Showing 39001 words to 41602 words out of 41602 words
suka shiga bashi hakuri da kyar yay shiru sanan yajuyo ya kalli Hassana dake kuka sosai, yace "stop crying, karki kara kuka sabida shi" share hawayenta tayi tass tana haki, sanan yatashi yace "nabaki 24hrs ki yanke decision din dakikeso kinason cigaba da zamadashi ko bakiso" sanan yajuya yakalli Mustapha yace "zaka tafi da ita asibiti ne ko zaka mata treatment anan"? Ahankali yace "zanje nasayo magunguna anan zan mata" gyadakai Baba yayi yace "tom" saikuma yacigaba da masifa yace "koku su Mustapha ban yarda ku wulakanta matan kuba, ba'a rayuwa haka, yaza ayai ku dauko yara daga gatan iyayensu ku auro saiku kawosu kuna wulakanta su kun zaci iyayensu basa sonsu ne eh? Koko basuda gatane? Idan kaji bakason mace ta gundureka ka tsaneta karabu da ita baka wulakantata kana azabtar da ita ba, inna dinna yusrun, shi addininmu fa mai sauki ne, wlh bazan lamunta ba, zaisan yatabamin y'a" yasakai yafice daga dakin fuuuu yaran suka bishi.
_Bari nai amfani da wanan daman namuku tallan clases din danakeyi na matan aure kadai mai suna EROTIC IDEAS, na wanan October._
_Erotic Ideas group na matan aure zalla ne, group ne damuke program guda HUDU aduk sati, ranakun sune ALHAMIS, JUMMA'A ASABAR da LAHADI._
_Duk ranan Alhamis munayin program mai suna MARRIAGE LIFESTYLE, wato ZAMANTAKEWAN AURE, inda nakema mata lectures kan yanda ake zama da miji dakuma dabarun zama da miji, ranan jumma'a kuma muna program din damuke kirada TALK & HEAL wato yi magana ka warke, inda matan aure zasu gayamana matsalolin dasuke fuskanta agidajen mazajen su, zasu iya turamin ta pc idan basuson asansu nisainai forwarding group mu taimaka musu da shawarwari dakuma dabarun dazasubi su magance wanan matsalolin, sai ranan asabar shine ranan LECTURES, inda zan dauki darasi dake dauke da dombin ilimi abu wanda ya dace mata su iya dangane da aurensu, mu koya musu ayi magana akai sosai, sai ranan Lahadi zamuyi lectures akan ilimin daya danganci yanda zaki gamsar da mijinki sanan ki gamsar da kanki, kisaka mijinki ihu agado yana kururuwa yana sambatu, mukoyar dake yanda zakiyi spicing up sexlife dinki, and yanda zaki dinga rayuwa da mijinki kullum kaman sababbin aure._
_Idan kinason shiga wanan group din zaki turo 2000 to 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din, wata daya ne group din, idan kinason ki cigaba da zama duk wata dubu dayane 1000 ne subscription, sababbin zuwa kuma new member zakiyi register is 2k ne, don karin bayani zaki iya tuntubata a number ta 07012181461_
M Shakur ??
Dayake karfe goma ne za'a shiga shari'ar su tun 9:30 duka itada family member ta na court din, tana sanye dawata Oman black Abaya mai bala'in kyau, tana tareda Mama dakuma Hussainanta dasukenan kamanninsu daya da jiya itama ta diro daga Dubai dan she needs to support her sister, saikuma su Baba da Hydar dake wani waje daban har lokacin babu Baban Khalid, karfe goma daidai aka shiga dasu cikin kotu kowa ya zazzauna akai shiru Hussaina takama hannunta tarike ganin duktai wani iri ahankali tace "calm down we are all here with you Hassana" gyadama sister kai tayi tana kakalo murmushi daidai lokacin Alkali ya shigo kotu aka tattashi saida ya zauna sanan aka zazzauna, akai shiru itadai sai tsoron rashin ganinshi take, daya daga cikin ma'aikatan kotune yatashi yabama alkali wani file sanan yajuyo yace "ayau shadaya ga watan Augusta zamuji karane tsakanin Hajiya Hassana dakuma Alhaji Alhassan Bakori, inda Hajiya Hassana ta kawo karan mijinta wanan kotun mai adalcine bisa wayan nan dalilan, bai damu da lafiyanta ba, baya kaunarta, yana wulakantata sanan abinharyakai ga yafara daura hannunshi ajikinta da sunan duka, inda tanaso alkali yaduba wanan lamarin sanan ya sauwake mata yaraba aurenta da Alhaji Alhassan Bakori, yanzudai zamu fara da kiran Hajiya Hassana datazo ta tsaya anan".
Rawa jikinta yafara hakan yasa Hussaina takama hannunta gamgam tace "hey take a deep breath calm down kinji, Allah natare dake" lumshe ido tayi sanan tabude ahankali tareda karanto addu'a sanan taji wani karfi da dakewa yazo mata ahankali ta mike tsaye sanan tafito looking so damn beautiful and matured, tawuce ta tsaya a inda aka nunamata ta tsaya.
Mutumin yacigaba yace "saikuma Alhaji Alhassan Bakori shima ina kiranshi dayazo nan ya tsaya" shiru akayi Hydar da Mustapha suka juya suna duba kotun koyazo amman babushi, sake kiranshi mutumin yayi. "Alhaji Alhassan Bakori" daidai lokacin Baban Khalid yawani danno kanshi cikin kotun yana sanye dawata mahaukaciyar gizna fara da saida takashema mutane ido, sai zuba kamshi yake idan kaganshi zaka dauke president ne, bayanshi kuma Attajiri ne shima yaci gayu sosai yasami waje yazauna kusada Baba yana gaidashi shikuma Baban Khalid yawuce gaba inda akace yatsaya, yana tsayawa yawani kalli Hassana dake tsaye awajenta sanan cikin daga murya da rashin mutunci yace "ke har kin kisa ki kawo karan Alhaji Alhassan Bakori kotu" jikake kotun yay tsit, mutumin dake kiran sunansu yace "Alhaji kayi shiru koma menene Alkali yanzu zai fara shari'a sanan zai bama kowa daga cikinku chance yay magana"
Ko takan mutumin baibiba yana kallonta still, yace "bari kiji nafi karfin ki kawoni kotu kitonamin asiri, Hassana kisani cewa ni Alhaji Alhassan Bakori nasakeki saki biyu!" Jikake tsit, wasu irin hot hawaye taji sun zubomata daga idanu data kasa controlling, sanan yawani tura hannu a Aljihu yaciro envelope sanan yafito daga inda yake yazo har gaban Alkali cikeda girmamawa yace "Alkali yanda Hassana bata sona nima bana sonta banama bukatar ta arayuwata, dan haka gasakinta nan" ya ijiye kan table din ma'aikatan dake nan kafin babban table din alkali, sanan yace "nabarku lafiya inada meeting da shugaban kasa" yajuya fuuuuuu yawuce, kaman dagaske Attajiri yatashi yana kiranshi. "Alhasann, Alhassan kai" yar guduman nan Alkali yadauka yabuga table, sanan yakalli Hassana dake hawaye sosai yace "koma ki zauna" kasa tafiya tayi, hakan yasa dasauri Hussaina da idanunta sukaija tazo takamota tafito da ita, sanan alkali yace "rayuwa kenan" bashi takardan akayi ya warware yabude sanan yace "Hassana mijinki yasakeki saki biyu, babu abinda zan iyayi kuma dan saki kona wasa gaskene balle kuma na gasken, ina ganin da wanan anzo karshen case dinku kenan tunda daman kuma abinda kuke bida kenan" yakara bubbuga guduman sanan yatashi yafice, nan aka tattashi banda su Mama sai lallashinta suke, dama sakin sukeso bawai wani abuba, but yanda yamata sakin rashin mutunci shine abinda yabatawa kowa rai, cikeda neman gindin zama Attajiri yazo yace "wlh Baba gabaki daya bansan case dinnan ma nafaruwa ba, Allah Alhassan baida hankali, ta ina zaitaba samun mata kaman Hassana? Shi baisan rayuwan aure hakuri akeba, kasan bai fadamin ba direbanshi ke sanardani fa, shine da sassafen nan daidai yana fitowa natareshi, ninema nasa yay latti sabida tsareshin danayi da fada, bansan abinda zaiyi ba kenan, dan Allah kuyakuri, zan mishi magana, kuyakuri wanan abu sam sam babu dadi cikinshi" Murmushi Baba yayi yace "karka damu wlh babu komi, haka Allah ya rubuta, kai kutashi mutafi" yay maganan yana kallonsu, dagata Mama tayi da Hassana danji tayi tama kasa tafiya hawaye sai fitowa kawai yake, girgizakai Attajiri yayi cikeda kula yace "Hasdana kiyakuri dan Allah kiyakuri kinji" babuma wanda ya kalleshi suka wuce da ita waje aka sakata amota sukai gida, shikuma Attajiri ranshi fess fess.
KARSHEN MATAN ASOKORO LITTAFI NA DAYA!!!
_Tofah yakuke ganin zata kaya???? Nifa at the point Alhaji Alhassan Bakori nake tausayi bama Hassana ba, dan yamugun tafka uban kuskure, mujedai zuwa_
SAIMUN SAKE HADUWA A LITTAFI NA BIYU DAZAIZO MUKU OCTOBER.
Anan nakawo karshen part 1 din book dinan, nadakatar dashine badan komiba sai final exam dina dazaran fara daga 20th har zuwa 13th of October, M SHAKUR dinku takusan zama graduate ???? kusamin Albarka kumin fatan alkhairi, thank you all so much. And inasonku gabaki daya.
_Bari nai amfani da wanan daman namuku tallan clases din danakeyi na matan aure kadai mai suna EROTIC IDEAS, na wanan October._
_Erotic Ideas group na matan aure zalla ne, group ne damuke program guda HUDU aduk sati, ranakun sune ALHAMIS, JUMMA'A ASABAR da LAHADI._
_Duk ranan Alhamis munayin program mai suna MARRIAGE LIFESTYLE, wato ZAMANTAKEWAN AURE, inda nakema mata lectures kan yanda ake zama da miji dakuma dabarun zama da miji, ranan jumma'a kuma muna program din damuke kirada TALK & HEAL wato yi magana ka warke, inda matan aure zasu gayamana matsalolin dasuke fuskanta agidajen mazajen su, zasu iya turamin ta pc idan basuson asansu nisainai forwarding group mu taimaka musu da shawarwari dakuma dabarun dazasubi su magance wanan matsalolin, sai ranan asabar shine ranan LECTURES, inda zan dauki darasi dake dauke da dombin ilimi abu wanda ya dace mata su iya dangane da aurensu, mu koya musu ayi magana akai sosai, sai ranan Lahadi zamuyi lectures akan ilimin daya danganci yanda zaki gamsar da mijinki sanan ki gamsar da kanki, kisaka mijinki ihu agado yana kururuwa yana sambatu, mukoyar dake yanda zakiyi spicing up sexlife dinki, and yanda zaki dinga rayuwa da mijinki kullum kaman sababbin aure._
_Idan kinason shiga wanan group din zaki turo 2000 to 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din, wata daya ne group din, idan kinason ki cigaba da zama duk wata dubu dayane 1000 ne subscription, sababbin zuwa kuma new member zakiyi register is 2k ne, don karin bayani zaki iya tuntubata a number ta 07012181461_
M Shakur ??
Ahankali Mama takama hannunta tarike tana shafawa tana kallon yanda take kuka saikuma ta girgizamata kai cikeda taysayinta tace "I want you to think this through yar albarka, ke kikasan mijinki, banda haka aure is not do or die, any decision dakika daura, we will support you, kece ke zama da mijinki bamu iyayenki ba, dan haka kiyi tunani mai kyau kinji" gyadamata kai tayi ahankali saikuma tadago kanta tarungume Mama sosai tace "nagode Mama" girgizamata kai tayi tace "karki karamin godiya gabaki dayanku yaranane, Allah yamuku albarka, mezakici naje nadafa miki dakaina" ahankali tace "tuwo damiyan kubewa danye" maidata tayi ta kwantar tace "tom shikenan bari naje" ta tashi tafita daga dakin itama.
Wuraren 12 Mustapha yadawo yashiga mata treatment sanan aka kawo mata tuwonta taci sosai sai bacci, dukansu tabasu tausayi, koda ta tashi da yamma taji dadin jikinta sosai aka sake kawo mata wani abincin batawani ci dayawa ba amman ciwon yaragu sai kanta dake kwankwasa haka suka cigaba da managing lafiyanta.
Bai dawo gidanba sai da magrib, yana shigowa Saudat tafesamai gulma da already direban shima yafara fadamai komi, dudda yaji wani iri amman ko ajikinshi yace bazai kiraba yacigaba da more amarcin shi dudda bini bini tana fadomai arai amman yaki kira.
Bayan kwana uku!
Tana zaune afalon Mama taji sauki sosai Mama na mata tsifa Baba ya aiko Hydar yakirata, gabanta saida yafadi amman tadaure tadauki mayafi tayafa sanan takalli Mama tace "Mama zoki rakani please" Mama bata misaba ta tashi sukai falon Baba, wanda daga Baba sai yayyinta aciki, wuri tasamu tazauna akasa sanan tace "gani Baba" gyaran murya yayi yace "Yan biyu dafarko nabaki 24hrs saikuma dan kaina nakara lokaci, nabari kika sami sauki dan kisamu ki kara tunani da kyau, dan haka inaso ki gayamin gaskiyan komi dake ranki dakuma hukuncin dakika yanke" shiru tayi nadan lokaci saikuma ahankali kanta nakasa tace "Baba kowace diya mace da abinda takeso takuma ke bida agidan aurenta, ni awajena kudi ko yawan dukiya bashine dadin aure awajena ba, kwanciyan hankali, farin ciki, kulawa, dakuma lokacin iyali shine aure awajena, wanda dukansu narasa, Baba Baban Khalid baya sona, bantaba ciwon kai yatambayeni ya jikinba, idanma ina ciwo idan inada sa'a shine zai kwana agidan yaraba daki dani, that's ranan da yan mutuncin shi kenan kenan, idan kuma basanan barin gidan yake yaafi hotel shi baison kamshim mai ciwo, bai damu dayanake ba kokuma yaya nakare, Baba idan zan fadi na buge na kurje agabanshi sannu bazaicemin ba balle ya tashi ya taimakamin natashi, baya kirana, bayida lokacina, Baba bai damu daniba, halayen dayake nunamin ire iren haka da gwaleni dayakeyi yasa I grew out of love for him, Baba, Mama ku iyayena ne idan namuku karya bazanma Allah ba, amman wlh harga Allah Allah yana ganin zuciyata banason Baban su Khalid yanzu ko kadan sabida yanda yake wulakantani, bakuma yaune nadena sonshi ba tunda dadewa, amman nacigaba da zama dashi ina kyautatamai sabida murayu tare kobadan komiba sabida yaranmu, amman at this junction bazan iyaba, yara nakowane kulansu da rayuwansu na hannun Allah ne baniba, shida yabanisu yasan yanda zaiyi dasu, kuma bama kananu bane dazan dinga tsoroba, kuma ko babu komi zan iyama Babansu shaida daya! Itace yanason yaranshi bazai taba wulakantamin su ba, Baba inason karaba aurena dashi bazan iya cigaba dazama dashi ba, zuciyata tagaji dakomi, kayakuri Baba wanan itace iyakan gaskiyata" tunda tafara maganan dakin yay shiru harta gama sanan Baba ya gyadakai ya kalli yaranshi maza yace "ina fatan kun dauki darasi daga maganan kanwarku" dukansu gyadamai kai yayi, Baba yace "wani zubin bakudi ne komiba, mace dakuka ganta anan tanada rauni, mace tafison mijin dazai sota damijin dazai bata kudi, kudi ba komi bane awajen wasu matan, kabama mace time, attention da care kaga yanda zata soka sama da komi, kardan kunzo kunyi kudi kufara wulakanta matanku, mata sun kashi gida biyu ne, akwai mai jure komi kome zaka mata taita jurewa tana shanyewa tana hakura, akwai kuma wacce bazata iyaba data tsaya jurewa tana shanyewa gwara tabarka which is kanwarku dinan dakuke gani, and I am so proud of her, I am so proud of you Yan biyu, Allah yamiki albarka, this shows kodayau zan mutu inada yarinyar dat can take care of herself, ta tsayawa kanta, Nothing beat peace of mind, bazan taba advising koyarda batawaba ta tsaya namiji yabata hawan jini yakasheta abanza yakaita lahira ba No" yabuga kujera yace "mace abuce mai rauni, ana bukata asota ne akuma kulada ita ba'a wulakantata ba, take care of your women mata deserve love, care, and attention, Allah yamuku albarka gabaki daya, kotu zata nemi Baban su Khalid, bayan an raba auren zan baki kudi ki kara expanding business naki, settle down mutuwan aure bashine end of the world ba hasalima is Nothing, kawai ki dage da addu'a sanan kizama mai yawan tsoron Allah kinajina" gyadamai kai tayi, yay murmushi yace "tashi kitafi kinji" tashi tayi ahankali saikuma tajuyo ta kalli Baban nata, batasan lokacin dataje da gudu ta tsugunna gaban kujeran dayake kawai tasa kanta aguiwanshi tahau kukaba sosai, tace "Baba u are the best father in this world, thank you Baba" dagokanta yayi yakai hannunshi yasharenata hawayen kaman wata karaman yarinya yace "I don't take my children for granted, babu wanda ya isa yabanzantar min da my girls, oya dena kukan ya isa haka, kome kikeso ki gayawa mamanki gatanan, ranan visiting din su Khalid kuma zaki kiga yaranki ki musu shopping okay" gyadamai kai tayi yace "to tashi kitafi" tashi tayi ahankali tawuce tatafi duk suka bitada kallo cikeda tausayi dakuma so, Baba ya kalli Hydar yace "start with the procedures, akaimai sallama yau yau dinnan" gyadamaikai yayi yatashi yafita feeling so proud of his Dad, Mahaifinsu wani irin kalan mutumne, tun suna yara yake koyamusu always respect women, mata abin tausayine, abin atausayamusu ne, sanan akuladasu alallashesu, idan kaduba kagani zakaga nafarko daga hakarkarinmu maza aka yosu, to akanme zaku wulakanta su, Baba kan yawan cemusu Annabin mu yariga ya kwatoma mata yancinsu dan haka dole mu daraja su, mu tausayamusu kodan hayayyafomana dasuke yi, Baba always say never hit a woman, Baba nada wani irin believe inhar ka kulada mace, kasota, kabata attention to wlh zata bika kaman kamata magani bazaka taba samin problem da itaba, murmushi kawai yayi yashiga mota yaja zuwa Shari'a court.