Showing 39001 words to 42000 words out of 76784 words

Chapter 14 - WA ZAI FURTA COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2024

15135

fada Yana dariya.
Ta ce hmm.
Zan Fara fita kasuwa gobe kin San talaka baya Zama......kana kasuwanci ne?
Eh, Ina bin wani ubangidana Ina mishi tsaron shago cikin sabon gari a garin Kano......kin San kasuwar sabon gari?
Naji dai ana fada.
Okay toh can.
Tausayin sa ya kamata.......rashi bai hanashi gadara da izzah ba, Mai Hali baya barin halinsa....kinyi shiru.
To Allah ya bada sa'a ka samo kudi da yawa Wanda zamuci biscuits next semester....ya kyalkyace da dariya ni Zan siya Miki?
Kwarai kuwa a rama wa kura aniyarta nima sai na ci kudin ka next semester.....hahahaha ya Kama dariya.
Naji Zan dage na samo da yawa.
Ke me Zaki kawo mun tsaraba?
Abinda kake so,
A'a kawai ki dai kawo man ko menene.
Hmmm, tace.
Ko bazan samu ba?
Zaka samu in shaa Allah.
To me Zaki kawon?
Ka fada Mana me kake so?
A a bani da zabi.
To shikenan ka jira zaka gani.
Na gode.
In kyaleki haka ko?
Okay gudnight ta kashe kawai....... Ya doka tsoki jira takeyi ne?
Yarinyar nan tafini
gadara wallahi.
Washe gari bai Sami kansa ba ko kadan, abubuwa sun taso, ba shiri karfe shidda ya bar kasar......
Yanayin abubuwan sai da ya kwana biyu bai samu yayi magana da Bilkisu ba.
Ta nemeshi a waya har ta gaji.
Da ta Kira sai a Fara nata faransanci Ashe France ya tafi ya Kuma chanza layi.
A Rana ta biyu ana ta meeting a katon office din sa Kira ya shigo through WhatsApp ya kalli turawanya ce kowa yayi shiru,
Ya daga... Hello Bilkisu.... Duk kasuwar ce wayar ka Bata shiga? Ina Kira sai wani yare ko ka Sanya Ni voice mail ne?..... Voice mail Kuma ? Yayi dariya kiyi hakuri wasu kayukane muke shiga Saro tattasai Kuma ba service wurin kiyi hakuri muna lissafi da Mai gida anjima zamuyi chatting......
Hakan kuwa akayi tun Sha daya suke chatting har kusan biyun dare.
Amma ita dashi lokutan sun banbanta.....
Daga ranar kuma bai Kara samun lokaci sunyi magana ba.
Fushi tayi Bata nemeshi ba, Suleiman kuwa duk bayan kwana biyu sai ya nemeta sun gaisa.
Ranar da zai baro France aka mishi waya zasuyi meeting Abuja da managers din, *Next, ShopRite da Sahad*
Dole sukayi landing Abuja.
Motoci shidda kebin bayan tasa biyu na gaba. Saboda tafe yake da nashi mutanen.
Ko a cikin motar waya kawai akeyi.
Bayan an gama meeting din suka zagaya ta kofar shiga ShopRite wurin ice cream security sai kyarma sukeyi yau ga Anwar...... An cunkushe kofar an tsaida masu shiga.
Ya Kira Angelina suna magana.........Ai sai ku bamu wuri mu wuce ko?
Da sauri ya waigo *Bilkisu ce* rike da iyayen ledoji..........πŸ˜„βœπŸΌ


*Ayi hakuri a hankali za a ji yanda labarin ya ke da yanda zai Kare* Banda sauri please mubi komai a hankali.
Zainab wowo ceπŸ’–πŸ’–πŸ˜„
πŸ‘‰πŸΌπŸ’–πŸ€ *WA ZAI FURTA?*🀐
1⃣4⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*


*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*****************
*ABUJA NIGERIA*

........ Ya juya da sauri ya kalli Anjelina Yana magana kasa kasa..... Jeki ce su bude kofa ta fita da sauri...
Ta rike kugu tana ta faman masifar su bude kofa zata wuce.
Ya juya a hankali, yana kallonta ta wutsiyar ido. Matsattsar doguwar Riga light pink ta saka da Dan karamin gyale fari iya wuya, kafarta cikin dogayen takalmi....
Anjelina na fada musu sukayi saurin bude Mata..... Ta bude baki iyyehhh ikon Allah yau Allah ya kawo mu ShopRite shiga da izini fita haka..... mtseww ta buga tsoki ta wuce..... Ya tuntsure da dariya....yarinyar can wata Rana sai ta janyo mun rigimar da za a daureta.
Ya fito a hankali Yana leke duk aka bishi da ido..... yallabai lafiya?
Yayi murmushi Ina zuwa ya fita da sauri.
Tana faman zuba kayan bayan mota.
Ya fiddo waya da sauri ya kirata, ya lafe bayan wata mota.
Ta zumburo Baki kafin ta dauka alamar tayi fushi ya kyalkyace da dariya Yana hangenta.
Sai yau ka tuna dani?
Allah ya Baki hakuri ayyukan ne sunyi yawa Kuma kinsan kauye service din waya sai a hankali... always excuses mtseew.
Yayi murmushi kiyi hakuri ai Yanzu na dawo gari Daman wasu Kaya ne muka siyo......
Naji dan kasuwa, Ina wuni......ta fada tana kokarin shiga mota ya musu nuni da hannu, alamar motar can zasu bi.
Ya manta ma da abinda ya kawo Shi,ya Abuja kina Jin dadin ki fa.
Hmmm kawai tace.
A hankali Yana janta da labari suna bin su a baya har suka je gwarunfa a road *111* gidan yake flat 4 Nan ne gidan su Bilkisu..... Next week fa za a koma school nasanka da Kara kwanaki wannan semester din ka Kara Alalh sai munyi fada...... Amma dai ba ranar da aka koman Zan dawo ba ko? Na Kara ko sati biyu.....daya dai wallahi Nima ranar Zan dawo......
Ya kyalkyace da dariya Hajiya kice kawai kina neman lift Kuma matsalar ba tare da Sadeeq nake dawowa ba Mai rabo ni har na gayyaci wasu.....mtsew a a ka manta... shikenan kayi zamanka....ta ajiye wayar daidai lokacin da motar ke kutsa Kai cikin gate din gidan.
Ikon Allah har taji haushi?...... Kamar yaje gidan yakeji Amma baya so yayi hakan Yanzu.
Komin dare yake son komawa kano, haka suka juya Yana waigen gidan.
Bai kirata ba, ya Bari sai zuwa anjima........
Suka kura ma jaridar ido, daddy yayi murmushi ai yaron nan ne wallahi. Na fada Miki kinki yarda Amma Bari Bilkisun ta dawo muji cikakken sunan sa a bakinta Amma tabbas prof. Hamza yace mun lokacin da na saka ayi binkice Kan dabi'un sa da irin rayuwar da yakeyi makarantar......
Da gudu ta shigo, mommy na samo cheese din kuwa....... Ba sallama?
Assalamu alaikum...ta fada tana dariya.
Gardama mukeyi da dadyn ku akan Anwar meye cikakken sunan sa?
*Hamza Yusuf Hamza*...... Duk suka kalli juna shida ita da sauri,..... Ta zaro ido lafiya? Yanzu Ina fitowa ShopRite ya kirani kuwa.....yace me? Duk suka hada Baki.
Ta tabe baki gaisawa kawai mukayi da yake kwana biyu bamuyi magana ba ya ce sunje kauye siyo ma ubangidan su wasu Kaya..... Nace damuwata ya koma school da wuri kada ya barni da tararrabi inyi ta zare ido saboda idan Yana kusa da anyi ban ganeba ya mun bayani shikenan.....
Aikin meye yake?
Daddy ya Kara bukata...... Daddy hoooo nace maka wani yake mawa fa tsaron shago sukeyi a sabon gari market...this is what he told me na.....
Tohhhhh, ai Yanzu muka fahimta. Jeki ciki abinki.
Kin yarda Yanzu da maganata?
Ta zaro ido shine da gaske wallahi.....baya son fada Mata Shi wanene Kuma makarantar ma badda sawu yayi.
Ba tace first class din ma boyewa yayi ba?.... Tabbas.
Yayi murmushi, shikenan mu Sanya su addu'a Kar ki saki Koda wasa ki sanar da ita, wata kila Yana da dalilinsa nayin hakan....
Hmmm. Tace duk jikinta yayi sanyi tana Kara maimaitawa a zuciya *Hamza Yusuf Hamza bushara* Shi ne *Anwar* ikon Allah.
Karfe biyun dare ya sauka Kano.
Bai Sami kwanciya ba sai uku saura, Shi yasa ya makara washe gari wurin tashi.
Sha biyu saura ya farka tun bayan da yayi sallar asubah ya koma.
Ko juyin farko batayi ba ya mirgina ya janyo wayarsa....... Cikin magagi ta dauka hello.......shine Kika ajiye mun waya jiya ko?.
Hmmm, ina kwana..... Duba agogo ki gani Sha biyu ta wuce kike faman ina kwana.
Ina labarin Suleiman,
Lafiya Lau.
Shi Dan wane gari ne....Ina ruwanka ta fada tana tashi zaune.
Yayi murmushi lallai dai Kam, babu ruwa na.
Next week result zai fito waye zai Miki registration?????... Suleiman nake turawa kudi Yana mun.....kenan yasan password din portal dinki....why not?
Shine ni ban sani ba?
Tayi dariya kawai.
Kinji?.
Nawa ka samo kasuwar? Nawa ne share na Kuma?
Ya kyalkyace da dariya....sai nazo zamuyi lissafi.
Ehee, hakan ya kamata.....tana so tace mishi suyi video call tana Jin nauyi.
Sun kusa awa kafin suyi sallama.
Tunda ya dawo Kano ayyuka sukayi mishi sauki a Rana sai suyi waya sau hudu, chatting kuwa Koda yaushe suna online.
Ya rasa inda zai Sanya kansa da tayin Yan mata.
Sati daya da komawa Bilkisu ta koma, Shi Kuma yace Mata sai satin sama, Amma duk Rana daya suka dawo Yana son Bata surprise ne banbancin shigar dare sukayo sosai don lokacin da suka zo dutsinma daya saura na dare.
.......ya kalli sadeeq an dawo fagen fama.
Suka kyalkyace da dariya.
Sadeeq ya Kara langabe Kai ka dubi girman Allah ko roba roban ne ka sai Mana muma wannan semester din...... Allah ban saye ka Bari kawai muyi ta aro muna 3 in1 hakan Yana matukar birgeni da saka ni nishadi......mtsew..kada Allah yasa ka siya mugu, ya wuce.
Ya bishi Yana dariya, inba kaiba Bilkisu duk duniya Yanzu kunfi sanyani ciwon Kai.
***************
*Federal University dutsinma*
Hutun ya amshe ta, tayi kiba ta Kara yin jawur, Bata son zuwa lecture din Dr Richard munafuki saboda ta tsane Shi. Kuma Yana iya bada test idan yaga ajin ba mutane.
Milk lace ne ta saka Yana da ratsin flowers orange dinkin Riga da skirt, sannan tabi da doguwar hijab.
Agogo kawai ta daura sai zoben azurfar da ke hannun hagu.
Tafiya take kanta a kasa, wani haushi take ji har cikin zuciyar ta idan ta tuna class din yau ba Anwar.
Ga mamakin ta ajin cike fiye da rabi duk an dawo.
Daga nesa Helen ke ihu oyoyo Bilki beauty....
Tana Yar dariya tana Kara sauri tare da ware hannu suka rungume juna.
Kinje America ne irin wannan fresh haka?....
Ta tun tsure da dariya suka fada aji........ Karaf sukayi tozali, ta zaro ido Anwar??????
Ya sakar Mata murmushi kawai, wani dadi ya ziyarce ta kamar ta ruga ta rungume Shi takeji, ya Kara kyau shima yayi haske, tayi kasa da Kai kawai tana murmushi.
Tana Shirin Zama ya taso... Helen move, ya janyota da hannu ya fiddo ta sit din, Shi kuma ya zauna.
Wani mugun kishi ya turnuketa ta kalleshi a hasale ji yanda ka wani kamata ba ka iya cewa ta wuce ko ta gafara dole sai ka cacukumota? Ta Kara sa maganar tana maka mishi harara......
An Kuma dawo fa, yau din nan har na Fara tabka laifi?.
Au hakan da kayi daidai ne??? To ka je Kama kadaddabeta Anwar mtseww ta doka uban tsoki.
Ya dafe Kai, ohhh my God, naji ban kyauta ba kiyi hakuri bazan Kara ba shikenan ko?
Kinji?
Naji, ta fada.
Ina tsarabata?
Ya Mika Mata hannu....... Tana daki na yi tunanin baka dawo ba.
Jeki daukon Ina jiranki.
Kana jirana a Ina? Lecture din Kai zaka mun?
Ai ba zai zo ba Yanzu ya Aiko kafin ya karaso...... Mtsew mutumen nan baiyi ba wallahi.
Tashi muje in baka......ta mike.
Ya shafa Kai da hannu, kije ki dauko mun Ina nan ki dawo.
Inje in kuma dawowa?
Eh, Mana.
Idan na biki muka je kina bani zaki gudu......ta yi Yar dariya in gudu kamar wata marar gaskiya?
Eh, nidai jeki dawo Ina Nan..... Me zakayi anan din?
Jiranki zanyi kawai har ki dawo, a a idan na tafi ka gama sai ka biya ka karba kawai.....wallahi bazan karba ba kuwa, ki je ki dawo akwai labarin da Zan baki.
Ta koma ta zauna, mu gama labarin tukun sai mu tafi tare ka karba.
Ya kalleta better.....
Ina Suleiman Shi bai dawo ba?
Wallahi ban sani ba.
Yasu mommy?
Lafiya Lau.
Meye Kika siyo mun tsaraba?
Tayi Yar dariya kana sauri ne? Ka jira zaka gani Mana..... Ina salalar business dina?
Ba kince zamuje na siya Miki abinda kikeso ba?
Tabbas, Amma dole inji dumus Kuma.....ya kyalkyace da dariya har Yana dukan table....Yan aji duk suka maido hankalin su sai dai ba Wanda kejin me suke cewa.
Watau kiji dumus...... Ta kalleshi tana murmushi eh Mana....... Ashe da gaske ka dawo.... Sukaji magana daga sama kwatsam, duk suka dago *Mufeeda ce* tsaye tana murmushi Tasha wanka..... Ya Dan Sha mur kamar bashine ya Gama dariya Yanzu ba.... Eh na dawo ya kike?
Qalau, ya hutu?
Lafiya.
Dan Allah kazo minti biyu Ina son magana...... Kodai ki Bari sai anjima ko Kuma ki fada anan.
Anjima yaushe.
Evening may be.......
To anjiman zamu hadu, ta juya ta wuce....
Mikewa tayi,
Ina zakije? Ya bita da idanu.
Ta tsuke fuska, daki.
Saboda mufeeda tazo?
Ta dalla mishi harara ta Isa ta koreni ne?
Idan Bata Isa ba ki zauna to, ko don kinji nace Mata anjima? Wallahi don ta kyaleni Ina zata ganni anjima din?.....
Na sani? Ai zata maka waya ko baka zo ba ko?
Wallahi na Miki alkawari bazan dauki wayar ta ba ko da ta kirani.
Kiyi hakuri zauna.......
Ta koma ta zauna. Ya kalleta Yana Yar dariya, saurayin ki ya shiga uku don kina da kishi sosai da sosai.
Tasha mur batayi magana ba.
Wayarsa tayi Kara, Yana dubawa yaga Alh. Murtala. Ya mishi text cewar zai Kira anjima.
Ya kalleta, haka shima Suleiman kike saka mishi doka da horashi Akan kula Mata?
Murmushi kawai tayi tace humm.
Ina ruwana da su? Kawai bana son raini ne?
Kiyi hakuri Zan Mata fada sai ta ringa Baki girma........
Ta kalleshi, ya gyara fuska alamar ba wasa.
Cikin semester din nan Zaki fiddamun gwana cikin su, Aure nakeso gaskiya.....
Saura kadan ta dora hannu a ka.
Ta ce hmm.
Ko bazaki fidda mun ba?
Ta daure ta cije ba tare da ta kalleshi ba tace cikin su wacece tafi birgeka?
Yayi jimmm, ai ruwan ido bazai barni na tantance ba, wace kike ga tafi?
Ta harareshi ban sani ba ta Mike Ina da aiki daki...... Ya gumtse dariya shima ya Mike.
Suka jera kamar ta kwasa a guje tabarshi agun takeji....... Kin San rayuwata Ina son mace wacce Bata da tsoro, .....,..ai shikenan bani ciki kawai, ta fada cikin Rai saboda nikam kamar farar Kura nake don tsoro.........Mai kyau, Mai ilimin addini, wayayya, fara Mai dogon hanci, Mai tsawon gashi, Yar gayu.......shin Wai ni Yanzu Ina ruwana kake ta faman lissafo mun kaje can ka Nemo Mana....
Yayi Yar dariya ke nake fadawa irin wacce zaki nemo mun..... Mufeeda kaje na zabar maka mufeeda ita ce keda duk qualities din da ka zayyano...... Ya Kara gintse dariya mufeeda ba Fara bace Kuma Bata da gashi dogo attach........ Har ma ka sani? Ta zaro ido.......
Eh, Mana kowa ma yasan haka tana boye gashin ta ne?
Mtsew....sai kaje sadeeq ya Nemo maka...... Ke Zaki Nemo.
Tayi murmushi ikon Allah dole ne?
To ai kece babbar kawar tawa ko?
Kema sai in taya ki zabe......Ni an mun miji..... Ya bazga uban tuntube saboda tashin hankali saura kadan ya Fadi tayi saurin tarewa kamar zata taba Shi tace subhanallahi sannu....
Ya Mike idanuwan say duk sun Fara chanzawa daga farare zuwa jajaye.....
Da gaske an Miki miji?
Ya fada Yana gyara takalmin sa, ta kakaro murmushi ta ce aikuwa dai Ina da Wanda Zan aura......
Bai Kara magana ba har suka je kofar gidan.
Ya tsaya kansa juyawa kawai yakeyi, ta fito da Yar karamar leda ta Mika mishi ga tsarabar.....ya kasa Sanya hannu ya karba.
Ta kura mishi ido ya sunkuyar da Kai kasa kawai.
Lafiya dai ko?,
Yayi shiru.
Gabanta ya Fadi...... Anwar lafiya?
Ta Kara fada a hankali .
Ya dago Kai, kirjinta ya buga duk ya wani gigice yayi kicin kicin da rai, ya sunan Wanda Zaki aura?
Ta kalleshi........ Wai shine abinda ya sanyaka damuwa......
Ya Mata wani kallo dole ta kawar da Kai saboda ta tsani kallon banza da rainin wayau.......
Akan meye zai dameni?
Tayi murmushi to naga ka chanza lokaci guda.......
Kaina ne yake mun ciwo.
Ga tsarabar.....ta Mika mishi ledar.
Ya juya ajiye wurin ki Zan karba......
Wallahi bai yiwuwa. Ina ce shine dalilin biyo ni.
Ya kalleta nace ki ajiye Kuma bana bukata.......
Ta tari gaban sa da sauri Wai me ya faru?
Bani wuri in wuce please.
Wallahi baka tafiya sai ka fada mun me ya Bata maka Rai....... ( Cikin zuciya kuwa sai dadi takeji watau Anwar ita yake so yake ta gewaye gewaye. )
Ya kalleta sai ya koma jikin bango ya harde hannuwa ya sokar da Kai .
Kai nake sauraro ta rike kugu.....ya yi shiru.
Ta Fara magana cikin fada fada.
Kace in nemo maka matar Aure na zabar maka ni Kuma bani da ikon da Zan ce Ina da Wanda nake so......... Ke ! Ya daka Mata tsawa.... Na ce kada kiso wani?
Tayi baya da sauri, cikin razana. Ya matso kusa da ita, da kiso wani da ki tsaya haka bai Dame ni ba, I have nothing to do with that, and it doesn't make any difference to me....... ikon Allah ta fada.
Kamar Yana jiranta?
Cikin bacin Rai ta kalleshi, Ni ya dameni ne? Ko mufeeda Shi yasa da ta tare ni tamun rashin wayau na Bari sai a gabanka na Mata warning... saboda bana tsoron ka baka gaba na..... Damko kafadunta yayi da hannu biyu ya buga bayanta da bango....... Wallahi tallahi idan Kika Kara........kwallah suka zubo Mata sharrrr ta fashe ta runtse ido.
Allah yaso duk ba a dawo sosai ba, kofar gidan ba kowa.
Ya runtse ido da karfi ya saketa a hankali......
Ta yunkura zata ruga gida ya tare ta da hannu idan Baki so in Kara taba ki kada ki motsa...... Ta fashe da kuka.... Hankalin sa yayi kololuwar tashi...... Bai San ya Fadi *Na shiga uku ba*
Bilkisu...... Tasa hannu ta toshe kunnuwanta....
Kiyi hakuri Dan Allah na gwadaki ne kawai.
Ganin yadan matsa baya ta yunkura zata Kara guduwa ya kuwa kamota da karfi ....... Yaya Zan ta Miki magana Baki ganewa? Nace idan Baki so na Kara taba ki kada kice Zaki gudu ko daman kina son hakan ne?
Ya fada cikin tsawa.
Ta Kara rushewa da karfi....na tsane ka wallahi bana son ganin ka , ka kyaleni.
Har cikin kasan zuciya yaji maganar. Ya daure yace ....naji kin tsaneni, kiyi hakuri nayi kuskure bazan Kara ba.....wasa nakeyi.
Nima ai da wasa nakeyi ka Fara .......wasa kikeyi ba a Miki miji ba?
Ta mishi banza...... Saura kadan ya Kara kamota don ya rungume ya saki wani murmushi: nasan wasa kikeyi Nima. Kawai Ina son ganin fushin ki ne don Shi kadai nayi missing cikin hutu.......kiyi hakuri I'm sorry ya rike kunnuwa.
Kinji?
Dan Allah kiyi hakuri wallahi bazan Kara ba....
Ta goge hawayen da kasan hijab dinta. Kawai tayi shiru kanta a kasa.
Baki da wahalar yin kuka meye na kuka anan Bilkisu....kina da shagwaba ko?.
Um? Baki magana?
Yau ni Kuma tawa ta sameni an Kara yin fushi Dani...... Dan Allah kiyi hakuri kinji.

Bani tsarabar ya Mika hannu........ Ta maida duka hannuwanta baya ta boye ledar har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login