Showing 102001 words to 105000 words out of 334042 words

Chapter 35 - JIDDARTUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Aug 2024

270112

Seeyama da Aisha da Safiyya suka xo gidan amsar ma Aunty sako wajen Umma, Seeyama tayi murnan ganin Jiddah a gidan, Umma tace "Sai ki shirya ki bi su Jiddah, idan na je anjima da daddare sai mu dawo tare" Shiru Jiddah tayi ta kasa ce mata komai, Seeyama tace "Ki tashi sister Jiddah Aunty na jiranmu" Mikewa Jiddah tayi a ssnyaye ta saka Hijab dinta, Driver Umma ta sa ya mayar da su can gidan saboda Jiddah, tun da suka sauka motar gaban jiddah ke faduwa ta dai bi bayan Seeyama rike da handbag dinta har suka shiga parlor, dai daikun baki ne da suka xo biki a parlon, Jiddah ta sunkuyar da kanta ta nufi bangaren Ummi, tana shiga parlon taga mata biyu a xaune, Xaunawa kasa tayi ta gaishesu, duk suka amsa, ba a dau lkci ba Ummi ta fito daga daki, ganinta tace "Daga ina haka, ina Aliyun?" Jiddah ta gaisheta sannan tace "Tare muka xo da su Seeyama" Ummi tace "Ohk toh ki shiga can ciki" mikewa Jiddah tayi ta wuce bedroom din Ummi, Hajiya Murja kawar Ummi tace "Kaddai ita ce matar Aliyun?" Ba tare da Ummi ta kalleta ba tace "Ehh ita ce" Hajiya Salaha tace "Allah sarki, ashe yarinya ce ma, toh Allah ya basu xaman lafiya, ga ta dai kamar ba sa wa ba hanawa" Ummi ta d'an yi murmushi kawai, Seeyama ce ta shigo parlon tace "Ummi Aunty Jiddah ta shigo nan" Ummi tace "Tana ciki" Seeyama ta shiga sai ga ta sun fito tare da Jiddah suka fita parlon, sosai gabanta ke faduwa tana tsoron kar ta hadu da Aunty har suka shiga dakinsu Ramlah, Ramlah na ganin Jiddah ta washe baki tace "Aunty Jiddah sannu da xuwa" Jiddah ta xauna tana murmushi tace "Ya gida" Ramlah tace "Lafiya lau, yaya fa?" Jiddah tace "Ya tafi kano" Seeyama tace "Shi sa ya kai ki gidan Umma?" Kai kawai Jiddah ta gyada mata. Suna nan xaune har aka kira magrib, bude kofar dakin aka yi Aunty ta leko tana cewa "Wai baxa ku fito kuje ku yi wanke wanken can ba dake bakin pampo gashi har anyi magariba, ko waye xai maku? Ai sai ku hakura xuwa gobe ku sakankance tunda nasan yan kauye masu wanke wanken xa su iso" Jiddah dake kan darduma ta sunkuyar da kai gabanta na faduwa, tsit Aunty tayi ganin Jiddah kan darduma, can tace "Ko da yake tun safe ai ku ke ta aiki, ke ya kike da suna??" Jiddah ta kalleta, Aunty tace "Ehh da ke nake kike kallona haka, tashi ki fita ga wanke wanke can bakin pampo kije ki wanke" Mikewa tayi da sauri, Seeyama ta mike tace "Ta barshi kawai xa mu yi aunty" Aunty ta jefa mata wani kallo tace "Toh ita xa ta yi, ku kuma xan aikeku yanxu tare da driver xa ku je min siyayya a supermarket" Jiddah ta nufi kofa ta bi gefen Aunty da ta bi ta da wani kallon tsana ta fita, kitchen Jiddah ta nufa ganin kofar kitchen din a bude ta fita taga uban kayan wanke wanke a bakin pampo ga omo da soso, ruwa ta tara ta fara wanke wanken, ba a dau lkci ba sai ga Aunty ta shigo kitchen din ta dinga fitar da plates wankanku tana ajiye su kan marasu wanki, ita dai Jiddah bata ce komai ba, har tukwanen sai da ta fitar da su sannan ta dau soson waya ta jefa mata tace ki tabbatar kin bi bayan tukwanen nan kin wanke su fess, xuwa gobe kuma xan san yanda xanyi da ke, daga haka ta juya ta koma ciki, Jiddah dai ta ci gaba da wanke wanken da take a sanyaye. Ba ita ta bar bakin pampon nan ba sai kusan karfe tara da rabi, duk ta gaji ga uban yunwan da take ji, bbu kowa parlon sai yara dake ta wasa, iyayensu kuma na can sama, Jiddah ta rakube jikin kujera tana jin kanta na mata ciwo, har ta mance rabon da tayi irin wannan aikin, tun bayan rabuwanta da Hansai, Aunty ce ta shigo parlon da sauri tana sanye da Hijab, har ta nufi kitchen sai kuma taga Jiddar a rakube a parlor, tana kallonta tace "Yauwa mu je ki rakani xan amso sako yanxu"


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



*Mîkyããj_Sããdy Beauty Soap*




*Hy my beautiful people ina gaisuwa🙋🏻‍♀️ku karka'de kunnuwanku da kyau ku ji💃🏻ina mai sanar muku da cewa akwai gara6asa me kyau ta musamman ga wanda suka saba sayen sabulunmu da ma wanda zasu fara saya🥰, akwai ragin kaso 20% bisa dari 100% ga wanda suka saba saye, sannan akwai ragin 10% bisa ga masu sha'awar fara saye🥰, akwai farashi mai sauki ga 'yan sari, me yapi wannan dadi kam🤔ki sayi guda 4 kanana a baki kyautar daya, ki sayi guda uku manya a baki kyautar karami daya, ki sayi bucket biyu a baki kyautar babban rubber daya😍 kema da kike da burin saya ku'dinki bai kai ba😰to ga naki, ki kawo customers uku ki karbi naki kyautar Sabulun😍😍*


*Kawata 'yar 'kwalisa me kike jira,ita mace fa kullum cikim yin ado da 'kãwa take😍 ya kamata ki yunkuro wajen ganin kin rabu da wannan kurajen da tabo tabon fuskan nan haka🥺, kinga kema sai a saka ki a layin masu 'kwalisa da bajakolin ado💃🏻😍uwar gida a daure ayi gyaran jiki, sbd karbar goron a wajen me gida🥰,, ina amaren bayan sallah ku pito ku sayi naku Sabulun kuje kuyi ta wanaka hmmm 😍kamshi kawai zaku yi tayi kaca kaca😍😍, laushin fata Baja baja😃😂😂a yunkuro azo a karbi kayan gyaran jiki tare da sabulun gyaran fata a wurin _Mîkyããj_Sããdy_🥰*


*Duk wanda suka gwada Sabulun mu sun san babu 'karanta a ciki🥰in dai fannin gyaran jiki ne to sabulunmu shine amsarku,, shi ke mai da fata ta zama babu Pimples, Acne, Spot, Stretch Mark, da Duk wata matsala da ta shafi fata,, akwai lightening, nd glowing😍*


_*In kina son jikinki yai su6ul da shi, fata tai santsi da sul6i, ki yi haske me aji, 'kamshi kaca kaca ko ta Ina, ki ta fresh abunki hankali kwance ki zama Wankan madara yauqin zuma😍💃🏻Anty madam😃To ki mallaki 3d (Extra Whitening Soap, Ko da kudinki sai da rabonki hajiyata)💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*_


*Akwai hadin:*
*Mai da tsohuwa yarinya*
*Uwargida ta koma amarya*
*Amarya ta koma tamkar 'yanmata*
*'Yan mata su koma 'yan dagwai²*




_Ga masu bu'kata sai su tuntu6emu ta kafar sadarwa kamar haka;_
_Call/WhatsApp:08061570778_
_IG@mik_yaaj_saady_



Mikewa Jiddah tayi tsaye tana kallonta, Aunty da har ta nufi kofa ta juyo ganin Jiddah bata biyota ba ta hade rai tace "Ba magana nake maki ba" Jiddah tace "Ban saka hijabi ba" Aunty tace "Nan nan ne ba nisa muje baxa ki rasa mayafi a tsakar gida ba" Jiddah bata ce komai ba ta nufeta, Umma ce ta shigo parlon da sallama, Aunty ta koma gefe tana yake tace "Sannu da xuwa Hajiya Ramlah" suka gaisa Umma tace "fita xa ki yi halan" Aunty tace "Ehh wllh sako xan amso nan bakin titi, da har nace mu je da Jiddan tace min Hijabinta na sama" Umma ta kalli Jiddah tace "Toh ki tafi saman ki dauko hijabin naki" Aunty tace "Aa bari kawai inje ae nan bakin titi ne" bata jira cewar Umma ba ta fice daga parlon tana jin wani mugun takaici, Umma ta kalli Jiddah tace "Kin ci abinci kuwa?" Jiddah ta girgixa masa kai, Umma tace "Toh saboda me, ke ba sai ki je ki diba ba, Ummi na sama ne?" Jiddah ta gyada mata kai, Umma tace "Mu je" Jiddah ta bi bayanta suka wuce sama, Bangaren Ummi suka shiga, bayan Umma ta gaisa da yayarta tace "Yaya wai bata ci abinci ba" Ummi ta kalli Jiddah tace "Ae nayi tunanin tana tare da su Ramlah ne, kuma an kai masu abinci tun daxu, taje can dakinsu ta diba" Umma ta kalli Jiddah tace "Ki je ki deba abincin a can" Juyawa Jiddah tayi ta fita, Umma na kallon yayarta tace "Naga kamar baki saki jiki da ita har yanxu ba yaya" Ummi tace "Aa ko daya, baki ganin ita ma ba maganar take ba" Umma tayi murmushi tace "Ae kam ni muna hira da ita" Ummi tace "Did u know what is baffling me Ramlah?" Umma ta girgixa kai tana kallonta, Ummi tace "Yanda Aliyu ya mayar da mu shashashai ya maida mu wasu 'yan yara, kinsan da gangan yaje yyi ma kansa aure da yarinyar nan?" Ummi tace "Me yasa kika ce haka yaya" Ummi tayi wani murmushi tace "Ai ni na haifesa ba shi ya haifeni ba, bai kuma isa yyi deceiving dina ba, he intentionally did what he did, abubuwan da nagani game da shi da yarinyar bai yi kama da abun da mutum yyi ba da son ransa ba, kinsan satinsa nawa rabonsa da gidan nan yanxu?" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Nima ae ya daina xuwa min yaya..." Ummi tace "Toh yayi kyau... Xai gane bashi da wayo" Umma tace "Amma duk da haka akwai ayar tambaya fa a kan xaman da suke, don duk inda kika ji kishin kishin din magana da akwai kamshin gaskiya, ina jiran Ahmad ne yanxu inji matsayin auren nasu" Ummi tace "Ni ma dai nayi shiru ne kawai, amma ban aminta da xaman nan ba" Umma tace "Toh kin ga, don dama da bakinsa yyi ta cewa xae rabu da ita, na dinga hanasa tare da Abbansa to wa ya sani ko watsar da xancenmu yyi" Ummi tace "Ni kuma haka kawai naji ina son rabuwan nasu Ramlah" Umma dai tayi shiru bata ce komai ba, can ta sauke ajiyar xuciya tace "Allah dai yyi mana me kyau, kuma bana tunanin ya sa ta a karatu har yanxu, and she doesn't look happy always...." Ummi tace "Sannan ina ma son xanyi magana dake tun kwanaki, kinga lamarin rayuwar Aliyu? dama ina son in cire idanuwana da komai na a kai, sai yaje ya kara rike warce yake ganin ta fini daraja da hannu bibbiyu, ita yake ga xai iya komai na sirrinsa, ita yake ga xai fi ji da yarda da maganarta, to suje su karata, ni gaisuwan da yake min duk sanda yaga dama ma ce masa xanyi na yafe masa ya daina" Umma tace "Wannan ba magana bane yaya, tun farko ke kika xuba ido aka janye maki shi, Ahmad ya sha kawo min wannan same complain din, idan baki manta ba akwai wani lkci da na maki magana a kan hakan kika ce min ai ba komai duk daya ne, wnn mata ni ban ta6a ganin makira irinta ba..." Ummi ta girgixa kai tace "Aa ba ruwanta, ai shi ba yaro bane ya kuma mallaki hankalin kansa, he knows what is right from wrong, kawai dai hakan yake ga yafi masa alkhairi, sai yaje ya karata, amma ina dab da yi masa wankin babban bargo a gidan nan" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Ki dai yi hakuri yaya, Allah xai ganar da shi, wankin babban bargo kuma sai dai ki hada har Kishiyarki don munafuka ce" Bayan kusan minti talatin Umma ta gama abinda ya kawota, sallama tayi da yayarta har ta nufi kofa tace "Toh in tafi da Jiddar ne don can ya kai ta" Ummi tace "Aa wannan kuma ban sani ba" Umma tace "Naji xa su fita saloon gobe, kawai su tafi tare ita ma tayi gyaran gashin idan ya so ko driver sae ya maido min ita goben" daga haka tayi ma yayarta sallama ta fita dakin. Kwana dayan da Jiddah tayi gidansu Abuturrab ta fadi ma yan garinsu gashi gidan ya cika da mutane yan biki, Aunty tayi mugun saka ta gaba tun da garin Allah ya waye, ko wani aiki da aike ita ake sa wa, da ta xauna xata tasota gashi abincin kirki ma bata samu ta ci ba, da rana yan matan amarya duk suka yi shirin tafiya saloon, dama kafin Ummi ta lura da Jiddah balle har tace mata ta bi su, aunty ta hada kayan wanke wanke a bakin pampo ta turata taje tayi, yawanci duk masu girki ranan sun xata ma mai aikin gidan ce Jiddah, ko mai aikin gidan bata yi aikin da Jiddah tayi ba tunda gari ya waye, cikin ruwan sanyi Aunty ke gallaza mata, duk tunanin Ummi kuma har da Jiddah aka tafi saloon don tun bayan da suka gaisa da safe bata ganta ba, a gajiye Jiddah ta fito daga kitchen wajen karfe hudu ga wani yunwa da take ji, wata tsohuwa ce ta mika mata purse tace "Yan mata ki kai min daki wajen Hajiya Hauwa ta adana min, kada a yasheni a gidan biki, dubu daya da dari biyar ce a ciki" Jiddah ta amsa tace "Toh" lkci daya Jiddah ta gane warce take nufi wato Ummi, bangaren Ummi ta nufa ta bude kofar parlon da sallama, Ummi da frnds dinta Uku ne a parlon sai wasu yan uwa guda uku, Jiddah ta gaishesu gaba daya, Ummi dai sai kallonta take da mamaki, Jiddah ta sunkuyar da kanta ta duka gefenta tana mika mata jakar tace "Ummi wai ajiya aka ce a kawo maki" Ummi ta amshi purse din tace "In ji waye?" Jiddah tace "Ai ban santa ba" Ummi tace "Dama baki je saloon din ba ke" Jiddah ta gyada mata kai kawai, Ummi tayi shiru tana son nuna ma yan uwan mai gidanta da kawayenta cewar ita ce matar Aliyu amma ta kasa, can dai tana kallon jiddah tace "Toh gobe sai a kai ki ke" a hankali Jiddah tace "Toh" daga haka ta mike, dai dai nan Abuturrab ya fito daga bedroom din Ummi, sosai gaban Jiddah ya fadi bayan sun hada ido, amma kuma sai taji dadin ganinsa ba kadan ba, duk yan parlon suka juya suna kallonsa, Ummi ma kallonsa tayi don tun daxu take fama da shi ya fito ya gaisa da yan uwan Abbansa su uku sun iso daga Damaturu amma ya ki fitowa wai ya gaji, gwara frnds dinta a parlon ya samesu da ya shigo, Hajiya Zuwaira ta rike ha6a tace "Dama Aliyu na ciki?" Ummi ta kirkiri murmushi tace "Eh bacci yake, saukansa daga kano kenan ko awa biyu ba ayi ba" Tuni Jiddah ta fita daga parlon, gaishesu Abuturrab yayi yana yake ya nufi kofa ya fita parlon Ummi ta bi sa da kallon mamaki har ya kulle kofar, har Jiddah tayi nisa yace "Keee" tsayawa tayi ta juya tana kallonsa, ya karasa inda take yana kallonta daga sama har kasa, gaba daya ta wani susuce, yace "Yaushe kika xo gidan nan" Ta sunkuyar da kanta tace "Umma ce tace mu taho..." ya kara kallonta daga sama har kasa sannan ya sa hannu ya ciro makulli a aljihunsa yace "Dakin dake ta can bangaren inda babu mutane, ki je can ki jirani" Tana kallon makullin tace "Bude kofar xan yi?" Ya hade rai yace "Aa kullewa xa kiyi, bakya jin hausa ne?" Juyawa tayi ta bar wajen don ta gane dakin da yake nufi babu wanda ke xuwa ta wajen, bata yarda ta kalli kowa ba har ta nufi bangaren ta sa makullin ta bude dakin sannan ta shiga, babban daki ne sosai babu abinda babu a ciki, sai dai abubuwan ciki ba masu hayaniya bane, sannan ba a wani cika kaya a dakin ba, xaunawa tayi kasa ta jinginar da kanta kan babban katifar dakin don gaba daya ta gaji, Bayan kusan minti sha biyar taji an bude kofar dakin ta daga kai da sauri, Shine ya shigo dakin, ya kulle kofa yana kallonta yace "Baki cin abinci ne?" Ta girgixa kai tace "Aiki nake yi shi yasa ban ci ba" Yace "Wani aiki?" Tace "Nayi wanke wanke da safe na share duk tsakar gidan, sannan na taya masu girki wanke naman kaza, wani wanke wanken ya taru na kara wankewa, kuma naje siyo ledan kwasan tuwo sau uku wajen da nisa sosai almajiri ne ya rakani, da na dawo kuma wani wanke wanken ya taru na sake yi, sannan na share tsakar gidan da aka bata...." Katseta yayi yace "Duk wa yake sa ki?" Ta sunkuyar da kai tace "Aunty" Bai ce komai ba, bayan kusan minti biyar yace "Tashi ki shiga bandaki ki hada ruwa kiyi wanka" Mikewa tayi ta nufi bandakin she looks so tired and worn out, ya juya ya fita ya sa ma dakin makulli ya cire ya tafi da shi, a parlor ya tadda Aunty na welcoming din bak'in da suka shigo da mugun fara'arta, ido hudu yayi da mahaifiyar Aneesah, Ya sauke kansa kasa sannan ya karasa cikin parlon ya gaisheta da ladabi bata ko kalli inda yake ba balle tayi kamar ta ji, Aneesah ce ta shigo parlon da jakar kayanta, Aunty ta rungumeta tace "Sannunku da xuwa manyan baki, ya hanya?" Aneesah na murmushi tace "Alhmdlh Aunty don ma dai jirgi muka biyo ai da sauki wahalan" Kofa Abuturrab ya nufa don ko hada ido bai son yi da Aunty, Babu yabo bbu fallasa yaji tace "Aliyu get them something meaningful to eat, kasan sha'anin abincin biki, ba lallai yayi suiting taste bud dinsu ba" Toh kawai Abuturrab yace ya fice daga parlon. Parking Abuturrab yayi bakin gate dai dai lkcn da driver ya sauke su Seeyama bakin gate din, duk suka nufi motarsa, bai amsa gaisuwar da suke masa ba, ya dau leda biyu na abinci yace "Ku kai ma Aunty" Seeyama ta amsa sannan suka wuce ciki, bayan few minutes ya bude motar ya sauka ya shiga cikin gidan rike da leda daya, direct part dinsa ya nufa, ya ciro makulli ya bude kofar ya shiga sannan ya kulle, Jiddah na kwance kan carpet idonta kulle, karasawa yayi yaga bacci take, ya buga katifar kusa da ita, firgit ta mike xaune, ya ajiye ledan hannunsa ya hade rai yace "Baki ce ma Ummi baki ci abinci bane duk yau?" Ta girgixa kai tace "Ban ganta ba tun da safe sai daxu da naje kai mata sako" Yace "Toh wa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login