Showing 72001 words to 75000 words out of 76784 words

Chapter 25 - WA ZAI FURTA COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2024

15136

ko?
Me yasa har yau mufeeda ta kasa kyaleka, saboda me baka son ta daina kulaka????
Ya daga hannuwa sama na rantse da Allah Ina so ta kyaleni Bilkisu baki ganin irin wulakancin da nake ma yarinyar can Amma taki zuwa???..... Kuma shine ke nuna tafi karfinka?
..... Zaiyi magana malamin ya shigo.....
Ya dauko wayarsa ya rubuta Mata text a WhatsApp...
```kiyi hakuri please```
Ya Dan zunguro ta galla mishi harara ya Mata nuni da baki cewar ta duba Wayarta......
Ta tura mishi da harara....
Ya rubuta ``` please sorry I don't want to see you pissed off```
Taki magana.
Ya Kara rubuta Mata..
```You snubbed your husband?``` tare da imoji na zare ido.
Ta Kara tura mishi harara
``` sai ya tura Mata kuka```
Ta Dan kalleshi ya langwabar da Kai ya rubuta... ``` wallahi Zan yi maganin ta please am sorry```
Ta danyi shiru sai ta rubuta mishi ``` it's okay```
Yayi saurin tura Mata ``` Oya smile na```
Ta Dan kalleshi ya sakar Mata murmushi... Sai kawai ta duke tana Yar dariya.

Malamin na fita ya hawo table ya zauna gabanta Yana Yar dariya *Mun shirya ko?*
Ta danyi murmushi.
Sai ki koyan abinda akayi tunda kin Hana ni naji komai... Ta harare Shi Nima halan naji?
Ya kyalkyace da dariya gaskiya wannan semester din akwai damuwa Anya Zaki Bari na ringa ganewa?
Ta Kara mishi harara...
Kun shirya ko? Ni an kyaleni cikin Rana daga Biko ya kalli Anwar Dan ubanka ka Kara Sanya ni cikin shirginku sai naci ubanka..... Tayi kasa da Kai tana murmushi Shi Kuma ya Kama dariya.
Suleiman yazo zai wuce Anwar yayi saurin rikoshi ranka ya dade idan ba hello ai akwai daga hannu ko?
Ya danyi murmushi ya Mika mishi hannu ya kalli Bilkisu, Hajia Allah yasa Allkhairi... Amin Suleiman Dan Allah ara mana abinda akayi Yanzu idan ka rubuta..... Anwar yayi fit ya fizge littafin ni zaka ba Alhaji ba ita ba.
Yabar masu book din ya wuce Yana Yar dariya....
Anwar kenan, yau kuma Suleiman kakeyi wa magana????
Ya Dan Sosa Kai gayen Yana bani tausayi wallahi duk wulakancin da na mishi a masallaci idan muka fito wallahi sai ya bani hannu.... Ta ce hmmm.
Ya dan harareta ba hakan Yana nufin fa Zaki ringa kulashi ba fa..... Amma ai ma gaisa ko?
Eh, Amma idan kin saka nikaf, Wai yau me ya hana ki Sanya? Ya zaro ido......
Ta langabe Kai kamar zata mishi kuka Anwar Dan Allah ka saukaka mun da nikaf...... Wallahi sai kin saka ya dire Yana masifa...kammm idan Kika Kara fitowa babu nikaf wallahi sai kin koma Koda kuwa za ayi test ko exam..... Shikenan naji ta fada tana zumburo Baki.
Muje ki ajiyeni gida...
Wai Kai duk motocin da na gani gidanku fa.... Yayi murmushi kawai.
Ta haraeshi Wai Kai an fada ma har Yanzu ba'asan waye Kai ba?
Ya watsa hannuwa tare da daga kafada.... Ta danyi dariya tana son wannan move din....
Ungo kaja mu toh,
Yayi gaba abinsa bai ko kalleta ba.......
Ta bude suka shiga ta bata wuta.... Duk aka bisu da ido..... Ba karamin tafiya sukeyi da zukatan dalibai da malamai ba, ya kalleta Yana dariya waya koya Miki mota haka?
Ta mishi banza, ya kwantar da sit ya Dora kafa bisa dash board yayi filo da hannuwansa kinji kunya ta Hana mufeeda shigowa school?
Ta galla mishi harara sai kaje ka shigo da ita ai..... Ya runtse ido Yana dariya.
Taci gaba da hararar sa tana magana watau Kai hankalin ka na gunta kana bin kwaf kwaf.... Ke rufan asiri ya tashi da sauri wallahi da wasa nakeyi zolayace..... Hey nawaoooo....
Ta kawar da Kai kawai .
Ya canza maganar da cewa, me Zaki dafa mun yau?
Ta yi shiru.
Kinji?
Har abinci Zan maka?
Eh Mana, kiyi mun tuwo please kinzo da manshanu?
Ta ce um.
Amma anan zanzo inci kinji ko?
Ta kalleshi da sauri yayi Yar dariya ko ke Zaki kawon gidana na jiraki?......... Taci wani uban birki ji kake kuuuuuuu....πŸ˜„βœπŸΌ
*Zainab wowo mamar Abdallah*πŸ’–πŸ’–


*YOU ARE THE BEST AMONG BESTEST, ALAWIYYA NASIR*πŸ’žπŸ€ *WA ZAI FURTA?*🀐
2⃣7⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

πŸ‘‰πŸΌπŸ’žπŸ’•πŸ’• *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*πŸ₯°πŸ˜πŸ˜˜.

πŸ‘‰πŸΌπŸ’—πŸ’• *Mz na nufin moza ( mother) watau ( Salamatu Dahiru ) wannan page din duka naki ne Allah ya bar mun me MZ ana mugun tare*🀝🏼 ```Aminatu na godiya kina qalbinta```

**************
*Federal University dutsinma*

Ya wuntsula ya Mike da sauri keeee kina hauka ne Zaki kifar damu, ki rufa mun asiri Ina son ganin Yan dagwai dagwai.... Ta galla mishi harara sauka munzo... Ya duba da sauri yaga an wangame get, zuwan keda wannan burkin ko kuwa kawon abincin?
Kinji?
Kazo kaci gidana..... Zaki zo ki daukeni?
In daukeka fa kace, Wai meye amfanin motocin can? Ta nuna da yatsa yayi murmushi kunyar hawan su nake Allah... Ta danyi dariya kunya?
Eh wallahi sai nake ga kamar kowa zai ringa kallona...

Sai Ni rasa kunya ka sa nake hawan Wagga?
Ya kyalkyace da dariya to ai ku Daman Mata da kyale kyale aka sanku duk neman da mukeyi suwa muke kaiwa kudin? Ko bakiji ance Mana *Bayin Mata muke?*
..... Nidai naji sauka ...kina korata?
A'a Ina dai son naje nayi tuwon ko?
Zaki zo ki daukon please?
Dan Allah Anwar kazo da kanka.... Ya bude motar fine... Zanzo bye take care ya shige .
Tayi Yar dariya kawai ta tafi.
Karfe takwas yazo shida sadeeq gidan falo biyu ne na farko da na can ciki, bai tsaya komai ba ya wuce ciki abinsa... Sadeeq Kuma ya zauna na farkon shida su Aisha.
Riga da skirt ne jikinta sun kamata, ta zumbula hijab ta wuce da abincin a tray.
Sai kace muna a gida, ji yanda ka dararrashe... Yayi murmushi kawai.
Ta zuba mishi komai ta mike.... Ina zakije?
Ke wace irin bagidajiya ce Yar kauye? Haka are serving Mai gida???
Ta galla mishi harara, ya ce, naji dai Amma zauna ki cire wannan hijab din..... Ta zaro ido to Bari na dauko kallabi ko gyale..... Ya ajiye chokali ya kalleta fuska daure.... Ina son ba daddy mamaki Amma da alama wannan gardamar taki zata janyo Miki.... Tayi saurin cire hijab din gashin ta ya warwaro bisa bayanta warrrrrr ya sauka....yabi gashin da kallon ya hadiye tuwo ba shiri Amma duk da Haka bai saki fuska ba....
Ta yi tsumu kunya ta baibayeta, musamman da ta lura Yana yawan kallon kirjinta. Kayan sun matseta duk ta takura.
Ba tare da ya kalleta ba ya ce ```Kinsan kina da kyau Bilkisu?```
Gabanta ya bada ras!
Jin tayi shiru yasa Shi kallon ta yace kinji??
Ta Kara yin shiru....wannan kalmar ta kinji idan ya fada tana Jin kamar ta gantsara mishi cizo....
Bazaki amsa ni ba?
Ya kafa Mata ido, ta danyi murmushi tana Kara sunne kanta sai murza hannu takeyi kamar Mai yin alwala....
Yayi murmushi,kina da kyau Bilkisu Ina son structure dinki ... Tsikar jikinta ta bada wani Yarrrr.....
Ya ajiye chokali tuwon yamun dadi akwai Wanda zakiyi mun dumame da safe?
Um, ta ce a hankali.
Amma kamar generator dinku bashi da karfi ko? Naji AC din Bata tafiya da kyau ko kuwa fault din nata ne?
Huh?? Ya ce Yana kallonta...
Kila, ta fada ahankali... Wai kin takura ne?
A'a ta fada tana sunne Kai.
Bana son wannan ruwan daukon wasu marassa sanyi a can...ya nuna karamin fridge... Ta Mike ya bita da kallo, Koda ta juyo yayi saurin kawar da Kai kamar Yana latsa waya..... Ta mika mishi ya hada da hannun da ruwan ya fizgota , ta fada jikin sa zata kurma ihu ya toshe Mata Baki..... Kina ihu su sadeeq zasuce ga Bilkisu can ana harka...ya fada Yana Yar dariya.
Ta runtse ido jikinta ya Fara kyarma.... Dan Allah kayi hakuri..... Wayyo na shiga uku...
Wannan kunyar taki ke tunzurani kinki sakin jiki dani..... Dan Allah Zan saki sakeni ka gani.... Ya zagayo da hannayen sa ta gaba ya harde su daidai kirjinta ya soko kansa ta wuyanta Yana Mata Rada..... Ke nifa ba dutse bane ko katako.... Ta runtse ido wayyo na shiga uku Dan girman Allah ka sakeni.
Zan sakeki Amma wallahi Kika motsa kinji na rantse yau ba me kwatarki.... Naji Zan tsaya please na tuba. .... Ya cire hannuwansa ... Ta saki ajiyar zuciya kanta kasa sai kyarma takeyi duk ta tsorata....
Kyarmar ta mecece ya riko hannunta..... Dan Allah kayi hakuri..ta fada kamar zatayi kuka.... Ya Kara rungumota Dan Allah ki jira....Anwar kace zaka ba daddy mamaki fa.... Eh na sani. Ya fada kasa kasa .
Dan Allah ka sakeni.... Ke wallahi bazan iya ba, Dole na ringa taba ki don ki Saba kunyar Nan tayi yawa....ke Yanzu na say Miki ido kawai ba Dan romance ai Kya ce bani lafiya...... Wayyo ni Bilkisu na shiga uku...ta fada a hargitse .
Ya shafa gashinta.... Ina son gashinki .... Jikin ta ya bada tsammmmm....ta runtse ido.
Dan Allah kizo muje gidana ki kwana.... Sai kawai ta rushe da kuka.... Ke wasa nakeyi yi shiru.... Ya saketa Yana dariya... Jikinta sai kyarma yakeyi.... Ta goge hawayen ya bita da ido.... Haka kike da tsoro?
Ta hada Kai da guywa kawai....
Ya Mike shikenan tashi ki saka hijab muje ki rakani ...ya dauko hijab din a hannunsa.
Ta Mike .... Wallahi ko kiyi shiru ko na tafi da ke ... Tayi saurin goge kwallan, yayi murmushi matso na Sanya Miki hijab din... Ta matsa ya rungumota..... Dan Allah ki Dan ban minti biyu .... Ta sunne jikinsa ta Kara sakin kuka.... Ya buga tsoki... Kedai wallahi akwai ruwa ruwa...
Aure Dadi gareshi ki kwantar da hankalin ki mu.... Ta Kara sunne Kai ..ya kyalkyace da dariya to sakeni shikenan ba abinda zamuyi.
Ya saketa a hankali, Ya koma ya zauna bisa kujera ya zuki iska ya fesar tare da fadin ohhh my God.
Tayi tsaye har lokacin Bata daina kyarma ba ya fizgota ta fada jikinsa Yana fadin idan Baki saki jiki ba Allah yau sai dai mu kwana anan.... Ta sunne jikinsa, kokarin dagota yakeyi taki yarda.... Yayi dariya to ki daga ni na tashi ko?
Ta kasa dagowa.....wallahi Zan birkitar dake... Ta Mike da sauri ya riko hannunta tare da mikewa ya janyo bayanta ya kwanto samanta kansa bisa kafadar ta Yana magana cikin Rada Rada.... Bilkisu Ina Jin tsoro fa Anya Zan iya ba daddy mamaki wallahi duk kin rikitani.... Nidai Dan Allah kayi hakuri Anwar na tuba..... To ki jiyo in Baki kiss...... Ta zame ta zukunna tare da kankame jikinta tana fadin wayyo.... Ya Dan zukunna shima.... Wallahi kiss kawai zanyi please....nidai Dan Allah ka rufa man asiri....
Yayi Yar dariya okay naji tashi na tambayeki... Ta Mike da sauri ya matso ta matsa baya... Ya kalleta ya da matsawa?
Ta zumburo baki kayi tambayar inaji.... Ya nufota ta ringa baya baya... Bata Ankara ba taji ta daki bango ta kankame jikinta.... Ya tsaya gabanta ya harde hannuwa ya goya su a kirji tare da kura Mata ido duk sun kankance.....
An taba kissing dinki?
Jikinta ya bata tsammm..... Kinji? Ya fada.
Bazakiyi magana ba?
Wallahi ban taba ba..... Hada wallahi?
Wallahi tallahi ta fada kamar zatayi kuka...
Kina so kiji yanda akeyi?
A'a Dan Allah kayi hakuri.. .... Me yasa bakya so?
Tsikar jikinta ta Kara bada Yarrrr.....kinji?
Hakanan...
Ya sunkuyo daidai fuskarta tare da dafe bangon da hannu yace ki shirya anytime from now Zaki ji yanda akeyi.
Ya tallabota yasa Mata hijab ya figi hannunta suka fito....
Sadeeq shida Aisha kadai a Falon Maryam tayi ciki abinta..... Ta kalleshi idan ka Gama muna waje.....
Kanta a kasa ta kasa dagowa ta sanyata jikin mota ya matso kusa da ita sosai kamar zasu hada jiki ya Fara Mata magana a hankali.... Ina so ki sani ni ba katako bane,in shaa Allah bazan kasa ba daddy mamaki ba Amma da sharadin sai kin daina wannan kunyar kin sakemun jikinki..... Ta runtse ido ya sunkuya Yana lekenta..... Wannan kunyar taki wallahi tana Sanya mun sha'awar ki Bilkisu tabbas idan Baki saki jiki Dani ba to I have no choice but to sleep with you..... Ta juya ta kife Kai ga mota *na shiga uku ni Bilkisu*..... Ya juyo da ita, matsalar bani da kunya ko a gaban waye Zan iya taba ki don haka kina da aiki ja don duk ranar da na bukaci taba ki Kika Hana kamar yau to ki sani Zan...... Anwar please.... Ta fada tare da runtse ido. Ya kyalkyace da dariya... Sadeeq ne ya fito Shi kadai ba Aisha .... Ya kallesu to pigeon muje ko?
..... Sadeeq yarinyar nan ta fiye kunya fa tana takurani da yawa...
Tayi sukutiiiii, Sade yayi murmushi Bilkisu ya da kunyar miji Kuma?
Ya zagaya ya shige mota.....Yana fadin kasan baka Gama ba ka fiddoni..?
Ya kalleta sadeeq bai gaji ba ko mu koma?.... A'a kuje Dan Allah...ya Kyalkyace da dariya matsoraciya kizo mun da dumamen school gobe zanci a mota kinji ko?
Ta Dan saki ajiyar zuciya ta ce toh.
Ya langwabar da Kai Bilkisu bana son tafiya wallahi.... Ta ce ya Salam! Amma a zuci...
Zan say kawo Miki irin pad din kamfanina kiyi amfani da ita ance tana da kyau sosai idan Bata Miki ba Kinga Dole a canza sabuwa..

Ta mishi banza.
Yayi murmushi kinji?
Um, ta ce.
Ko Zaki bini..


Ta ingijeshi ta kwala. da gudu ya tuntsure da dariya ya fada mota...... Sadeeq anya Zan iya zuba ma yarinyar can ido?
Ka rufa Mata asiri Dan Allah... Ya fada Yana Yar dariya.
Amma fa tana da tarbiyya sosai could you imagine ta tsorata simply don na yi hugging dinta?
.....wallahi Anwar Bilkisu na bani mamaki ta fita daban daga cikin Mata maganar gaskiya wannan lokacin kafin ka sami yarinya Mai kamun Kai irin ta Yana da wahala kasan abinda ke bani mamaki?
Ya girgiza Kai..
Yanda she's fully hijabite wallahi kaga fa tun zuwan ta school din nan Bata taba Sanya gyale ba Bata shigar banza ga addini sallah Bata wuce ta cikin jam'i naji ana rade radin ita za a ba Amira....
Ya danyi murmushi, wallahi har tausayi ta bani Yanzu duk jikinta ya tsinke da rawa sadeeq ta tsorata da nace zanyi kissing din ta wallahi hada kuka....
Ya kyalkyace da dariya ya ce baiwar Allah.
Sai ka lallaba ta ka Kara daurewa kada ka janyo ma kanka jangwam ta rikice maka Kuma...... Naga alama fa akwai rikici .
Kasan Aisha ta nuna tana da interest akaina?
Ya kalleshi haba???
Ya Dan Bata rai, no Bata mun ba, Ina son mace mai Jan aji nafi so na Sami mace wacce Ni ke binta tana ban wahala ba ita ce zata ringa zakewa ba..... Kamar Bilkisu kenan? Ya katseshi Yana dariya... Yayi murmushi Anya Zan Sami kamar ta at least ma ko wacce bata kaita ba.. da tana da kanwa ko Yar shekara biyar ce Allah da Zan jira..

Suka kyalkyace da dariya.

Ya zuki iska ya fesar.... Gaskiya Ina bukatar matata .....ka rufa mata asiri Anwar Dan Allah kaifa da kanka kace zaka bada mamaki...... Kai nifa ba katako bane ko?.
Eh,but at least ka duba yanayin idan ta Sami ciki fa?
Shine me? Ya harareshi, Ina nufin kaga na farko tun a laulayi idan Mai Shan wahala ce an Sami matsala musamman ga karatunta, kaga automatic spill over, na biyu bazata taba fita zargin mahaifan ta ba cewar ita ta sanar da Kai akwai Aure bayan an gargadeta da tayi shiru,na uku karatu da goyo Anwar is not easy akalla.... enough jor.... Ya daga mishi hannu... Amma Zan ringa Dan romancing dinta gaskiya ban iya daurewa..... Romance din zai ringa Sanya maka sha'awa akwai ranar da wallahi zaka kasa controlling kanka tunda kamar yanda ka fada din Kai ba katako bane...... Ya Allah !!! ya fada tare da maida Kai ya kwantar bisa sit, sadeeq meye dabara?
Ina ga mu rage ziyarar su gida , ka ringa tsareta school duk maganar da zakuyi nasan idan kana ganin jama'a bama zaka kawo komai a ranka ba..... Nawaoooo,!!! Ya fada tare da tashi zaune.. gaskiya nidai an kwareni ....
Sadeeq ya kyalkyace da dariya rawar kanka ta janyo maka....... Ya Kai mishi duka, naje nayi.
Yanzu dai ai daga wannan semester din saura daya ko?
Biyu dai....
Ya katseshi ...ya ja dogon tsoki kawai ya kwanta tare da runtse ido. Sadeeq ya bishi da kallo Yana murmushi......
Wai ya mufeeda ta hakura ko?
Ya yatsuna fuska, ance har yau ta kasa shigowa school saboda kunya..... Maganin ta kenan... Ya tashi zaune Yana Yar dariya kasan ni duk wake bani dariya?
Ya ce sai ka fada.
Helen, tunda akayi case din nan Yanzu ko layin da nake zaune Bata bi kasan arna da shegen tsoro....... Suka kyalkyace da dariya.

Bilkisu ta zabga uban tagumi har lokacin jikin ta bai daina rawa ba, kirjinta kuwa sai dakan uku uku yakeyi, *Na shiga uku ni Bilkisu Wai kiss* .... Nikam dama na hakura da Abujan da Yanzu Ina can zamana qalau..
Ta runtse ido lokacin data tuna ya zagayo da hannayen sa bisa kirjinta ya kwanto jikin ta...... Tsikar jikinta tashi Yarrrr lallai akwai damuwa .... Ta bude ido su maza basa da kunya ko kadan....
Haka ta kwanta tana ta juye juye da ta tuno Shi da yanda ya ringa Mata sai ta kudundune jikinta ta boye kanta cikin filo.....
Murjanatu cikin masu aikin gidan ta Kira da sauri ta ce maza ta dumama tuwon jiyan kafin ta fito wanka.....
Yau taga amfanin nikaf, saboda da Babu ita tasan bazata iya kallon Anwar ba.....
Tana shiga ajin anata raba test din da Richard munafuki yayi. Two over ten, three mutum biyu keda 5 su chinayye...... Itama two taci, Anwar ya saka tashi aljihu kawai lokacin da ya buda yaga yaci nine....
Ya kame Baki na shiga uku.... Mutumen nan wallahi mugu ne daman yafi so mu fadi.... Sadeeq na bayanta ya ce nawa Kika ci Bilkisu?
Ta mika mishi 2 ce shegen kaifa? Yayi murmushi three..... Anwar yayi fit ya fizge takardar ya na zagayo ya kalli root dake kusa da ita yace ban wuri.... Ta kwashi takardun ta ta koma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login