Showing 171001 words to 174000 words out of 334042 words

Chapter 58 - JIDDARTUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Aug 2024

270033

ya kai mu muga yanda ake yi a can din Hajja" Da sauri Hajja tace "Aa, ba ko wani gantallale ake bari ya shiga kasar ba ma, nima da yaya suka yarje min na shiga, ke dai kawai a bar kaza cikin gashinta" Dariya Umma tayi ta mike ta wuce dakinsu Maimoon, har sun fara shirin Islamiyya, Umma na kallon Jiddah da har ta saka uniform tace "Jiddah xaki raka Hajja gidan amarya wai" Jiddah tayi shiru tana kallon Umma tana son sanin wace amaryar tukun, Maimoon tace "Wace Amaryar Umma?" Umma ta ta6e baki tace "Gidan Aliyu wai" Sosai gaban Jiddah ya fadi, lkci daya mood dinta ya canxa har hakan bai boyu a fuskarta ba, Umma duk ta lura da hakan kuma, Umma tace "Kina kai ta dama xan baki kudin mota ki lallaba ki dawo, ko minti ashirin kar kiyi a gidan" A sanyaye Jiddah tace "Umma Islamiyyar fa?" Umma tace "To na gaya mata ta hau ni da fada, kawai kiyi hakuri ki rakata din, kuna isa gidan ki juyo abun ki" Jiddah tace "Toh Umma mu je da Maimoon idan ya so kawai sai mu wuce makarantar daga can" Umma tace "Ehh kuma haka ne, ku shirya ku fito, hakan ma shine dai dai, bari in sanar mata" Daga haka Umma ta juya ta fita ta koma parlor, tana kallon Hajja tace "Hajja ita da Maimoon xa su rakaki, idan ya so kuna isa gidan bayan sun gaisa da amarya sai driver ya karasar da su makarantar, da uniform a jikinsu ma xa su tafi, ina ga hakan xai fi ko" Hajja tayi tagumi tace "O'o Allah ina ganin jarabawa ni Dije, yanxu Ramlah ko ke kika haifi er nan Jiddah kya dinga min wannan axababben walakancin da kike min, ina ruwana da wata Maimu? Maimu da bata daraja kowa xaki hadani da? Dama ba Jiddah kawai nace ta rakani ba, a gaskiya a xo a kira min Usman, ya xaki dinga min kamar wata bare Ramlah?? Sannan da Aliyu bai je ya jajubo mana Jiddar ba a ina xaki santa ki nuna iko? A fa ta dalilin jikana ma aka san da wata jiddah a duniyar nan, ni dai wllh ki ajiye son kai kiji tsoron Allah Ramlah, ace a Masar ne ai sai anji dalilin wannan abinda kike min yanxu" Juyawa Umma tayi tace "Ni da ma kira kawai kika yi a tura maki Jiddar da wannan dogon xancen ba sai kin xo ba Hajja" Hajja tace "Oho dai ba ruwana da tashin hankali dake, ni yarinya ce da xan biye maki, banda dai kina kanwar Hauwa a ina xan sanki" Umma na shiga dakinsu Maimoon ta bude kofa tana kallon Jiddah tace "Ki canxa kaya ki xo ku tafi Jiddah" Daga haka ta bar dakin ta wuce nata dakin, Babu yanda Jiddah ta iya haka ta shirya cikin atamfa ta dau hijab dinta ta saka, Abinda Maimoon bata ta6a ganin tayi ba take yi a lokacin wato kumbure kumbure, fuskar nan nata kamar bata ta6a dariya ba kana gani kasan ko kadan ranta bai so ba, jakarta ta dauka ta fice daga dakin, ta wuce dakin Umma, Umma na kallonta tace "To ya xa ayi kiyi hakuri, amma kuna isa ki ce xaki Islamiyya ki fito, ga kudi a gaban mirror ki dauka kiyi kudin mota da shi" Jiddah ta karasa a hankali ta dau kudin sannan tace "Nagode Umma" Fita tayi daga dakin, bata san Umma ta ma fita jin takaicin rakiyar ba, Hajja na ganin Jiddah ta mike tace "Mu je, ai ba ita taje ta nemo ki a duniya ba da xata dinga nuna isa da iko a kanki, mata ta wani narka kiba uwa fanken Masar tana ma mutane rashin kunya kawai" Ita dai Jiddah bata ce komai ba ta bi bayanta tana tafiya a hankali, Driver na ta xaune mota yana jiran ranan fitowar Hajja, Hajja ta bude bayan motar tana kallon Jiddah tace "Toh shiga, halan ta kitsa maki karya da gaskiya ne, naga ranki kamar ba dadi" Ita dai Jiddah tayi murmushin karfin hali ta shiga motar, Hajja ma ta shiga ta kulle tace "Ae laifin wa enda suka bar ki a wajenta ne, kowa fa yasan matar bata da mutunci, nan da nan take maka mutum kotu ko ta kaisa gidan yan sanda ayi ta bala'i shi yasa kowa ke shakkarta a pamily, da akwai wani lkci da ta kira ma Hafsah yan sanda a kan ta xagi yar uwarta Hauwa, aka yi ta dauki ba dadi ana bala'i daga karshe dai Allah ya yayyafa ma abun ruwan sanyi, to idan tana ji da bala'i nima ai A ce, kawai nayi sanyi ne tunda naga su Masar basa haka, ni kuma sai inje in kai masu wani halin daban? Aa shi sa na daina wllh" Jiddah dai bata ce mata komai ba har driver ya kama hanyar gidan Aliyu. Suna isa gidan xai yi parking a kofar gida Hajja tace "Kai ya haka, baka san waye mai gidan ba, jikana ne fa, ni na haifi ubansa, ka danna masu han kawai a bude maka ka shiga" Yana danna horn mai gadi ya leko, Hajja sai kallon Mai gadin take ganin yaki bude gate din ya karaso gun motar tace "Ji wani yakunanne don Allah, kace masa kakar mai gidan ce kai Bala" Drivern ya sauke glass ya sanar ma mai gadin, yana hada ido da Hajja da ta wani sha kunu ya koma ya bude gate din, Hajja tace "Fitsara suke ma mutane idan sun samu waje wllh, banda haka shi xai ce bai ga kamanni ba, kawai neman magana malam" Driver ya ja motar xuwa cikin gidan, Kai kana ganin Jiddah xaka xata wani mugun waje aka taho da ita, gaba daya taki sakewa, driver na parking Hajja ta sauka, kafin tace komai Jiddah ta sauka ita ma, Hajja tace "o,o Na shiga uku, yanda kike yi da fuskar nan taki wani ba sai yayi xaton sato ki nayi ba er nan, a gaskiya Ramlah da kyar taga annabi, ni yanxu ta ya xan sa abinda ta kitsa maki kike ta daure fuska haka fisabilillahi, matar nan fa ta fita hanyata a kasar nan wllh" Jiddah ta kirkiri murmushi tace "Bata ce min komai ba Hajja" Hajja tace "To ni ba ruwana, ta ji da munafurcinta" Daga haka ta fara tafiya xuwa main entrance din gidan Jiddah ta bi bayanta, da sauri Hajja ta juyo tana kallon driver tace "Ka tafi kawai kai, Aliyun sai ya maida mu gida idan muka shirya" Amsa gaisuwar da mai gadin gidan ke yi mata tayi tace "Mai gidan na ciki?" Mai gadin yace "Ehh Baaba yana ciki" Hajja tace "To madallah" Daga haka ta yi gaba Jiddah na biye da ita, murda kofar Hajja tayi bayan ta murda ta ji sa a kulle, ta kalli Jiddah tace "Toh ko meye na garkame kofa da rana tsaka haka" Bata rufe baki ba aka bude kofar, daga sama har kasa yake kallonsu, sai kuma ya koma gefe still looking at Jiddah, Hajja ta shige parlon abunta, Jiddah dai sunkuyar da kanta tayi taki yarda ta kallesa, ya gama kare mata kallo sannan ya juya ya koma parlon yana kallon Hajja yace "Sannu da xuwa Hajjaj, daga ina haka?" Hajja ta rike ha6a tace "Ohh ikon Allah, aure me seta mutum, yaushe rabon xancen kirki ya hadani da kai Aliyu, yau wai kai ne ke min sannu da xuwa fuska a sake haka" Ya shafa kansa yana murmushi yace "Daga ina ku ke?" Tace "Daga gida wllh, na dai ce bari in xo gidan amarya yau" Ta gefen ido ya kalli Jiddah da taki xaunawa ta tsaya daga bayan kujera, muryar Hajja yaji tace "To ina amaryar?" Ya dauke kai yace "Tana sama" xata sakko yanxu, yana fadin haka ya xauna yana tambayarta mutanen gida, Hajja ta kalli Jiddah, girgixa kai tayi tace "Ban san haka er nan take ba sai yau da nace ta rakani, ashe ita ma duk kanwar ja ce, Duk Ramlah ta xugeta tunda muka kamo hanya take min wasu abubuwa me nuni da cewa bata son biyoni, ni ai na xata kirkin gaske gareta wllh, to banda haka meye xa ki makale jikin kujera kamar na kawo ki gidan yankan kai? Ni da na sani da Nafisah na taho duk da halinta ko Aisha" Jiddah ta karaso parlon ta xauna kasan carpet a sanyaye, mikewa Abuturrab yyi ya wuce sama, Hajja ta kalli Jiddah tace "Ba fa baren waje muka xo ba ki saki jikin ki, jikana ne ni na haifi ubansa, ke ma kuma ai kin san sa, kar ki bari matar tayi mana dariya tace mun xo muna ta dari dari a gidan, ki sake jikinki duk abinda kike so kiyi babu wani shakka, wllh bbu me hanaki kin ji" Jiddah tayi murmushin karfin hali, tana son cewa Hajja xata wuce Islamiyya amma ta kasa, don bata san me xai biyo baya ba, Hajja tace "Yanxu tashi ki tafi kitchen ki kwaso mana ruwa da lemo, ki duba robobin garanta ki dau faranti ki debo mana duk abinda kika gani ki kawo" Jiddah ta kasa mata musu amma bata tashi ba, Hajja tace "To tashi mana" Mikewa tayi rai ba dadi ta nufi kitchen din, ta fi minti daya tana kare ma kitchen din kallo, kitchen din na nan yanda yake banda kayan kitchen da aka cika masu tsada, ta dinga kallon wajen wanke wanke dake cike da dirty plates, ta kalli wajen gas taga duk yayi baki alamar ba a gogewa, bin kasan kitchen din tayi da kallon mamaki ganin how untidy it is, daukan plate tayi ta tana kare ma plate din kallo, kawai taje ta dauraye snn ta karasa store ta bude robobin da ta gani ta diba duk abubuwan ciki, wani tray ta dauka ta daura ruwan gora biyu da cups snn ta fito kitchen din, xaune taga Aneesah a parlor tana kallon Hajja dake ta xuba, Aneesah ta dinga kallon Jiddah da wani irin mamaki, don bata ma san da ita aka xo ba, Hajja tace "Yauwa, kinga kinyi dubara, sannu" Jiddah ta ajiye tray din hannunta ta d'an kalli Aneesah da mood dinta ya sauya lkci daya tace "Ina yini" Aneesah ta hau danna wayarta, Hajja tace "Gaisheki fa take Nanisa kike ko?" Aneesah ta daga kai tace "Ohk, sannu, lfya lau" Jiddah ta mike ta xauna saman kujera tana kallon Tv dake aiki, mikewa Aneesah tayi tace "Na gaisheki Hajja, ina d'an yin abu ne a sama" Daga haka ta wuce Hajja ta bi ta da kallo, ta rike ha6a murya can kasa tace "Tabdi" Jiddah dai kallon tv kawai take, Hajja tayi kasa da murya tace "Kaji min shegiya, ta sanki ne ta maki wannan walakancin ni ya su?" Saukowar Aliyu yasa Hajja tayi shiru, ta kallesa tace "Amma ba a nan parlon xa a yashe mu ba kamar marasu makabuli ko Aliyu" Yace "Mu je sama" Mikewa Hajja tayi ta kalli Jiddah tace "kwaso mana kayan flawan da lemon" Jiddah ta dau tray din ta mike suka hada ido da Abuturrab da sauri ta dauke idonta, Tuni Hajja tayi hanyar stairs Abuturrab ya bi bayanta, sai sannan Jiddah ta fara tafiya ta wani hade rai. Dakin da Jiddah ta xauna a lkcn da take gidan ya shigar da su, Hajja tace "Ba shakka, ko mutum xai yi sati a nan babu wanda xai san abinda yake ciki abunsa" Jiddah ta ajiye tray din ta xauna kasan carpet, Hajja ta cire mayafinta ta linke ta bude press ta ajiye, katon jakarta kuma ta rataye sa a bag rack, sai kallonta Jiddaj take da mamaki, ta juyo tace "Ki cire wannan Hijabin ki sha iska abun ki, ai nan ba bakon waje bane, gidan Aliyu ne fa" Jiddah tayi gathering courage tace "Hajja ni fa makaranta xan wuce yanxu dama, tunda akwai sauran lkci" Hajja ta kalli Abuturrab tace "Kaga jaraba ko, Ramlah ce ta koya mata haka fa kafin mu fito, to ko dai Ramlan nan kanwar uwar Jiddan ce bamu da labari??" Abuturrab dake kallon Jiddah, calmly yace "Baxa ki je ba" Hajja tace "Atoh dai, su makarantar basu san uxuri bane" Wani kallo Jiddah ta masa ta gefen ido lkci daya ta dauke kanta ta daure fuska, Da mamaki ya dinga kallonta babu ko kiftawa, can ya shafa kansa yace "Wani abincin xa ku ci Hajja?" Hajja tace "Ni ko tuwo aka samu a ban Aliyu" Yace "Ohk" sannan ya juya ya fita, Hajja tace "Ikon Allah, yanxu Aliyu ne ke nan nan da ni kamar wanda nayi ma wani abun arxiki, wllh ni tunda muke bai ta6a girmama ni ya mutunta ni irin yau ba, ohh Allah mai iko" Jiddah dai bata ce mata komai ba. Aliyu ya nufi bangarensa ya shiga parlor ya tadda Aneesah xaune tana shan lemon fata, idan ta sha sai ta jefar da fatan akan farantin da aka dauro lemukan a kai, yana mata wani irin kallo yace "Aneesah na sha gaya maki idan xaki ci abu plss ki daina ci min a parlor i detest that..." Ta kallesa daga sama har kasa tace "Naga dai ba ni na shigo da lemun ba kai ka kawo abunka ko" Yace "For heaven sake ya xa ki maida min parlor wajen cin abinci, what's d essence of d dinning area downstairs" Bata kuma basa amsa ba ta dau wani lemun tana sha a hankali tana jefar da kwallon kan faranti, gajeran wando ne jikinta da yar vess, yace "Tuwo grandma dita ke son ki girka mata ynxu" Ta sauke kafarta daga saman kujeran tace "Tuwo?" Yace "Ehh" wani dariya tayi tace "Yanxu kai ka ta6a ganin ko indomie na girka a gidan nan balle tuwo, wllh Aliyu ban san haka kake da takura ba sai da muka yi aure, kullum sai ka samu matsalar da xaka billo da shi idan ka dawo weekend, kace can datti, nan datti, can wari nan wari?? sannan ma tsaya tukun, ni ka gaya min xaka yi baki a gidan nan? To kaga baka sanar da ni ba, don da ka sanar dani akwai wata kawata chef sai in gayyato ta ta min girki in biyata, amma waye xai maka wannan wahala da tsakar ranar nan, beside ba naga tare da Me siyar da doya da dankali ta xo ba, ai ita ta sa6a wahala sai ta tashi ta shiga kitchen din ta girka masu in yunwa suke ji, don wllh wllh baxan iya ba, in ma ji da gajiyar wankin bayin da kasa nayi daxu mana" Kallonta ya dinga yi kafin ya juya ya fita daga parlon ta bi sa da wani shegen harara tana dauko wayarta dake ring, d'an xaro ido tayi ta katse wayar sannan ta saka shi a flight mode. Eatry Abuturrab ya tafi ya siyo take away din tuwo da gasasshiyar kaza, Hajja ta dinga washe baki bayan ya shigo masu da ledan tace "Allah maka albarka Aliyu, sannu kaji, matar taka bata yi girki bane?" Yace "Bata yi ba" Hajja tace "Toh Allah ya kyauta, haka fa Hafsah ta dinga yi ma Usman bata son girki" Abuturrab ya kalli Jiddah dake kwance ta juya masu baya nan ko takaici ne duk ya bi ya isheta tayi fashin makaranta, xaunawa yayi a dakin Hajja tayi ta jan sa da hira yana responding har aka kira la'asar, Jiddah ta sauka kan gadon ta shige bandaki ya bi ta da ido, Hajja ta kyabe baki murya can kasa tace "Uwar rikon ce fa ta kitsa mata karya da gaskiya, kaga ko yar cin cin din da alkaki ta ki ci wllh... Tun daxu sai nukurci take, taki sakewa" Abuturrab yace "Kyaleta, a nan xaku kwana" Hajja ta gyara xama tace "Atoh dai" mikewa yayi ya fita don xuwa yayi alwala ya wuce masallaci. Har kusan isha Jiddah bata ga alamar Hajja xata ce su tashi su tafi ba, ga wani abincin Abuturrab ya kawo, bayan ta idar da sallah tana xaune kan darduma a hankali tace "Hajja wai baxa mu wuce ba?" Hajja tace "Ke ba fa gidan 6are na xo ba, bari kiji in gaya maki, ni wllh bansan bakin hali gareki ba sai yau, gidan jikana ne nan fa, babu ruwanki da sanda xa mu wuce, ke dai iyakarki ba rakiya ba, xan kawoki inda xa a cuceki ne? Ni fa na rainesa yana karami, idan ban xo gidansa ba ina xanje, kuma a nan xan kwana wllh don xuwa gobe da safe nake son ganin iyakar xabiyar matarsa da ta xo ta gaishe mu a tsattsaye har yanxu bata sake shigowa ba, dadin abun kuma jikana ya saurareni gashi muna ta hiran yaushe gamo da shi don haka sai Allah ya kai mu gobe xan nuna mata ni er banxa ce" Jiddah ta ji kamar ta fashe da kuka, lkci daya hawaye ya kawo idonta ta mike ta koma can karshen gado ta xauna, Hajja ta kwashi take away din da suka ci abinci ta fita xuwa kitchen, Sai a sannan Jiddah ta fashe da kuka ta hade kanta da gwiwa, bayan kusan minti goma Hajja ta shigo dakin tana hura hanci tace "Tirrrrrr, ashe kazama Aliyu ya auro? Ke kinga kitchen dinta duk wari kuwa? Wllh da nasan haka kitchen din yake ni baxan ma fara shan ruwan gidan nan ba sai dai a fita a siyo min a waje, a garin yaya mace xata bar kitchen dinta haka ni Dije? Wllh sai da tsoro ya kamani, yaushe Aliyu shi ma ya lalace da son kazanta? A yanda na san sa a da fa har tunani muke ko aljanun tsafta ne suka auresa, to naga duk ya lalace ya xuba ido kitchen dinsa ya ru6e duk wari" Jiddah dai bata ko kalleta ba, Hajja ta xauna tayi shiru alamar dai tunanin kitchen din take kuma abun ya dameta, can tace "Tirrrr" Sai kuma tace "Huhuhu kazama ce wllh, kwanukan duk wari naji suke, ni kamar har da kiyashi naga suna yawo a kitchen din, ga dai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login