Showing 129001 words to 132000 words out of 214133 words

Chapter 44 - CUTARWA AYSHERCOOL COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

22036

yayi zancen ya ji sanyi, amma ya san sai ta sake yin wani abun da zai tunzura shi, dan haka ya zaunar da ummi yana gaya mata, tare da nuna mata kuɗin, ya tambaye ta wani irin kaya take so.

Jiki a sanyaye ta ce "Duk abun da ka yi mini na gode kawu, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan magabata"

Ya amsa da "Amin ummana, ki yi ta addu'a kina haƙuri kin ji ko? Nasara ba ta zuwar wa bawa daga kwance babu jarrabawa"ta jinjina masa kai ta ce "In sha Allah"

Iya tayi mamakin jin abun da kawu Ilya suka ce mata an kai wa ummi, ta riƙe baki ta ce "Shi kuwa wani asarren ne zai kwashi wannan mummunar yarinyar mara fasali, har da kashe mata maƙudan kuɗi haka?"

Kawu Ilyasu ya ce "Oho musu, kuma yaron ma wai bai taɓa aure ba, amma an cuce shi gaskiya"

"Ai ba zai wuce yahaya shi yake ƙuƙƙula wannan abubuwan ba, kuma zai zo ya sameni har in da nake"

Magana ta cika gagarawa, cewar ummi ta samu wani hamshaƙin attajiri a kano za ta aura, kuɗin aurenta kawai naira dubu ɗari biyar.

Aka din ga surutu da yayata zance, har da masu zuwa yi wa iya Allah ya sanya alkhairi.

Kasancewar Alhaji Sabo da suka kai wa raihan kuɗi, matarsa ƙawar mami ce sosai da sosai, bayan gama bawa matarsa labarin abun da ya faru, ta ɗauki waya tana yi wa mami mitar duk ga ƴaƴan su amma raihan ya tsallaka waje zai auri bazawara.

Mami ba ta gane zancen ba, sai da ta yi mata dalla-dalla, hakan ya ƙara tunzura mami, ta tafi sashin Alhaji kamar za ta kama da wuta.

"Alhaji Tahir" ta kira sunansa kai tsaye.

"Na'am Bilkisu ya aka yi ne?"

"Wallahi raihan ba zai auri bazawara ba, ba zai yiwu ba, wai ka san yarinyar da zai aura bazawara ce?"

"Na sani, ba shi ya ce yana so ba?"

"Kuma ka kwashi kuɗi har 500k ku ka kai, to wallahi sai dai ayi wadda za ayi, auren nan ba za ayi shi ba, ban lamunci auren fari ya auri wata bazawara ba, lallai yarinyar nan munafuka ce macuciya, har aure ma ta taɓa yi"

"A irin wannan ƙadamin, idan ɗa namiji yana son abu ba ya ji ba ya gani, ba ya ganin aibun abun, ki bi a sannu kan yaron nan ya fara bujure miki, na so ace matar Alhaji Sabo ba ta yi gaggawar gaya miki ba, da kaina zan gaya miki, amma tun da ta riga ta gaya miki shikenan "

"Ba wani baka yi niyyar gaya mini ba, to idan shi ba shi da hankali, ni ina da shi"

Ya girgiza kai ya ce "Hankalin nan dai ban ga alama ba da saura bilki, baki san rayuwa ba haryanzu "

"Ni ka ke cewa bani da hankali?"

Ya tashi tsaye ya riƙo hannunta da ƙarfi ya ce "Ni da ke duk musulmai ne, da aka haufa a cikin musulunci gaba da baya. Kuma muna koyi da rayuwar annabi sallalahu alaihi Wasallam ne, idan kuwa haka ne, sunna ce mai ƙarfi raihan zai yi koyi da ita.
Bilki yaranki Allah ne ya shirya miki su, ba wai dan kina da techniques na yadda ake tarbiyar yaran ba, mutane da yawa na ganin bai dace biye wa yarana da nake yi a kan abun da suke so ba, ina tunatar da ke zamani ya sauya, ka yi wa yaranka tarbiyya dai-dai da zamani sai a zauna lafiya. Wannan baloƙoƙon da ki ke kamar a zamanin da, ba abun da zai haifar miki, illa bijirewar yaron nan, shawara nake baki kar ki matsa da yawa, dan yana wani stage ne da ba ya ji ba ya gani, cikar muradi kawai yake fata, amma idan kin ƙi ji gaki nan ga shi" kamar ta shaƙe Alhaji Tahir haka take ji, tare da jinjina tsantsan rashin hankali da wauta irin na raihan, da ma ba ta ce za ta yi masa aure ba, ta bar shi a haka, kawai daga cewa za ta yi masa aure, ya jajubo wannan ina da munin wai ita zai aura.

Raihan ya fito daga Masallaci sallar la'asar, Ummi ta kira wayarsa, ya samu wuri ya tsaya tare da ɗagawa "Hello my love"

Cikin sassanyar muryarta da yake cewa iyayi ta ce "Barka da yamma"

"Yauwwa barka, kin wuni lafiya?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya su mami?"

"Duk suna lafiya, ina noor ɗina?"

"Tana tahfiz" ta faɗa a hankali.

Ya ce "Kirana ki ka yi ki ji muryata love?"

Ta ɗan yi murmushi ta ce "Muryartaka ba gata nan a what's app ɗina ba? Su Alhaji sun zo ɗazu"

Yayi murmushi ya ce "Shiyasa na ji bakin ki yaƙi rufuwa, zaki yi wuf da ɗan kyakykyawa yaron da ki ka raina"

Ta ce "Hmm amma kuɗin da su Alhaji suka kawo, har da kayan lefe ko?"

"Yaushe muka yi haka da ke?"

"Ba muyi ba tambayarka kawai na yi, kuɗin da yawa ka manta na taɓa aure ne?"

"Ke ki ka san kin taɓa auren ai, ni ban sani ba, kuma ke ina ruwanki da abun da zan yi, ke da ba kya so na, ina ruwanki idan zan yi lefen koma ba zan yi ba"

"Yi haƙuri" ta faɗa a sanyaye.

Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ummi ke malama ce, annabi Sallallahu alaihi Wasallam, mutum ne mai hidimtawa iyalinsa, kuma rayuwarsa ce abun koyi a garemu, haka zalika mahaifina mutum ne mai hidimtawa iyalinsa sosai haka na tashi na ga yana yi, kuma babana mudubina ne, bana cikin maza masu nakasashiyar zuciya duk abun da na kashewa wadda zan aura ribata ce, kin san tsare hakkin iyali yana ƙarawa namiji kima da kwarjini a wurin iyalinsa. To balle ni da nake yaro kuma ba a so na, dole sai na yi aiki tuƙuru tukuna, dan saya wa kaina kima a wurin matata"

Ummi ta numfasa ta ce "In dai kai Allah ya ƙaddara ka zama mijina, ba ka buƙatar wahalar da kanka, zan yi maka biyayya iya yi na, ban yi wayo sosai da mahaifiyata ba, amma mama mace mai matuƙar biyayya ga babana"

Cikin yanayi na nishaɗi ya ce "Allah ya sakawa iyayenmu da mafificin alkhairi ummi, ya nuna mana auren nan lafiya" Ummi ta yi shiru ta kasa amsawa.

Hira suka yi sosai, sannan suka yi sallama.

Raihan yana zaune a ɗakinsa yana danna system yana shan lemon kwali, Salim ya yi sallama a ɗakin.

Raihan ya amsa yana mamakin ganin Yaya salim a ɗakin nasa, dan sai ya shafe shekara bai shiga ɗakin sa ba.

Kamar wanda yayi baƙo raihan ya tashi yana faɗin "Sannu da zuwa yaya"

Salim ya jinjina masa kai ya zauna, ya kalleshi ya ce "Yanzu muke magana da hajiya, ashe yau an yi maka engagement? Ubangiji Allah ya sanya alkhairi babban mutum, girma zai ƙara hawa kanka, Allah ya sanya alkhairi"

Duk in da ɗan uwa yake ɗan uwa ne, maganganun ummi suka din ga dawo masa, ya dubi Salim ya ce "Na gode sosai da sosai yaya, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya sa ayi naka kafin ayi nawa"

Salim yayi murmushi ya ce "Sai ka ce wasan yara? Allah ya baku zaman lafiya, ace ina gaisheta" yayi maganar yana shafa sumar raihan.

Salim shi ne babba, aƙalla ya kai shekaru talatin da huɗu, ya fi Sagir sauƙin kai, ba shi da magana, sannan mutum ne mai son kaɗaici, amma akwai abokan banza, dan su suka koya masa shaye-shaye.

Raihan ya ce "Za ta ji, amma ita tana yawan cewa a gaishe ku, da kai da Yaya sagir"

Ya ɗan kalli raihan ya ce "Ta sanni ne?"

"Eh, ummi ce ai ƙawar maryam, ta sanku, sannan ina yi mata zancenku"

Ya ce "Ohh that dark lady, mai brwon eyes ko? Wow na yi maka murna she's decent and good lady"

"Amm yaya dan Allah da gaske ummi mummuna ce? Mami tana ta complain a kan hakan"

Salim ya ce "Ita wannan mamin naka, ra'ayi idan ba nata ba, kowa bai iya ba, just go ahead, ita kuma mamin ka yi ta sakata a addu'a, Allah ya kwantar maka da hankalinta shikenan kawai"

Raihan ya riƙe hannun Salim ya ce "Na gode sosai Babban yaya, Ubangiji Allah ya baka kujerar MD Tahir and Son's"

Salim ya ce "You are not serious, kai dai Allah ya tayaka riƙo, ya sanya maka albarka, take care" ya fice daga ɗakin.

Raihan yayi shiru, babu shaƙuwa sosai a tsakaninsu, saboda shi raihan a Bauchi ya ƙarasa girma, gidan yayar Alhajinsu Hajiya Aisha, mijinta da ita da Alhaji duk cousin's ne, shi kuma su Salim suna nan kano, kuma mami ba ta da aiki sai gaya masa yayi a hankali da Hajiya da yaranta ba sa ƙaunar su, kuma kar su Sagir su koya masa shaye-shaye.

Sai dai shi bai ga alamar hakan ba, hasali ma ba sa wani shiga shirgin sa, dan ba sa'aninsa bane ba, har gara Sagir ma suna faɗa da raihan sosai. Hajiya kuwa kamar ɗan da ta haifa haka ta ɗauki raihan da ma duk ƴaƴan mami, amma matan duk mami ta hure musu kunne.

Farida ko a jikinta, jin an kawo kuɗin auren Ummi, dan kawai jikinta bai bata ummi wani mutumin kirki za ta aura ba, dan da an kawo abun arziki da jiki na rawa dr. Zai gaya mata, sai dai yayi mata shiru bai gaya mata me aka kawo ba, kuma wa za ta aura ba.

Noor ta kasa nutsuwa saboda murna, sai tsara yadda bikin zai kasance take yi, har da cewa sai dr. Ya ɗinka mata sababbin kaya guda hamsin har da irin na amarya da ango.

Saboda tsokana ta je ta samu kausar tana bata labarin yadda raihan yake, ta koreta amma ta ƙi tafiya ta cigaba da cewa "Kin ganshi kuwa? Wallahi duk saurayinki babu mai kyan sa, fari ne fa sosai da sosai, wallahi motarsa ta fi biyar, masu kyau ɗan bala'i, idan yana magana yana ɗage girarsa guda ɗaya, me kyau da shi" kasancewar hankalin kausar ba a kan noor yake ba, ya sanya sam ba ta fahimci me noor ɗin ke faɗa mata ba.

Mami ba ta nemi raihan ba, sai yau da safe ya je karyawa, tayi masa shiru, ya gaisheta ta amsa masa, ya kammala cin abinci, ya tashi zai fita, ta janyo hannunsa da ƙarfi ta tankaɗa shi har ɗakinta ta mayar da mukulli ta rufe, ta dawo ta ɗauke shi da mari har kashi biyu.

Sai dai ya tsaya yana kallon mami da mamaki, ba tare da kuma ya yi yinƙurin kare marin ba.

Ta ɗora da ɗura masa ashar, amma ya sunkuyar da kansa ƙasa yana kallon tiles.

"Ashe ba ka da hankali raihan, ba ka da mutunci ba ka san abun da yake maka ciwo ba, ashe yarinyar nan bazawara ce, ka je zaka auri bazawara sauran wani, da ƙuruciyarka da komai, ashe baka san me yake yi maka ciwo ba?
To ai dama ni na ce zan yi maka aure ko? To na janye na fasa, ba zaka yi auren yanzun ba, sai ranar da ka fuskanci kai mutum ne da daraja da girma. Dan haka umarni nake baka ba shawara ba, ka je ka janye maganar auren nan. Saboda hauka tana bazawara ga muni da rashin gata, amma ka ɗauki kuɗin aure har dubu ɗari biyar, ka bayar a kai, to baka isa ba wallahi, idan har ni na haifeka ka ka je ka gaya wa mahaifinka ka fasa auren nan, ba zaka aureta ba dan kai kaɗai ne kawai zaka gaya masa haka ya yarda, idan ba haka ba zaka fuskanci abun da baka taɓa tununi daga gareni ba, na gaya maka. Ka wuce ka je ka same shi ka ce masa ka fasa yanzu ba anjima ba. Matar da na zaɓa maka ita zaka aura, duk matan garin nan masu kyau da aji, ba ka ga kowa ba sai wannan cilakowar?"

Tuni fuskar raihan ta yi jawur, jijiyoyin kansa suka mimmiƙe, saboda tashin hankali da ɓacin rai, ya buɗe ƙofar ya fice, yana gazgata maganar ummi da ta taɓa ce masa su mata mutane ne masu masifar son kansu, bai yi mamakin hakan daga mami ba, duba da yanayin halinta kuma gashi jiya ya ga Anty rakiya ta zo gidan, ya san ita zata sake ziga mami, amma ita bazawara ba mutum ba ce?.

Zuciyar sa na wani irin tafasa ya tafi sashin Alhaji, Alhaji tashin sa kenan, yana ta shiri za shi Abuja, ya ga raihan, bai yi wa raihan magana ba, Raihan ya ce "Na fasa auren ummi, na janye, ka karɓo kuɗin auren, amma idan aka karɓo kuɗin auren nan an karɓo kenan aure sai dai in ga ana yi, babu ƴar da za a sake kaiwa kuɗin aure da sunan zan aureta" yana gama maganar ya juya ya fice.

Alhaji bai yi niyyar dakatar da shi ba, dan ko magana bai yi masa ba, ko raihan bai yi masa bayani ba, ya san bilki ce ta kunno shi, dan raihan akwai ladabi, idan ya je bango kuma akwai taurin kai, dan haka Alhaji ya ƙyale shi, da nufin idan ya huce sai su yi maganar.

Ummi na wurin aiki tana ta shigar da sabbin price a computer, ta ga raihan ya shigo, fuskar sa babu walwala.

Bai ce mata uffan ba, ya zagaya ya zauna a kujerar kusa da ita.

"Baka gaya mini zaka zo ba, ai da na dafo maka wani abun, baka da lafiya ne?"

Ya girgiza mata kai ya ce "Bauchi zan tafi daga nan, na zo mu yi sallama ne, babu lallai na dawo nan kusa"

Da sauri ummi ta ce "Saboda me?"

Ya kalleta wani abu mai ɗaci na kaiwa na komowa a zuciyarsa, ga wani irin tausayin ummi da yake ji, idan ya fasa aurenta bai yi mata adalci ba sam.

"Ka gaya mini mana, menene meyafaru gaba ɗaya ka yi wani iri, me aka yi maka ne?" Tayi maganar cikin rauni sosai, saboda ba ta fiye ganinsa a irin wannan yanayin ba.

Kasa magana yayi, ya tashi ba tare da ya ce mata komai ba zai tafi, karo na farko ta riƙo hannunsa a nata ta ce "Ka zauna ka gaya mini menene, ka ɗaga mini hankali ka gaya mini menene?"

Ya zauna a hankali ya ce "Ummi, ban san me yake shirin faruwa ba, daga yanzu zuwa ko yaushe abu mai daɗi ko akasin haka ka iya faruwa, dan Allah ko me ye ya faru, ni dai ki saka a ranki ina son ki sosai da sosai ummi, kuma ba zan daina sonki ba, ki tsananta yi mana addu'a, ko da ke ba kya so na, ni ina sonki ummi"

"Raihan, dan Allah idan a kaina ne, kar ka samu matsala da ƴan gidanku, ahali sun fi komai daɗi, ni daga baya ka sanni, zaka iya canza ni, su kuwa fa, in dai nice babu komai zan fahimceka amma ahalinka na da muhimmanci a rayuwar ka, ni tsangwama da kyara na saba da su"

"Amma ba zaki dauwwama a cikin su ba, akwai hatsari mai girman gaske a rabani da ke, ko kin auri wani ba ni ba, ba zan iya rabuwa da ke ba, zan tafi bauci wataƙila zan shafe tsayin lokaci, amma zamu din ga waya in sha Allah, take care am going to miss you dear" yayi maganar yana shafar gefen fuskarta. Ya tashi ya fice.

Haka kurum gabanta ya tsananta faɗuwa, a duk lokacin da ya ce ko tayi aure ba zai iya rabuwa da ita ba, sai ita ma ta din ga jin irin haka a zuciyarta, kamar itama ba zata iya rabuwa da shi ɗin ba.

Jikinta duk yayi sanyi, har ta kammala aiki ta tashi, bayan ta koma gida tana ta neman layukansa, amma shiru ba ta samunsa a wayar.

Sai washegari ya kirata da wata lambar daban, ya ce mata yana bauchi cikin ƙoshin lafiya, da wannan lambar za ta din ga kiransa.

Jin muryarsa wasai ya sanya ta cewa "To amma yanzu zaka dawo ko?"

"Ko zan dawo ba yanzu ba, kewarki ce kawai take damuna"

"Dan Allah ka dawo ka ji babban mutum, manya ba sa haka, idan laifi muka yi mutanen kano, tuba muke yi kar a hora mu da yi mana yaji, ka san menene zan dafa maka abinci mai daɗin gaske, na san abun da ya saka bar garin zuwa yanzu ka huce ai ko? Zan yi maka girki"

Raihan yayi dariya ya ce "Matar raihan, kirarin nan kawai ya ƙara sanyaya mini zuciya, kar ki saka na ɗaukko mota na taho mana. Ke dai ki yi ta addu'a kamar yadda na ce miki kin ji ko?"

"To shikenan, amma dai ka yi tunani a kan lamarin nan".

Can gida kuwa Alhaji Tahir ya saka mami a gaba da masifa, tare da cewa duk in da ɗan sa yake sai ta fita ta nemo shi, dan ba a samun sa a waya, baya gida kuma baya office.

Abu kamar wasa, hankalin mami ma ya tashi, ba ta yi zaton raihan zai yi haka ba.

kwana kusan biyar, babu raihan babu dalilinsa.

Dr. Ya samu ummi ya ce mata ta shirya kayanta, washegari za su yi tafiya ta kwanaki uku, ta sanar a wurin aikinta.

Ummi tayi ta mamakin, ina za su je haka afujajan babu cikekken shiri babu komai.

Ba ta matsa masa da tambaya ba, ta shirya kayan kamar yadda ya umarce ta.

Mami kuwa, Anty rakiya ta bata shawarar ta je har gida ta ci mutuncin ummi, kuma ta tursasata ta gaya mata in da raihan yake, dan ba zata kasa sani ba.

Alhaji Tahir ya shigo a fusace ya ce "Kin yi naki role ɗin, barkana tun da na san in da ɗa na yake, amma bari na gaya miki wani abu, idan har kin cigaba da dagewa ba za ayi auren nan ba, to ki tabattar da zan kawo yarinyar nan matsayin matata ta uku, dan ba zaki zubar mini da mutunci a idon duniya ba"

Gabanta ne yayi wata irin mummunar faɗuwa, wayarta ta fara ringing, cikin rawar jiki ta ɗaga. Saboda kura ta san gidan mai babban sanda bijirewa ɗaga wayar ka iya jefata cikin matsala.

"Bilki, ashe baki da mutunci baki da hankali? Ashe wayewar ta ki ta ƙarya ce, saboda wulaƙanci da rashin mutunci ke da ba a aure, da zamu bari Tahir ya aureki ne? Ke kin san auren zumunta muke yi, da matarsa ƴar uwassa tana son shi yana son ta, ya auro ki, mu a cikinmu waye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login