Showing 18001 words to 21000 words out of 214133 words

Chapter 7 - CUTARWA AYSHERCOOL COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

22018

je ki cire uniform, ki yi salla" Iya tayi mata tsawa. Yayi shiru ransa a matuƙar ɓace, bai taɓa tunanin ganin ummi a cikin wannan mummunan yanayin ba.

Ta fito kanta babu ɗan kwali, gashin nan a cukurkuɗe, sai soshe-soshe take yi, saboda yadda ya addaba mata da ƙaiƙayi.

Ya dubi iya ya ce "Shikenan, tun da kun ce cikin ba naku bane ba, baku san da shi ba, ni ba dan wani abun hannunku ya sanya muka zo muka sanar da akwai cikin ba, saboda a cika umarnin Ubangiji, amma tun da abun haka ne, Allah ya kyauta, mu mun ji mun gani, mun karɓa. Amma dan Allah ku bani ƴar ta in kai mata, mariya ta kasa zaune ta kasa tsaye, hankalinta yaƙi kwanciya, ku bata ƴar ta dan Allah"

"Ba rashin ummi ne ya hanata nutsuwa ba, mugun abun ta ne yake koma mata kanta, hakkina da na ɗa na ba zai taɓa barinta ba, ya din ga bibiyar ta kenan"

Ganin idan ya cigaba da zama, wannan jayayyar zata kai su ga maganar banza, ya sanya ya tashi tsam, ya ce "Shikenan babu laifi, Allah ya kyauta"

Jin ya ce zai tafi, ya sanya ummi fitowa da gudu daga ɗaki, ta ce "Ba zaka tafi da ni, ka kai ni wurin maman ba?"

Ya durƙusa ya shafa kanta ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah nan gaba kaɗan, zaki koma wurin mamanki, Allah ya yi miki albarka" ya ciro kuɗi dubu biyar, ya bawa iya ya ce "Dan Allah a canza mata uniform, a saya mata wasu ƴan kayan buƙata"

Ba kunya iya ta amshe, tana harare-harare.

Ummi ta tsaya tabi bayansa da kallo har ya fice.

Dukan da aka yi mata a kanta ne, ya sanya ta dawowa hayyacinta, ta firgita ta kalli Iya.

"Duk wanda ya sake zuwa gidan nan, ki ka ce ya kai ki wurin uwarki, sai na saka idris ya zane miki jikinki, wato salon ace ba a kula da ke, saboda ƙwarewa a munafunci kin tsotsa a nono ko?" Tayi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa.

"Munafuka, ga muni ga kinibibi, tashi ki wanke kwanukan nan na safe" sumi-sumi ta nufi wurin tara kwanukan wanke wanke, ta haɗa ta fara wankewa.

***
Bayan sallar magariba, yaya garba ya je ya samu mahaifinsu ya sanar da shi cewa iya ta ce ba su san da ciki ba, dan haka a nemi ubansa.

Malam yayi shiru, lamarin ya girmame shi ya ce "Haka suka ce?"

"Wallahi, matar nan ba ta da mutunci ba ta da imani ko kaɗan, ba ka ga Yarinyar nan a halin da na baro bata ba, kamar ƴar jari bola saboda azabar datti da ƙazanta"

"Ƙyalesu, yarinya kullum muna yi mata addu'a, in sha Allah babu wanda zai sake bi ta kansu, ita kuma Allah ya raba ta da ciki lafiya"

Ya amsa masa da "Amin"

***
Na'ima kuwa ummi na ranta, amma babarta ta ce mata ba ita ba ummi, dan kakarta ba mutunci ne da ita ba, kar ta yi mata wani sharrin.

Sai dai ta kan ƙulle abinci wasu lokutan, ta tafi da shi makaranta ta bawa ummi.

Yanzu babu mai yi wa ummi wanki balle guga, dan haka dauɗa kamar ka kankarota a jikinta.

Ummi na iya ƙoƙarin ta wurin kaucewa haɗuwa da idiris, ga bala'in tsoronsa da take ji, saboda dukan da yake yi mata idan tayi laifi babu tausayi babu imani.

Allah ya taimake ta, wasu lokutan magaji na taka masa burki a kan wasu abubuwan.

Tsabar rashin gyara, ya sanya kwarkwata cika wa ummi gashi, kayan ta duk suka cukurkuɗe suka yi mata kaɗan, tana zaune har sakkowa kwarkwata suke yi daga kanta, suna bin ta, sai dai ta ɓuya tayi ta kashewa, ba ta son a gani.

Ga wasu irin manyan ƙuraje da suka din ga fitowa a cikin gashin kan nata, suna ɗurar ruwa, suka ƙara bawa kwarkwatar nan damar hayayyafa babu ji babu gani.

Banda zarnin fitsari da warin datti, babu abun da take yi, dan kuwa da kanta take yi wa kanta wankin kayanta, wando sai ya fi kwana uku a jikinta, ba ruwan iya balle ta ce cire ki wanke.

Sa'adatu ce babar auwwalu, ta fara lura da wannan ƙurajen na kan ummi, ta kamata ta buɗe kan, ta ga ƙazantar da take cikin gashin.

Ta nuna wa iya, Iya ta yamutse fuska ta ce "Taɓ gaskiya ba zan iya taɓa wannan kan ba, to gashi ne ba kaɗan ba, gaba ɗaya ba irin namu ba, kalar na mutanen ƙetare, shiyasa nake cewa anya ma kuwa tamun ce, duk zuriyar mu, babu irin wannan gashin, yanzu meye abun yi kar kan ya ruɓe ace ni ce ina kallonta, na bari ya ruɓe ji yadda wani mugun ruwa yake tsatstsafowa da ƙwayayen kwarkwata a ciki".

"Aikuwa sai dai a aske kan nan, dan ban ga yadda za ayi maganin abun nan ba"

Cikin ƙyanƙyami, sa'adatu ta sauke wa ummi gashin nan tsaf, ta koma sai ka ce namiji, ga hudar kunnenta ma, tana ruwa saboda tsufan ɗan kunne a kunnenta, ba a taɓa cirewa ba.

Iya ta saka aka haɗa kanwa da gishiri, da omo aka wanke kan nan, ummi ta din ga wani irin masifaffen kuka, saboda azabar raɗaɗi, da bal'in zafi haka nan da ruwan sanyi aka tuɓe ta, aka wanketa a tsakar gidan, iya har tana cewa wannan baƙar fatar ba da dutsen goge faso za a wanketa ba kuwa?. Wata irin annakiyar dauɗa ta din ga zuba daga jikin yarinyar. Yara suka cika sashin danƙam suna kallon ummi, da tana ta ƙoƙarin rufe jikinta, amma azabar wahala da zafi ya sanya ta manta da tsiraicinta.

Ummi na ji na gani, aka ɗaure gashinta a leda kaya guda da shi aka zubar, iya ta ce a sakawa kan ummi fiya-fiya, idan ba haka ba, sauran ƙwan zai ƙyanƙyashe kansa.

Ba tare da tunanin wane hali zata shiga ba, suka shafe ƙwallon kan da suka saukewa sumarta da fiya-fiya, hakan ya sa ta din ga tari da atishawa, gaba ɗaya kanta ya juye, ta din ga jiri, kan dare zazzaɓi ya rufe ta da ciwon kai.

Ba wanda ya kula ya saya mata magani, haka ta kwana tana rawar sanyi, da ta yinƙura ta tashi, sai ta tafi luuu zata faɗi.

Da safe gwaggo ta bata, koko da ƙosai, sai dai ta kasa ci, ta cigaba da kwanciya tana burgima a ƙasa, kanta yana ciwo, ga tari da take ta faman yi.

Cikin barccin wahala, ummi ta ji wani ƙamshin turare mai daɗi, ta ji magana sama-sama kamar muryar babanta.

Da sauri ta buɗe ido, ta yi ƙuri da ido tana kallonsa, ga iya a gefe suna magana da shi.

Yayi murmushi ya ce "Uwata ta kaina, kin tashi? Ƙaraso mu gaisa" sai yanzu ta lura ba baba bane ba, mutumin nan ne mai kama da shi.

Tasowa ta yi da sauri, sai dai ta faɗi, saboda jirin da take ji.

Da sauri ya tashi, ya ce "Iya ba ta da lafiya ne?" Iya ta taɓe baki, mussaman jin ya kirata da uwassa ta kansa ta ce "Eh zazzaɓi take".

"Subhanallah, kuma ba a kaita asibiti ba?"

Ya zaunar da ummi, ya sinsuna kanta ya ce "Ya na ji kamar kina warin fiya-fiya? Ya cire hular kanta, sai ga kai sol ba gashi, ga dagwalon gyambo a kan, ciwon duk yayi baƙi saboda fiya-fiya.

A razane ya ce "Meye wannan? Iya meya sameta a kanta?"

"Kwarkwata ce, da wasu ƙuraje, shi ne aka aske kan aka shafa mata fiya-fiya"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, iya wannan ai ganganci ne, ina laifin a kaita asibiti, wannan ƙaramar yarinyar a saka mata fiya-fiya a ka, ai shi ya sanya mata zazzaɓi".

"To ban da kai yahaya, ana ta abun da za a ci, waye yake ta wani asibiti, wa zai bayar da kuɗin kai ta wani asibiti?"

Miƙewa yayi ya ce "Wannan abun kunya da yawa yake"

Cak ya saɓa ummi a kafaɗarsa, yayi waje da ita, iya ta biyo shi tana tambayar ina zai kai ta?.

"Asibiti zan kai ta, idan ta mutu ba makawa ku ne ku ka kasheta" yayi waje da ita.

A mota ya kwantar da ita, ya ja suka tafi.

Sosai likitoci suka din ga faɗa, dan ma asibitin kuɗi ne, aka sake wanke kan ummi, da magunguna, aka saka mata ruwa saboda zazzaɓin da ya rufeta, take ta rawar sanyi.

Ya fita ya sayo kayan marmari, da ta farfaɗo zazzaɓin ya sauka, ya din ga bata da kansa.

"Kana kama da baba" ta faɗa a lokacin da zaƙin kankana ya ratsa kwanyarta, wanda rabon da ta sha har ta manta.

Yayi mata murmushi ya ce "Ai nima baba ne"

"Ai an ce baba ba zai dawo ba, ya mutu yana cikin kabari".

"Haka ne mamana, kina yi masa addu'a ko?" Ta gyaɗa kai alamar eh.

"Yanzu me ki ke son na saya miki?"

"Littafi" ta bashi amsa.

"Littafin makaranta?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya ce "To shikenan, zan sai miki in sayo miki kifi ko nama, wanne zaki ci?"

"Nama" ta faɗa tana murmushi.

Yayi mata murmushi shi ma, ya ce "To bari su sallame mu, sai na saya miki mu tafi gida"

Har ummi ta ɗan murmuro, ya saya mata tsire a hanya, da babbar robar youghurt, ya sai mata litattafai, da sabuwar jakar makaranta. Babban abun da ya burgeta da shi, shi ne yadda take ta ce masa ta gode, a yanayin tattaunawar da yayi da ita, ya san baƙar azaba kawai take sha, bai ga dalilin da ya sanya iya riƙe ummi ba, kuma shi ma idan ya ce zai tafi da ita can gidansa, faɗa za suyi da Fauziyya matarsa, dan ya san ba zata karɓi ummi ba.

Gashi shi bai san a ina mahaifiyarta take a Maiduguri ba, dan lokacin da balarabe yayi aure, yana kudu karatu.


A mota ya sanya ummi ta ci, har ta ƙoshi, wani irin daɗi take ji, yau ta ci kayan daɗi, wataran tana kallo ake kawo wa Iya, bata sammata.

A ƙofar gidan yayi parking, ya buɗewa ummi ta fito, ya riƙo ledar maganinta, ya riƙe hannunta suka shiga cikin gidan.

"Baƙar randa, baƙin zunubi, an dawo jinsinmu na maza" Alhassan ya faɗa yana ƙyaƙyata dariya".

Yahaya ya tsaya cak, ya kalle shi ya ce "Alhassan, wa ka ke cewa baƙin zunubi? Ummi ba ƙanwarka ba ce ba? Dan me zaku din ga aibata ta?"

Alhassan ya yi shiru ya sunkuyar da kai.

"Kai da ubanka na halitta, da zai halittoka  da wannan kunnuwan kan kamar zomo na zikiri, ga ƙaton kai kamar marmara?"

Ya girgiza kai alamar a'a, nan yayi ta yi masa faɗa, ya shiga cikin gida nan ma ya ɗora, tare da yi wa iya ƙorafi a kan lallai ta sanya ido, a daina ci wa ummi zarafi, idan ba haka ba, zata dashi ba ta karsashi a cikin al'umma, saboda gudun kar a aibanta halittarta.

Jin sa kawai Iya take yi, amma ba dan ta ji zata iya hana wani aibata ummi ba, dan ita ma aibata tan take yi.

Yahaya ya kawo kuɗi ja bawa iya nata, kamar yadda ya saba yi mata alkhairi, ya sanya a ka kira masa magaji, ya bashi dubu goma ya ce "Ga dubu goma, dan Allah duk abun da Yarinyar nan take buƙata, ko na rashin lafiya, ko na makaranta ka cira ka saya mata, idan da damuwa zan rubuta lambar wayata, a kira ni a sanar da ni duk abun da take buƙata, zan biya.
Zumunci bai ce haka ba, mahaifinta ya rasu, an rabata da mahaifiyarta, kuma aƙi tsayawa a kula da ita, dan Allah a kula da marainiya".

Hashim ya ce "Ina sha Allah kawu, za ayi duk abun da ya dace" ya dubi ummi ya ce "Sannu ummi"

Ta ce "Yauwwa"

Yahaya ya miƙe ya ce "To iya, sai wani lokacin kuma, ayi ta haƙuri, Allah ya rufa mana asiri"

Iya ta kwaɓe baki ta amsa da Amin.

Da sauri ummi ta riƙe rigarsa ta ce "Baba yaushe zaka dawo?"

"Da wuri in sha Allah ummi".

"To ka ce ina gaishe da mama"

Ya kalli iya, iya ta kawar da kanta gefe, ya ce "Iya yakamata a sanya lokaci a kaita ta ga mahaifiyarta, bai kamata idan ma wani abu ne a tsakanin ku da mahaifiyarta ya shafe ta ba"

Iya ba dan ɗan abun duniyar da ya bata ba, da babu abun da zai hana, ta ɗura masa ashar. Sai dai ta yi masa shiru, ya ƙaraci maganarsa ya tafi.

Hashim ya tafi raka shi, suna tafe yana sake jaddada masa, dan Allah a kula da ummi, babu wanda yafi ƙarfin Allah ya jarrabe shi da irin abun da ya jarrabe ta.

Suka ɗan yi hira a kan karatun Hashim, yake gaya masa ai yayi jamb, ya ce duk yadda ake ciki, idan yana buƙatar wani taimako yayi masa magana.

Suka yi sallama ya dawo sashin Iya, sai dai fa iya nata jibgar ummi da kara, Idris na tsaye yana kallonsu.

Da sauri ya ƙarasa ya ƙwace ummi, ya ce "Iya daga asibiti fa aka dawo da yarinyar nan"

"A'a daga mutuware aka dawo da ita, duk yadda nake ƙoƙari a kan yarinyar nan, bata da wani buri da ya wuce ta tozarta ni, ta nunawa duniya azabtar da ita nake yi"

"To yanzu iya me tayi miki?"

"Ban sani ba, tun da makaho ne kai, baka gani, munafukar yarinya, wallahi duk ranar da wani ya kuma zuwa gidan nan, ki ka yi masa zancen uwarki, sai mai shirin tafiya kabari ya fiki kwanciyar hankali, sai na casa ki, shegiya mai idon munafukai"

Ummi ta cukuikuye rigar hashim tana kuka.

Iya ta kalli Hashim ta ce "Kai ma ɗaya munafukin, bani kuɗin da ya baka, ai ba ita kaɗai ce ƴa a gidan ba, kuma idan bayarwar ne, ai ni yakamata ya bawa"

Cikin takaici ya ce "Amma iya...

"Rufe mini baki, ka bani na ce kan na ɓata maka rai" ya ciro kuɗin ya ajiye mata, ya fice.

Ummi da sauri ita ma ta fita, jikinta na ciwo, ga zazzaɓi na sake son rufe ta.

Ta koma ƙofar gida, ta samu in da rana take da saura, ɗumin yana ratsata.

Auwwalu ya taho da tawagar abokansa, har ya wuce ta ya dawo ya ce "Yara baƙar randa ta koma baƙin namiji, aski aka yi mata fa"

Ɗaya daga cikin yaran ya ce "Haba dai"

Ya ce "Bari ku ga" ya tunkari ummi, yana zuwa ya fara ƙoƙarin ja mata hijjabi, ta rirriƙe hijjabin ta fara kuka.

Ƙarasawa yaran suka yi, suka taya shi,  kasancewar maza ne, gashi ba ta da ƙwari ga rashin lafiya, suka kayar da ita, suka yage hijjabin.
Ta saka hannu bibbiyu ta rufe kanta, tana kiran mama.

Saboda mugunta irin ta yara, daga haka suka din ga kai mata duka a ka, wai sun ci ladan aski.

Suka tuburbuɗata a cikin ƙasa, duk ta kurje jikinta, kan da aka yi wa dressing, duk suka cika shi da ƙasa.


Mariya daga alhinin mutuwar miji da rabuwa da Ummi, mariya ta zarce da damuwa, ba ta hira ba ta walwala, sai dai kullum cikin wuni a ɗaki, duk lokacin da ta kwanta, ba ta da wani aiki sai mafarkin ummi, da kuma marigayin mijinta.
Asibiti da maryam ke kaita awo, suka ce da zarar ta fara naƙuda, a kai ta asibiti ta haihu a can, saboda hawan da jininta yayi.
Sai dai kusan kwanaki uku kenan, tana jin ciwo, kuma sai ta yi ta mafarkin gata ta haifi ummi tan jaririya, amma tayi shiru da bakinta, taƙi faɗa.

Mama ta shiga ɗakin, da niyyar tashin mariya ta yi salla, ta tarar da ita tana jijjiga, sai datse harshenta take yi, tana mimmiƙewa ga kuma haɗe da jini na fita daga bakinta.

Ayshercool
08081012143
                         *CUTARWA!*



BRIGHT PENS
(FREE BATCH)

arewabooks ayshercool7724
Watpad ayshercool7724
Subscribe my YouTube channel https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

P7

A guje mama ta koma tsakar gida, tana ƙwalawa malam kira, a kan ya zo ya ga abun da mariya take yi.
Suka dawo a tare, ya tarar da yadda jikinta yake ta rawa tana jijjiga, ya fita da sauri, aka nemo maƙwabcin su, kasancewar yana da abun hawa, aka saka mariya a mota suka tafi asibiti.

Can kuma hashim ne ya fito zai fita titi, ya hango yara sun yi dandazo, har zai wuce ya hango ƙafar ummi, ya ƙarasa da sauri, ya tarar da ita a kwance, yara sun yage mata hajjabi, ta sanya hannayenta biyu ta rufe kanta, sai kuka take yi.

Wani irin baƙin ciki ya turnuƙe masa zuciya, ya rasa dalilin da ya sanya yara suka tsani ummi haka, kodayeke iyayensu suka gani suna yi, da sun tsawatar musu da tarbiyantar da su a kan girmama halittar ɗan Adam komai muninta, da ba su yi mata wani abun ba.

Kai tsaye ya je ya tarwatsa yaran, yayi nasarar kama auwwalu, ya din ga kifa masa  mari, yana ball da shi, yayi masa dukan tsiya, sannan ya ɗaukko ummi ya shiga da ita gida.

Gaban iya ne ya faɗi ganin yadda ya shigo da ummi, ta miƙe tana faɗin lafiya?.

"Wallahi auwwalu ne ya tara yara, suka cire mata hijjabi suka yi ta dukanta a waje"

"Saboda iskanci, me tayi masa?"

"Oho masa"

"Kema uban waye ya ce ki fita?" Tayi maganar tana kallon ummi, da take ta zirarar da hawaye.

Ya ce "Dan Allah iya ki yi haƙuri, a jigace take, jikinta zafi rau da zazzaɓi"

Ya karkaɗe mata ƙasar nan, ya samu ruwa ya din ga shashshafa mata a jikinta, ya kaita ɗakin gwaggo ya kwantar da ita.

Iya kuwa mita take tana "Na rasa wannan baƙin jini na yarinyar nan, ƴa sai ka ce mujiya, ƴan uwanki yara ma gudunki suke yi, kodayeke ai dole a guje ki, wannan munin gaba ɗaya kalarki ba irin ta mutane ba" Hashim bai kula iya ba ya fice, saboda haushinta da yake ji, dan ya fara tsinkewa da lamarin son zuciyarta, gashi babu wanda zai iya tarar ta ya gaya mata gaskiya kowa tsoronta yake ji.

Duk yadda likitoci suka yi ƙoƙarin ceto ran mariya da yaronta, Allah bai yi ba, yaron ya zo babu rai, kuma alamu sun nuna ya kwan biyu da mutuwa a cikin ta, saboda yadda fatarsa ta fara marmasowa.

Sai dai har kusan kwana biyu da haihuwar ta, an kasa samo kanta yadda yakamata, da magani ya sake ta sai jini ya sake hawa.

Sai suka shafe sati uku a asibiti, sannan aka sallame su, suka koma gida, sai dai abu idan ba ya zama dole ba, ba ta magana.

Tunani kawai take yi, ko ta saci jiki ba a sani ba ta je ganin ummi, amma ta tuna wulaƙancin da iya ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login