Showing 75001 words to 78000 words out of 214133 words

Chapter 26 - CUTARWA AYSHERCOOL COMPLETE HAUSA NOVEL

01 Sep 2024

22062

TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

21

Mamaki ne ya cika shi, har sai da ya bayyana a kan fuskarsa, bai taɓa tunanin ummi za ta iya furta abun da ta gaya masa ba, saboda tun fil azal tamkar sokuwa take ba ta da wani karsashi balle ta yi faɗa.

Bai gama nazarin ba, ta angije shi tayi wucewarta tana tsaki, abubuwan da suka faru a baya, suna sake dawo mata tamkar yanzu suke faruwa.

Ƙarshen cin mutunci da tozarci yayi mata a garin nan, wanda yana daga dalilan da ya sanya ba ta ƙaunar sake zuwa gagarawa, haryanzu baƙin ciki da mugun tabon da take da shi a garin, yana damunta.

Dan har cikin zuciyarta tana fatan a gidan duniya, Allah ya yi wa Idiris abun da ya yi mata kafin ya koma ga Allah, ba ta sani ba ko a gaba ta iya yafe masa, amma har zuwa wannan lokacin, ba ta ji alamar manta abun da yayi mata ba, balle ta yafe masa.

Ranar da ya fara kwana a ɗakinta, ya korota waje, ta kwana cir a tsaye ruwa yana dukanta, saboda mugunta da zalunci.

Tayi iya ƙoƙarin ta wurin danne hawayen da ke ta ƙoƙarin zubo mata, ana ta hotuna, angon inteesar sagir, da kansa ya ce ummi ta zo ayi musu hotuna.

Idiris ya jinjina kai, tare da tabattarwa da kansa zaman birni, da kuma zuwa jami'a ne ya sanya ummi lalacewa, domin kuwa an ce dama ƴan matan jami'a ba su da mutunci lalacewa suke yi.

Duk in da ummi tayi sai ya bita da kallo, tamkar wani shashasha, hindu da yake yi wa kallon wayayyiya kyakykyawa, yanzu duk ta tararraɓe, haihuwa uku tayi, har da waccan mai sunan Iyan, ƙirjints da yake ɗaukar hankalinsa, duk sun zube, kullum daga ciki sai shayarwa.

Amma yanzu ummi komai nata a tsaye kyam, dai-dai da jikinta, duk da tana ta rufe jikin nata da mayafi.

Bayan la'asar suka ce zasu yafi, dan ba su zo da niyyar kwana ba dama, saboda sanin halin farida.

Duk lalacewar naka naka ne, ummi ta ji daɗin zuwansu sosai da sosai, tayi ta yi musu fatan alkhairi har suka tafi.

Idiris kuwa kamar maye, saboda azabar kallo, har suka ɗauki hanya suka tafi.

Kallo ɗaya zaka yi wa rahama da yaronta, ka san ba a kwanciyar hankali take ba, ga dai kuɗi miji yana da shi, amma yarkace-yarkace hak take, dan hatta kayan sawa wasu lokutan farida ke bata ko ta sayawa ɗan, duk wannan ƙafafar da ikon babu shi, duk ta zama so silent.

Taro ya watse, aka kai amarya, ummi kuma ta sake cin uban aikin gyaran gida, ranar monday kuma ta tafi makaranta.

Gaba ɗaya jikinta a mace yake, da ƙyar take tafiya ma duk jikinta ciwo, saboda azabar aikin da ta sha, ba ta samu damar hutawa ba, a haka a tafe har gajiyar ta ware.

Karatun ummi yayi nisa, kuma haryanzu ba a samu wanda ya doke point ɗin ta ba, duk da ba ta fasa fuskantar ƙalubale ba.

Dan haryanzu farida da kausar ke cin ƙaniyarta.

***
Tana zaune ta duƙufa tana ta aikin shirin dutse, ɗanlami yayi masa jagora har cikin ɗakin da take zaune.
Ɗakin tsaf da shi, sai ƙamshin turare yake yi, kai ba ka ce mara lafiya ce a ɗakin ba.
Ta ɗaga kai ta kalleshi, ta sunkuyar da kanta ta cigaba da aikin gabanta.

Ya ɗan ƙare mata kallo, shekaru sun ɗan ja, ta girma yanzu, amma tsaf da ita, tana samun kyakywar kulawa.

Ya dubi ɗanlami ya ce "Ɗan uwa, kuma a haka ba ta da lafiya?"

Yaya ɗanlami ya ce "Babu lafiya, wasu lokutan dai hankakin yana dawowa, wasu lokutan kuma sai ciwon ya dawo tayi ta shirme. Amma a hakan nan da take, za ta yi wanka, tayi shara tayi kwalliya ga shirin dutse nan ma gashi ka ganta tana yi, likita ne ya ce a samo mata abun da zai din ga ɗebe mata kewa.
Ka ga yanzu tafi sati ba ta yi magana ba, ba ta duka ba ta zagi, kaga daga mutuwar mijinta, ga rabata da ummi, ta zo ta haihu ɗan ba rai, tayi jijjiga depression yakamata sai kuma dai ta samu matsala gaba ɗaya.
Ban taɓa tunanin wani daga dangin baban ummi zai biyomu ba, dan mun yi alƙawarin ba zamu sake zuwa ba, irin jafa'i da mugun bakin da mahaifiyar ku tayi wa ƴar uwarmu, ya sanya muka ce gara mu yanke alaƙa da ku kawai".

Dr. Yayi ajiyar zuciya ya ce "Tun da na ɗauki yarinyar nan, nake fafutukar neman ina ku ke, ni ban san garin nan ba, ainihin in da kuka zauna aka aureta, mun je aka ce ba kwa nan, abubuwa dai duk ba su yi daɗi ba, sai fatan Allah ya kyauta".

Mama da yaya maryam da suke gefe suka amsa da amin, dan maryam ta zo gida yau, babu tsammani suka ga kawu yahaya.

Maryam ta ce "To ya ummin take? Ba ka zo mana da ita ba?"

Ya girgiza kai ya ce "Ba yanzu ba, ummi na nan a jami'a".

Yaya maryam ta ce "Dan girman Allah, ummin?"

Yayi murmushi ya tashi ya ƙarasa gaban ta ya zauna yana kallonta, ba tare da ta ɗago ba tayi murmushi ta ce "Baban ummi"

Ya ce "Na'am".

"Jigidata da ka tsinka mini nake gyarawa"

Sunkuyar da kai suka yi cike da jin kunyar abun da ta faɗa, dan tafi sati ma ba magana.

Yayi murmushi ya ɗebi dutsen da take ta shiryawa ya ce "Gaskiya ban kyauta ba, ki haɗa wata maza".

Ta sake yin murmushi ta ce "Da na san zaka dawo, ai da na yi kitso, an yi mini lalle, kaina ba kitso, bana son kitso tun da ka tafi bana son kitso" tayi maganar tana cire hular kanta, gashin kanta baƙi wuluk ya bayyana.

Yaya maryam zata yi magana, ya ɗaga mata hannu tare da girgiza mata kai, ya ce "To tun da na dawo yanzu sai ayi ko?".

"Ba zan yi ba, tun da ka tafi ka bar ni, ka ƙi ka dawo, Iya ta ƙwace mini ummi, ɗa na ya mutu ka ƙi ka zo ka ganni kuma bani da lafiya" tayi maganar tana kuka wiwi.

Ya ce "To ki yi haƙuri, ki yi haƙuri ba zan sake tafiya naƙi dawowa ba"

Ta riƙo hannunsa ta na cigaba da kuka ta kwantar da kanta a hannunsa ta ce "Baban ummi"

Ya amsa mata da "Na'am"

Ta ɗaga kanta ta kalleshi ta ce "Ka je ka karɓo mini ummina, Iya ba zata din ga yi mata wanka ba, ko idan yamma ta yi ta saka mata kayan sanyi, ba ta son ummi, dan Allah baban ummi ka karɓo mini ummi, kaga katifata ta ishemu ni da ita, idan ka sai mana gida sai in dawo gagarawa ko?"

Ƙura mata ido yayi, cike da matsanancin tausayinta, lallai yana daga horon da za ka yi wa uwa, ka rabata da ɗan ta, duk da tana cikin hauka, amma ba ta manta da ƴar ta ba.

Yayi ajiyar zuciya ya ce "To shikenan, ki daina kukan ya isa haka, mayar da hularki, kiyi haƙuri" ta ɗauki hularta ta saka.

Ta ja bakinta ta sake yin shiru.

"Zan kawo miki ummi in sha Allah, amma ba yanzu ba".

Yaya maryam ta ce "Saboda me? Abun da ta daɗe tana jira kenan, ka taimaka".

Ya ce "Ina da dalilina, kuyi haƙuri dan Allah"

"To amma mu ai ka bari muje in da take".

Kawu yahaya ya ce "Da ina da ƙudurin rabaku da ummi, da ba zan neme ku ba, ina da hujja mai ƙarfi sosai.
Zan cigaba da shiga lamarin nemawa mariya magani in sha Allah, komai zai daidaita kuma zai wuce".

Ba haka suka so ba, amma ba su san takamaimai menene dalilinsa na ƙin haɗa su da ummi ba.

***
Hangen dala ba shiga birni ba, domin kuwa inteesar tayi zaton soyayyar da suka sha da sagir a waje, ita za aje a cigaba da yi a gidan, sai abun da take so shi zai din ga yi mata, amma ina.
Ya nuna mata shi namiji ne, mage mai kwanciyar ɗaukar rai, a gida ta saba ba abun da take yi, ummi ce take komai. Yanzu kuma ya ce shi ba zai ɗauki ƴar aiki ba.
Dan haka sai komai ya din ga bata wahala, asubar fari zata tashi ta haɗa masa breakfast, gashi su yi ta faɗa dan abincin nata ba daɗi, ga almubazzaranci kamar ba mace ba.
Ga rashin kunya da rashin iya magana, gashi ɗan uwan mata, yana da tarin yayye da ƙanne mata, ga uwarsa mai shegen sanya ido. Sai ƙannensa su zo gidan su fi sati, gasu manya duk sun girmeta, su yi ta yi mata rashin mutunci, idan tayi magana su ce za su yi mata dukan tsiya.

Abun duniya ya damu inteesar, ta dawo gida tana kuka, ta gayawa mamanta.

Farida a zatonta zata iya maganin abun, ta kira Sagir tana masifar dan me ba zai tsawatarwa ƙannensa ba?
Ya ce mata ba zai iya ba, baya son ya saɓawa mahaifiyarsa.

Abu kamar wasa aka fara jamb, kawu yahaya ya turawa inteesar kuɗi, ya ce taje tayi jamb, a nema mata admission.
Amma sagir ya ce ba yanzu ba, sai ta haihu, domin kuwa a lokacin ma laulayi take yi.

Kawu yahaya bai matsa ba, farida ta din ga masifar dan me ba zai dage sai inteesar ta fara makarantar yanzu ba?

Ya bata amsa da "Yanzu ya fi ni iko da ita, shiyasa tun tana ƙarƙashin ikona, na so ta fara makarantar, yadda bai isa ya hana ba, amma ku ka dage, dan haka ni ba abun da zan ce".

***
BAYAN WANI LOKACI!.

Kasancewar tsakiyar damuna ne, an ɗan kwana biyu ba a yi ruwan sama ba, dan haka ana tafka zafi, ga uwar rana da ake ƙwalawa.

Tamkar ba ita ranar ke duka ba, haka take tafiya sannu a hankali, tana ratsa layukan unguwar, sannu a hankali take tafiyar, tamkar tana tausayin ƙasa, kamar mai rangji haka take tafiyar kamar tana tausayin ƙasa.

Ta cikin niƙabinta take kallon dogon layin, tare da lissafa sauran tafiyar da ta rage mata, ta isa in take fatan zuwan.

Layin shiru, sai lokaci lokaci, ababen hawa ke giftawa, manyan gidajen layin ko ina a rufe.

Ƙarar babur ta ji, kasancewar gefen hanya take bi, ya sanya ko a jikinta, dan ko waiwaya wa ba ta yi ba, ashe layin da yake gabanta yake ƙoƙarin shiga.

A ɗan fusace ya ce "Ke, kurma ce ne? Sai mutum ya tureku, ace bai kyauta ba, ba ki ji ina horn bane?"

Ta tsaya cak, ta ɗan ja wasu seconds, sannan ta juyo ta kalleshi ta cikin niƙab, sai dai ba ta ce komai ba.

Maimakon ya wuce ya tsaya ya ji me za ta ce, idan rashin kunya za ta yi masa, ya ƙare mata ta tas.

A hankali ta ce "Sorry, ga hanya wuce" tayi maganar tana ɗan ja baya ta bashi hanya.

Fuskar ta a rufe da niƙabi, amma muryarta ce ta saka shi ƙara kallonta.

"Malama idan zaki ware murya ki ware, da na bugeki ai ba zaki maƙale murya ba".

Ta ce "Ikon Allah, me muryata kuma tayi maka, ai na ce ka yi haƙuri ka wuce"

Tsaki yayi ya ja babur ɗin sa ƙirar lifan, ya yi gaba.

Ita kuma ta yi ajiyar zuciya, ta cigaba da tafiya.

A ƙofar ƙaton gate ɗin gidan ta tsaya, mutum biyu ta tarar sanye da uniform na security, suka dubeta suka ce "Gurin wa zaki je?"

Ta ce "Habu baka gane ni ba?"

Jin muryarta ya sanya shi cewa "Ahha wata sabon gani, ke dama kina duniyar nan?"

Ta ce "Ina nan mana, ya aiki ya kwana biyu?".

"Alhamdilillah, gaba ɗaya tun da ƙawarki ta bar gidan nan muka daina ganinki"

"To ai gashi na zo wanke laifina yau, ina fatan mami na nan?".

Ya ce "Eh tana ciki"
Ta ce "Yauwwa na gode" ya buɗe mata ƙaramar ƙofar gate ɗin, ta shiga ciki.

Ɗayan ya kalleshi ya ce "Ka barta ta shiga? Baka kira hajiya bilkin ba, kuma ba ta ɗaga niƙabinta ba".

Habu ya ce "Ai ƴar gida ce, ƙawar maryam ce, tun da tayi aure ne ta daina zuwa".

Ya ce "Ok, na so ta ɗaga niƙabin naga fuskarta, muryarta tayi mini daɗi".

"Ji ɗan wahala, ka sani ko yanzu tayi aure, ka shiga hankalinka".

Ummi kuwa sashin mami ta nufa, fasalin gidan yana nan yadda yake, amma yanayin fentin da aka sassauya masa da wasu abubuwan zaka san arziki ya fi na da.

A falo ta tarar da mai aiki, duk da ƴar bata san ƴar aikin ba, suka gaisa sannan ta tanbayeta ko mami tana nan.

Mai aikin ta ce "Eh, tana falon sama"

"Ki ce mata ummi ce ta zo" mai aikin ta jinjina kai ta nufi ƙafar benen ummi kuma ta zauna.

Bai kai mintuna biyar ba, mai aikin ta saukko, ta ce wa ummi ta shiga.

Ummi ta tashi ta bi bayan ƴar aikin.

Da sallama ummi ta shiga, mami ta waiwayo tana cewa "muryar wa nake ji ne haka? Gaskiya koma nayi fushi"

"Tuba nake mami"

Sai dai tana zagayowa, ta tarar da na kan babur da ya kusa tureta da lifan, yana zaune ya barbaje ƙafa a kan centre table, sai yanzu ta gane a in da san shi.
Sai da ya ɗan sake ɗaga kai ya kalleta shi ma.

Nan suka gaisa da mami, mami nata mitar ummi ta ɗauke ƙafa ta daina zuwa tunda maryam ta bar gidan.

Ummi ta kalleshi ta ce "Ina wuni?"

Ya basar ya ce "Lafiya ƙalau"

Mami ta ce "Laaa ka amsa kuwa? Kema meyasa ki ka gaishe shi? Ƙaninku ne fa, ƙanin maryam ne Raihan ne.
Kai kuma ka amsa kamata yayi fa ka gaisheta" ya wani basar.

Ummi ta ce "Ƙyaleshi mami, ai dama su Allah ya bawa girman" tayi maganar tana ɗaga niƙabin fuskarta.

Sai yanzu shima ya ganeta, ranar saukarsu da maryam a makaranta.

Mami ta ce "Ya wani je ya tara gemu, yafi kowa girma kai ka ce wani babba ne, ni wannan gemun ina tantama idan ba mai ya shafa ya fito ba, dan ga gemun nan dai, amma hankali da saura".

Ummi ta yi murmushi ta ce "Girma ya riga hankali kenan" sai da ya ɗan buɗe baki jin abun da ummin ta faɗa.

Mami ta ce "Eh mana, ya  makaranta ummi?".

Ummi ta ce "Mami makaranta muna jiran result"

"Masha Allah, lokaci ba wahala har kin gama ummi, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi, to ya batun aure kuma? Ko invitation ki ka kawo mini?".

Ummi ta sunkuyar da kai, tayi murmushin yaƙe ta ce "Tukuna dai mami"

Mami ta ce "Ya salam, Allah ya kawo nagari ummi, yanzu fa maryam kusan shekarar ta bakwai da aure, ke kuma shiru duk ƴan islamiyyar ku sun yi aure, saura ke, amma kar ki damu komai lokaci ne"

Ummi ta ce "To mami, bari na yi alwala dan Allah"

Mami ta ce "To shikenan ba damuwa, je ki yi"

Ummi na tashi raihan ya kalli mami ya ce "Dan Allah mami fisabilillahi meye na tambayar invitation ta kawo miki? Da shi ta kawo miki ai ba sai kin tambaya ba, kin ce shekarar maryam bakwai da aure ita ba ta yi ba, kin dawo kin ce tayi haƙuri lokaci ne, kamar fa kin mari mutum ne kina sane sannan ki ce yayi haƙuri".

Mami ta ce "To uban tsari, ai da tausayi yakamata ace ita ma ta tashi haka, in da take tana shan wahala, matar yayan babanta ke wahalar da ita, shiyasa nake tambayarta ko auren ne ya zo, ta huta".

"Matsalarku kenan mata, kune maƙiyan kanku, ladan ake rubutawa mace idan ta azabtar da ɗan wani? Kuma duk tausaya matan da ki ke, tun da dai ba ki samo mata mijin nan ba, ai sai ki yi mata addu'a, is like an insult at times, ka tambayi mace maganar aure, ni idan mace ne faɗa za ayi da ni"

Mami ta ce "Kai,tashi ka je mini aike na uban tsari".

"To ɗaukko kayan, ki haɗo da kuɗin shan mai".

"Duk kuɗin da babanka yake baka, sai ka damfareni dan zan aikeka, to ba zan bayar ba".

Ya kashingiɗa ya ce "Mami idan kina son aiken nan a kan lokaci, ki bayar da cin hanci " tashi mamin tayi tana hararsa.

Hakan yayi dai-dai da fitowar ummi, fuskarta a jiƙe da ruwa, gaban gashinta duk a kwance, gashin girarta ma tamkar za su haɗe.
Fararen idanuwanta suka bawa brown ɗin ƙwayar idonta fitowa sosai da sosai.
Ƙwayar idonta yake son kalla, domin tabattar da kalarta, sai dai bata bashi damar hakan ba, dan mayar da niƙabin ta rufe fuskarta, ta tayar da salla.

Mami ta dawo falon da ATM ɗinta, tana yi wa Raihan kashedin ya je ya dawo da wuri.

Ya karɓi ATM ɗin yaƙi tashi, ummi ta idar da sallar, tayi Addu'a ta cewa mami za ta tafi, tashi yayi ya riga ummi fita.

Mami ta ce sai ta tsaya ta ci abinci, amma ummi ta ce sauri take yi.

Ta ajiye wa mami kyautar kwalbar turaren humra.

Kuɗin motar da ta bawa ummi ma, ƙin karɓa ta yi, kuma da ganinta ka san tana buƙata amma mursisi taƙi karɓa ta tafi.

A babban falo ta tarar da shi, yana taje sumar kansa.

Har zata fita ya ce "Ki tsaya mu tafi tare na ajiyeki ko a titi ne"

Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a na gode sosai, zan ƙarasa" bai kuma ce mata komai ba ta fito daga falon.

Ta fita harabar gidan, hakan yayi dai-dai da fitowar wata babbar mace, ta sha ado da lace blue, hannunta da wuyanta duk gold.

Wani matashi yana biye da ita, kai da ganinsa ka ga ɗan shaye-shaye.

Da sauri ummi ta ƙarasa in da matar take, ta ɗaga niƙabinta ta durƙusa ta gaisheta.

Matar ta faɗaɗaɗa murmushinta ta ce "Ummi yau kece a gidan, ba dan Allah yasa na fito ba tafiya zaki yi bamu gaisa ba?"

"Ba haka bane hajiya, a gurguje na shigo ne, kusan kullum ta hanyar nan nake bi, shiyasa na ce yau dai bari na shigo"

"Eh amma zaki tafi bamu gaisa ba ummi, ya gida ya makaranta?"

Ummi ta amsa da Alhamdilillah.

Hajiya ita ce uwar gidan mami, tun lokacin maryam na nan, tana son mu'amala da ummi saboda nutsuwarta, amma ummi ta janye jikinta ta daina zuwa gidan ma, saboda ba a ga maciji, tsakanin mami da Hajiya.

Ummi ta gaida Salim da suke tare da hajiya, ya amsa mata sama-sama.

Hajiya ta ce "Ummi kin yi aure ne?" Ummi ta girgiza mata kai.

"Ai da kin yi aure ban sani ba, sai mun yi faɗa".

Kamar an jefo shi, ya dafo kafaɗar hajiya yayi ƙasa da murya ya ce "Ku daina yi wa mutum irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login