Showing 111001 words to 114000 words out of 214133 words
kayan ɗaya bayan ɗaya da kallo.
Cikin haƙilo farida ta ce "Sai ta yi maka bayanin in da take samun wannan kayan, idan ba wani mugun abun take aikatawa na rashin gaskiya ba"
Tsulum noor ta tsoma baki ta ce "Kai, yaya raihan ne fa ya saya ya bata, ko yaya ummi?"
Kamar gunki ummi ta sake sandarewa, dan ba ta san ta aka yi noor ta riƙe sunan raihan haka ba ma.
Dr. Ya durƙusa ya tsince kayan, ya mayar cikin ledarsu, ya miƙe tsaye ya kalli farida ya ce "Bani mukullin da ki ka rufe mata ɗaki"
"Ban gane ba, me ka ke nufi?"
"Abun da ki ka gani, ba budurwa ba ce ba? Ke abubuwan da ake kawowa kausar cikin gidan nan zama ki ke ki tuhume ta?"
"Amma tsakani da Allah ka taɓa ganin wani yayi sallama da ita da sunan yana sonta, da zai saya mata wannan kayan masu tsada?"
Ya wuce ɗakin farida, tabi bayansa tana cigaba da masifa, ya ɗaukko mukullaye, ya dubi ummi ya ce "Mu je"
Tabi bayansa hawaye na zuba daga idonta, ya buɗe ɗakin nata, duk an hargitsa shi.
Ya ajiye mata kayan, ya kalleta ya ce "Mamana, na yarda da ke ɗari bisa ɗari, na san ba zaki aikata wani abu na Allah wadai ko a bayan idona ba, goya miki baya baya nufin, ki aikata abun da bai dace ba, ba zan matsaki a kan lallai sai na san me ki ke ciki ba, ni uba ne, kuma malamin makaranta, na san yadda zan tafiyar da tarbiyar yarana.
Kin mai munzalin da bin diddigin rayuwarki, ba shi ne mafita ba, amma dai ina sake yi miki tuni, da ki ji tsoron Allah, ki kuma kare mutuncinki, amma har ga Allah ni bana zargin ki, ki goge hawayenki ki samu ki huta, ni ban gaji da zamanki da mu a gidan nan ba, saniya ba ta taɓa gazawa da ƙahonta, dan haka ki kwantar da hankalinki komai mai wucewa ne, kuma in sha Allah zaki sha mamakin abokin rayuwar da Allah zai zaɓa miki, ke dai ki cigaba da tsare mutuncinki"
Ummi ta jinjina masa kai, ya fita daga ɗakin, ta zauna a hankali tana kallon kayan, tayi shiru tana nazari, idan har zargi zai shiga zuciyar dr. Game da ita, gara ta nemi duk mai yiwuwa ta rabu da raihan. Tabbas kaya ne masu tsada da ta cancanci a tuhumeta a kansu, da kawu ya matsa ta ina zata fara yi masa bayanin wannan alaƙar ta su, da ba kowane mai hankali ne zai sanyata a gurbi mai ma'ana ba.
Ya zama dole ta nesanta kanta da raihan, duk da abu ne mai wahala a wurinta, daga haɗuwarsu zuwa yanzu, ya gina wani tarihi da ba zai rushe ba a rayuwarta, raihan na daga cikin mutane masu muhimmanci da ba zata taɓa mantawa da su ba, zuciyarta ta saba sa shi, ta shaƙu da shi, ya bata ƙarfin gwiwa daban-daban, ya sanya ta jin ita cikakkiyar mace ce ɗan Adam da zata iya gogayya da kowa, tabbas raihan ya cancanci a kira shi ƙaraminsu babbansu, domin kuwa a manyan ba kowa ne za a samu da irin qualities ɗin sa ba.
A hankali ta tattare kayan, ta gyara ɗakinta, ta rama sallolin da suka tsere mata, ta cigaba da tunani.
Ta ɗaukko wayarta ta duba, missed call ɗin sa duk a wayar, har da saƙo yana tambayarta meyafaru ba ta ɗaga wayarsa?.
Ta kashe wayar gaba ɗaya ta ajiye, tana son fara koyawa kanta janye wa raihan.
Ta yinƙura ta fito daga ɗakinta, amma ta jiyo hayaniyar kawu da farida, kuma duk a kanta, jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, da tana da wurin zuwa da zata bar wa farida gidanta, ko kawu ya samu sassauci daga wulaƙancin da farida ke yi masa.
***
Anty Rakiya ta cigaba da matsa lamba, da ƙarfafa mami, a kan lallai a haɗa auren nan na zumunci, ita kuma mami ta cigaba da matsawa raihan, tare da ziga Alhaji a kan lallai a takura raihan yayi aure.
Abun ya fara damun raihan, dan haka ya samu hajiya da maganar, Hajiya ta ce "Babban mutum, menene a ciki dan ka yi aure, gaskiyar maminka ne shi ne cikar kamalarka ai".
"To hajiya sai in yi aure su yaya ba su yi ba, kuma nema ake fa a sakani na auri wadda ba na so, ni bana son yarinyar nan"
"Raihan, dan ka riga su Salim aure babu laifi a ciki, bujirewa umarnin mahaifiyarka ba shi da fa'ida, ko ba ka auri wadda take so ba, ka yi ƙoƙari kai ka kawo musu wadda ka ke so"
Yayi shiru yana nazari, sannan ya kalli hajiya ya ce "Shikenan hajiya na gode sosai da sosai"
Ya tashi ya fita, yana nazarin maganar Hajiya.
Gefe guda kuma yana mamakin kasa samun ummi a waya, har ta what's app, ya fara tunanin ko dai wani abun ya sameta ne.
Yaje wurin aikinsu Ummi, ya tambayi mai yi musu shara, ya ce masa ba ta je ba.
Ita ma ummi a lokacin da take ƙoƙarin ƙauracewa kiran raihan, headmastern su ya kunno kai, sai ya din ga kiranta a waya, wai su gaisa, wannan satin har da bata dubu biyu wai ta hau mota, saboda ɗawainiya da take yi da ɗalibansu.
Hankalinta ba a kan wannan yake ba, kamar ta fi raihan azabtuwa da ƙauracewar da ta yi masa, gashi pressure cikin gidansu, ta ƙara yawa, dan kuwa farida kullum cikin masifa da tashin hankali take a cikin gidan nan.
Babu tsammani dr. Ya samu ummi ya ce mata "Mamana, wani mutum ya zo wurina, ya ce mini yana sonki, kuma babu daɗewa yake son ayi auren, na bashi damar ya zo ku gana, sai dai ba ina nufin lallai sai kin aure shi bane ba, bana son yi masa karambani, ganin babban mutum ne, amma duk yadda ku ka yi sai ki gaya mini"
Ummi ta amsa masa da to ne, amma ta shiga cikin fargaba da zullumi, tare da tunanin, waye wannan? Kai tsaye ya tafi wurin dr.?
Abun yayi ta bata mamaki, sai dai sam ba ta ɗokin abun, domin kuwa bayan saka wayarta a flight mode, sai ta koma tana duba messages ɗin raihan.
Gaba ɗaya ummi ta manta da dr. Ya ce za ta yi baƙo, saƙon raihan na ƙarshe ya tsaye mata a rai.
"Ummi na bincika kina lafiya, amma you are avoiding me, ban sani ba ko nayi miki laifi ne, idan na yi miki laifi ne dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mini, ina cikin damuwa sosai wallaahi, ban zaci shaƙuwarmu ta kai in shiga damuwa haka ba, dan Allah ki yi mini reply ummi, zan tafi italy gobe in Allah ya kaimu da asuba, dan Allah ki yi mini magana"
Ajiye wayar ummi tayi, idonta na cika da hawaye, "Ban kyauta maka ba raihan, amma yanzu ko na yi maka bayani ba zaka gane ba, buyagi zaka yi mini" tayi maganar a hankali, tana sake kallon wayarta.
"Yaya ummi, wai baƙonki ya zo" noor tayi maganar ba tare da ko sallama ta yi ba.
Ummi ta jinjina mata kai, tare da jin matsananciyar faɗuwar gaba, dan wannan ne karon farko da zata tsaya tayi zance da wani, da sunan yana sonta, gashi alamu sun nuna da gaske yake, tunda ya biyo ta wurin dr., Duk da abun da take ta addu'a a kai kenan, idan tana da rabon aure, Allah ya kawo mata miji nagari, sai dai gaba ɗaya ba ta murna da lamarin a yanzu, kuma ta rasa dalili.
Sai dai ta tsinke da al'amarin, ganin headmastern su a gareji, wai shi ya zo wurinta, kenan shi ne baƙon?
Suka gaisa suka zauna a kan fararen kujeru, tana bin sa da ido, dan ba ta gama yadda da shine baƙon ba.
Yayi gyaran murya ya ce "Wato ummi na san zaki yi mamakin ganina, da dalilin zuwana, duk da nasan mahaifinki yayi miki bayani.
To ni dai ummi ba wani abu ne ya kawo ni wurinki ba face alkhairi, na daɗe ina sonki, tun ranar da na ga kin cire hijjabi kina alwala, watannin baya baki ganni ba ke amma, to a lokacin gidana mata huɗu ne, amma yanzu Alhamdilillah mun rabu da ta ukun, dan haka akwai gurbin mutum ɗaya, ya sanya na ce tun da naga alamar babu tsayayye bari ni na tsaya, mu dai-daita mu rufawa juna asiri, dan yanzu kin san maza tsada muke yi" yayi maganar yana murmushi yana kallonta.
Ummi dai sama-sama take jin sa, ƙasan zuciyarta lissafi take yi, ta yi wa raihan reply ko ta ƙyale shi, ta san duk daɗewa idan ya dawo sai ya nemeta.
Dan haka sama-sama take jin maganganun headmastern.
"Ba zan takuraki yanzu ba, amma dai ki yi tunani, dan kuwa da wuri nake son ayi auren nan, bana son ɓata lokaci, kuma za ayi abu ne dai-dai talaka da tsarin addini, ba wani ɓarnar bidi'a, in kawo abun da Allah ya yassare ayi"
Ummi ta yi ajiyar zuciya ta ce "To malam, idan na yi tunanin sai mu yi magana"
Ya ce "Yauwwa ummi, Allah ya wuce mana gaba " ta amsa da Amin, ya tashi ya tafi, ita kuma ta dasa sabon zama tana nazari da tunani.
Sai da ta ji sauron wurin na neman halakata, sannan ta tashi ta koma cikin gida.
Kitchen ta nufa ta zubo abinci, zata fito farida ta tare ta ta ce "Ubanki ne ya kawo abincin?" Ummi ta girgiza kai.
"To ajiye ki fita, mayya mara zuciya, ai si ki je wurin waɗanda ki ke bi ku watse su saya miki kaya, su saya miki abincin, wallahi takura da masifa yanzu ki ka fara ganinta, sai ranar da ki ka bar mini gida, ko ki yi aure, ko ki koma in da ki ka fito ko ki bi duniya "
Salin alin ummi ta ajiye abinci, ta bar kitchen ɗin.
'Tabbas! Tura ta kai bango, yakamata na yi wani abu na matsa daga gidan nan, na fuskanci ƙalubalen da ke gaba, zaman gidan nan yana neman fin ƙarfina" tayi maganar a zuciyarta.
Abokin kukan nata ga ƙoƙarin da take yi a kansa, ta nesanta kanta da shi.
Abubuwa suka cigaba da ɗaukar zafi, dan da kawu zai koma aiki, sai da ya gindawa farida sharaɗi, a kan muddin ya dawo ya tarar ummi ba ta nan, sai ya saketa.
Farida har mamaki take yi, yanzu asirin ya daina kama dr. Al'amari in dai ya shafi ummi, ba ya saurarawa.
Ummi ta din ga sallar dare tana kai wa Allah kukanta, amma a ƙasan zuciyarta ta ji ta amince da auren headmaster, no matter what wahala ba yanzu ta fara shigar ta ba, tarwatsewar gidan dr., Da kuma alƙarsu da raihan su ne manyan barazanar ta a yanzu, idan ta yi aure ta san ta rage kaso mafi yawa daga matsalolinta.
Raihan ya sha mamakin burus da ummi ta yi da shi, ba dan ba ta ganin saƙonninsa ba.
Gajeren saƙo ta tura masa "Baka yi mini komai ba raihan, tarayyarmu na barazana ga kwanciyar hankalina, da jefa zargi a zuciyar mariƙana, ka yi haƙuri da hukuncin da na yanke"
Message ɗin ya nuna blue tick, alamar ya ga saƙon amma yaƙi reply, tun ummi na jiran yayi reply, har ta sare, sai kuma abun ya dame ta ta rasa sukuni, ga headmaster ya matsa mata kamar maye, ita har mamaki take yi, duk lokacin da suka shafe, bai ji yana son ta ba, sai watannin baya da ya ganta tana alwala, mata huɗu sun rabu da ɗaya zai aureta, kodayeke wannan duk bai dameta ba, wutar gabanta take ƙoƙarin kashewa, dan haka ta ce masa ta amince.
Tamkar ya goya ummi, saboda murna da nishaɗi, ta amince da aurensa, ya ce mata zai zo wurin kawu su yi maganar kawo kuɗin aure, ta ce masa baya nan sai ya dawo.
Ya fara yi wa ummi huɗubar shi talaka ne, dan haka kuɗin sadaki, da na lefe da na aure, zai bayar dubu ɗari, dan Allah ta ce ta yarda a haka, ko da babanta zai ce ba yadda ba.
Ummi ta amsa masa da to, dan ba ta da burin da ya wuce ta ɗaga daga gidan nan, ita ma tana burin ta ganta a ɗakinta, ko ta samu sauƙin gorin da take sha.
Kullum cikin duba wayarta take, taga raihan yayi mata reply na message ɗin da tayi masa, amma yaƙi yin reply, wasu lokutan tana kallon sa online, amma bai yi responding ba.
Tunani ta din ga yi hanyar da ta bi tana neman maraba da raihan tayi musu tsauri daga ita har shi, amma ta san idan tayi masa bayani, ba zai taɓa tsayawa ya fuskanceta ba, dan akwai shi da kafiya wasu lokutan.
Noor tana ta gyara wa ummi kan mudubin ta, tana jera mata mayukanta tana faɗin "Ai yaya ummi ba sai kin cigaba da ɓoyewa ba, kawai ki jera abun ki, dama na san dr. Ba zai yi miki faɗa ba" ta lura hankalin ummi baya kanta, dan haka ta ce "Wai yaya ummi me ki ke jira a wayar ne, ko salary ki ke jira ne?"
"Noor raihan ya daina kulani"
Noor ta ɗan waro ido ta ce "Faɗa ku ka yi? Innalillahi yaya raihan ɗin namu?"
Ummi ta ce "Ni na fara daina kula shi, noor bana son zargi ya shiga ran kawu a kaina ne, kuma aure nake son yi, bana son na yi aure mu kasa rabuwa".
"To yaushe zaki auren?"
"Malam ya ce idan kawu ya dawo zai zo su yi magana ya kawo kuɗin aure, sonake ya kawo kan raihan ya dawo"
Noor ta kwaɓe bakk ta ce "Wai wani malam, ni fa bana son malam ɗin nan, Astagfirullah bari dai na yi shiru, amma dan Allah kar ki auri wani malam, ki auri raihan mana" ummi ta zare ido ta ce "Ke ƙanina ne fa, kamar ɗan uwa yake a wurina, malam ya ce zai bayar da dubu ɗari kuɗin komai da komai, kar a wuce wata uku, amma ban san yadda za su yi da kawu ba".
Kamar shashasha noor ta kalli ummi ta ce "Wai ke yaya ummi, ni na rasa me zance, shikenan ke ba za a kawo miki lefe ba? Matansa fa uku, gashi tsoho, to kina son sa ne?"
"Mama ƙyaleni, surutun nan naki ma ya fara damuna".
"Hmm, Yaya raihan yayi fushi da ke fa, har makarantarmu ya je, bayan mun dawo daga gagarawa, ya tambayeni idan tare muka dawo kuma lafiyarki ƙalau, na ce masa eh. Ya jinjina kai ya tafi"
Cikin tsananin mamaki ta ce "Ya aka yi ya san makarantar ku har ya je? Sau biyu fa kawai kuka taɓa haɗuwa, Kin ga dalilin da yasa nake son mu rabu, raihan ya iya rigima fa"
Noor ta ce "Eh amma yana da kirki sosai ai, tun da ya taɓa bani kuɗi, wannan malam ɗin gaskiya talaka ne, ko kuma wayo, dubu ɗari fa ba ta da yawa sosai, shikenan ke ba za a kawo miki akwatuna masu yawa ba, kamar na inteesar"
Ummi kawai ta kwana ta yi wa noor shiru.
Ta cigaba da kallon wayar, a ranta ta ce 'Haba babban mutum, manyan ba sa haka fa' ta cigaba da duba chats ɗin su na baya.
Headmaster ya kira dr. A waya, yana tambayarsa yaushe zai dawo, so yake da ya dawo, ya kawo kuɗin, dr. Ya ce masa baya son gaggawa ya jira shi tukuna.
Wasa-wasa kusan sati uku kenan, raihan da ummi ba su yi magana ba, ba kuma dan hakan yana yi wa kowanensu daɗi ba.
Ummi ta kira direban da yake aikowa ya karɓar masa abinci, ta tambaye shi ko raihan ya dawo, ya ce mata a'a.
Yanayin sintiri da nacin da headmaster yake yi mata, abun har mamaki yake bata, kamar ya ɗauketa ya kaita gidansa ya ajiye.
In da Allah ya rufawa ummi asiri, aikin nan nata, tana ɗan samun salary, idan tayi girki ta gama farida sai ta hanata abinci, tayi ta janyo mata masifa da bala'i da miyagun alkaba'i, tare da fatan ta sha wahala a rayuwa kamar yadda ta wahalar da ita a gidan aurenta.
Ummi a ranta ta ce 'Wahala waccece ban sha ta ba, kuma ban cutar da ke ba a zamanmu ke ki ka cutar da ni!"
Tun da dr. Ya zo gida, headmaster yake sintiri, a kan zai kawo kuɗin, dr. Ya ce ya ɗan ba shi lokaci tukuna.
Hatta wurin aiki manager ya lura yanayin ummi ya sauya, kamar wani abu na damunta, amma dai yayi shiru bai ce mata komai ba.
Dr. Ya kira ummi ya tambayeta ko tana son malam Isa, ummi ta ce eh.
"Ummi, kar takura ko damuwa ta sanya ki kai kanki ga halaka, rauwar aure ba rayuwar gida ba ce da babu nauyin kowa a kanki, kar ki kai kanki in da zaki yi dana sani, mutumin nan babban mutum ne, kar ki zo daga baya azo a samu matsala, ki dai je ki sake tunani" ummi ta amsa masa da to, ba dan ta so ba, ita fatanta kawai dr. Ya amince.
Kasancewar yau babu coustomers, ummi ta bar reception ta koma in da take zuwa ta yi salla ta ci abinci ta kwanta, tana cigaba da duba chat's ɗin su da raihan.
Ƙamshin turaren raihan ne ya fara yi mata sallama, ta zaci hallucinating kawai take yi, sai dai ba ta gama tunanin ba, ta ganshi a tsaye a kanta.
A zabure ta tashi zaune, tana bin sa da kallo.
Wani irin kwarjini ta gani a tare da shi, wanda ba ta taɓa gani a tare da shi ba, fuskarsa a matuƙar haɗe, kamar ba ya dariya.
"Raihan" ta kira sunansa a hankali.
Ya nemi wuri ya zauna, ya ƙura mata ido sannan ya ce "Salma wannan shi ne tukuicina daga gareki ko? Ko rabuwa ki ke son mu yi, yanke alaƙa da ni kai tsaye ba tare da wani dalili ba kina ganin shi ne mafita? Bafa a rana ɗaya muka gina alaƙar nan ba, ummi dama zaki iya wulaƙanta ɗan Adam har haka kamar yadda ki ka yi mini?"
Cikin rauni ta ce "A'a raihan, ba haka bane ba, dan Allah ka fahimce ni" nan ta gaya masa bayan dawowarta gida abun da ya faru, yadda farida tayi mata bincike ta nuna wa dr.
"Raihan wulaƙanci ba halina bane ba, ina ma naga ƙarfin gwiwar da zan iya wulaƙanta wani? Raihan ba kowa zan yi wa bayanin alaƙarmu ya kalli abun da