Showing 87001 words to 90000 words out of 334042 words

Chapter 30 - JIDDARTUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Aug 2024

270107

cire Hijab din jikinta ta linke ta ajiye ta bude jakarta ta ciro sabulu da sponge, toothpaste da toothbrush, xata wuce bandakin yace "Tawul din fa?" Dawowa tayi a hankali ta kara bude jakar ta dau towel dinta ta wuce bandakin, ta kusa minti biyar tsaye bayan ta gama wankan ta rasa yanda xata fito daure da towel, gashi bata shigo da hijab ba, gajiya tayi da tsayuwa daga karshe ta bude kofar a hankali tana lekan dakin, bata gansa a dakin ba, ta fito da sauri, ta fiddo kayan da xata sa da turarruka da mai, tana rufe jakar ya shigo dakin, kasa dago kanta tayi ya rufe kofar, bata yarda ta kallesa ba ta mike ta dau kayan nata ta shiga bandaki, sai da ta gama sakawa sannan ta fito ta mayar da turare da cream din cikin jaka ta tafi kan darduma ta xauna, yana xaune can gefen gado ya kalleta yace "Tashi ki kwanta" sunkuyar da kanta tayi, sai kuma ta mike ta tafi can karshen gadon ta kwanta, ba a dau lkci ba kuma bacci ya dauketa, karfe daya nayi ya kashe laptop dinsa ya ajiye sannan ya dau pillow ya ajiye a kasa ya kwanta. Da asuba ana idar da sllh Abuturrab yyi wanka ya shirya, tun ana sllh Jiddah ta tashi amma bata juya ba balle ya san idonta biyu, tana jinsa yana shiryawa har ya gama, kallonta yayi ya buga gadon yace "Ke baki sallan asuba ne dama?" Mikewa xaune tayi ba tare da ta yarda ta kallesa ba ta wuce bandaki, kwance ta gansa da ta fito idonsa a lumshe ta tada sllh bayan ta idar ta kwanta kan darduma, karfe bakwai da few minutes Abuturrab ya tashi, tashinta yyi ta mike xaune da sauri, yace "Anjima idan anyi knocking ki bude kofa ki karbi abinda aka kawo, apart from that ban ce ko bakin kofar ki je ba, kin ji me nace maki??" A hankali tace "Toh" Sai da ya fara kunna TV dake dakin ya kai tashar hausa sannan ya dau jakarsa ya nufi kofa ta bi sa da kallo har xai fita ya juyo, da sauri ta dauke idonta daga kallonsa, yace "Saura ki bude kofar a haka baki sa hijab ba idan aka kwankwasa" bai jira cewarta ba ya fita dakin ya kulle kofar, mikewa tayi ta hau saman gado ta ci gaba da baccinta. Karfe takwas taji an kwankwasa kofa, mikewa tayi har ta nufi kofar haka ta dawo da sauri ta dau hijab da ta daura kan riga da wandon jikinta na bacci, sannan ta nufi kofar ta bude, abinci aka kawo mata ta amsa tare da godiya ta juya ta koma cikin dakin, sai da tayi wanka ta shirya sannan ta yi breakfast din da aka kawo mata. Throughout ranan haka ta yini ita kadai dakin sai dai tayi kallo idan ta gaji tayi bacci, tana farkawa ta ci gaba da kallon, abincin lunch da aka kawo mata ma sai kusan la'asar ta ci, karfe biyar da rabi tana tsaye bakin window taji an bude kofar, da sauri ta juyo, shigowa dakin yyi, ya ajiye ledan hannunsa,duk da wayar da ta gani kare a kunnensa hakan bai hanata ce masa Ina yini ba, ya xauna gefen gado ya ci gaba da wayarsa, bayan ya gama ya tashi ya fita ta bi sa da kallo, sannan ta kalli ledan da ya ajiye. Sai bayan magrib ya shigo tana xaune saman darduma ta bi sa da kallo har ya xauna ya bude ledan da ya shigo da shi ya fara cin naman tsiren dake ciki, dauke idonta tayi bayan few minutes tace "Kace min gidanmu xaka kai ni, baka kaini ba shine xaka kawo ni nan, ni wllh ka maidani wajen Babarmu" Bai tanka ta ba, hakan bai hanata maimaita abinda ta fada ba, ya juya ya kalleta yace "In maida ke wajen Baabarku?" Tayi shiru bata ce komai ba, mikewa yayi ya koma gefen gadon ya xauna yana facing dinta yace "Tambayarki nake?" Ta sunkuyar da kanta tace "Ehh kai kaini wajenta" Yace "Ohkk... amma bari in tambaye ki" Ta dago idanuwanta ta kallesa yace "Kina tunanin xamana da ke ba burden da damuwa bane a gareni?? Ina nufin baki san cewar rayuwar ki tare da ni nauyi babba na daura ma kai na ba da rashin kwanciyar hankali? Do you think ko matata ba iyakar abinda xan mata nake maki ba? What's so important about staying under same roof with you? Kina tunanin ni ajin ki ne da nake kula ki nake kula al'amuranki? Toh bari ki ji, ni din nan da kike gani ba ajin ki bane, ina taimakon ki ne saboda Allah ba don komai ba, gidan naku da kike cewa in mayar da ke an gaya maki baxan iya daukan ki in maida ke ba duk abinda xai faru dake ya faru? Toh bari ki ji, sau da yawa tausayi kan canxa mutum, banda haka bani da abinda xan yi dake a waje daya, and i mean it, ni ba ajinki bane" Yana fadin haka ya mike ya fice daga dakin, ta bi sa da ido kafin ta sunkuyar da kanta.


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems

Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada

Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240


Har karfe daya da wani abu na dare Jiddah bata yi bacci ba, abu bai ta6a tsaya mata rai irin abubuwan da Abuturrab ya gaya mata ba, gashi har sannan ko digon hawaye bata yi ba, amma abun ya ki barin xuciyarta, da yake a kasan darduma ta kwanta kuma bai bi ta kanta ba yyi kwanciyarsa saman gado, ta mike xaune a hankali ta daura kanta bisa gwiwanta, sai a sannan hawaye ya shiga sauka idonta, gaba daya taji da ma ta hakura da aurenta da Iliya, taji ta gwammace gwara ta koma gidansu komin abinda xae faru, taji gwara ta gudu kawai, daga kai tayi hawaye na sauka idonta ta kallesa, duk da wutan dakin a kashe yake, tana ganinsa kwance saman gado. Da safe bayan ya gama shirinsa haka ya fita ba tare da yace mata komai ba, tun bayan da ta gaishesa bata ma san ko ya amsa ba har ya fita bata kalli inda yake ba ita ma, sae dai bata ga ya dau jakar laptop dinsa ba. Bayan fitarsa da minti kusan talatin ta mike ta dau Hijab dinta ta saka ta bude kofar dakin ta fita, a reception din hotel din ta gansa xaune da shayi a kan table din gabansa idonsa a kan screen din wayarsa, sosai gabanta ya fadi tayi still a inda take, dago kai yyi suka hada ido, tana ganin haka ta nufi kofar fita da sauri, da ido ya fara bin ta da mamaki, lkci daya kuma ya mike ya bi bayanta, fita tayi compound din hotel din, ya fara kalle kalle sbda baya son attention, luckily babu mutane haraban hotel din, hakan ya kara masa kwarin gwiwan bin ta ya fixgota ta fashe masa da kuka tace "Ni ka kyaleni in yi wucewata, wllh baxan xauna a nan ba wajen Baabarmu xan koma" Bai saurareta ba ya ciro makullin motarsa a aljihu ya ja ta xuwa parking space da motarsa yake ya bude back seat, turata ciki yyi ya kulle motar, sannan ya jingina jikin motar ya rungume hannunsa yana imagining... assuming baya xaune downstairs tafiyar xata yi da gaske, Jiddah ta dinga rusa kuka cikin motar, ya fi minti 7 a tsaye kafin ya bude motar ya shiga ya kulle, can gefe ta koma tana shessheka taki kallonsa, yana kallonta fuskarsa a daure yace "Ina xa ki tafi kika ce?" Cikin rawar murya tace "Gidanmu mana" Yace "Auren xa ki je a maki da mashayin saurayin naki?" Tace "Ehh" da mamaki yake kallonta, tace "Ni kawai ka mayar da ni, na yarda xan auresa din" Dauke kansa yayi bai ce komai ba, bayan few seconds ya kalleta yace "Toh ba kaduna muke ba yanxu, nan kano ne, ki jira idan mun koma kaduna sai in mayar da ke gidan naku da kaina ba sai kin tafi ke kadai ba, kin ji?" idonta ta fara gogewa tace "Yaushe xa mu koma kadunan?" Yace "Aiki nake yi a nan, sai ranan alhamis" Wani hawayen ya taru idonta, yana kallonta yace "Kin ji abinda nace?" Hawayen ya xubo mata tace "Har sai alhamis kuma?" Yace "Jibi ne alhamis din ai" Ta sunkuyar da kanta tana goge hawayenta, shi dai kallonta kawai yake ko kiftawa babu, a hankali tace "Toh" Bai kuma cewa komai ba, ya juya ya bude motar ya sauka yana dubanta yace "Sauko" Ba musu ta sauko daga motar tana wani kumbure kumbure, yana kallonta yace "Wani man kike shafawa?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Wanda ka siya min mana" Bai ce komai ba, bayan few seconds yace "Toh kar ki kara shafawa" ta kallesa yace "Mu tafi ciki" Ba musu ta fara tafiya ya bi bayanta, ba komai ya sa ya tambayeta ba sai ganin yanda ta kara haske, which he don't like, ko kadan baya son idan mace ta doso waje ayi noticing dinta, haske kuma na daya daga abinda yake sa ayi noticing mace a waje, ita kam Allah ya hore mata wannan, juyawa tayi ta kallesa suka hada ido ta ci gaba da tafiya yana biye da ita, har suka shiga reception din sannan taji yace "Tafi ki shirya ina jiranki, minti ashirin na baki" Bata ce komai ba ta wuce sama ya bi ta da kallon gefen ido, kallon agogon wrist dinsa dake nuna karfe takwas da rabi yayi, he will be piloting around 10:30, shi kuma bai son xama daki tare da ita shi ya sa ya sakko ya xauna reception din. Karfe tara dai dai Jiddah ta sakko, tun da ya kalleta sau daya ya dauke kansa... Abaya ce baki a jikinta, i need not to say yanda kayan ya haskata, sai karamin jaka da takalmin kafarta same color, ta iso table din da yake xaune, lkci daya kamshin turaren da ta saka ya baxa wajen, ya fi minti biyu bai ce komai ba, can dai ya kalleta yace "Baki xo da Hijab bane?" Ta girgixa masa kai kawai, Bai kuma ce mata komai ba, ta xauna d'an nesa da shi, sai a snn yace "Me xaki ci?" Tayi shiru bata ce komai ba, chips and egg ya sa aka kawo mata sai shayi, ya sa ta tafi sama tayi breakfast din, ta mike ta wuce, ya bi ta da kallo, lkci lkci yake duba agogon hannunsa dake nuna after 9, tashi yyi ya wuce sama, ya tarar ta gama, jakarsa ya dauka yace "Kina bata min lkci Malama" Tashi tayi ta bi sa suka fita ya kulle dakin, tana biye da shi har suka iso gun motarsa, ya ajiye jakar a back seat ya shiga maxaunin driver ya tada motar, xagawa tayi a hankali ta bude front seat din ta shiga ta xauna, warming din motar yayi suka fita haraban hotel din ya dau hanyar Airport. Abuturrab ya samu discount wajen yankar mata ticket din Business class, wanda hakan yasa take cikin boarding group na farko, duk wanda ya ga jiddah a lkcn xai xata ba farkon boarding din plane dinta bane, she is so calm, but deep inside her she is so so Afraid, bata ta6a tunanin haka jirgi yake da girma ba, snn bata ta6a mafarkin xata ga jirgi ido da ido ba balle har ta shiga wataran, kuma tunda ta shiga jirgin ta xauna idonta ke kasa, sai ka lura da ita sosai xaka gane a tsorace take, daya daga flight crew member ce ta nufota tana murmushi da ladabi tace "Ina kwana Hajiya..." Jiddah ta daga kai ta kalleta a hankali tace "Ina kwana" Cabin crew din na murmushi ta xauna kujeran gefenta tana kallonta ta buda mata ido sannan ta shiga fastening Seat belt dinta, wanda da alama Abuturrab ne ya sa ta gwada mata yanda zata saka seat belt din, Jiddah dai kallonta kawai take har ta gama sakawa, Flight crew din tace "Toh saka naki haka" Ba musu jiddah tayi yanda taga tayi, matar tayi murmushi ta yi unfasten din nata ta mike tace "Toh ki cire, sai jirgi xai tashi xa ki saka, Allah ya sauke mu lafiya" Jiddah ta cire, matar ta kuma sakar mata murmushi ta juya ta wuce, jiddah ta bi ta da kallo don kayan jikinta yayi mata kyau sosai ba kadan ba, ba su fi ashirin a Business class din ba, kowa kuma harkan gabansa yake, tunda wani mutumi ya xauna gefenta ta xama so uncomfortable, ga kamshinsa da ya cika wajen, shi dai bai kalleta ba sai operating din wayarsa da yake yi attentively, bayan minti ashirin duk passengers din sauran class din suka gama boarding plane din, Nan aka fara announcing ayi fastening Seat belt, ganin kowa na saka nasa ita ma ta fara kokarin saka nata, amma sai ta kasa sakawa sai fama da belt din take, sai a sannan mutumin dake gefenta ya kalleta ta gefen ido, ganin ta rasa yanda xata saka, ya kai hannunsa ya saka mata, bata iya ta kallesa ba kuma bata ce komai ba, a haka jirgin ya fara tafiya, dukar da kanta da yaga tayi na kusan minti 5 yasa ya sake kallonta yace "Are you okay?" Da sauri ta dago, dai dai nan jirgin ya daga, ta rufe bakinta hankalinta a tashe tace "Amai nake ji wllh" da mamaki yake kallonta yace "Amai?? Ohk hold it for a while" Ita dai hannunta na bakinta tana gyada masa kai, he gets she might be prone to motion sickness... ya jira har sai da jirgin ya tafi can sararin samaniya suka kai cruising altitude, duk da seat belt sign that is still on... hakan bai hana shi cire nasa seat belt din ba sannan ya cire mata nata, And he led her to the lavatory, wata cabin crew ta nufosu tana kallonsa tace "Is she alright?" Yace "Sure she will be" yana tsaye har jiddah ta fito daga lavatory din tana sauke numfashi, banda jiri babu abinda take gani, ga kanta dake juya mata, yace "How are you feeling now?" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yace "Toh mu je" Tafiya ta fara yi ya bi bayanta, har xuwa wajen seat din nasu, ta xauna sannan shi ma ya xauna, kamar ya lura she is so uncomfortable from d clouds she is seeing via the porthole that she is sitting beside, rufe wajen yyi yana kallonta, hakan da yayi ya taimaketa sosai kuwa, bayan some minutes da take off dinsu aka kawo masu snacks with drinks, kallonta yayi suka hada ido, bayan an ajiye masu ya dau nasa ya fara ci, ganin bata ci komai ba har ya gama cin abinda xai ci ya kalleta yace "Ain't you eating?" Tayi shiru bata ce komai ba, bai kuma yi mata magana ba, har ta fara bacci, seeing how uncomfortable she is sleeping yasa ya bata access to his shoulder, a haka kuma ta dinga bacci har aka fadi nan da mintuna nawa xa su shiga lagos, shi ya saka mata seat belt din nata bayan an bada umarnin yin hakan, dalilin da yasa ta tashi daga baccin da take kenan, jiddah bata san lkcn da ta rikesa ba ta rufe fuskarta a jikinsa da xa su yi landing, Cikin kuka take gaya masa amai take ji, ya dago kanta yace "Hold it for a while..." ya bude porthole din da ya rufe yana nuna mata, juyawa tayi ganinsu a kasa jirgin na gudu ta ji hankalinta ya d'an kwanta, amma har lkcn xuciyarta bai daina bugawa ba, shi dai kallonta kawai yake, can ta kallesa, d'an murmushi yyi yace "Ya sunanki?" Ta sauke idonta tace "Jiddah" yace "Jiddah!!" Ta gyada masa kai, yace "Wannan ne farkon hawanki jirgi Jiddah?" Ta gyada masa kai, bai san lokacin da yyi murmushi ba yace "I see, to mun kawo lafiya, hope ur next flight won't be as
frightening as this?" Ita dai bata ce komai ba,
yace "Ke kadai kika xo lagos?" Ta girgixa masa kai tace "Aa ni da yayana" yace "Wow, yana ina?" Ta buda masa hannu alamar bata sani ba, yace "Ba tare ku ka
shigo jirgin ba?" Tace "Toh ni ban sake ganinsa ba" yana waige waigen business class din yace "Ohk, sunana Yousuf.... Yousuf Umar" yana fadin haka ya ciro wayarsa yace "Sa min digit dinki so i can say hi some other time Jiddah" Tayi shiru tana kallon wayar tasa me kyau kirar samsung, can tace "Ni ae bani da waya" da mamaki yace "Baki da waya?" Ta gyada masa kai yace "Ban yrda ba" tace "Wllh, wanda yayana ya bani yana gida" ganin how she is speaking innocently yasa ya yrda, ya ciro Complimentary card dinsa ya mika mata yace "Toh ki min alkawarin xa ki kirani ga number na nan" ta dinga kallon katin dake dauke da number sa kafin tace "Alkawari fa kace" yace "Eh Jiddah" jan fingers dinta ta fara yi bata ce komai ba ya bude jakarta ya sa mata katin dai dai nan kuma jirgin ya tsaya cak,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login