Showing 165001 words to 168000 words out of 214133 words
gane in fita ba?"
Ta ɗan kwaɓe fuska ta ce "Eh wanka zan yi"
"Ina zamana ki ka ce na zo na shafa miki abu, yanzu kuma ki ke korata?"
Ummi ta ce "To ai dama iya shafa mini nake son ka yi, hannuna ba ya kaiwa tsakiyar bayana".
Raihan ya ce "Tun da na shafa miki ni zan ɗauraye ki, nima kalli yadda ki ka ɓata mini jikina da wannan abun, sai na sake wanka" yayi maganar yana cire vest ɗin jikinsa, da duk tayi yellow.
Raihan a rayuwar sa yana matuƙar son soyayya da kulawa, sai da ya auri ummi ma ja gane hakan, dan shi da duk hakan ba ya gabansa, kuma a hankali ummi na rage wannan kunyar ta sa da take ji.
Bayan sun fito daga wankan, ya zaunar da ita a gaban mudubi, yana shafa mata mai, ya jona hand dryer, zai busar mata da gashi.
Ta cikin mudubi ya kashe mata ido ya ce "Ya dai? Wanka da miji ya fi lada fa, sai wani ɓata rai ki ke yi, kuma kin fi fita fa da na wanke ki?" Yayi maganar yana murza fatarta yana murmushi.
"Au da bana fita?"
"Gaskiya dai, ki din ga biyana ina yi miki wankan, na shafa miki kayan shafe-shafen naki, kuma in yi miki wanka, ki din ga biyana, idan ina yi miki sai kin fi fita"
Ummi ta ce "Hmm kalli agogo, sai makara ka ke yi, kuma sai na kira Alhaji na gaya masa wasa ka ke yi da aiki, ba ka fita da wuri"
Yayi dariya ya ce "Sai in ce masa ke ki hana ni fita, ki ka tsare ni da soyayya, na kasa fitowa" miƙewa tayi ta ce "Kai ba ka jin kunya fa ko?"
Kamar ba za su rabu ba, haka ya shirya suka fita falo, ta raka shi har gaban motarsa ya tafi.
Ta koma ciki tayi ta fama da aiki, dan kaf ɗakunan gidan nan, kullum sai ta shiga kowanne ta gyara.
Wajen ƙarfe sha biyu ta kammala aikinta, ba ta karya ba sai a lokacin ta yi farfesun kifi da dankali, ta koma falo ta zauna tana karyawa, ga ƙamshin turaren wuta yana tashi, ga Tv tana yi.
Ta ƙarewa falon kallo, ta kalli kwanon hannunta, ta yi murmushi ta ce "Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabatta gareka, tsarkakken sarkin da babu wani kafinsa kuma babu a bayinsa, Sarkin da ni'imarsa da yalwarsa ba su da iyaka" ta furta hawaye na taruwa a idonta, ba ta taɓa tunanin irin wannan rayuwar ta ƴanci ba.
Ta ɗaga wayarta ta kira maiduguri, sun daɗe suna gaisawa, bayan sun gama ta kira raihan.
Sun daɗe suna waya, suna hira sai da ya ce mata zai shiga meeting sannan ta katse wayar.
Kasancewar kifin da ta ɗiba tayi farfesu da yawa raihan ya kawo, dan haka ta tsiri yin girki da kifin, a cewarta a kai wa dr. Wani wani kuma a kai gidan su raihan. Dan raihan ya riga ya bata damar duk lokacin da take son yin alkhairi, ya baga dama ba sai ta tambaye shi ba.
Tun la'asar da raihan ya dawo gida ya ci abinci, take lallaɓa shi ya kai abincin nan, amma sai yawo yake yi mata da hankali.
"Dan Allah MD ka kai abincin nan kar yayi sanyi"
Ya ce "Zan kai, yauwwa tafiyarmu fa sai next week in Allah ya kaimu"
Jiki a sanyaye ummi ta ce "Ka gaya wa mamin zancen tafiyar ne?"
"Meyasa ki ka damu ne? Zan gaya mata in sha Allah, kar ki damu ba wata matsala in sha Allah, zan kai abinci da daddare yanzu so nake na kasance da ke, wuni muka yi fa ba ma tare"
Ta yi shiru ba ta ce komai ba, ya fuskanci ta na tsoron abun da ka iya biyo baya idan ya sanarwa da mami zai tafi da ita china, dan ita a so samunta kawai ya ƙyaleta shi yayi tafiyar sa.
A booth ɗin mota ya tafi da abincin sallar magariba, bayan ya idar ya fara zuwa gidan su ummi, sannan ya tafi gidansu.
Bai san Alhaji ya gaya wa mami zancen tafiyar ba, ya fara shiga sashen hajiya, suka gaisa ya ajiye mata abincin, dan ya san idan ya kai wa mami, ba burgeta zai yi ba ƙarshe ta ci zarafin Abincin ma.
Bayan sun gama gaisawa, ya shiga sashen mami, sai dai yanayin fuskarta ya nuna masa akwai matsala.
"Ina wuni mami?"
"Nemi wuri ka zauna" tayi maganar ba tare da ta amsa masa ba.
Ya zauna yana satar kallonta.
"Ni na haifeka ko waccan mummunar yarinyar?"
"Wace irin tambaya ce haka mami, me kuma tayi?"
"Yanzu raihan ka yi riƙar da zaka tsallake maganata ka ce zaka ɗauketa ka tafi china, tawa maganar ka banzantar da ita ko?"
Raihan ya ce "Wallahi mami Alhaji ne ya shirya tafiyar, ba laif....
"Rufe mini baki ina magana kana magana, na kusa kawo ƙarshen auren nan, na fuskanci ba haka suka ƙyaleka ba, tun da ka fara bijire mini, kama aure kai da Safiyya babu fashi, umarni nake baka ba shawara ba, na soke tafiyar nan" yayi mata shiru, ta ci masa mutunci daga shi har ummi, tare da aibata ummi yadda take so, tayi ta gama bai tanka mata ba, ya tashi ya bar falon.
Bayan fitarsa Nihal ta fito ta ce "Mami, dan Allah ki din ga sassauta adawa da auren nan, kina gani fa kin gama banbamin ki, ko amsa bai baki ba ya tafi"
Mami ta ce "Shi ya isa, ban haifi ɗan da zai bijire mini ba a kan mace wallahi"
Nihal ta kalli mami ta ce "Idan kuma safiyyan ma yayi mata haka fa, ya so ta kamar yadda yake yi wa wannan? Tun da kin ga yanayin halinsa ɗaya da Alhaji"
Mami ta ce "Gara safiyya wannan ai tawa ce, ba wani abu"
Nihal ta numfasa ta ce "Mhmm to mu kuma fa? Wasu fa zamu aura, mu ma ayi mana yadda ki ke yi mata kenan?"
Cikin mamaki ta ce "Au goyon bayan sa ki ka fara kenan ya wulaƙanta ni?"
Nihal ta yi murmushi ta ce "Ahh haba dai, kawai dai wani hasashe nake yi ne, Allah ya kyauta"
Ummi kuwa ta sha kwalliyar dare, tana jiran dawowar raihan, amma yanayin yadda ya shigo ya tabattar mata da akwai matsala, ko kallon in da take bai yi ba, ya wuce wani bedroom ɗin.
Jikin ummi yayi sanyi sosai, ta shiga tunanin ko ta yi wa raihan wani laifin, amma ta ga lafiya ƙalau suka rabu, hakan ya tabattar mata da ba ita ta yi laifin ba.
Bayan mintuna talatin, ta je ta leƙa ɗakin da ya shiga, ya kwanta yayi ruf da ciki, ta na son shiga amma idan yayi irin wannan burkicewar tsoronsa take ji, dan haka ta ƙyale shi.
Da safe ma ko karyawa bai yi ba, dan tana kitchen ya tayar da motarsa ya fice, sai ta ji gaba ɗaya duniyar ta yi mata zafi, kamar ta ɗora hannu a ka tayi ihu.
Raihan kuwa ga damuwar abun da mami tayi masa, ga tausayin ummi yake ji, har cikin ransa yake jin idan ya auri Safiyya ba zai yi mata adalci ba, dan jin ummi yake yi a kowanne sashi na zuciyarsa, haka zalika ma yaushe ya auri ummi, da har za ace ya kawo wata?.
Ya ji ba zai iya cewa ummi ya janye tafiyar su ba, hakan kamar zubar da kimarsa ne tare da kimar ita kanta mamin da ta kasa gane hakan, dan haka ya ji bai zai iya cewa ya fasa tafiyar nan ba da ummi, ya san duk abu Alhaji zai tsaya masa.
Sai ƙarfe huɗu na yamma ya dawo gida, ya kwaso gajiya sosai da sosai, sai dai kamar mai aljanu ya koma normal har yana ce mata gajiyar da ya yi kamar yayi gudun kwana biyar.
Ta biye masa ya gama cin abinci, ya koma falo zai yi kallo, amma ta bar falon ta koma bedroom.
Ya bita ɗakin ya tarar da ita ta fito da kayan wardrobe tana gyarawa.
A ɗan shagwaɓe ya ce "Yanzu fisabilillahi ba ki yi aikin bana nan ba, sai yanzu da na dawo, sonake ki zauna a kusa da ni mu yi hira" ta ɗago da idanunta ta kalleshi, ta kawar da kanta tana tura baki ta cigaba da aikinta.
Ya ƙarasa gabanta yana cewa "Wai madam ya ne? Me na yi miki ne?"
Cikin rauni ta ce "Kai zan tambaya me na yi maka? Kawai ka share ni, har da canza ɗaki kuma ni ban san me na yi maka ba, sai yanzu zaka din ga yi mini wasa ba zan yi hirar ba" tayi maganar har muryarta na rawa saboda shagwaɓa.
"Ohhh sorry kairun nisa'i, ba ki yi mini laifi ba, ba na son laifin da ba naki ba ya shafe ki ba ne, kin san idan ina fushi sai a hankali yanzu ba gashi na saukko da kaina ba, ai idan ke ki ka yi mini laifi ke zan yi wa, bana son in ɓata miki rai ne alhalin ba ke ki ka yi laifin ba".
"Ni ba ruwana da kai, har da wani canza ɗaki, to ka tafi kenan kwaso maka kayanka zan yi na mayar maka ɗakin da ka kwana, nima na huta"
Ya kwashe da dariya ya rungumota jikinsa ya ce "Ke idan wani ya gaya miki wannan tatsuniyar zaki yarda? Raba ɗaki da ke, ke ko a baki ya yi miki ma'ana? Iya wuya muna tare sai dai ki yi ta haƙuri. For now dai a yafe mini laifina"
Ta ɗaga kai ta kalleshi ta ce "Bribe me tukuna"
"Da me?"
Cikin nutsuwa ta ce "Ka fasa tafiya da ni, saboda hankalin mami ya kwanta bana son ta yi mini fushi da kai"
Yayi saroro yana kallonta, ya maze ya ce "Ba na ce miki zan kula da komai ba? ba zata ƙi ba ai"
Tayi murmushi ta ce "Na san a kan maganar ne ka yi fushi jiya, idan damuwarka ta wurin aiki ce ina ganewa, haka idan da mami ne dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ba wani abu ka je ka dawo".
Raihan ya ce "Ba yadda ki ke tunani ba ne, za ta amince fa, honeymoon zamu je"
Ta waro ido ta ce "Wane honeymoon kuma? Me ya rage kuma wani honeymoon zamu je, ai ka gama honeymoon ɗinka a nan"
"A'a fa, ga aiki ga stress, gara muje mu samu cikakken lokacin cin soyayyarmu ba hayaniya" yayi maganar yana sumbatar bakinta.
***
An kai ruwa rana sosai da mami a kan tafiyar nan, Alhaji ne ya tsaya tsayin daka a kan tafiyar, ya ce idan raihan ya dawo ayi zancen auren safiyya.
Duk da farida ta san sirikar ummi ba ta sonta, amma ba ta zaci ummi za ta samu kwanciyar hankali da nutsuwa haka ba, Ummi ta je ta yi musu sallama a kan tafiyar su china. Duk wanda ya san ummi a baya ya ganta yanzu ya san a cikin ni'ima take, iya kyan da fatarta tayi ka san tana samun kulawa.
Noor ta din ga murna, jin ummi za ta je china har da cewa ta gaisar mata da su bursuli.
Kwanciyar hankalin ummi ya tsayewa farida a rai, tare da jin cewar kausar ce yakamata ace a cikin wannan kwanciyar hankalin, inteesar dai ga ta a cikin daular, amma mijinta ba ya ɓanɓaruwa, gashi ya juya mata baya. Ashe tun kan aure ya kai ta aka yi mata allurar family planning, wai yafi son su gama cin amarci kan su tara yara, babu wanda ta gaya wa daga baya kuma abun ya bata matsala ciki yaƙi zama, wadda ya auro kuma ta samu ciki sai wulaƙanci take fuskanta iri-iri. Ga kausar ba makaranta ba mijin aure duk da ga kyau ga kwalliya.
Abdul kuma babu ƙwaƙƙwaran aikin yi.
Saura kwana uku tafiyar, Ummi da raihan suka je maiduguri ma, Mariya kamar ta haɗiye ummi, suma sun yi farinciki ganin ummi, raihan yayi musu alkhairi sosai da sosai.
Suke gaya mata har a lokacin bayan bikinta, dr. Yana zuwa ya kawo musu sha tara ta arziki, tare da duba lafiyar Mariya.
Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa ummi ba, karamcin kawu yahaya ya sanya ba ta taɓa mantawa da shi a cikin Adduo'inta, kuma a duk lokacin da ta samu abun alkhairi take kai masa da iyalinsa.
Jin mami ta matsa a kan maganar auren raihan, ya sanya jikin ummi yin sanyi, a baya tana ganin babu wani abu idan raihan ya ce zai ƙara aure, amma a yanzu fargaba ta shige ta da tsoro.
Dan a gabanta mami ke kiransa ta jaddada masa maganar auren, ko ma safiyyan ta kira shi wai zata gaishe shi, tana iya kokarinta wajen kar ta nuna masa wani abu na ɓacin rai, dan tana ganin idan ta yi masa haka ba ta yi masa adalci ba. Ta ji gaba ɗaya tafiyar ma ta fita daga ranta ba ta so.
Sai dai suna barin ƙasar, ta ɗan samu nutsuwa, mussman da kullum tana tare da raihan tana shan soyayya da kulawa kala-kala a wurin matashin mijinta.
Sun samu zuwa wurare masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga manyan manajojin su raihan, da suke kasuwanci tare. Shi yake kula da komai nasu kama daga masauki zuwa abincin su da sauran buƙatu.
Ummi ba ta taɓa tunanin ganinta a ko da airport ba, sai gashi ta keta hazo, ta bar ƙasa Nigeria.
Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda ba ta ga mutanen ƙasar na muzanta halittarta ba, sai ma bayan shirya musu wani cin abinci da managern yayi, da iyalansa da wasu daga abokan kasuwancin su, suke cewa ba su taɓa ganin baƙar fata mai kyan ummi ba.
Da aka fassara mata da turanci abun da suka ce, saboda galibi ba su iya turanci ba, mamaki abun ya bata, wai idonta mai kyau da fatarta, har ta fara tunanin ko ba'a suke yi mata, suka din ga layin hotuna da ummi.
A duk lokacin da suka fita shaƙatawa, sai mutane su yi ta kallonta, har wasu su nemi su ɗauki hoto da ita, suna yi musu tambayoyi mussaman idan ta yi shigar hausawa, duk da ta fi saka rigunan abaya a kan kayan hausawa.
Duk da ummi na ƙoƙarin kare mutuncin aurenta, da matan su kawai take gaisawa tayi hotuna, sai da kishin raihan ya kasa ɓuya.
Sun fita baki wani ruwa da daddare shan iska, take tambayar raihan "MD dan Allah mutanen nan da gaske suke, ko zagina suke yi da suka ce ina da kyau?"
Ya ja hancinta ya ce "Idan na faɗa ai ba kya yarda, you are beautiful baby"
Ta saka hannu ta shafi fuskarta ta ce "An ce fararen fata suna ƙyamar baƙaƙe, amma ni har ƴan uwana baƙaƙen ƙyamata suke yi"
Ya kwantar da muryarsa ya ce "Mutanen china suna da ƙarancin nuna wariyar launin fata, su kuma mutanenmu son zuciya ne kawai, da rashin bawa abun da muke da shi muhimmanci".
Ta sake jan numfashi ta ce "Ni fa bayan baba da mama, kai ne kawai ka ke cewa ina da kyau, sai noor gani nake duk Nigeria na fi kowa muni"
Ya ɓata fuska ya ce "Ban hanaki faɗar irin wannan maganar ba? Me ki ke nema a yanzu da Allah bai yi miki ba? Ubangijin da ya yi ki yana sonki, mama na sonki nima ina sonki to me ki ke nema kuma?"
Ummi ta girgiza kai ta ce "hmm MD kenan, idan aka ce ina da kyau wallahi sai in ji kamar zagina ake yi, saboda na fi sabawa da jin kalmar cin mutunci "
"Ni kuma wallahi a duniya, a yanzu dai ban sani ba ko a gaba, amma wallahi ba ki ga yadda ki ke yi mini kyau ba Salma, komai naki son shi nake, wallahi duk macen da na gani, sai in ga ba ta kai ki ba. Ina kaucewa auren Safiyya ne saboda a yanzu dai na ƙara aure ba zan iya adalci ba son da nake yi miki daban ne, a ƙasan zuciyata nake jin ki, bana son wani abu na rashin daɗi ya raɓe ki, ban san ya zan misalta miki ba ki gane ummi, kawai ni dai ki yadd ki saka a zuciyarki ina sonki, kuma wallahi ban taɓa ganin muninki ba ko sau ɗaya. Kawai ji nake duk matar da zan aura ba zan samu biyayya da kulawar da nake samu a wurinki ba, mutane kawai suna ganinmu ne, amma ba za su gane tarin baiwa da Allah ya yi miki kala-kala ba, su muninki suke gani, ni kuma abubuwan da nake gani game da ke ba zasu lissafu ba. Ina sonki kariun nisa'i"
Sanyin iskar wurin, da daɗin kalaman raihan, ya sanya wani irin shauƙi ya kama ummi, tare da jin ta a sama, kalaman na raihan suka sanya ta ji kamar a duniya babu wadda ta fita sa'ar miji. Abu kamar a mafarki ita da ake cewa ba zata auru ba, sai dai a taimaka a aureta saboda muninta, amma yau gashi Allah ya gwangwaje ta da miji na kere wa sa'a, kalaman na raihan ko ƙarya yake yi mata sun yi mata daɗi.
Ta rungume shi sosai ta ce "Allah ya barmu tare har aljanna Zaujul janna, kana cikin mutane masu muhimmancin da suka haska fitila a rayuwata mai cike da ƙalubale kala-kala, dan Allah kar ka daina sona, ko zaka yi aure a gaba ko ka so wata, dan Allah kar ka daina so na, ko da ka daina sona ka ɓoye mini dan Allah, kulawarka tayi tasiri a rayuwata idan na rasa soyayyarka da kulawarka komai nawa zai koma farko, kai kaɗai ne hope ɗina yanzu, an ce wataran ana gajiya da juna dan Allah kar ka gaji da ni" ta ƙarasa maganar kamar mai magiya.
Ya saka hannayensa biyu yana shafa bayanta, yana jin yadda take kuka.
"Soyayyar da aka gina da tubalin toka ita ke gushewa, tamu kuma da tubalin dutse muka gina ta, ni da ke har aljanna babyna" ya ƙarasa maganar yana ɗago fuskarta yana share mata hawaye.
Tausayin ummi ya cigaba da mamaye masa zuciya, tare da jin zai jure kowane ƙalubale ummi ta samu farinciki.
Kwanakin su ummi takwas a ƙasar, ɗaya daga cikin waɗanda suka ci abinci tare da su ummi, ta nemi iznin ummi a kan tana son ɗora videonsu da suka yi ita da ummi, a YouTube, babu tunanin komai ummi ta ce mata to, saboda yadda ta san da shigarta ta