Showing 333001 words to 334042 words out of 334042 words

Chapter 112 - JIDDARTUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Aug 2024

269968

murya tace "In sha Allah" Washegari Karfe goma saura Jiddah ta gama duk abinda take, bayan Hansai tayi breakfast ta shiga gidansu Hajiya Fatima, ita kuma Jiddah suka fita tare da Abuturrab, shi ke driving din, tana xaune front seat rike da Little Jiddah a kafarta, motoci ne sun kai biyar anyi parking kofar gidansu Abuturrab, Abuturrab ya nemi waje shi ma yayi parking ya sauka, Jiddah ma ta sauka, ya amshi little Jiddah a hannunta suka shiga cikin gidan, ganin guards din palace din bauchi ya gane uncle dinsa ma na gidan, Tun daga nesa yake kallon El-Basheer dake tsaye tare da Ahmad, ya karasa suka fara gaisawa da Ahmad sannan ya mika ma El-Basheer hannu yana kallonta, El-Basheer yace "And i am hoping u will be unblocking me this very moment" D'an murmushi kawai Abuturrab yayi yana patting shoulder dinsa yace "I neva did block you brother" Jiddah ta sunkuyar da kai ta gaishe su, El-Basheer na ganin little Jiddah ya wara ido yace "Waow, and at last, my wife is born..." Karasawa tayi ya amshi yarinyar a hannunta yace "Waoow she is so cute" Jiddah na kallon Ahmad tana murmushi tace "Aunty Ramlah fa yaya Ahmad?" Yace "Tana ciki" Juyawa tayi ta karasa cikin gidan, Maimoon ta taso da sauri ganin Jiddah ta rungumeta cike da murnan ganinta tace "Mrs Aliyu" Jiddah na murmushi tace "Mrs Yusuf" Dariya kawai Maimoon tayi, Jiddah ta janye jikinta ganin su Ummi a parlon tace "Bari in gaida su Ummi" xaunawa kasa tayi gefen Ummi ta gaisheta, Ummi ta amsa da fara'a, ta mike ta tafi kusa da Umma tana jin kamar ta rungumeta tana murmushi tana kallonta tace "Umma ina yini" Umma tace "Lafiya lau Daughter, ina Ummin?" Tace "Tana wajen yaya Bashir" Ramlah dake xaune ta daga ma Jiddah hannu tana murmushi, Jiddah ta daga mata hannun ita ma smiling at her, gaida few visitors dake parlon tayi, sai ga Hajja ta fito daga dakinta sanye da kaya na alfarma ta sha gwal a wuya da kunne tana taku dai dai, Akwatunanta uku fal da kaya ana biye da ita da shi.. Wai ashe Masar Hajja xata koma shine yan rakiya xuwa airport suka cika gidan Alhaji Usman, yan kano ne, yan Bauchi ne, har ma da yan zaria, Umma na murmushi tace "Hajja kuma sai Masar" Hajja na daga shoulders ta nufi kofa tana cewa "A bi min akwatuna a hankali kar su yi ko kwarzane a cuce ni, mu a Masar a nutse ake jan akwati" Dariya Maimoon ta dinga yi har da saukowa daga kan dining, Ummi ta mike da su Umma suka bi bayan Hajja suna murmushi, Abba da Mai martaba da sauran brothers dinsu duk suka fito compound jin Hajja ta fito bayan awa daya da ta dauka tana shiri a dakinta, kace wani karamin biki ake yi a compound din gidan saboda mutane, a haka duk suka nufi airport don a private jet xa a kai ta kano sannan ta hau jirgi xuwa Masar..... Waige waige ta dinga yi a airport tana neman Jiddah tana ganinta ta yafito ta, Jiddah ta nufeta Hajja ta jawota kusa da ita tace "Toh Allah ya kaddara saduwan mu Jiddah ni xan koma Masar kuma ban jin xan sake dawowa kasar nan" A hankali Jiddah tace "Aa xaki dawo Hajja" Hajja ta girgixa kai tana kyabe baki tace "Lala, abubuwan kasan nan duk ba tsari, toh me xan dawo yi?? ni dai ina 'ya ta ta ke?" Jiddah tace "Tana hannun Yaya Bashir" Hajja ta d'an waiwaiga ta tabbatar babu idon kowa a kansu ta kamo hannun Jiddah ta saka mata gold na dankunne tace "Gashi ki ajiye ma 'ya ta, tana shekara biyu cif cif ki saka mata kuma kada kice ma ko wani shege ni na bata balle a kullaceni suce ban ba ma yaransu ba to me na hada da su? ko shi gantallalen Aliyun kar ki gaya masa don babu abinda na hada da shi ma din" Rungumeta Jiddah tayi cikin sanyi tace "Mun gode Hajja Allah ya kara girma, Allah ya kai ki lafiya, in Allah ya yarda mu ma muna nan xuwa wataran" A haka suka rabu da Hajja ana ta daga mata hannu har ta hau matakalan jet din tare da mai martaba da Abba da Alhaji Umar, sai ta juya tana fuskantarsu kafin ta shiga jirgin ta daga masu hannu gaba daya sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tace "To a yayyayafe.... mu dai mun koma Masar!!!" Me Abuturrab xai yi banda dariya little Jiddah dake hannunsa na tayasa.



*kada a manta littafin Jiddatul Khair na kudi ne, ba kyauta ba, a xo a sauke hakki a xauna lafiya sisters and brothers*

It's 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah



Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!😃

A nan kam na ajiye alkalamina✍🏻 na kawo karshen littafin _Jiddatul Khair_ darussukan dake ciki Allah ubangiji ya sa mu amfana da shi, kura kuren ciki kuma Allah ya yafe min....😰


Na sadaukar da littafin nan xuwa ga beloved Dad dina, Alhaji Bello Ahmad.... Ur daughter Jiddoh is always proud of u Papa, Allah ya baka kwanciyar hankali na har abada, ya kara maka budi da daukaka, ya kareka sharrin masu sharri, ya kara maka lafiya da duk sauran musulmai Ameeeen🥰

Gaisuwa ta musamman xuwa ga mahaifiyata Hajiya Hajarah, she is my first love, my world, my role model and my everything, Allah ya bar min ke Hajiya yaya, Allah ya kara maki lafiya ya karo arxiki me albarka, My Siblings Ahmad, Maryam, Yahaya, Fatima, Khadija, Aliyu, Ilham, Sudais, Fadeel, Papi auta, Lil Khaleesat, Baby, Haneef, Ashraf, Jamcy, Humaira, Yusuf Black, Mujaheed, Big Ilham, Aneesah, i love u all!! Allah ya albarkace ku gaba daya, ina sonku har raina, small mummies...., Aunty Rukky, Anty Didi, Uwar Ashraf ur daughter Jiddoh is greeting with respect, Allah ubangiji ya jibanci lamuranku.... Hajiya Pc (Sadiya Chamo) ga gaisuwan ku dake da tawagar Khaleesat's palace, duk na gaisheku ina sonku fisabilillah, Hafsat Ado i greet and appreciate you sis...🥰😘 And finally my lovely fans, words alone isn't enough to express my feelings toward u guys, billah ina sonku, ina alfahari da ku, ina maku fatan alkhairi da fatan gamawa da iyaye lafiya Ameen!!!

Taku har ko da yaushe, Hauwa Bello Jiddah A.K.A Khaleesat Haiydar📚✍🏻


Na bar ku lafiya😊


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login