shigo sit din ya zauna, ita kuma tana ciki.
Dagowar da zatayi taji ta fada bisa kafar mutum ta mike da sauri innalillahi.... Wai kanka daya Anwar??? Ta daka mishi tsawa.
Idan baki so na Miki abinda Kika tsana ki zauna silently muyi magana wallahi idan Kika kuskura anan zan Miki abinda...... Bazan zauna ba bani wuri in wuce.
Naki na bayar ko Zaki daukeni da tsiya ki fitar? Me yasa kike da gardama Bilkisu???
Kai Kuma me yasa baka da zuciya?.
Yayi murmushi nima Ina neman amsar nan wallahi..... Ta ja tsoki kanka akeji bani wuri.
Ya kalleta alamar ba wasa yayi baya da hular sa , kin san Allah idan Baki zauna ba Zan daura ki a bisa cinyata ki zauna in kuma rikeki har sai na gama maganar da zanyi ko bazan iya ba?
Tayi shiruuuuu, sai Kuma ta zauna saboda tasan karamin aikin sa ne sai dai idan ya aiwatar daga baya ya bada hakuri.
Ya bita da ido Yana murmushi..... Ta Kara tsuke fuska Ina sauraron ka ba ka tsareni da ido ba......
Me yasa Kika tafi Kika barni jiya?
Saboda ka gane baka gabana bana son wannan shisshigin, Kuma na Kara fahimtar fakai bana son kana taba ni na tsani hakan .
Kin tabbatar bana gabanki?
Ta kalleshi shekeke Zan ma karya ne don Ina tsoronka ko kana nufin...... Ina nufin mufeeda ce ta Kara Bata Miki Rai ko?
Mufeeda? Mtseww a'a ka manta.
Idan ba ita bace me yasa Kika hasala sosai Kika tafi Kika barni?
Saboda ka rike ni na kuma fada maka bana so..... Me yasa ke bazaki daina abinda nima bana so ba?
Ajiyeni kayi? Ko kana iko dani da zaka Sanya mun doka kace kuma dole sai na bi?
Kiyi hakuri, ya fada a hankali.
Tayi sokoko ta kasa ci gaba da masifar.
Ya tsareta da ido, Dan Allah kiyi hakuri naji nayi kuskure bazan Kara ba I'm sorry please.
Tayi shiru,
Bana son fadan nan wallahi, bana son kina wannan tada jijiyoyin kina fushi dani bana so ko kadan please kiyi hakuri shikenan ko?.... Ba shikenan ba, sai ka mun alkawarin bazaka Kuma taba ni ba sannan.
Yayi shiruuuu, gaskiya ban yi alkawari ba amma Zan kiyaye.
Ya wuce ko?
Eh, ta fada a hankali.
Mun shirya?
Ta dan harareshi.
Yayi Yar dariya. Mun shirya ko?
Um, ta ce tana murmushi.
Hmmm, Bilkisu kenan kina yarda Kika ga dama.
Karfe nawa Zaki kawon tuwo?
5, ta ce .
Lokacin na gama mutuwa da yunwa ko?
Ba abinci dare zakaci ba?
Waya fada Miki?
Shi zanci a matsayin lunch..... Tuwon???
Yayi Yar dariya yes!
Hmmm,
Zaki kawon irin two din nan?
I'll try. Ta fada a hankali.
Waye Zaki Aiko ko nine Zan turo?
Zan kiraka idan na gama dai.
Ya Mike tashi muje.
Ga book din ta Mika mishi .
Yayi Yar dariya daman ke nake bukata ba Shi ba...... Ta zaro ido what?
Ya Kara yin dariya ya ce Ina nufin ke nake so kizo inyi magana dake ba littafin ne a gaba na ba.
Tace hmmmm.
Suka jera suna tafiya..... Tana tsallaka titi sadeeq ya karaso suka wuce.
Ta zagaya can baya wurin Mai nama ta siyo tsoka Mai kyau ta Shani kilo daya.
Tana shiga ta cire hijab ta Fara hada Miya...( Duk kudi irin nasu Bilkisu baisa anyi sake da koya Mata girki ba ) har catering school tayi ga karance karance da tambaye tambaye saboda girki na daya daga cikin abinda take so a rayuwarta.
Ta shirya miyar kuka Mai Rai da lafiya, naman yayi ruguf a ciki wurin Aisha ta Samo kukar da daudawa saboda bata dasu Kuma Bata Kai ga ta siya ba, anan daman take siye.
Duk wacce taji kamshin sai ta leko. Tana gamawa ta daura tuwon bai wani dauki lokaci ba, karfe daya da kwata ta kullashi a leda, ta janyo sabbin coolers manya cikin kwali Wanda batayi amfani dasu ba daya kawai take amfani da ita karamar tana zuba Miya.
Ta jera tuwon guda Sha biyar aciki.
Ta zuba Miya ga Mai bi Mata duk naman ta kwashe musu kaf! Ta bi da manshanu saboda bata rabo dashi ita ma'abociyar taliyar hausa ce dahuwar daudawa Tasha manshanu.
Ta kwalala mishi ta rufe.
Ta jera a basket ta Sanya mishi gwangwanin biscuit biyu cikin wadanda ya siya Mata da lemuka kala kala, ta dauki basket din da 200 ta fita.
Napep ta tsaida tare da mishi kwatancen hostel..... Zan kirashi ya fito sai ya karba sunan sa Anwar..... Anwar? Ya zaro ido... Anwar din zai fito ya karba? Ta banka mishi harara ka San sa ne?
Ni kuwa na sanshi an bani abinci na Kai mishi kwanaki nafi awa banga kowa ba na Kira abokin sa da aka bani number sa Koda yaji zancen nawa ya kashe waya bai Kara..... Malam zaka Kai mun sakon Nan ko na nemi wani?
Zan Kai Hajiya Amma idan bai karba ba Ina Zan ganki saboda wadancan kayan har Yanzu suna gidan mu...... Kaga compound gashi can??? Ka ce Bilkisu kake nema ta ajiye mishi basket din ta bashi 200 ta juya kawai.... Ya kalleta a yamutse wahalallu.....
Ta kanga waya a kunne tana Kiran sa..... Barci yakeyi kasa rika Kuma yanajin dadin barcin.
A hankali wakar *Because you love me* ta Fara tashi ta cylindion.
Yayi firgigi saboda Bilkisu kadai keda ring tone din.....
Hello ya fada cikin muryar barci.
Ina hanya Zan kawo maka tuwon na kusa karasowa na sameka bakin gate din ku kada ka barni Ina jira......ta kashe wayar.
Idanun sa suka bude tangaran ya bi fuskar wayar da kallo..... Ya Mike zumbur ya zura jallabiya ya fice da silifas kafarsa.
Dai dai tsayuwar Mai napep din Yana hango napep yanufe ta da sauri Yana lekawa..... Kai ne Anwar?
Sai kawai yayi murmushi watau yarinyar nan dabara tayi mishi don ya fito?
Ya kalleshi eh, tare da Mika hannu ya karbi basket din.
Yasa hannu aljihun jallabiya ya fiddo 500 ya Mika mishi.... Ta biya yallabai.
Yayi Yar dariya to in mayar kenan baxaka Kara ba tunda na fiddo?..... Yayi charaf ya karbe Yana fadin wazai mayar da alheri?.
Na gode yaba napep wuta Shi Kuma ya nufi hostel Yana murmushi.
Ya bishi da kallo Yana jinjina Kai. Yanda suke fama da student wurin neman ragi da amsar chanji amma ga wani na kyautar 500, ita Kuma ta biya 200 zuwa kawai..... Wurin Nan akwai magana ya ce kafin ya chilla keken titi.
Sadeeq nata barci bai motsa ba. Yasa kafa ya Kai mishi harbi.... Tashi Dan ubanka Bilkisu ta Mana girki..... Zumbur ya Mike Yana kallon basket din.... Yayi dariya wallahi tuwon ne ta kawo .

Yunwa sukeji Daman, sadeeq ya Fara kwashe lemukan Yana ajiyewa kasa, sannan ya fiddo coolers din, kamshin manshanu ya buge dakin Anwar ya hadiye wani tsinkakken miyau ya gyara Zama .
Baiwar Allah hada biscuit ta debo da lemuka...... Tana so ta rage su ne sun Mata yasa Anwar ya katse Shi Yana murmushi.
Sun kwashi tuwon sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login