Showing 90001 words to 93000 words out of 214133 words

Chapter 31 - CUTARWA AYSHERCOOL COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

22034

mota da buƙatu?"

"Eh zan yi in sha Allah, Allah ya sanya mata albarka"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Amin, bari sai na kira su na gaya musu, na ji yaushe zaki fara zuwa"

"Yauwwa yaya Abdul, na gode sosai da sosai"

Yayi murmushi ya ce "Sai ka ce na baki kyautar wani abun, Allah ya taimaka".

Suka je gida tana ta tunanin da wa zata yi sharing wannan abun farincikin, na samun aiki, ita ba ƙawaye ba, kuma ba abokin hira ba, tayi tunanin ko ta gaya wa raihan, amma sai ta ga hakan kamar ta zaƙe, dan haka ta share shi bata gaya masa ba.

Ranar litinin, ta ga kiran wayar raihan ya zo su tafi, wanda ranar zata je ta yi sallama da ƴan wurin aikinsu, ta fara zuwa wancan kanti na furnitures.

Tun da ta nufo motar yake kallonta, sannu a hankali, tafiyar ma cikin nutsuwa da yanga take yin ta.
Maimakon ta shiga ta zagaya ta in da yake zaune ta ce "Ina kwana?"

"Lafiya ƙalau, ina shirin aikin?"

"Sai 9 zan je idan Allah ya kaimu, zan yi musu sallama, na samu aiki a wani sabon shago, MIKIYA GALLERY, can zan koma zuwa"

Yayi shiru yana kallon ta, ya ɗan rausayar da kai ya ce "Rashin muhimmancin nawa har ya kai abu ya faru ki ƙi gaya mini?".

"A'a ba haka bane ba, abun ne bai tabatta da wuri ba"

"Shikenan na gode, Allah ya taimaka" yayi maganar ransa a haɗe.

"Raihan haushi ka ji, walla....

"Shhhh, na fuskanci na fiye shishshigi, am sorry" yayi maganar yana kunna motar.

Ummi ta yi saroro ta kasa magana, ba ta son ace tayi laifi a rayuwarta, mussaman raihan da yake ta ɗawainiya da ita, ba ta zaci za ji haushi ba.

"Matsa zan ja motata"

A hankali ta ja da baya, ya ja motar, yana kallonta ta mirror, ta tsaya kamar sokuwa tabi motar da kallo.

A hankali ya furta 'Lets see, if it will works'

Jiki a sanyaye ta din ga gudanar da al'amura ranar.

Ta je sabon wurin aikinta, sai dai hankalinta baya jikinta, ta din ga kiran wayar raihan, amma yaƙi ɗagawa.

Whats app ta koma, ta yi masa message nan ma bai amsa ba, sai dare sannan ya kirata.

"Raihan dan Allah ka yi haƙuri, ban san zaka ji haushi ba, ka yi haƙuri mana".

"Yaya ummi ba sai kin bani haƙuri ba, laifina ne da nake yi miki shishshigi, duk da yanayinki na rashin son mutane".

"A'a ba shishshigi ka ke yi mini ba, ka yi haƙuri mana"

Ya wani hura hanci ya ce "Ok, Allah ya taimaka".

Ta ce "Yauwwa na gode, zan din ga gaya maka abu idan ya faru"

Ya ce "Promise?"

"In sha Allah "

"To shikenan, abu na daɗi ko akasin haka, kar mu ɓoyewa juna"

Ummi ta ce "To"

"Good dear, gobe in Allah ya kaimu zan zo na ga wurin"

Tayi murmushi ta ce "To Allah ya kawo ka"

"Amin, goodnight" suka yi sallama tana jinjina daru irin na raihan.

Status take kallo, ta kai kan status ɗin raihan, yana tsaye a gym, ya tsaya a jikin mudubi yayi hoto, daga shi sai gajeren wando, ya ɗaga wani ƙarfe jijiyoyin jikinsa duk sun ɗaga, ga cikinsa ya rabu kashi shida
(six packs) ga ƙirjinsa kwance da gashi har saman cikin sa.

Tayi reply da "Babban mutum meye haka?"

"A ina?"

"Ka saka hotonka babu kaya, ba mutunci a haka, dan Allah ka cire"

Ya amsa mata da "Ai ni ba mace bane"

"Duk da haka, manya ba sa haka, a cire dan Allah 🙏"

Yana daga kwance yake murmushi, ya ce "To shikenan, an gama babbar yaya, in sha Allah ba zan sake sakawa ba".

"Yauwwa babban mutum, Allah ya yi albarka ya kula da rayuwarka"

"Amin ya rabb yayata, godiya nake Allah ya kula mini da ke"

"Amin tare da kai" ta ajiye wayar tana murmushi.

Washegari har shagon ya je ya tarar da ummi, sai dai ya ji daɗin ganinta a kauwwame a wuri ɗaya, ba wani aiki take na wahala ba.

Ya samu wuri ya zauna suka gaisa da manager, ya hau yi wa ummi hira.

Da farko a ɗan tsorace take, ko manager zai ce tayi laifi, amma yaga bai ce musu komai ba, har lokacin tasinta yayi, yana wurin.

Da suka fito ya kalleta ya ce "Wai nawa zasu din ga biyanki ne?"

Cikin murna ta ce "Dubu sha biyar duk wata"

"Me?"yayi maganar yana yatsune fuska.

"Dubu sha biyar" ta maimaita masa.

"Share-share zaki din ga yi ne? Ki zo ki wuni a dubu sha biyar, duk girman shagon nan dan son kai".

Ummi ta waiwaya ta ga babu wanda yake jin su ta ce "Kayi a hankali, dubu sha biyar ina laifi, da waye ya bani?".

"Degree holder da aikin dubu sha biyar a wata, me 15k zata yi miki a wata, mussman ku mata masu tsarabe-tsarabe, ni fa a wata data da katin waya na dubu ashirin nake sawa zuwa sama" Ummi ta buɗe baki tana kallon sa, saboda abun ya ɗaure mata kai, har ya kaita gida mita yake yi, yana nanata dubu sha biyar ta yi kaɗan, tayi masa shiru taƙi kula shi. Dan in dai shariya ce ummi ta ƙware a wannan fannin.

"Ni ki ka share ko, wato idan na gaji na yi shiru?" gyara zamanta tayi tana cigaba da kallon window.

A hankali ya ce "Miskili ka fi mahaukaci ban haushi".

***
Misalin ƙarfe goma sha biyu da rabi na dare, raihan da mahaifinsu, chief accountant da sauran accountants mutum biyu, lawyoyin Alhaji Tahir su biyu, sai kuma manajojinsa, zaune a wani katafaren office, ko ina fitilu kamar rana, kowa gabansa da ruwa da lemo, gefe ga flask na shayi, gaba ɗayansu raihan ne kawai yaro a cikinsu.
Ɗaya bayan ɗaya kowa ya din ga gabatar da bayaninsa n shekara a kan ɓangaren da yake jagoranta.

Suka kammala tsaf, sannan raihan ya tashi, ya yi connecting system ɗin sa da projector, ya fara bayanin abubuwan da ya tattara daga bayanan su, ribar da suka samu a shekarar, ya tabbattar wa da mahaifinsu duk sun bibiyi shige da ficen kuɗi na shekarar, kuma sun yi dai-dai da bayanan da abun da kowane accountant yayi presenting.
Ya ware harajin da zasu biya, na ciki da wajen Nigeria, ya ware kuɗin zakka, kuɗin abun da ake rabawa ma'aikata na riba bayan albashinsu, abubuwan da suke buƙata, kuɗin duk wani abu da ya shafi sadaka da makamantansu, da kuma kuɗin umara na mutum goma, kamar dai yadda Alhajin ya umarce shi.

Tafa masa Alhaji Tahir ya hau yi, ya ce "Ƙaraminsu babbansu, am so much proud of you, ban zaci zaka iya ƙoƙari haka ba, saboda na san aikin ba ƙarami bane".

Chief accountant ya ce "Ni kaina ya bani mamaki, yayi ƙoƙari sosai da sosai, na bi duk abubuwan da yayi, kamar dai yadda ka saba ne, yayi iya yin sa, kuma da alama zai kamanta adalci kamar dai kai, sai dai rigimamme ne"

Alhaji Tahir ya yi murmushi ya ce "Ai na san halin kayana" suka yi dariya baki ɗaya.

Suka ƙarasa tattaunawa, da bibiyar abubuwan da Raihan ya gabatar, daga bisani Alhaji Tahir ya ce kowane ɓangare su rubuto abun da suke buƙata, na gyara ko makamancin haka, raihan zai duba, shi zai je hutun taƙaitaccen lokaci.

Duk suka gamsu da abubuwan da aka tattauna, tare da yi wa Alhaji Tahir addu'a saboda mutum ne mai farantawa ma'aikatansa, dan ya ce abokan nemansa ne, bayan iyalansa ba shi da sama da su.

Dirver ya ɗauke su zuwa gida, a hanya raihan ya ce "Alhaji"

"Na'am babban mutum"

"Tsakani da Allah aikin nan da wahala, kuma ko murmurewa ban yi ba, ka ce a kawo mini duba wani abu, ni fa ban san komai ba, dan Allah a kaiwa su yaya sagir, gaba ɗaya ƴan kwanakin nan saboda aikin nan, ko bacci bana yi sosai" ranƙwashin da Alhajin yayi masa ne ya sa shi yin shiru yana kallon sa.

"Kana da nasibi a kan harkar kasuwanci raihan, amma wasa da shiririta sun yi maka yawa, da aikin kashe-kashen kuɗi, office zan baka a head branch, a din ga baka salary"

Cikin sangarta ya ce "A'a dan Allah, shagona fa da nake ta processing, ka fa bani jari rance, ka manta, kayana sun kusa zuwa fa".

"Na sani raihan, akwai abun da nake targeting ne"

Raihan ya ce "To, Allah ya taimaka, amma ba sai na sake duba wani abun ba ko? Kuma ba sai na yi maka aikin ba ko?".

"Sai fa ka yi, gara ma ka shirya"

Raihan ya kifa kansa ya ce "Wayyo mami, dama ban dawo kano ba"

Alhaji Tahir yayi dariya ya ce "Ko ina ka tafi, i know how to deals with you, Munnir ya sangarta ka, kashe kuɗi kawai ka iya, baka iya nema ba" yayi maganar yana murɗe masa kunne.

Raihan ya ɗago da sauri ya ce "Ka tambayeshi ka ji, na sayar da agoguna, na sayar da takalma, kuma na tara kuɗi"

Alhaji Tahir dariya kawai yake yi wa raihan, so yake dole sai ya zame, kuma ya san dalilin sa na yin haka, dan raihan akwai biyayya in dai abu zai faranta masa rai zai yi, da mamansa ne ma suke faɗa wasu lokutan ba su fiye shiri ba, idan ta zo da abu na son zuciya, ya ce ba zai yi ba.

Duk da ummi ta ɗan girmewa Raihan, sannu a hankali ya nuna mata shi namiji ne, domin kuwa yafi ummi wayo nesa ba kusa ba, dan bata ankara ba, suka yi wani irin mugun sabo da ita da shi, duk ɗari-ɗarinta da shi, ta sake jiki da shi, dan barkwancinsa kawai nishaɗi yake saka ta.

Kullum a wurinta yake karyawa, da safe sai ta tafi masa da abinci, kuma cikin ikon Allah babu wanda ya sanya mata ido ya lura da shige da ficenta.

Shi kansa raihan a tarayyarsa da ummi, ya san tana da baki dan tana magana tana tsoron yi ne, saboda yanayi na yadda al'umma suke karɓar ta.

Idan suna hira, wasu lokutan manager sai ya kalleta ya ce "Wai ummi dama kina da baki haka?" Sai ta yi shiru ta daina maganar cikin jin kunya.

Gaba ɗaya ta daina jin nauyin raihan, haka kurum sai ya zame daga office, ya taho wurin aikinta, manager har tambayarsa yake "Wai kai Raihan baka sana'a ne? Kullum kana liƙe a wurin ummi?".

Kasancewar manager matashi ne, da kaɗan zai girmewa ummi, ƙanin mai shagon ne, dan haka Raihan ya ce "Eh ni bani da sana'a, zaman banza nake a yanzu, shiyasa kullum muke tare da ita".

"Ta ce Abdul yayanta ne, kai kuma ƙaninta, anya ba ka girmeta ba kuwa? Ka yi ta mata wayo, ta zo da ɗan abincinta, ta ajiye maka ka zo ka cinye, ka hanata sakat da surutu, ka zo in baka aiki kaima".

Raihan ya ce "Allah ya kiyaye in yi aiki ku biyani dubu sha biyar, dan wayo, dan kun ganta saliha, ai ta kusa daina aikin nan".

Manager ya ce "Ai tawakalli ta fika, shiyasa take aikin, kai ka raina sana'a, kullum kana liƙe da ita, ka cinye mata abinci, kuma kana jiran a biyata ka karɓe mata kuɗi".

Raihan ya ce "Wai manager abincin nan daga gidanka ake kawo wa ne? Ina ruwanka ne ka dameni fa"

Idan suna abun su shi da manager, sai dai tayi ta dariya, kamar sako da sako manager komai sai yayi magana, shikuma raihan baƙar magana da neman tsokana.

Ummi na jin daɗin aikinta a wurin nan, ko albashin farko ba a bata ba, amma manager yana daga cikin mutanen da suke mutuntata, bai taɓa nuna mata ƙyama ba, kuma tana iya ƙoƙarin ta wurin kula da coustomers ɗin su, idan ta je da wuri ba ruwanta, har share-share yi take yi tayi mopping gaba ɗaya ba ta da damuwa.

Zamanta a wurin yana rage mata damuwoyi da yawa.

Yanzu ma tana ta bawa raihan labarin rigimar noor, ba ta da wata hira sai ta noor.

Cikin nishaɗi take hirar, Raihan yana kallonta, ya ce "Ya aka yi haƙorinki ɗaya ya ɓalle ne? Ko dai da kina yarinya kin yi rashin ji ne?"

Ta yi murmushi tana dariyar yaƙe, da tuna yadda aka yi haƙorin ya ɓalle ranar salla ta ce "A ƙaddara bana jin magana ne, na taho da gudu ranar salla, na faɗa cikin kwanuka na buge baki da tukunya, haƙorin ya ɓalle" tayi maganar tana tuna yadda idiris yayi ball da ita ranar.

Raihan yayi dariya ya ce "Ai da alama, kuma fa da ya ɓalle ɗin yafi kyau, amma dai mijinki sai ya rage sadaki, saboda ɓallewar haƙorin nan, duk da ta wani fannin sai ya ƙara, tun da kina cikin matan da malaman fiƙhu suka ce a ƙarawa sadaki".

Basar da zancen tayi, saboda jin zai ɗaukko wani babban karatu mai nauyin gaske, ita ina ta ga ko saurayi balle ayi zancen ƙari ko ragin sadaki, ita da tun da take, ba wanda ya taɓa cewa yana sonta?.

Raihan yayi mugun sabo da abincin ummi, kusan kullum a wurinta yake karyawa, ba tare da ya san abincinta take sadaukarwa ta bashi ba.

Suna tafe a hanya ta ce "Raihan, manager ya ce a satin nan fa za a biya salary"

"Dubu sha biyar ɗin ki ke wa wannan washe bakin?"

"Eh mana, idan Allah ya saka mata albarka zaka sha mamaki".

Ya ce "Oho dai, amma dubu sha biyar ya fi kuɗin mayukan da zaki shafa a sata" ta ware ido ta ce "Ni ɗin? To wallahi vaselin nake shafawa ko man kaɗanya"

Yayi murmushi ya ce "Amma zaki kai ƙaninki shopping ko? Muje ki yi mini sayayya"

"Me ka ke so in saya maka?"

Raihan ya ce "Sai mun je sai in zaɓi abun da nake so"

Ta ce "To shikenan, in sha Allah idan aka biya sai mu je, nima na je shopping ban taɓa zuwa ba fa, to ina zamu je?"

"Ki yi tunanin in da ki ke so mu je" ta jinjina masa kai tana ta murmushi, wai duk saboda dubu sha biyar take wannan farincikin.

"Yauwwa, ya ake ciki da aikin Alhaji kuwa?"

Ya ce "Hmm kin san ya kuma haɗa ni da wani, alhakin fitar da zakka, da mutanen da zai biyawa umara da aikin hajji"

Ummi ta ɗan yi shiru ta ce "Masha Allah, sai ka tsaya ka ji tsoron Allah, kar ka bari son rai ya shiga lamarin, wataƙila ya yi hakan ne dan ya gwadaka, ka bawa wanda suke buƙata kayi adalci"

"Haka ne ya sayyada, shiyasa ban so ya sakani ba, kin san ina da yayye, kamar ba zasu ji daɗi ba tun da su ne manya, tunda ki ka ce ina ma zaki sake ganin baba ya saki aiki, zaki yi farinciki, sai na sha jinin jikina, komai lokaci ne, wataran da kuɗi nima zan nemi na ganshi ya sakani aiki, ba zan ganshi ba"

Ummi ta ce "Wannan haka yake, Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana, ya yalwata arzikinsa"

"Amin ya Allah sayyada"

***
Kamar kullum sai da ya mayar da ita gida, sannan ya koma office ya cigaba da ayyukan sa, bayan la'asar ya koma gida.

Mami na ganinsa ta hau murmushi, wanda har hakan ya bashi mamaki, ya ce "Mami na ga kina ta fara'a"

Ta ce "Ashe kai Alhaji ya saka duba mutanen da za a bawa zakka, da wanda za a kai umara bana, har da aikin hajji mutum uku?"

Ya kalli mami ya ce "In ji wa?".

"In ji ubanka, da baka gaya mini ba, ai ni mijina ne ya gaya mini"

Ya ɗan yi miƙa ya ce "To shikenan tun da ya gaya miki"

Mami ta ce "Ohh, Allah dai ya cika mini burina, to su wa ka zaɓa? Dan ina da vacancies".

Ya dubi mami ya ce "Vacancies kuma, na me?"

"Ahh wanda za a bawa zakka mana da wanda za a kai umara har ma da aikin hajji".

Raihan ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Amma ni mami, duk a gidanku su Anty Saude, ba wanda ba a kai aikin hajji ba wasu umara, ƙawayenki kuma duk suna da rufin asiri, to wa kuma za a baki? Ai gara a kai waje wasu ma su amfana"

Ta ce "Kai dalla yi mini shiru, nima na san waɗanda suke da buƙata, ka bani vacancies, da kuma kuɗin da zan bayar nima, duk shekara Alhaji yana bani, maganar ma na yi masa ya ce kai ya bawa wannan damar".

Raihan ya ɗan ɓata fuska ya ce "Haba mami, dan Allah me zaki yi da kuɗi? Zan baku vacancies huɗu, ke biyu Hajiya biyu shikenan, kuɗin zakka kuma gaskiya ba zan iya baki ba, an ware percentage ɗin share ku fa, a ribar da aka fitar ta shekara za a baku"

Mami ta shiga tafa hannu, ta ce "Raihan, wai tsaya ni da hajiyar nan muka yi naƙudarka, da komai sai ka daidaitani da ita, kuɗin mijina ka ce ba zaka bani ba Raihan, shikenan ba zan kyauta ko sadaka ba nima?"

Ya miƙe yana zumɓura baki ya ce "Dan Allah mami kiyi haƙuri, nifa ba haka muka yi da Alhaji ba, what if gwadani yake yi, wallahi kin fi Hajiya yawan ci masa kuɗi ma, haba mami dan Allah" sai ta kasa magana ta bi shi da kallo, gashi dai ita ta haife shi, amma idan ya botsare, wasu lokutan kasa magana take yi, dan bata san dalilin da ya sa yake yi mata kwarjini ba wasu lokutan, idan ta yi ba dai-dai ba ɓaro-ɓaro yake gaya mata.

Manager ya kira ummi a waya, ya ce ta turo account number zai tura mata kuɗinta na albashi.

Bata da account number, dan haka ta kira raihan jikinta yana rawa dan farinciki ta ce "Raihan, manager ya ce na tura account number, zai turo mini salaryna, amma bani da account, ka bani naka na bashi"

Yayi dariya ya ce "Gaskiya banki za su rufe mini account ɗina idan aka saka dubu sha biyar, ni kuɗi idan bai kai dubu ɗari ba, basa shiga account ɗina".

Ta ce "To ko kawai in bari sai da safe idan Allah ya kaimu, idan na je sai ya bani a hannu kawai ko?".

"Ina da lambarsa zan tura masa, amma dan Allah kar ki kasa bacci saboda dubu goma sha biyar, kuma kar ki manta kin yi mini alƙawarin zaki kai ni shopping".

Ayshercool
08081012143
What's app only please 🙏
       *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P25

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login