Showing 282001 words to 285000 words out of 334042 words

Chapter 95 - JIDDARTUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Aug 2024

270072

dama idan ba tashin hankali ba a gidan nasa yau, ke kuma Ramlah halan har yanxu yan sanda basu gaji da ganin fuskarki bane a yankin nan? Komai kice yan sanda abu da xa ayi solving cikin gida sai ki kwasa ki kai ma yan sanda? Who does that for God sake?" Hajja ta rike kai tace "Huhuhu Allah ya wadaran naka ya lalace, na kara tsoron Hauwa, na tsorata da lamarinta!! waiiiiii Allah" Umma dake ta kallon Ummi babu ko kiftawa tace "Fine and good, daga yanxu duk wani abu da ya shafi gidan Aliyu dama na cire hannuna in sha Allah" Ummi tace "Aa gwara ki cire wllh da wannan sintirin gidan yan sandan dai, don wannan ba yi bane... kullum ana ganin yan sanda na kai komo a gidansa, babu saiti ne abun?" Umma tace "Ai sai ki tsaya ki saurareni yaya, ban gama ba" Ko kallonta Ummi bata yi ba, Umma tace "Amma kinga a kan lamarin Jiddah? Wllh babi wanda ya isa ya sa in cire hannuna, sai inda karfina ya kare ba sani ba sabo, kuma wallahil azeem sai an biya aika aikan nan da yar iskar tayi mata a daki, babu ruwana da wanda xai biya, kawai abinda na sani a mayar ma yarinya da dakinta yanda yake, kuma wllh baxata koma gidan ba sai an canxa mata kayan dakinta dai dai da yanda nayi mata" Hajja tace "Lallai... Toh da fa, ai babu tantama Hauwa ta aiki Nanisa tayi aika aikan da tayi, ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba, sannan Usman na dawo xan basa shawaran ya dawo da matarsa Hafsah tun dai kishiyar abar dadi ce, kowa sai yayi ta fama da na shi" Ummi tayi murmushi tace "Kowa fa da halinsa yake xaune Hajja, ni wllh bana mata bakin cikin dawowa dakinta, karya ce ke karewa ba dai gaskiya ba..." Kwafa Hajja tayi ta nufi dakinta, Umma kuma ta fice daga gidan gaba daya.... Abuturrab na xaune parlor tun bayan fitar su Umma, gaba daya good mood dinsa yau ya baci, hukuncin da xai ma Aneesah kawai yake tunani, ga shi Ummi ta hanasa hukunci me kankat wato saki, abubuwan da ta dinga masa tun farkon aurensu ne ke dawo masa da yanda ya sameta ba virgin ba, and he hate himself for everything, he hate himself for being silent for that long babu wani hukunci da ya dace da ita banda ya rabu da ita na har abada don ba canxa halinta xata yi ba, ba daina abubuwan da take yi xata yi ba, babu abinda yake basa mamaki irin yanda ya iya xama da ita for this long duk da mugun kazantarta, a yanda ya ba ma tsafta muhimmanci a rayuwarsa bai ci ace ya iya ci gaba da xama da Aneesah ba, kai bai ma ta6a xaton xai iya rayuwa a inda kazanta yake ba, duk wa ennan tunanin suka hadu suka sa yaji inaa baxai iya rayuwa da ita a matsayin mata ba, banda he was impatient tun xamansu na farko da Jiddah ya gano me tsafta ce sosai, bai ta6a dawowa ya tarar da gidan ko jikinta ba dai dai ba, komai ya gwada mata a rananta na farko a gidan yayi sinking a kanta, bude kofar parlon aka yi ya daga kai da sauri Umma ta shigo da Maimoon da wasu yan mata biyu, ko kallonsa bata yi ba ta wuce sama su Maimoon na biye da ita, Maimoon sai boye hannunta take cikin Hijab dinta, Abuturrab ya bi su da kallo har suka haura sama, next thing da ya fara ji shine fashe fashe da tarwatse tarwatse a sama, ya jinginar da kansa da kujera sai kuma yayi murmushi, shi dai ko motsawa bai yi ba har suka sauko kasa bayan minti talatin, Umma ta nufi kofa kamar boss su Maimoon na biye da ita a baya, ko da wasa Maimoon bata yarda ta kalli inda Abuturrab yake ba, ya bi su da ido har suka fita sannan ya mike ya haura sama, dakin Aneesah da ya gani a wangale ya nufa, ya tsaya bakin kofa yana kallon yanda suka yi kwatsa kwatsa da dakin don har ya fi na Jiddah muni, har akwatunanta sai da suka faffasa, ga show glass dinta me shegen tsada da aka kawo mata kwanan nan shima duk sun hallaka shi, ya fi minti biyar tsaye kafin ya juya a hankali ya bar bakin kofar, yana tunanin dama haka auren mata biyun yake? Shi ya xata a film kawai irin haka ke faruwa, so even in reality, reality din ma a gidansa, ya sauke wani ajiyar xuciya shi dai baxai ce ya ji haushin su Umma ba ko kadan that serves Aneesah right, downstairs ya koma ya ci gaba da xamansa a nan. Throughout ranan a dakin Ummi Aneesah ta yini, haka nan kawai taji hankalinta ya kwanta sosai, ko ba komai ta samu saukin abinda xuciyarta ke mata tun shekaranjiya, ganin idon Ummi ya sa duk aka kira sallah kafin a ajiye mic a masallaci xata tashi taje tayi alwala a bandaki, da yake kafin su dawo gidan sai da Ummi ta kai ta chemist aka duba mata yankewan da tayi aka yi mata alluran tetanus sannan aka bata drugs shi sa ta samu saukin xafin wajajen da ta yanke, rabon da ta ci abinci har ta manta sai yanxu a dakin Ummi da aka kawo mata tuwo me xafi da miyar kubewa, ramar da tayi was so obvious shi yasa Ummi ta sake tausaya mata don a hakikanin gaskiya kishiya ko ma wace iri ce babu dadi kai ko da kishiyar rana daya ce, balle wnn irin bambanci da Abuturrab ya nuna kiri kiri ai sai mutum ya hadiyi xuciya ya mutu, Aneesah ta gama cin tuwon ta ajiye plate da bowl din gefe ta tafi bandaki ta wanke bakinta ta fito ta xauna saman darduma, ita fa bata ji tayi regretting abinda ta aikata ma dakin Jiddah ba, da son samu ne har da motar ya kamata ta hada a lkcn, ta share hawayen da ya kawo idonta duk da xuciyarta ya rage xafin da yake mata amma har sannan bai dawo dai dai ba, duk son da take ma Abuturrab xai walakantata ya ci mata fuska haka dama... tana son kiran Aunty da yan uwanta amma bbu dama tunda bata taho da wayarta ba, bude kofar dakin aka yi ta daga kai, suna hada ido ya wani daure fuska ya juya ya fice daga dakin don bai san tana ciki ba da baxai shigo baz ta bi sa da kallo. Main parlor ya koma ya xauna sai ga Ummi ta fito daga bangaren Abba wanda ko minti talatin bai yi da dawowa gidan ba, ya gaisheta ta amsa tana kallonsa, mikewa yayi yace "Abba ya dawo ne?" Tace "Ehh" parlon ya nufa ya shiga ya gaida Abban nasa, yana xaune cikin parlon Hajja ta shigo, Abba ya gaisheta da ladabi yace "Dama yanxu xan shigo ai dakin naki Hajja" Hajja tace "Aa ba ruwana ni ba sai ka shigo ba, ni da abu ya tsaya min a rai ba gashi na taho da kaina ba" xaunawa tayi parlon tace "Toh abubuwan da suka faru dai yau Usman da a Masar ne kai da kake tushen komai xa a daure, abubuwan da suka faru yau kam sai godiyan Allah waiiii, Aa ban ta6a ganin haka ba ko a pim" Abba dai kallonta yake ta yi, Hajja tace "Toh ba dai komai bari Ramlah ta iso na sa yara sun kira min ita daxu so nake ayi komai gaban idonta, tun da na dawo Masar abubuwa ke ta faruwa a garin nan, wanda lkcn da nake bauchi babu haka wllh" Abba ya sauke ajiyar xuciya yana kallon Abuturrab yace "Do u have any idea of what happened?" Hajja tace "Aa ba sai ka juya masa yare ba, ni nan xan maka bayanin komai tunda a kan ido na aka yi, amma sai Ramlah ta iso, to amma kafin ta iso ina son kayi kiran Hafsah ta xo, nasan ai tana garin, kayi kiranta ta xo gidan nan" Kallonta kawai Abba yake, Hajja ta kalli Abuturrab tace "Ta shi mu je, idan kowa ya hallara sai a dawo ayi magana sinka sinka" Ya kalli Abbansa, Abba yayi masa alaman da su tafi, mikewa yayi ya bi bayanta suka fita, shi fa duk gaba daya tunaninsa na kan Jiddah amma shakkan xuwa gidan Umma yake, bai ta6a tunanin xai yini yau ba tare da ita a gefensa ba, is she even feeling much better now? Ta iya ta ci abinci kuwa, duk wa ennan tunanin suka taru suka damesa a dakin Hajja, wanda kawai Hajja surutunta take bai san me take cewa ba, Da karfi Hajja tace "Ko ba haka ba Aliyu?" Ya daga kai ya kalleta duk da bai san me take cewa ba a hankali yace "Haka ne" Tace "Atoh, kowa xai san ni er banxa ce wllh, shiru shiru na nacutata tun ba yau ba na sani" Yana kallonta yayi kasa da murya yace "Hajja don Allah idan an xauna kice masu su bar ni in tafi da matata, sai ta xauna bangarena kafin a canxa mata kayan daki, ita kuma Aneesah dama xance taje gida ta huta ne na kwana biyu don na gaji da halayyanta wllh" Hajja tace "Nima nan da ba gida daya muke ba na gaji da ita balle kai, ita kuma Jiddah uban wa ya isa ya hanaka tafiya da ita mutum da matarsa, ai dama tare nace Ramlah su taho, kafarta kafarka, babu shegen da xai shiga hakkin ka ina gidan nan" Sosai Abuturrab ya ji hankalinsa ya kwanta, sallama aka yi bakin kofar dakin, Hajja ta daga kai da sauri tayi mici mici da ido kamar me son gano muryar, Sai kuma ta amsa tace "Bismillah" Aka bude kofar Aunty ta shigo dakin kanta a kasa hannunta rike da karamin cooler, Hajja sai satan kallonta take, Aunty na murmushi ta xauna saman carpet bayan ta ajiye coolern hannunta tace "Sannu Hajja" Hajja tace "Yauwa sannu" Cike da ladabi kanta a kasa tace "Ina yini Hajja?" Hajja ta hade hannunta yanda manya ke gaisuwa tace "Lafiya lau Hafsah, lafiya lau wllh" Aunty tace "Fatan mun same ku lafiya, ya jiki jiki" Hajja tace "Aa wllh Alhmdlh, ashe kina dai kadunan" Aunty tayi d'an murmushi tace "To ya xa ayi Hajja, muna nan wllh, sai yanda hali yayi" Hajja tace "Allah sarki, to sannu da xuwa" Aunty tace "Yauwa Hajja, rayuwar ce sai hakuri wllh" Abuturrab da ya dauke kansa da farko don bai yi niyyar gaisheta ba sai kuma ya juya ya d'an kalleta babu yabo babu fallasa da nufin gaisheta, amma me?? buda ido yyi sosai ganin abu take kokarin cusawa karkashin gadon Hajja tana jan Hajja da xance, ya kalli Hajja dake ta wani murmushi tana cewa "Hakuri kam ai ya xama wajibi a wannan xamanin" Aunty ta gama tura abinda xata tura ta dauke hannunta da sauri, sai kuma ta mike tace "Toh Hajja bari in karasa parlon Yallabai shi yayi kirana dama" Hajja tace "Aihoo ai ni nace ya kiraki, ni na sa shi wllh" Aunty tace "Allah sarki Hajja, bari in je in dawo" Xata fita suka kusa cin karo da Umma, Aunty ta koma gefe, Umma ta shigo Aunty na wani murmushi tace "Ina yini Hajiya Ramlah" Umma bata tsaya ba tana tafiyarta tace "Lafiya lau" Kujera ta nema ta xauna, Aunty ta amsa gaisuwar Jiddah da wani irin fara'a tace "Sannunku da xuwa" Jiddah ta sunkuyar da kanta ta karasa parlon ta xauna saman carpet daga kusa da Hajja, Abuturrab sai kallonta yake babu ko kiftawa, Aunty dai ta fita parlon ta nufi bangaren Abba tana murmushi. Hajja ta yi wani murmushi tace "Shegiya matsiyaciya wai ni xata yi ma siyasa kamar warce bata yi xaman Masar ba, to xata ci kaza kazanta yau wllh" Tana fadin haka ta bude warmer din da Aunty ta ajiye taga farfesun kayan ciki sai turiri da xuba kamshi yake, Hajja ta kalli Jiddah da ta sa hijab har kasa tace "Maxa Dauki d'an iskan naman nan ki boye a hijabinki ki tafi can kwararo ki juye ki dauraye mata kulanta ki kawo, maxa maxa" Jiddah ta mike ta amshi warmer din ta nufi kofa a hankali Abuturrab ya bi ta da kallo, yana son tashi ya bi bayanta but he have to bring out abinda Aunty ta tura karkashin gado kuma yana son yin hakan ne ba tare da kowa ya lura ba, a hankali ya gaida Umma ta amsa tana danna wayarta, Hajja tace "Bari Jiddar ta dawo duk mu baxama parlon Usman" Umma dai bata ce komai ba, ba a wani dau lkci ba Jiddah ta shigo ta ajiye warmer din sannan ta xauna Hajja tace "Allah ya maki albarka, tashi parlon Usman xa mu tafi" mikewa Jiddah ta kara yi, Hajja ta mike Umma ma ta tashi suka nufi kofa gaba daya Abuturrab ya bi su da kallo, bayan fitansu ya tashi ya tafi karkashin gadon dai dai ta inda Aunty ta xauna ya tura hannunsa a hankali yana laluban kasan, bai ga komai ba alamar ta wuntsular da shi can ciki, hakan yasa shi dage katifar dakin, can ya hango wani katon abu kamar laya an garkame da wani irin kwado ya dinga kallon abun snn ya ciro handkerchief dinsa ya durkusa ya dauka yana kallo da wani irin mamaki, nannadesa yayi da handkerchief dinsa ya saka a aljihu snn ya mayar da gadon yanda yake ya fita dakin xuwa parlon Abbansa. Abba ne xaune parlon sai Aunty, Ummi da Aneesah dake xaune kasa daga gefen Ummi, Jiddah kuma ta xauna kasa kusa da Umma, Hajja ta shimfida darduma tayi xamanta a kai ta mimmike kafa tana kallon Aunty da Aneesah kasa kasa, xaunawa Abuturrab yayi shi ma a kasa, Abba ya bude taron da addu'a sannan yana kallon Hajja yace "Kin yi kirana kwanaki kadan da suka wuce ban samu tahowa ba sai yau, ina fatan lafiya Hajja" Hajja ta gyara xama tace "Toh ni dai kafin ince komai a nan so nake in ji ko kauron Mama nayi maka ya sa kaji gwara ka mayar she ni gantallaliya kawai Usman" Abba dai yayi shiru yana kallonta, Hajja ta kalli Aunty da kyau tace "Maimaita abubuwan da kika gaya min a parlon Aliyu ranan" Sosai gaban Aunty ya fadi ta dinga kallon Hajja.


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsAppBayan few seconds Abba ya kalli Umma yace "Furnitures din na nawa aka siya mata?" Umma ta gyara xama tace "2.3m" Abba yace "Shkkn, xa a san yanda xa ayi, Allah ya rufa asiri" a takaice Umma tace "Ameen" kallon Jiddah tayi tace "Tashi ki dauko min jakata a parlon Ummi mu tafi, dare na yi Jiddah..." A hankali Jiddah ta mike ta nufi kofa Abuturrab ya bi ta da kallo, sai kuma ya kalli Umma, bayan fitar Jiddah da few seconds ya kalli Abba yayi kasa da murya a hankali yace "Allah ya kara girma Abba, mun gode" Abba yace "Ameen" mikewa yayi ya nufi kofa da sauri, Aneesah ta bi sa da ido har ya fita, sai kuma ta daga kai ta kalli Ummi cikin sanyin murya tace "Nagode Ummi, Allah ya kara girma" Ummi tayi murmushi tace "Ameen, sai ayi ta hakuri kuma" mikewa tayi ta fita parlon ita ma, Umma dai ta ta6e baki ta kalli Abba ta ga Ummi yake kallo.... Jiddah na shiga parlon Ummi ta dau jakar Umma da wayarta dake ajiye saman kujera xata fito aka bude kofar parlon, ta daga kai da sauri, suna hada ido ta sauke nata idon har ya iso inda take tsaye, ya jawota kusa da shi yyi wrapping hannunsa daya a bayanta ya dago kanta yana kallonta yayi kasa da murya yace "How are u feeling now?" Ta dauke kanta tace "Fine" Da damuwa yace "Are u sure? Me kika ci a gidan Umma daxu? Where u able to eat?" Tace "Na ci" yace "Kina kai mata jakar ki fito mu wuce gida yanxu" Ta xaro ido tana kallonsa, ya hade rai yace "To bin ta xa ki yi?" Kafin tace komai aka bude kofar parlon, da sauri ta turasa ta koma baya, Aneesah ta shigo parlon babu ko sallama, kallo daya tayi masu ta wuce dakin Ummi fuskarta a daure ta kulle kofar, Abuturrab ya bi ta da wani harara, Jiddah dai bata ko kalleta ba ta bi gefensa xata wuce ya rikota da damuwa yace "Are u serious bin ta xa ki yi Jiddah? Kin ga fa gobe xan koma aiki" Ta kallesa a hankali tace "Toh ni baxan iya ce mata a'a ba" amsar jakar da wayar yayi a hannunta yace "Ki tafi dakin Hajja ki jira ni" Bai jira me xata ce ba ya nufi kofa ta kasa cewa komai ta bi sa da kallo har ya fita, direct parlon Abba ya koma ya shiga da sallama bai bari sun hada ido da Umma ba ya ajiye mata jakarta da wayarta a gefe kansa a kasa yayi masu sae da safe, daga haka ya fita daga dakin, Ummi ta bi sa da kallo sae kuma ta mike ta bi bayansa, tana fitowa Main parlor tace "Aliyu" Abuturrab da har ya nufi dakin Hajja ya juyo yana kallonta sannan ya dawo, tace "Tafiya xa ku yi gidan naka yanxu?" Ya sunkuyar da kai yace "Eh Ummi" tace "You should be taking them both then" Ya daga kai ya kalli Ummi amma ya kasa ce mata komai, Ummi tace "Ka tsaya kallona ko da matsala ne?" a hankali ya girgixa mata kai, tace "Toh sae da safe, sae ayi ta hakuri kuma, Allah ya baku


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login