Showing 24001 words to 27000 words out of 41602 words

Chapter 9 - MATAN-ASOKORO COMPLETE HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

22 Sep 2024

6113

ranta yagama yadda nurr d'in nan budurwarce"da ita yakeyin waya"Dole tasanar wa mommy sbd tayi wani abu akai.gaba d'aya hangosa take kwance kan 3seeter Yana waya dg shi sai vest d boxer..ta lumshe ido tana ayyana yadda zataji dad'i idan ta auresa.

Nurr kuwa zafi taji aranta sosai"dama yanada Mata betab'a sanar Mata ba"wata zuciyar tace"to ke Ina ruwanki da matarsane?meye naki najin zafin.... ringing d'in wayar yakatse mata tunaninta.kamar kada yad'aga tadai daure ta d'auka.

My nurr kina jina?"

"Uhumm!

kina tambayar inada Mata ko?

Da sauri tace".eh"

Yana murmushi yace".ah ah nibbu wata macen Dana tab'aji ta burgeni saike kawai"yarinyar nan dakikaji ta kirani da Yaya"kanwata ce uwa d'aya uba d'aya.ajiyar zuciya tasaki ab'oye"kafin tace".hmmm!nikawai ma ke burgeka to meyasa? nima bazan iya ganewa ba my nurr!Wai sadaukinah kana nufin bakada budurwa? tafad'a tana dariya k'asa k'asa.hmmm Allah yakyauta mun yin wata budurwa.wannan sai Mubarak(sir Mubarak) to meyasa sadaukinah?bbu komai my Nurr"kokinaso nayi budurwar?hmmm kabari sai lokacin dakamun aure saikayi taka budurwar...gabansa yaji yafad'i sosai ,ga haushi yaji na maganarta.wanda yarasa dalilin jin hakan.sadaukinah !uhumm inajinki my Nurr"aure kikesone?lahh nifa wasa nakeyi bayanzunba.ah ah inkinaso fad'amun naji waye saurayin naki ko?"yafad'a Yana jin fad'uwar gaba.fatansa tace". bbu saurayin datake dashi.cikin turo baki tace".nima kamar yadda bakada budurwa to nima Banda saurayi..to shikenan hakan yafimana ko my Nurr? eh Mana"yanzun Kinga 10 ta wuce da asuba zankiraki kitashi sallah.to sadaukinah nagode.karki damu kikularmun da kanki"insha Allah"tafad'a tana kashe wayar.

Ajiyar zuciya yasaki"Yana tunanin abubuwa masu yawa dayakeji ko yake tsintar kansa dashi akan nurr"Amma zai yiwa Mubarak wasu tambayoyi akan abubuwan dayakeji game da itah...

Nisaibah kuwa"tana zuwa tasanarwa da daddy amsar sir faruq ta wuce bed room d'in mommy.

Harma tafara bacci "Amma Saida Nisaibah ta tayar da ita... cikin damuwa tace"wlh mommy Yaya soyayya yakeyi da wata yarinya NURR! Toke tayaya kikasan hakan?"yanzun daddy ya aikeni gunsa ,shine nasamu suna waya da ita wlh.mommy tace"karki damu kibarni dashi"mommy abin nan fa abin dubawa ne"Ina zaton kamar fa yarinyar d'alibarsace"sbd naji Yana cewa gobe taje skul da wuri kartayi latti...to indai hakane Dole gobe kije skul d'in kibinciko Mana ita ko y'ar gidan uban wacece ita.dole tarabu dashi wlh"zankuma mishi barazanar Zan tsine mishi albarka koyarabu da ita.to mommy kinsan tsinuwarki bazata iya binsaba tunda bakece kika haifesaba.

Eh Mana"sbd natsoratar dashine Mana"to Kuma in dg baya kuka bijiro Masa da maganar aurena"bazai Miki kallon Maison kantaba....hakane Kuma kinyi gsky"yanzun kibincika yarinyar"inhar Yar gidan matsiyata ce.to Kinga saina fake da hakan nace yarabu da ita.kuma Mije gidansu muyi Mata barazana itada iyayenta. dole tarabu dashi"abinda yasa yanzun bazamu yarda muce ya aurekiba.sai kingama matsewa sosai sbd zubar miki cikin da akayi.inkuma kinje kinsake bawa wani kanki ke kika sani"munaso nan da wata 5 haka.lokacin zakiyi service naki sai asaka ranar aurenku ko?"eh wlh mommy hakan yyi.kwanciyarta mommy tayi ,itakuma ta wuce nata d'akin da d'okin safiya tayi take skul d'in su nurr...

Washe gari....??[9/9, 2:08 PM] Maman Nasreen: *washe gari*
cike da d'oki nurr ta shirya.tanata zuba k'amshi yanzun har wata y'ar kiba tayi sbd kulawar data ke samu agun sadaukinta.tasaka suit nashi awata leda"ta fito dg gidan.nafef ta hau sbd tayi saurin zuwa tunma 7."tana isowa office nashi ta hango abud'e"skul bag nata takai class ta ajiye. kafin ta fito ta nufi office nashi....sir faruq kuwa har mafarkin nurr yyi jiya"da wuri yashigo skul d'in sbd kawai yaganta.amma dayaga alamar batazo ba"ya wuce office nashi yad'auki wayarsa yafara k'ok'arin kiranta..saidai yaji wayar akashe"my Nurr kodai kintaho ne?naso ace abud'e wayar take dasai naje nad'akkoki kawai.yafada afili shi d'aya"Yana tsaye gaban table nasa"gefen window yakoma Yana k'ok'arin bud'e window d'in yaji siririyar muryarta tayi sallama"juyowa yyi suka had'a ido"atare suka sakarwa juna murmushi...tana k'arasowa ciki tace". sadaukinah Ina kwana?"lfy qlau my Nurr"yanzun nakiraki naji wayar akashe"eh nabarta agida ne shiyasa.okay kizauna mana Aida sauran kusan 35 minit akoma class tunda ba'a assembly.zama tayi kan kujerar kusada table d'in"ahankali tace".kaima sadaukinah kazauna Mana"zama yyi Yana murmushi yace".my Nurr inafatan kinyi karatu sosai?sbd Kinga nine foamaster naku"Kuma nizanyi invigelating naku"nasani Mana sadaukinah.nayi karatu sosai insha Allah bbu damuwa"paper d'in ka za'a yi after break ko? eh itace"Kuma zanyi Kuma kamun masu satar amsa.to nidai bazance komaiba"gashi kayan aro"tafad'a tana ajiye mishi ledar da suit nashi ke ciki ta bud'a"murmushi yyi yace"ni wlh nama manta da ita my Nurr"kokinaso nabakine?um um wlh taya zansaka wannan? tamun yawafa"tafad'a cikin shagwab'a.inyeee!nurrin sadaukinta"shagwab'ar tamiki kyaufa.rufe idanunta tayi tana murmushi"nifa gsky banason wannan kunyar taki gsky"to ai kunya adoce ga mace sadaukinah"hakane my nurr!wai yaushe zamuje agyara Miki gashin ki?"sai mungama exams"ok to shikenan"meyasa bakyayin lalle?banaso ne(ta b'oye Masa ne..qda tanama ta abinda zata sawa cikinta ta Ina zata sami damar yin wani lalle) to nikuma inaso naganshi ahannunki da k'afafunki"shikenan insha Allah zanyi maka idan angama paper.... k'ok'arin mgn yakeyi Nisaibah ta shigo cikin office d'in bbu ko sallama...da ido ta tsare nurr tana kallo tamkar me nazartar wani abu"K!lfy zaki shigo bbu ko sallama?wani abu yafarune agidan??"duk sir faruq ya tambayeta fuskarsa agimtse.yyinda itama nur ta kalleta sau d'aya taji gabanta yafad'i.nisaibah kuwa gabanta yafad'i sbd ta tsorata da kyawun yarinyar...kayi hakuri Yaya dama mommy tace"nazo na karb'i key d'in motarka zata aikeni.. tafad'a tana k'ok'arin had'a ido da nur"ita kuwa nur d'auke kanta tayi batasake kallon nusaibah ba...Kinga motata b
bata sa'anki bace"kije gun driver yakaiki ko ina kike so Mana... shikenan Yaya na wuce"bece komaiba"juyowa tayi had'e da cewa nurr!da sauri nurr tad'ago kanta suka had'a ido.adedenan akayi ringing d'in tafiya class"Nisaibah batace komai ba" ta juya tafita sbd tagane wannan itace nurr d'in dayakeso"sir faruq kuwa yasha alwashin zata gane kuranta namishi shishshigi"sbd yagano tsabar jin gulma yasakata Kiran sunan nur"sbd tagane idan itace nurr..kallon nuratu yyi wacce keta mamakin wannan budurwa data fita..my Nurr kitafi class ganinan zuwa zanje na amso Question paper naku.dato ta amsa tana tashi ta fice dg office d'in.

Nisaibah kuwa bata tafiba ashe"saima wata SS 2"ta tsayar tana tambayarta tasan wata nurr?"tace ah ah"kafin nisaibah tace wani abu nurr nafitowa dg office d'in"ta nunawa wadda suke tare itah"tace"kinsan waccan yarinyar?lubna tace"eh mate d'in muce sunanta nuratu ai...yauwa ga wannan amma fad'amun sunan anguwarsu.nisaibah tafad'a tana mik'a Mata dubu 1"da sauri ta karb'a tana jin dad'i"kafin ta sanar mata, da Mata kwatance. sbd anguwarsu guda da nuratun..da sauri Nisaibah ta wuce sbd hango sir faruq yafito Yana rufe k'ofar office nashi...

Masha Allah paper tayi sauk'i alhmdllh"Kuma yamusu tsanani Gurin invigelating d'in"

Koda aka fito break k'in fitowa nurr tayi sbd bataso yace tazo suje skul shop yasiya Mata wani abun.

Lokacin da aka koma break kuwa"sir faruq harda dorina yashigo ajin "bbu mutunci ,fuskarsa agimtse ya shigo yabawa nurr Questions papers d'in ta raba"sannan akayi tsit kowa yaduk'ufa rubuta abinda yasani"yyinda barira gabanta keta fad'uwa sbd ba duka ta iya amsoshinba"nurr na lura da ita saida tagama tukun"taciri gefen Question paper d'in ta rubuta Mata kamar haka
*ki kwafi inda baki ganeba"amma kibi asannu sbd sir*
Tana rubutawa ta faki idonsa ta ajiye kan cinyar barira.ajiyar zuciya barira ta saki tana k'ok'arin d'an kwafan abinda zata iya sbd tana tsoron Kar sir faruq yaganta...

**************
Alhassan kuwa yakasa samun nutsuwa akan soyayyar nurr .balle yanzun yadda yaga kyanta ya bayyana.tazama cikakkiyar budurwa.gefe guda Kuma har yanzun Yana barikinsa"sbd yanada yawan buk'atar mace.amma iyayensa sunk'i mishi aure sbd sunfiso yagama karatunsa.duk abinda sir faruq yamasa bawai mantawa yyiba"yabarshine saiya mallaki nurr sannan yamaida mishi da murtani.sbd Saida yyi bincike yagano ashema yasan sir faruq d'in.

Da wuri yashirya ya nufi anguwarsu su nurr"aka kuwayi sa'a baffa ado na nan lokacin daya aika amishi sallama dashi..
Baffa ado cike zumud'i yafito k'ofar gidan"alhassan yarusuna Yana gaidashi"baki washe yace"ah ah tashi tashi"dama Kaine ke tafe?ai nuratun ma tatafi wannan k'addarar rar makarantar ta boko.alhassan yace"bbu komai baba ga wannan ayi cefane....zaro ido baffa ado yyi sbd uban damin kud'in da alhassan yamik'o mishi"hannuwansa na kirma ya amsa Yana cewa ayi haka kaikuwa?bbu komai baba indai zaka bani dama na auri nurr" ashirye nake danamaka abinda yafi wannan ma.bakada matsala yaro nabaka nuratu har abada katuro magabatanka"nagode baba "Amma inaso kayiwa wannan saurayin nata mgn yadena zuwa gunta...yo ai bana zaton sonta yakeyi ai malamin sune aboko...d'an Jim alhassan yyi Yana tunani"saikuma yace"amm baba yanzun inaso mudaidaita kanmu nida ita tukum saina turo magabata na.baffa ado yace"hakan yyi kyau"yanzun anjima saika dawo tad'i ko? alhassan na murmushi yace" to baba nagode.sallama sukayi ya wuce da nufin yadawo anjiman...baffa ado yashige gida cike da farinciki"Amma har ransa yanajin shakkar sir faruq, musammun akan abinda yayiwa alh tukur"hakan yasa shi jin tsoro ,yanzun ko dukan nur yadena.yanajin bazai iya yiwa sir faruq mgn ba wai yadena zuwa gun nurr...

Su nurr kuwa itace tafara submitten"sir faruq yasakata ta k'arb'i nakowa"shikuma Yana zaune yanamata kallon k'asan ido"komai nata burgesa yakeyi"atsarinsa bayason farar mace irinsa"gashi ita black beauty ce"yalura nurr Bata cika yadda suna had'a ido dashiba"koma sun had'an zatayi saurin d'auke kanta"Yana lura da ita sai idan Yana latsa waya ko Yana note jikin Allo take kallonsa.kunyarta da kawaicinta had'e da batada son abin duniya"sunfi komai burgesa sosai ahalayenta"ayanzun haka soyake da anyi hutu suka dawo last term sukayi exams d'in shiga SS 3 zai maida ita private skul ta Ida SSCE d'inta acan...kallonta yyi lokacin dayaga saura mutum 1 zata bada paperta duk sauran members d'in class sunyi submitten sun fita.satar kallonsa tayi..caraf suka had'a ido"murmushi suka sakarwa junansu atare.bayan ta gama karb'a tace"sadaukinah gashi !konakaimaka office?saina wuce gida..um um tare zamuje namaidake da kaina...turo baki tayi cike da shagwaba tana nok'e kafad'ar ta tace".wlh anfara samana ido dg y'an anguwarmu har y'an skul d'in nan...tab'e baki yyi had'e da cewa susuka sani"bana tsoro ko shakkar kowa idan natashiyin abu.duk Wanda yafassaramu da wani abu"damuwarsace"hakane sadaukinah Amma pls kabarshi nahau adaidaita Mana"nagama mgn my Nurr nizankaiki gida na ajiyeki titin farko kafin ashoga layinku"is okay?to sadaukinah nibazan yi musu dakaibah"yauwa my nurrinah!Amma meyasa yau bakice nayi kyauba?"yafad'a fuska bbu walwala.kallonsa tayi"dariya ta tuntsure da ita" har fararen hak'oranta suka bayyana.yana kafeta da ido Yana kallo"cike da burgewa"hmmm! sadaukinah banace kafi kyau da manyan kayaba?shine yau kasaka k'ananun Kaya ko?"my Nurr nafasa sakasu sosai awannan satin"gara nad'an sabinta ko kuwa?hakane Kuma"suma ai sunamaka kyau k'ananun Kayan"kinsan wani abu?batare data kallesa ba tace".ah ah"nabada Mana d'inki nidake na shadda" sadaukinah baka gajiya da kashe kud'i wlh"indai akankine Zan iya kashe konawane.murmushi kawai tayi"sbd ita azatonta bawai iri d'aya yabada ba ad'inka.shikuwa iri d'aya yabada ,ita doguwar riga..

Fitowa sukayi dg class d'in"duk skul d'in anwatse kowa yatafi gida"sai jefi jefin mutane kawai.. office nashi suka wuce ta rakashi ya ajiye papers d'in"kafin suwuce bakin get suka shige motarsa...saida suka hau kan titi yace"my Nurr dame dame kikeda buk'ata ne? girgiza Kai tayi had'e da cewa bana buk'atar komai wlh.sadaukina bansan dame zan sakamaka ba?" akan d'awainiyya da kulawa da kakeyi dani..karki damu my Nurr kinji"yau zakije islamiyya ne?eh zanje insha Allah"okay"idan wannan yaron yazo gunki bance kifitaba"to insha ALLAH namaka alk'awari..
gsky week end zanzo nakaiki wani shago amiki lalle"inaso naganshi ahannunki"kinji?to za'amun tunda kanaso"tafad'a tana murmushi"parking yyi agefen titi"ta fito Yana cewa ki kunna wayar my Nurr kinji?jinake kamar karki tafi..nima haka sadaukinah"kibari Zan kamiki babbar waya mudinga video call"kamar tayimishi gaddama"saita tuna ai bayaso.hakan yasa tayi shiru kawai"kikulamun da kanki my nurr"to sadaukinah Allah yatsare hanya.ya amsa da ameen Yana kallonta"harta b'acewa ganinsa..

Koda ta Isa gida"bacci ta kwanta sbd lokacin 12 tunda exams akeyi da wuri aketashi skul..sai 1:30 tafarka"wanka tayi da sallah.kafin ta share d'akinta"taci bread da kifin gwangwani ta kora da fanta"duk acikin kayan da sadaukinta ke siyamata..doguwar riga tasaka ta feshe jikinta da turaruka"ta zauna tana karatun exams...baffa ado yashigo d'akin Yana cewa ke maza tashi kije ga alhassan can"yazo kugaisa dashi,shine nazab'a miki amatsayin mijin aurenki"d'ago kanta tayi ta kallesa"tanajin Bata tab'a jin tsanarsa ba irin yau"gsky baffa saidai kayi hakuri Amma bazan fitaba.tunda banasonshi to akanme Zan b'ata mishi lokaci? kutumar ubancan!ke kin Isa nace Abu kimusamun ko?to dan ubanki Baki isaba wlh"Dole kije ko kinaso ko baki so"Yana fad'in hakan yafice dg d'akin Yana cewa bara nadawo nasameki ad'akin nan...tana ganin yafice tasakawa k'ofar net d'in sakata.tayi zamanta"

Baffa ado kuwa fita yyi waje yasami alhassan dayazo tun d'azun.yace mishi gatanan zuwa"

Saidai lokacin da yaga bbu ita bbu alamar fitowarta yasakashi fitowa Afusace yanufi"k'ofar d'akin"saidai yajita arufe"cikin b'acin rai yace"ke y'ar iska wuyanki yyi k'wari ya Isa yanka ko?shine kikeyin musu Dani"wlh koki bud'e k'ofar d'akin nan kokuwa ninasan mezan miki..kaga shegiyar yarinya,shi waccan baturen dakika k'wallafa ranki akanshi inda gaske yakeyi yafito yafad'a Mana..uffan nurr batace ba"ak'ule baffa ado yace"bara naje nadawo yanzun"nazo na balle k'ofar naga ta k'aryar iskanci.yana fad'in hakan yajuya ya bar gidan.awaje yabawa alhassan hakuri akan yak'ara jira.alhassan kuwa duk yak'agu yaganta.yace"to shikenan Yana jira"saima gyara zamansa yyi akan dankalin k'ofar gidan.

Nurr kuwa kuka tafashe dashi"tarasa meyasa baffa ado kemata haka?gashi har 3 tayi sotake 4 ta wuce islamiyya"yanzun idan ya b'alle Mata d'an net d'in dashine rufin asirin d'akin tayi Yaya?wayarta dake ringing ta katse mata tunanin ta..
*sadaukinah*
d'agawa tayi tana sakarmishi kuka...my Nurr lfy kisanarmun meke damun ki??yanzun nan naji gabana yafad'i Dana tunaki ,shine nace bara nakira"agajerance tasanar mishi alhassan yazo Yana waje"Kuma baffa ado yanzun zaizo ya b'alle k'ofar d'akin" yadaketa sbd tak'i zuwa gun alhassan..kinutsu my nurrinah bbu abinda zaimiki ganinan zuwa yanzun gidan naku..share hawayenta tayi had'e da cewa to shikenan.amma sadaukinah karkayi fad'a da alhassan ko baffana"kaji Dan ALLAH?"karki damu my Nurr"Yana fad'in hakan yakashe wayar.... k'ok'arin ajiye wayar takeyi taji sallamar wasu mata"nacewa Wai bbu kowa agidan anata sallamane?"mik'ewa tsaye tayi sbd hango Nisaibah datayi itada wata matsa suna jifar tsakar gidan da kallon wulak'anci"hakan Kuma yayi daidai da shigowar baffa ado.wanda da zarto ahannunsa sbd yab'alle k'ofar...??????
[9/9, 2:08 PM] Maman Nasreen: .....Afirgice nuratu tayi saurin bud'e k'ofar sbd gudun karyayiwa net d'in illah"kinganta can mommy"cewar Nisaibah tana nuna nuratu da yatsa.bayin Allah suwaye kune?"baffa ado yafad'a Yana kallon su"wani banzan kallo na raini da wulak'anci mommy tamishi tana yatsina.kafin ta had'e fuska tace".nice mahaifiyar faruq malaminsu wannan kazamar y'ar taka...wani mugun fad'uwa gaban nuratu yyi"cikin tashin hankali tayi baya ta koma d'akin"Nisaibah taja tsaki had'e da cewa munafuka aida kinfito manah.bewar Allah inason jin dalilinku nazuwa gidana"baffa ado yafad'a cikin mamakin nusaibah nazagin nuratu datayi...wanikallon rainin wayo mommy tayiwa gidan.kafin tace"wannan kangon shine gida?to bara nafad'a maka da babbar Murya"ruwa basa'an kwando bane"Kuma wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa wlh"munfi k'arfin had'a zuri'a da irinku matsiyata"kajawa y'ar ka kunne"tarabu da d'ana bbushi bbu itah har abada... wannan wane irin rainin hankali da wulak'anci ne?ku dabbobin inane dazaku shigo gidan mutane Kuna wannan burgar?"cewar goggo kande amatsife tana fitowa dg cikin d'akin ta.baffa ado yaji dad'in abinda tace sbd shi yakasa cewa komai.sai kallonsu kawai yakeyi.idan kin Isa dashi d'an naki shiya kamata kijawa kunne bamuba ko?tsaki mommy taja had'e da cewa kekuma asuwa?Kuna fama da bak'in talauci d'aya muku Kant....matsowa kusada ita goggo kande tayi tana cewa"kinci kanbura ubaki"idan banmiki shegen dukaba"kice Nina y'a bace.nadakeki nadaki banza sbd gidana kikazo.kufice. Kubawa mutane wuri"Allah yarabamu da irin arzik'inku naciwa mutane zarafi.k'ilama inza'a bibbiya kud'in naku Bata hanyar halak kuka samesuba"
Gaba d'aya mommy shiru kawai tayi, sbd batayi zaton za'a musu hakanba.nur dake d'aki tana sauraron komai sai kuka takeyi"yyinda baffa ado yamaidasu kamar TV"
saida yaga goggo kande ta Kai aya alafazinta tukum yace"kufita kubawa mutane guri.tsaki Nisaibah taja had'e da cewa mommy muje zasu gane kuransu wlh.kudai gane kuranku y'an wahala"cewar goggo kande tanajan tsaki,yyinda mommy taja kwafa had'e da cewa kundaiji abinda nafad'a muku?muddin bata rabu dashiba"tokuyi kuka da abinda zai biyo baya..tana fad'in hakan suka fice dg gidan...

Alhassan kuwa har yanzun Yana nan zaune kan dakali"suna fitowa sir faruq nakawowa ...wani mummunan fad'uwa gaban sa yayi"arikice yanufesu Yana cewa mommy mekukaje yi gidansu nurr?"tsaki taja had'e da cewa bbukai bbu talaka har abada"wuce muje banyarda kasake zuwa gidan nanba ko zuwa gunta.idan hakan yafaru banyafe makaba.... innalillahi wa inna ilaihir raju'un"ya fad'a arud'e Yana runtse ido.mommy kinsan mekike fad'a kuwa?bansaniba "zaka wuce muje ko kuwa? alhassan dake zaune Yana sauraren komai yakece da dariyar mugunta Yana tab'e baki.wata iriyar zuciya tazowa sir faruq iya wuya.k'ok'arin nufar alhassan yakeyi.. mommy ta ruk'osa da sauri"tana cewa bakaji mena fad'a maka bane?"adedenan Kuma baffa ado yafito dg soron gidan Yana rik'e da hannun nurr daketa kuka shab'e shab'e da hawaye.gabanta yakoma fad'uwa sbd ganin sir faruq"yakafeta da ido babu ko kiftawa.

Jitake abun kamar amafarki ne ba gaskeba... b'ata tab'a zaton haka iyayensa sukeba"azatonta suma masu kirkine irinsa"zaka wuce muje ka tsaya kana kallonta.kasani bazan canzaba"muddin kazo inda take kokulata banyafe makaba...zaro ido nurr tayi cikin tashin hankali tana k'ok'arin barin wurin"baffa ado yace"gidan uwarwa zakije? alhassan yayi saurin cewa"ah ah baba barta ta tafi ko ranta yadena k'unci"zuwa dare insha Allah zandawo gunta fira...sakar Mata hannu baffa ado yyi"da gudu nurr Takoma cikin gida tana kuka..sir faruq kuwa jiyakeyi tamkar alhassan yawatsa mishi wuta akan kalamansa ga nurr"zare hannunsa da mommy tarik'e yyi yabar gun da k'yar. zuciyar sa na wani irin k'una"ya wuce inda yayi parking motarsa"

Suma su Mommy gun tasu motar suka wuce"yyinda baffa ado yatsaya suna mgn da alhassan...

Nuratu kuwa d'akinta tashige tafad'a kan katifarta tasaki kuka mecin rai"meyasa sadaukinah kashigo rayuwata?bacin kasan mahaifiyarka bata k'warai bace"bazan iya jure rashinkaba sadaukinah! Allah yasa mafarki nakeyi bagaske bane...duk tafad'a afili tana kuka.baffa ado yashigo gidan Yana k'wala Mata kira"banza tamishi tana cigaba da kukanta"yyinda goggo kande ta fito"tana kallonsa tace"nagaji da mugun halinka wlh"asanadin k'wadayinku kaida y'ar ka kunjawo anzo har gida za'a cimana mutunci ko?"Allah yawadaran kwad'ayi wlh...tana fad'in hakan ta wuce d'akin ta.baffa ado yaja kwafa had'e da cewa zanyi maganinki kema... d'akin nurr yanufa yasameta tana kuka"Dan uwarki akansa kike kuka sbd bakida zuciya ko?banza tamishi"to Bari kiji ko kukan jini zakiyi bbuke bbushi"sannan aurenki da alhassan Dole ne.sbd haka kishirya da dare zaizo tad'i agunki"Yana fad'in hakan yajuya ya fice.jitakeyi kawai gara ta mutu kota huta da wannan masifar datake ciki"
*hasbinallahu wani imal wakeel*
Taketa ambata aranta"tana sakin ajiyar zuciya"Kiran Sallar la'asar yasakata tashi tafito ta wanke fuskarta tayi alwallah..

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login