Showing 3001 words to 6000 words out of 41602 words

Chapter 2 - MATAN-ASOKORO COMPLETE HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

22 Sep 2024

6107

that cannot even read ABCD to Z, koyanaso tai bala'i dashine dan tasan dagangan yamata haka ohonmai.


Jin ranta na tafarfasa yasa tajawo wayanta daga cikin jaka taciro tashiga dial calls dinta saiko ga number Martala Driver tai dailing number shi, yana tsaye bakin titi suna hirada mai rake dake yanka rake saiga wayanshi tashiga ringing dasauri yatura hannunshi cikin wandon yaciro wayan techno yar rakani toilet, musamman yasa akamai Saving number Hajiya da S shikuma Alhaji da A dan yagane idan takira yana ganin kiranta yadaura hannunshi aka amugun rude cikin hausanshi nayan kauye yace "na shiga uku na lalace, Hajiya" dawani irin gudu yajuya ya kalli asibitin hangota tsaye yasa damugun sauri yajuya yasake tura hannu cikin aljihu yaciro wata 500 yamikama mai raken yace "kai bani Hajiya ta tafito, yau nidai nasan na shiga uku" baima jira cewanshi ba ya fizge ledan yawuce, Mai rake yace "ga chanjin ka kabari" titi yashiga da gudunshi yace "nabaka" da gudu ya tsallaka titin ya shiga asibitin duk tana binshida mugun kallo, yana karasowa gabanta ko wata wata baiyiba yawani irin zubewa agabanta yace "Hajiya dan Allah kiyakuri, wlh nasan kinsha gayamin muka fita na tabbatar ina cikin mota idan kinfito, tuba nake Hajiya, Allah yahuci zuciyanki, Allah ya sanyaya kafadunki, tubanake Hajiya" ayanda takejin haushi zata iya shureshi da kafafunta tadai daure cikin fushi tace "my friend will u stand up and open car for me" dasauri yace "eh Hajiya mekikace"? Wani irin runtse ido tayi cikeda takaici tuna bamaya gane turenci, dan dagokai yayi ya kalleta ganin yanda tayi yasa yace "dan girman Allah kiyakuri Hajiya wlh daman rake nasayo miki wlh" yamikamata raken dake leda, bude idanunta tayi tadakamai tsawa. "Murtala katashi kabudemin mota nabar wajen nan!" Abirkice dukya rude yatashi garin hakama yasaki ledan raken suka watse awajen tabishi da mugun kallo dayasa yatashi da sauri yatura hannu a aljihu yaciro hadadden car key sanan yadanna lock tabudu, kafin yabude kofar owner sit yasaukarda kanshi kasa yace "Allah yahuci zuciyan Hajiya, tuba nake matan ranka shi dade, takawanki lpy uwargijiyata, shiga muje" mtswww taja wani wahalallen tsaki tajuya tashiga cikin motar ahankali kanta na mugun sarawa yamaida kofan yarufe, raken daya watse awajen ya kalla har ranshi soyake yatsugunna ya kwashe kayanshi amman tsoron masifan hajiya yake, bude gaban motan yayi ya shiga ya rufe yaja sit belt yasaka saikuma ahankali yaleko bayan sit din ya kalleta kanta na kasa tana kallon wayanta datake latsawa kaman mara gaskiya ahankali yace "Allah huci zuciyan Hajiya" dagokanta tayi tazubamai red eyes dinta dahar lokacin suke nuna alamun kuka, hakuri zai batafa amman ganin yanayin idanunta yasa dasauri yace "Hajiya kuka kikayi? Innalillahi maiya sameki anmiki wani abu a asibitin nanne? Waya batamiki rai eh inje inkoyamai hankali wlh saina barar da mutum na shemar dashi, waye ne Hajiya"? Yanda taga yadamu sosai danya nuna afuskanshi yasa har ranta saitaji dadi, dan yatsine fuska tayi cikedason yamata shiru dakuma tarin gajiya tace "nagaji ne kaini gida kawai nahuta Murtala" da sauri yajuya yatada motar yajada sauri yace "Hajiya sannu, kinga baki saba wanan aiki hakaba, keda kikeda likita dayake zuwa har gida yadubaki maisa kikazo asibiti nan kikabi layi saisa kanki keciwo, sannu Hajiya, Allah huci zuciyanki, yanda kikagajin nan bazanbi hanyar zuwa ASOKORO ba dan akwai go slow, akwai wata short cut hanya dazanbi yanzun nan zakiga munkai ranki shi dade".



Chat me up directly by clicking on this link
https://wa.me/+2347012181461



_This is the only free page of this book, like I said, wanan novel din bakaman normal novel dina bane, I interviewed so many couples, I want to show the world inda akafi samun matsaloli arayuwan auren mu tayau and how to go about it. I trust my fans, u all knows yanayin rubuta, ku gyara zama, wanan littafi shine ga darasi gakuma dadi, lemme say it again please ??, anybody less than 18 shouldn't read this book, thank you._

Chat me up directly by clicking on this link https://wa.me/+2347012181461


_This book is 2k, idan kinaso pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank and send evidence of payment to my watsapp number 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting_?? _MATAN ASOKORO_ ??


?? _MATAN ASOKORO_ ??





???M SHAKUR

_RANAKUN POSTING *SUNDAYS*, *TUESDAYS,* *FRIDAYS*_


_DAN GIRMAN ALLAH KARKI KARANTA THIS BOOK IN BAKI BIYABA, KUJI TSORON ALLAH_



EPISODE 2??

Ko alamun taji magananshima batayiba saima cigaba da danne dannenta datayi awaya tana chatting a group dinsu na ASOKORO WIVES, gajiya tayi saikawai ta ijiye wayan sabida yanda kanta kewani irin sarawa datarasa maisa, sanan gently ta jinginar da kanta jikin kujera ta lumshe ido. "Hajiya wai lapiyanki kalau"? Bude idanunta tayida sauri jin Murtala yasake mata tambaya ta madubin mota suka hada ido dan gajeren wahalallen tsaki taja tamaida idanunta ta lumshe su ahankali back, maida hankalinshi yayi kan tukin harsu ka shigo ASOKORO District, Usman katsina street suka shiga yay horn agaban wani makeken mansion da tsayawa bayaninshi aikine ganin ba'a bude gate dinba yasa yace "auuuu kullum saina manta abin nan" yay maganan yanadan juyowa ya saci kallon Hajiya yaga tana kaman bacci danhar lokacin idanunta a lumshe yasan inda idanunta biyu datamai bala'i kan kullum saiya mantada remote din da ake bude gate dinsu dashi, remote din dake motar yadauka ya danna gate din yabude sanan yasa kan motan suka shiga cikin gidan gate din yarufe kanshi, kafin ahankali yabude kofa yafito sanan yazagayo ta bangarenta yabude kofa tareda bending kanshi cikeda respect yakira sunanta ahankali danya tadata daga bacci. "Hajiya, Hajiya" dan bude idanunta tayi ahankali tazubasu akanshi awulakance, baidamuba yace "mun iso gida ne daman saisa natadake" yunkurowa tayi tanajin kaman kanta zai fice amman saita daure tafito hakan yasa shima ya matsa yakoma baya, fitowa tayi daga motar ta tsaya da kyau da sauri tasake kulle idanunta jin wani irin jiri take gani hakanan all of a sudden, hakan yasa Murtala daya koma baya yace "Hajiya karkice nacika tambaya amman kaman bakida lpy wlh, duk jikinki ya nuna hakan" bude idanunta tayi tazubamai wani matsiyacin kallo dayasa yaji cikinshi ya murda ahankali yamaida kanshi kasa, daukekai tayi tace "kwasomin jakata da wayata" tai maganan sanan tajuya tafara tafiya gashi daganan parking space zuwa flat dinta dadan tafiya, amman hakan take tafiya ahankali dai dai gudun kartaje tazube dan bamatasan meke damuntaba jitake kaman sauran kiris jikinta yakasa daukanta, akwai staircase haka dazai sadata da kofan shiga flat dinta ahankali take hawa staircase din cikeda karfin hali irin nata da kyar ta iya daga kafanta tahau na karshe batasan meya faruba tadaijita akasa sharaf, sanan kuma taji ihun Murtala sama sama, kara lumshe ido tayi tabude sanan taga Murtalan agabanta ya tsugunna ya haukace yakasa tabata sama sama takeji yana Hajiya, Hajiya, sake lumshe tayi tabude batasan meke going on ba tadaiga waya akan kunnenshi saikuma kawai taji yadauketa, kadan kadan take bude idanunta she could feel and see yanda heart dinshi ke beating, ke racing sosai na fargaban kar wani abu yasameta saikuma dip ta dauke wuta.


Kwantarda ita yayi akan katafaren doguwan kujeran dake falon cikin jerin hadaddun kujerun dake wajen, sanan yatashi da sauri hannunshi har rawa yake ya shiga dailing number Alhaji for the second time yamugun damu dudda yasan Hajiya was never nice to him but still baisan wani abu yasameta.......



Wajen 30 big men ne zaune awani babban conference room, sunci uban suit, wani hadadden magidanci mutum dake zaune kan kujeran CEO ne ke magana yana bayani da turenci, ringing dawayanshi yasakeyi for the forth time yasa yakalli wayan, daukan wayan yayi a hannu yatashi tareda fadin "excuse me" sanan yafita daga conference hall din yakara wayan akunnenshi, kafinma Murtala yay magana yashiga balbaleshi da masifa. "Ka kirani kace tasuma nace ka dauketa ka shiga da ita ciki zan kira Dr, basaika jiraba, saidamuna kake da kira kasan wani irin meeting nakeyi ne? Kaiwani irin wawan bakauyen yarone wai? In nagama I will call d Dr yazo yadubata, kawai yanzu ka tsaya tareda ita, karka barta ita kadai, babu abinda zai sameta ai Hassana is a strong woman she will be fine" ya katse wayan zai maida a aljihu saikuma yaciro yama kashe wayan gabaki daya dan yasan Murtala baida hankali he will keep calling him this meeting is very important anjima idan suka gama zai kira Dr su yasa yaje yadubata, da sauri yawuce yakoma ciki wearing a smile akan face nashi yace "sorry gentlemen let's continue"......




Jikin Murtala har bari yake gabaki daya yama rasa maizaiyi gashi babu kowa gidan, dan ka'idan su shine ma'aikatansu basu kwana, da maid, gardener da sauransu duk dasafe suke zuwa suyi aiki sutafi, koma sunanan shibaisan mezaimataba, yana tsaye kanta chan yaga tai wani irin nishi ta bankare ta tashi, saikuma tafara Jan numfashi kaman numfashinta naso yadauke tana kakkama wuyanta, tsugunnawa yayi gaban kujeran cikeda damuwa yana tura hannunshi a aljihu yana ciro wayanshi zai sake dailing number Alhaji yace "Hajiya meke damunki na shiga uku, Hajiya badai mutuwa zakiyiba" ina Hajiya bamatasan wayeke akanta ba, yay dailing number kashe, sau uku yana kira wai akashe daidai lokacin tafado dagakan kujera tana nishin idanunta na kakkapewa shibaimasan meyakeba kawaidai yaganshi ya dauketa ko nauyinta bayaji yafita da ita daga dakin yawuce yabude mota yasata yagyaramata kafafuwa yarufe sanan yashiga gaba danna remote yayi gate yabude yasakai yafice aguje yana tuki yana juyowa yana kallonta yanda yaga tana battling da numfashi yasa kawai yasaki kuka. "Hajiya kiwa Allah karki mutu, kar yan biyu sudawo Marayu wayyo Allahna" kawai shima yahau kuka kaman yaro, wani babban government asibiti dakenan a ASOKORO yakaita yay parking yana kuka sosai yay cikin asibitin yana ganin wani Dr yafito shida nurse kawai fizgo hannun Dr yayi yana kuka sosai, Dr ma tsorata yayi dan yadauka mahaukaci ne yace "Malam lafiya"? Cikin kuka Murtala yace "Hajiyata batada lpy likita zoka taimaka mata dan Allah bata iya numfashi" jin maganan dayayi yasa Dr yabishi Nurse din dasuke tarena binsu har motansu yakaishi yabude Dr naganin yanda takeyi yama nurse alamu data kawo gado dasauri nurse tajuya shikuma Dr yashiga motan trying to help her yabude mata baki yana tambayan Murtala dake kuka har lokacin yace "meya sameta"? Cikin kuka sosai yace "kaman kanta keciwo saita sume saikuma tafara nishi haka" daidai ankawo gadon da za'a daurata, kallon gadon yayi ya kalli yanda Dr da Nurse ke kokarin cirota su sakata agado yace "ina zaku kaita"? Dr da hankalinshi baya kanshi yace "ward mu mata treatment" dasauri yace "likita karufamin asiri kabata magani anan cikin mota kokamata allura kawai mutafi yan gidansu basa kwanciyan asibiti sunada likitansu na gida, yanzu ma babu kowa agidan ne" likitan baimabi takanshi ba dan daga gani kasan illiterate ne, idan yabar matarnan within good 10min heart dinta zai daina aiki tamutu dan as it is ma yanzu heart dinta is very weak, ciki sukaida ita Murtala nabinsu abaya yana gayamusu zasu sashi a matsala, suna shigarda ita emergency room suka rufo kofa hakan yahanashi shiga, zama yayi akasan wajen yana share hawaye na tausayi dakuma fargaban irin fadan dazaisha awajen Hajiya da Alhaji yau yamusu asalin karambani wlh.



Yana zaune wajen wata nurse tabude kofa tafito yana ganinta yatashi da sauri yace "Ya jikin Hajiya"? "Da sauki, yanzu munsamata oxygen and per hour is 15k, yanzu anaso kai deposit din naira dubu hamsin" da sauri ya kalleta yace "eh dubu hamsin" gyadamai kai tayi tace "yes inba hakaba bazamu cigaba da treatment dinta ba, yanzu dai ansamu munyi stabilizing situation din idan kabiya kudine zamu cigaba" shiru yayi kaman wawa saikuma yace "kucigaba to bari naje nadauko kudin agida" Nurse din tace "you have an hour daga yanzu zuwa Magrib" juyawa yayida sauri yafita yaciro wayanshi yana dailing number Alhaji amman har lokacin akashe, rasa yanda zaiyi yayi yawuce yakoma mota yaja motar yakoma chan gidan, bangarensu boysqutars dakinsu yawuce direct, wata katuwar ganamasgo yayi yabude sanan ya shiga cirowa yana ijiyewa kan katifa sanan yaciro watayar leda baka yakoma gefe ya zauna yabude ledan albashinshine dayake cirewa yayi saving duka duka 80k ne yamaida ledan ya kulle sanan yatashi yafito daga dakin dasauri lokacin ana shirin kiran salla komawa asibitin yayi yabiya kudin komi yarike sauran 30 a aljihu sanan yatafi masallaci kafin yadawo yasake samun wuri gaban dakin ya zauna yasake ciro wayanshi yay dailing har lokacin wayanshi akashe abin yabatamai rai amman kuma meruwanshi shidan aikine tashi yayi yawuce masallaci jin ana kiran isha'i yayi yafita waje yaje yasha shayi da indomie sanan yadawo yasake zama awajen shiru babu wanda ya cemai wani abu har bacci yasake kwasheshi yay kwanciyanshi kan yar kujeran yana sharara baccin shi gwanin ban tausayi kana ganinshi kasan yagaji.....





Kaman an tsikareta tabude idanunta ahankali tanabin inda takeda kallo tabbas tasan nanba gidanta bane, ahankali tajuyarda kanta karin ruwa datagani dakuma oxygen da akai hanging datagani yasa ta lumshe ido dan tagane she's sick but inane nan? Yunkurawa tayida kyar ta tashi tazauna tanadanjin jiri kadan, sanan ta kakkalli gefenta but babu jakanta babu wayanta balle takira wani, sakebin dakin asibitin tayida kallo taga emergency room ita kadaine aciki nothing to talk about wanan wani irin local daki takene, jitayi warin asibiti da dakin keyi na irritating nata yasa cikeda karfin hali irin nata ta yunkura tasauka daga kan gado tana zura takalminta takama karfen da ruwan kejiki dasauri ta lunshe ido, ahankali taja tasaka hannu tabude kofan tafita tana tafiya kaman zata fadi, tabi wajen dakallo babu kowa a wajen kaman ance ta kalli side dinta Murtala tagani ya kudundune jikinshi kan kujeran wajen yana bacci yana sosa hannu daga gani kasan sauro ke cizonshi, tsareshi tayida idanu ranta nabaci mesa zaikawota irin wanan asibitin, wani irin sarawa kanta yayi sabida bacin ran dataji saikuma wani irin mahaukacin jiri yazomata tai baya zata fadi tana kokarin rike karfwn da ruwanta ke sagale shikuma yabugi bango yay lara hakan yasa firgigit Murtala yafarka tareda dagokanshi ganin Hajiya idanunta na juyawa tana kokarin faduwa but tana kokarin hana kanta yasa yawaniyi tsalle yace "Hajiya" tareda tarota tafada kan kirjinshi, ko kawo wani abu baiyiba kawai yadauketa chak dukya rude sanan yaja karfen ruwan yabude dakin yace "mesa kika fito Hajiya aidakin kirani" ahankali tabude idanunta tana kallon fuskanshi yanda damuwa yanuna ko'ina akan fuskan, kirjinshi nabugawa fat fat fat tsoron karta fadi dayaji yasa taji something that is very very strange azuciyanta, she just wish and wish inama Baban Khalid ne haka looking so worried and so concern about her datafi kowace murna aduniyan nan. "Hajiya!" Firgigit tafarka daga tunanin dataje ashema harya zaunar da ita kan gado, cikeda damuwa yace "menene kikeso maiyasa kika fito tsakar daren nan? Jirifa ke mugun damunki? Meke miki ciwo yanzu? Nakira Dr"? Tunda yakemata tambayoyin take kallonshi saida yagama sanan tahade rai tace "ubanme nakeyi awanan kazamin asibitin? Wayakawoni nan?" Shiru yayi yasaukarda kanshi kasa shidaman yasan yayi laifi. "Ina maka magana kamin shiru Murtala!" Tadakamai tsawa dayasa tasake kama kanta dasauri jin kaman zaifita tace "wa....." ganin yadago kanshi ya kalleta yasa tahadiye sauran wash din tai maza ta cire hannun tasake daure fuska zatai magana yace "Hajiya dan Allah kiyihakuri kinji, bakida lafiya baki bukatan hayaniya da fada ko fushi, kinajin sauki zan gayamiki komi kinji Hajiya" ahankali tajinginar da bayanta da bango tanadan yatsine fuska tace "ka kira Alhaji? Meyasameni, mesa kakawoni nan"? Yanda tamai maganan babu wasa yasa yace "kina sauka akan mota kika fita kin fara hawa stairs kawai naganki akasa kina wani irin nishi........." nan yagayamata komi har zuwa yanzu, dan murmushi tayi tace "ayya meeting din must be very serious, jeka kiramin Dr" tai maganan kaman bakomi da sauri yafita daga dakin, daidainan hawayen data rikesu tunda yafara gayamata abinda yafaru yazubo mata sharrrr yanzu inda ace Murtala bai kawota wanan kazamin asibitin ba dahaka zata mutu abanza, Baban Khalid bai kira Dr ba saima kashe wayanshi dayayi irin ko ajikinshi dinan, baimaso adameshi da batun rashin lafiyanta yana aikin office, Baban Khalid Mijine wai ko Makiyi? Ta tambayi kanta! Jin alamun tafiya yasa da sauri ta share hawayenta tass, daidai anbude kofa Dr yashigo Murtala biyedashi yana kallonta yace "Hajiya kuka kikayi"? Wani irin mugun kallo tamai tace "fita daga dakin nan zanga Dr" babu gardama yajuya yafita yarufomusu kofa, Dr yay murmushi yace "why are u treating someone that saved your life today like this"? Murmushi yayi yakaraso gabanta yana gyara karin ruwan yace "I understand he's your driver, but koma a direban ne i must applaud his effort, I am telling u dabadan guy dinan ba we would've lost you by now, at the time daya shigo dake this hospital inda ace kin kara just 5min without seeing a Dr da heart dinki yadaina aiki, haka yashigo dake he was crying sosai" dasauri ta kalli Dr tace "crying"? Murmushi Dr yayi yace "abin yabaki mamaki ko kema, aiko kuka sosai kaman yaro wai dan Allah mutaimaki Hajiyan shi, ya tsareni wai a mota zan miki treatment baki zuwa asibiti da kyar fa yabari muka shigodake that zakiyi fada" for the first time tadansaki murmushi iya lebe, saikuma ta kalli Dr tace "what is wrong with me Dr, maisa nai passout like that"? Kujera Dr yaja yazauna sanan yace "kinada wata damuwa ne, is there anything wrong with you or bothering u"? Wani kallo tamai saikuma ta tabe baki tace "ni babu abinda kedamuna, namaka kala damai damuwa ne kakemin wanan tambayan" shiru Dr yayi yana kallonta, daga this magana datayi yagane yes tanada damuwan but she's the hard and strong type no need to even pressure her bazata fadimai ba hakan yasa yace "some of your results are out, some kuma sai gobe dasafe, kinada hypertension, and heart dinki at this junction is very very weak, bawai kinada ciwon zuciya or anything bane no! Just that heart dinki is weak, dole ki kulada kanki tsantsa dam at any point u can just collapse kimutu, dole kicire ma kanki damuwa, you should

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login