Showing 24001 words to 27000 words out of 76784 words

Chapter 9 - WA ZAI FURTA COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2024

15138

tafiya da kyar kawai taji anfinciko hijabin ta.......jira karamar Yar iska.
Kafin ta Ankara sun Mata zobe.
Ta kallesu daya bayan daya tace *Anzo wurin* cikin zuciya.
Lafiya?
Ta bukata tana musu kallon up and down.
Ko zamuji na jaki ne tukun?
Ko Kuma Ni ko?
Wallahi tallahi duk Yar iskar da ta Kara ja mun jiba sai naci kutumar........ke banza...mufeeda ta katseta.
Wani kallo ta wurga Mata nice banza?
Eh kece banza ko Zaki Rama ne?
Akan meye Zaki kirani banza?
Saboda Anwar..!
Wallahi idan Baki fita harkar sa ba Zaki......Zaki fiddani karatu FUDMA?
Ta bukata.
Amma ke a matan ma rakiya kikayo, ai mace idan ta cika mace namiji binta yakeyi ba itace ke bin sa ba. Kije ki tambaya Dani da Anwar waye ke bin wani?
Ko an fada Miki dashi da Babu suna da banbanci a wurina?
Karatu ma da mukeyi Shi ke rokona da inzo ba Ni ce ke makalewa ba. Ta fiddo waya ta latso missed calls.....ta nuna Mata fuskar wayar kalla ki gani.....don haka wallahi tallahi sai kinyi Dana sanin kirana banza......ta ingijeta ta wuce , gigin yasa jamcy ta Kai hannu zata rikota ji kake faaass.... Ta wanka Mata Mari , Marin da ya janyo duk illahirin masu wucewa da wadanda ke zaune sannan ta daga murya....duk wacce Kuma take ganin ita Yar Tasha ce tazo ta yi gigin kwatanta abinda tayi ko a nemi wata ta Rama Mata...... Bilkisu lafiya meke faruwa?
Suleiman ta gani.
Tayi murmushi cike da takaici duka na suka zo yi saboda inji tsoro in daina karatu da kula Anwar .
Duka?
To bisimillah kuzo ku dake ta wallahi summa tallahi da na karya hannun yarinya ko waye ubanta....duk suka juya suna gunguni, yace:, Yan iskan karya.
Muje kyalesu. Suka jera.....
Haushi ya kamata lokacin da ya Kira taki daukar wayar.
Tasan akan maganar test din *GST* ne. Yasan cewa ta tsani CBT,
Ya buga tsoki, duk duniya Babu Mai Sanya mishi ciwon Kai irin Bilkisu.
Bakin Auditorium din cike da dalibai abinka ga general course. Tana can gefe ta makure sai faman karatun past question takeyi, Shi kuwa sai wurge wurgen ido yake ta inda zai hangota,
Mufeeda na can jikin bedi sun Kura mishi ido.
.......Wai Daman kina Nan? Yanzu naga Anwar Yana nemanki nace bamu hadu ba, Aisha ce ta karaso rike da past Q din itama.
Yana Ina?
Gashi can....
Ta Mike , okay jirani Ina zuwa.
Yana hangota ya nufo ta.
Tayi kamar Bata ganshi ba ta nufi inda su mufeeda.
Ya biyota.......ke nake nema fa tun dazun kin Kuma hangoni kina neman sharewa........ Da karfi ta finciko mufeeda tare da bankada ta kusa dashi har yayi saurin ja da baya ganin zata fado jikinsa.
Ya zaro ido.....ita Kuma ta juyo a hasale ta Kara maida keyar ta tare da nuna ta da yatsa.......Ni agabansa Zan Miki *warning*
Ko a Yanzu wakika ga yabi wani cikin mu?
Tuni an musu zobe ana kallon ikon Allah,
Ta daka Mata tsawa nace ubanwa Kika ga yabi wani cikin mu?
Na tabbatar tun dazun ya ganki anan Amma bai nemeki ba saboda haka kece *BANZA* Gashi nan nabar Miki Shi duniya da lahira idan kina bukata Ni karatu ya kawoni ba shashanci da bin maza ba don haka idan kina son sanin wacece Bilkisu please try and confront me again wallahi you'll regret it for the rest of your life useless fool.........
Kawai ta bi cikin mutane ta wuce abinta.😝

Zainab wowo ce daiπŸ˜„βœπŸΌπŸ’–
🀐 *WA ZAI FURTA?*🀐
0⃣9⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*Wallahi tallahi inajin dadin masu kirana da mun text WhatsApp musamman don jinjinawa Aunty Rabi dayi Mata addu'a da masu yiwa mahaifina addu'a na gode Allah yabar kauna my fans my pride ana mugun tare irin sosai dinnan*πŸ’–πŸ€πŸΌ.
*Arziki irin na Aunty Rabi kowa ke fata Wanda zaka ba kowa ba arziki irin nasu o'e ba daga mu sai 'ya'yanmuπŸ™„ Wanda ya tsargu dashi nake*πŸ˜πŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸƒπŸ»β€β™€

_Wayata na bani matsala wallahi Shi yasa bana update da wuri_


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Ke ta tabance UMMI MAMAN KHAIRAT DA ZARAH, makwabciyar Alawiyya Ina godiya*

πŸ‘‰πŸΌ *Unex*πŸ’–( Babu kamar ki ).

*Alawiyya Ina Kara godiya fa Allah yabar tare Allah yabarki da malam ya tsone idon munafukai*πŸ˜„

πŸ‘‰πŸΌ *AUREN FARI FANS*πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•one love well.

*INA CIGIYAR MZ*πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ˜„

***************
*KADUNA RIGASA*
Tabbas Ummi Taji uwar bari,
Ta zabga uban tagumi, competition zanyi da Amira wallahi dole in ajiye wannan jahilcin in kwatar ma kaina yanci. Mutane dake cewar duk namijin da yayi sabuwar Amarya uwargida ta Zama banza yau na karyata hakan, naga inda year gida ke fin Amarya daraja da kima.
Tun kafin inzo gidan Nan yakeyi man gargadi akan matarsa, ban Kara tabbatar da hakan ba sai da nazo, Bata laifi, bata gundurar sa. Ya Zama wajibi Nima nabi hanyar da tabi don mallakarsa.
Ranar ya koma aiki, tunda ya tafi tana bangaren Amira suna fira, abin ya bata mamaki ganin ba wani alamun sauyi daga fuskarta, ta sakar Mata jiki suna ta fira Mai dadi ( ba abinda yafi Zama lafiya dadi, abinda mutane suka kasa ganewa kenan ).
Ta Dan muskuta Aunty wata alfarma nake nema wurin ki.
Ta kalleta cikin natsuwa sosai kafin tace Ina jinki ummi.
Wallahi Aunty na rasa gane Kan Abban Ahmad ko wane lokaci duk abinda nayi Ni Kam ban iya ba.
Kinga ko abinci na dafa mishi idan na kawo mafi yawa fushi yakeyi yabarshi a wurin Koda kuwa nayi abinda yake so. Idan Kuma na sameshi daki...........ohhhhh na fahimci zancen ki. Ta katseta tana Yar dariya.
Baya Miki korafin Baki da kula?
Wallahi yanayi Aunty.
Yawwa, kin gane, Shi mutum ne Mai son kula gaskiya.
Misali: wurin abincin da kike korafi, Shi yafi so idan Kika kawo mishi abinci ko ki zauna kuci tare, ko Kuma ki zauna kusa dashi yanaci Koda kuwa kin koshi, ya tsani ki bashi abinci kibar wurin.....ke abinda ma yafi so Bari in fada Miki shine ki na bashi da kansa.
Ya tsani lokacin da yake zaune dake ki maida hankali akan waya ko kallo ko wani abu saboda Shi mutum ne Mai tsananin son kula.
Ko a kwanciya ya tsani mace tayi mishi tabababaaa Nan da Nan sai ya harzuka.......gabanta ya Fadi...tohhh wannan dalilin ke sawa kullum sai sunyi rigima?
Ikon Allah.
Ta yi shiru dai, taji Amira ta shiga ranta sosai ganin ba bakin ciki ba Jin zafi ta zauna tana Mata irin wannan bayani Mai tsada Wanda ta tabbatar idan ita ce bazatayi hakan ba.
Kunya ta kamata sai kawai ta sauko bisa kujera.....Dan Allah Aunty Amira kiyi hakuri abubuwan da nayi a baya wallahi hada zuga irin ta mutane Amma Yanzu na gane........Dan Allah tashi ki zauna ba komai. Shawarar da Zan baki shine ki kuji fitar da sirrin auren ki ga ko wanene wasu ba shawarar kwarai zasu Baki ba, ko meye kiyi keda mijinki ba Wanda yaji ya gani ko wace Kika gani gidan aurenta wallahi hakuri takeyi. Shi Aure 90% hakuri ke raya Shi sauran 10%din ne ilimi da soyayya. Saboda haka Dan Allah ki zauna mu fahimci juna tunda kaddara ta hada mu ba kanmu aka Fara ba iyayenmu da kakanni duk haka muka gansu Kuma zamansu lafiya ba don Babu kishi ba sai don hakuri da hangen nesa.
In shaa Allah Aunty Zan kiyaye Allah yayi Mana jagora..........
Tirkashi, competition zai tashi muje zuwa muga cikin Amarya da uwar gida wacece zata amshi first position????????
**************
*Federal University dutsinma*

Yana son buga tsalle ya kasa , kanshi ya kumbura jinshi yake Babu kamar sa, ya gyara kwalar rigarsa sannan ya kalleta sama da kasa I warned you several times but u refused to listen to me, idan takamar ki *Hauka* ki sani Nan school din akwai *iyayenki*.........Shima yasa Kai yabi bayan Bilkisu. Wuri ya dauki ihu.......mufeeda tayi tsaye ta kasa motsi tana sonyin kuka Amma ta daure kada ta Kara zubda ma kanta abin magana......
Yasan wata sabuwar rigimar ce, tana niyyar Zama Aisha tace me Kuma ya faru naji ana ihu?
Ni da waccen sakaran fa, ta tareni jiya suna mun wani kuri na banza akan Anwar shine na kaita gabansa nayi Mata nawa gargadin ta gane cewa ni ba tashi nake ba........wa?
Aisha ta bukata tana zaro ido.....dai dai lokacin da ya karaso tayi kamar Bata ganshi ba tace *Anwar* Mana.
Me nayi? Ya bukata tare da tsareta da ido,
Wai ke me yasa bakya Sona da kwanciyar hankali?
Ta kalli Aisha tana Yar dariya kinji fa?
Sannan ta kalleshi, Da sunyi mun tsinannen duka jiya ai Ni Dana shiga tashin hankali ko? Ya zaro ido, duka?
Ta balla mishi harara wallahi tallahi duk ranar da ka janyo mun duka wajen ajabon Yan matanka a school dinnan har Kai sai sunja maka bala'i don security office zanje nayi reporting......ya kyalkyace da dariya Yan matan nawa ne ajebo?
Ke meye naki da zasu dake ki?
Ban sani ba kaje su baka amsa........ya Kara dariya matsa in zauna.....da sauri ta matsa ganin Yana kokarin Haye Mata kafa.......kana da hankali Anwar?
Wani lokacin Ina taba hauka,, ya fada Yana dariya.
Aisha Mike Kai wallahi bazan biye muku ba Bari in koma baya inyi karatu.
Ita da yunkura zata tashi yayi saurin rike habar hijab dinta ya mayar da ita ta zauna....... Ba inda zakije wallahi.
Wai ke me yasa kin rainani?
Idan kina son abu gardama banayi sai nine Zaki ..........zaniyi me?
Mutane fa na kallon mu ya sunan abinda kayi?
Aisha ta girgiza Kai ta wuce tana murmushi.
Tasha mur, karatu zanyi ko ka tashi ko Kuma Ni na tashi.......babu daya ciki. Kiyi abinki bazan dameki ba.
Gobe ne birthday dina me Zaki bani gift?
Tayi murmushi kai dai ka cika roko wlhi. Zan siyi ledojin pure water na ba Yan class suyi maka wanka,
Tabbb, ai bazan zo class ba gobe saboda hakan.
Wasa kakeyi ......
Allah kuwa.
To shikenan ka huta.
To meye Zaki bani?
Ta kalleshi cike da kosawa to meye Zan baka ne?
Gift!, Yace Yana Yar dariya.
Ta Sha mur, ka Fadi abinda kakeso Zan baka.
Zakiyi mun special girki, sannan ki kaini shopping.......... Ta kyalkyace da dariya.
Yabi kumatun ta da kallo Yana son dimple dinta ainun.
Shikenan Zan maka what next?
Karfe nawa zanzo?
Da safe kafin na tafi class kaga gobe har 6 Ina school.....no is too early. Bayan magrib dai......... Bana fitar dare sai dai kazo 2 kafin muyi lecture 4........ Hmmm shikenan ya fada ba don ransa yaso ba sai don gudun kada tace duka ta fasa.
Tare suka shiga test din ka kujerarta ga tashi. Ta kanga mishi fuskar computer din Yana tashi yanayin nata.
Sai gashi suna gamawa taci 20/20 Shi Kuma Yana da 18/20.
Tayi ta tsalle tana Murna.
Sun jero sai dariya takeyi tana Jin dadi, ta kalleshi yau wace rana naci CBT 20 last session wallahi naci da yawa 11 ko 12.
Murmushi kawai yayi.
Ta hango su Aisha shikenan bye bye wanna go thank you till tomorrow.
Ya juyo zai magana tuni ta tsallaka tana sauri so takeyi kawai ta Basu labari.
Ya danyi tsoki kawai ya wuce.
Nawa kuka samu?
Aisha ta yatsine fuska 13, khausar tayi tsoki Ni 10....... Wallahi saura kadan na shiga cikin department dinku Kinga ruwan Yan 7,8 da 9?
Ta zaro ido wallahi Anwar yayi mun duka na cinye........duk suka zaburo 20?.
Cike da Murna tace wallahi kuwa.
Ohhh Allah ya kashe ya Baki inji Aisha.
Ai yau nayi sa'a Kuma wallahi ba layi daya muka hau ba.
Yana tsaye shagon Abdul ya hangosu.
Kamar ya kwada musu Kira kwatsam sai ga Dr Dan Musa ya tari gabansu.
Bilkisu see me by 2 in ma office........okay sir. Ta ce kawai suka wuce.
Wahalalle naga ubanda zai gani.
Baki zuwa? Inji khausar,
Eh, kullum aikin kenan kuma ba wat maganar arziki ba kame kame.
Anwar ya bishi da harara lokacin da yazo zai gitta.
Bayan sallar la'asar ta tafi dakin su Jennifer sukayi mata kwatancen gidan zainab wowo wacce keyi wa Yan makarantar cake. Ta iya cake sosai na biki da birthday ga sauki.
Aisha ta rakata. Mata Mai fara'a ta amshe su hannu biyu biyu.
Sannan suka ce cake sukeso na birthday Amma na maza.
Tace ba matsala.
Ko na nawa kike so Zaki samu. Kuma karfe nawa? Akwai Wanda Zaki ba yakai man goben wajen 1:30 haka?
In shaa Allah bani number da za a nemeki da ita.
Sukayi musayar number ta biya kudin babban cake na gani na fada.
Bayan sun fito ta kalli Aisha Zan surprising din sa ne.
Suka biya super market ta siyo manya manyan lemuka carton daya *na grapes*
Hmm kawai Aisha ta ce tana murmushi.
Ta harareta, Fadi ta cikinki Mana, *there's nothing ooo just wanna surprise him and show my gratitude on what he has done for me Sha*
I knew, inji Aisha tana Yar dariya.
Karfe shidda na safe ta tura mishi text ```Happy birthday Anwar wishing you more dollars in your account, you are an amazing person stay blessed```
KO minti daya ba'ayi ba yayi reply
``` Thank you my personal person```
Murmushi kawai tayi.
Shi kuwa ya karanta text din yafi sau dari.
Ko wa ka gani a class da ledar pure water saboda Shima haka yakeyi wa mutane Amma ba Anwar ba alamar sa, ko su sadeeq Basu San cewar baya zuwa class ba.
Bilkisu kadai tasan haka.
Sadeeq ya karaso kusa da ita hajia Kira Mana Anwar please...
Tayi murmushi yace yau bazai shigo school ba.
Aji ya dau surutu suka ce ko hostel ne yau sai sun bishi.
Kamar yanda sukayi alkawari da zainab sai ga cake...... Cake abinda ka cake sky blue yayi kyau karshe an nado Shi a leda cikin kwali. Sai kamshi ke tashi. Flowers din sunyi kyau Mai Rose ne da wasu design cake din ya tsaru.
Tana kwance daki ya kirata.
Yana jiranta bakin hanya.
Ta ce toh, sanye yake da round neck shirt orange Mai ratsin fari a jikinta an rubuta *You are mine only* a gaban rigar. Dark blue jeans ne wandon da facing cap Fara anyi rubutu orange *Mine for ever* daga sama.
Kunnensa like da ear piece. Kanta a kasa tana tafiya a hankali.
Ya saki ajiyar zuciya kadan idonsa na kanta har ta karaso.....
Murmushi ta sakar mishi kafin tace happy birthday once again.
Godiya! Ya fada Yana latsa waya Shi adole ba kallonta yake ba.
Ta harareshi dai dai ya Dan dago.
Yayi murmushi ko amsar Bata Miki ba?
Yayi kyau karshe....ta fada a zuci a zahiri Kuma tayi shiru kawai.
Muje.......tace tare da yin gaba kadan.
Ki jira muyi hoto Mana..... Da wa? Tabb
Ya Dan Sha mur, dake ko bazakiyi ba?
Eh, tace tana Kara ci gaba da tafiya.
Yaji haushi sosai.
Are you serious? Ya biyota.
Ta Dan waigo *did I look like a joker?*
Dan Allah kizo muyi pic Bilkisu........ Ta zaro ido Wai da gaske kakeyi?
Sai ta danyi dariya kawai ta sunne Kai....
Ya ja tsoki, don ya karanci kunya takeji.
Suna Isa shagon ta ce me kake so?
Ya Sha mur Yana fushi duk abinda ya Miki.
Tayi kamar Bata lura ba ta amso meat pie da soya milk drink na cikin kwalba Mai tsadar guda goma.
Ta fito, gashi sai me?
Ya karba da hannu daya dayan Kuma Yana latsa waya. Yace shikenan thanks.
Duk taji ba dadi kamar tace suje to suyi hoton Amma gaskiya Bata iyawa.
Suka jera zuwa bakin hanya sai fushi yakeyi.
Zaka koma hostel ne?
Akwai abinda Zan Miki ne idan na tsaya?
Zan baka sako ne muje da mashin din a bakin gidan mu ka karba....... Ki je ki kawon Ina Nan.
Har lokacin fuskarsa ba fara'a.
Ta langabe Kai Wai Anwar fushin na menene?
Mtsew kawai yaja guntun tsoki.
Kaji?
Oh my God , me kike so Yanzu Wai?
Muje ka karbi sakon.
Jeki gani Nan zuwa.
Har zata Kara magana sai Kuma ta fasa ta wuce don itama ta Fara kulewa.
Tana niyyar shiga gida taji tsayuwar mashin, da sauri ta waiga sai kawai tayi murmushi ganin shine ya Dan harareta.
Tayi ciki tana dariya.
Kwalin lemun ta Fara fitowa dashi tasa agaban mashin din sannan tace Ina zuwa ku jira.
Ta dawo da cake din ta Mika mishi ga cake kaci sosai........ Da sauri ya kalleta.
Tayi murmushi.
Kamar zaiyi magana sai Kuma ya fasa yace da Dan mashin din muje.........
Kamar tace dawo muyi hoton Amma bakinta yayi nauyi.
Haka ta shiga gida sukuku............
A hostel party sosai akayi yaji dadi abinda tayi mishi Yana son Allah ya kawo ranar da Shima zai Bata mamaki. Amma rashin yin hoton nan ya Bata Masa rai matuka, ya Fara gajiya da halin ko'inkula da ta keyi mishi, yanda Yan Mata ke rokonsa akan suyi hoton dashi Amma shi yau yabroki mace suyi taki amincewa *dame Bilkisu ke takama?*
Wajen Sha biyu ya tura Mata text *Thanks for the cake* sai da safe ta gani.
Bata Sami halin reply ba.
Yana zaune ta shiga class din Koda suka hada ido tayi murmushi Shi Kuma ya daure fuska ya kawar da Kai.
Gabanta ya fadi, ranta ya Fara baci menene abin Jin haushi daga tace bazatayi hoto dashi ba? Ya taba ganin tayi hoto da wani ko wata?
Ta ajiye books dinta ta Isa wurin sa.
Ina kwana?
Ya dago Kai tare da cire ear piece. Ya kalleta Yaya? Fuskar sa ba yabo ba fallasa,
Zamuyi macro after this lecture please if you are free........ It's alright. Ya fada a takaice.
Ta juya ranta ba dadi.
Yan aji sai zolayar sukeyi jiya yaji tsoro baizo class ba kada a mishi wanka yana ta dariya da yazo zasu hada ido sai ya kawar.
Duk taji babu dadi.
Ana Gama lecture wasu suka shigo alamar venue din su ne.
Fitowa sukayi, ajin dake hade dashi ba mutane sosai Yana tsaye bakin taga tace Anwar muje Nan naga ba kowa......... Anwar let's snap please Helen ta karaso tare da dafa kafadarsa.......
Wani dadi ya ziyarce Shi yace anzo wurin.
Ya kalli Bilkisu okay jirani Ina zuwa.
Kawai suka Fara hotuna. Kamar jira akeyi sai ko wace ta taso wasu ma wucewa zasuyi ga Anwar da farin jini
Nan da Nan hankalin Bilkisu ya tashi ta kasa daurewa ganin yanda suke faman rikeshi wasu na kwanciya kafadar sa.
Ta shiga ajin idanun ta duk sunyi ja.....
Yafi mintuna talatin tana zaune ta ma kasa tashi suk tana hangensu ta taga.
Sadeeq ya karaso maigadon ya naga kinyi zaune baku Fara ba?
Eh, hotuna yakeyi yabar Ni Nan kamar sakarai, ta fada a wahale kamar zata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login