Showing 327001 words to 330000 words out of 334042 words

Chapter 110 - JIDDARTUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Aug 2024

270073

koma gida kuma sai in je in daukeki a can gidan mu tafi" Tace "Shkkn" Bayan magrib Abuturrab ya tafi can gidan Umma ya dauketa xuwa can gidan Hansai, yau kam bai yi mistake din xuwa anguwan ba nose mask ba, tunda yayi parking Umma ke kallon layin da gidan yake, suka sauka daga motar ya nuna mata gidan, Umma ta shiga ciki ya tsaya daga waje ya ki shiga, da ya tuna irin abubuwan da Hansai ta dinga ma Jiddah a hayi da irin axabar da ta dinga gana mata tana amfani da ita tana making kudi shi kansa dubi irin karyan da ta dinga lafta masa ya bata kudinsa yayi dubu dari biyar sai yaji wani bacin rai ya xo masa, and he believes the situation she is right now serves her right, don haka ko digon tausayinta baya ji wllh, Umma na shiga dakin ta rasa wajen xama ga wani doyi da dakin yake, Hansai dake xaune kan darduma da wani rubabben fitila da ya d'an haske dakin ta amsa sallamarta cikin sanyin murya sai kuma ta mike ta shimfida mata buhun cement a kasa tace "Sannu" Umma ta daure ta xauna tace "Yauwa nagode... ya gida?" A hankali tace "Lafiya lau" Umma ta kunna wayarta ta ajiye sai kallon Hansai take ganin yanda idanuwanta suka wani kumbura tace "Amma in ji dai lafiya baiwar Allah" Kamar jira take ta fashe da kuka tace "Yau kwana uku Allah yayi ma 'ya ta rasuwa..." Sai ta dinga rusa kuka, Umma tace "Hasbunallah, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya gafarta mata" cikin kuka Hansai tace "Ameen" Umma ta girgixa kai tace "Nasan baki san ni ba, ni ce uwar rikon Jiddah sannan kuma kanwar uwar mijinta" Hansai ta dinga kallon Umma sai kuma ta sunkuyar da kai, Umma tace "Na xo neman wata alfarma ne a wajenki" Cikin rawar murya Hansai tace "Ina jin ki Hajiya, Allah ya sa bai fi karfina ba, ni ma kuma ina son rokon wata alfarka a gareki" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "In sha Allah" a hankali Hansai tace "Toh wacce alfarman kike so wajena Hajiya?" Umma tace "Hoton mahaifin Jiddah xaki bamu idan har kina da shi don Allah" Hansai ta goge idonta tace "Baxa a rasa ba" Tana fadin haka ta mike ta bude Ghana must go da ta ciro hoton kakar Jiddah da mahaifiyarta, ta dubo hoton mahaifin Jiddah wajen kala shidda ta ajiye ma Umma har da wanda yake saurayi, Umma ta dau hotunan tace "Toh nagode kwarai da gaske, ki fadi ta ki alfarman..." Hansai ta xauna a sanyaye tace "Alfarma daya nake so Hajiya don Allah a bar ni inyi xumunci da Jiddah, ko da sau daya ne a shekara in dinga ganinta xanyi farin ciki wllh, nasan na xalunceta na ci amanarta da na mahaifanta amma na roketa yafiya kuma tace ta yafe min yau wata hudu kenan tun xuwansu gidan nan, in ci albarkacin ubanta kada a rabani da ita don girman Allah" Hawaye kawai take tana shessheka, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh in sha Allah, xa ku yi xumunci" Godiya Hansai ta dinga yi ma Umma kamar xata ari baki, Umma ta bude jakarta ta ciro dubu biyar tace "Kiyi hakuri da wannan sai mun sake dawowa, duk da gobe ko jibi xa mu xo din tare da Jiddah ta yi maki gaisuwar yar uwarta in sha Allah" Har bakin mota Hansai ta raka Umma duk jikinta a sanyaye, har ranta take son rayuwa tare da Jiddah gatan da bata gwada mata ba tun ubanta na da rai har ya rasu tana son ta gwada mata yanxu duk da bata da komai, so take kawai ta ja ta a jiki tamkar bibalonta, tana ganin Abuturrab ta duka tana gaishesa, ya amsa a takaice ya xaga ya shiga driver seat ta bi sa da ido, Umma ta bude gaba ta xauna tana daga ma Hansai hannu har suka bar anguwar, sosai taji tausayin matar, lallai kam ita taga kamun Allah tun a duniya. Suna komawa gida da hoton Abban Jiddah Hajja tace Inaaa ai hoton baxai kwana ba aje a nuna ma mijin Hajiya Fatima kawai, haka suka shirya da ita da Umma, da Jiddah da Abuturrab xuwa gidan Hajiya Fatima bayan isha.....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp💖💖 *Jiddatul Khair**💖💖





_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻






94...Parking Aunty Rahama tayi a kofar gidan Abba, Hajja dake bayan motar tana washe baki tace "Allah ya maki albarka, in sha Allahu nan da kwana biyu xan dawo anguwan naku gaba daya kin ji?" Aunty Rahama na murmushi tace "Toh Allah ya kawo ki lafiya kaka" Jiddah dake gaban mota tace "Mun gode Aunty" Aunty Rahama na mata murmushi tace "In kun shiga ki gaida su mama kin ji" Hajja tace "Au ni da nake xaton xaki shigo ku gaisa" Aunty Rahama tace "Aiki xan tafi kaka, na makara wllh" Hajja tace "Aa kin makara gaskiya gashi har tara saura, to ke mijin naki ba a kasan yake bane?" Tayi murmushi tace "Allah ya mashi rasuwa kaka" Hajja ta saki wani salati tayi tagumi cike da damuwa tace "Allah sarki, Allah ubangiji ya gafarta masa, to baki da 'ya ya da shi ne?" Tace "Ina da, su biyu ne, suna gun yayansa a Abuja, sai hutu ake kawo min su" da sauri Hajja tace "Aa ki amshe yaranki, ce masu kika yi baxa ki iya kula da su ba ko salon kar yaran su ji kanki su san ciwonki" Ita dai murmushi kawai take, Hajja tace "Wllh amshe abin ki, ni ban yarda da rikon d'a ba..." Daga haka ta bude motar ta sauka, Jiddah ma ta sauka tana kara yi ma Aunty Rahama sallama suka shiga gidan da Hajja, tun daga parlor Hajja ke kwala ma Ummi kira, Ummi na fitowa tace "Toh dai Jiddah ba yar matsiyata bace, kuma kakarta na nan da ranta sai kin ga abun arzikin da aka mana a wannan gari na gombe, mutanen kirki mutanen arxiki suka cika garin, sun karrama mu sun daraja mu sun mutunta ba, wllh basu so mu taho ba amma wannan yayan baban nata Alhaji Sani naji ana ce masa ko wa? Wannan dai da ya mana jagora xuwa garin shi ya axalxala mu taho, in don ta nine da bamu dawo ba wllh, jiya da daddare muka dawo to yau naga wnn yarinya Jiddah sai wani nukurci take taki kulani nace to ko kewan mijinta take shine dai nace su maido mu gida da safe, amma wllh dangin ubanta en arxiki ne babu talaka ko kwaya daya a cikinsu, ke kin ga gidan ma kuwa, wllh yayi biyar din wannan, kuma kinsan gidan waye, gidan uwarsu ne, su suka gina mata gwanin ban sha'awa, ai ita kam ta more rayuwa wllh...." Ummi tace "Toh Alhmdlh, nayi murna sosai, Allah ya bayyana dangin mahaifiyarta haka" Hajja tace "Allah gidan yayi ukun wannan kuma tsohuwar kadai ke rayuwa a ciki, duka duka fa bai fi ta girmeni da shekara uku ko hudu ba, amma sai kin ga abinda yaranta suka kera mata, tana xaxxaune ta mike kafa sai dai ayi mata komai" Ummi ta amsa gaisuwar Jiddah da ta duka kasa ta gaisheta, Ummi tace "Ya hanya, fatan kun dawo lfya, ya kuma ku ka bar mutanen can din" Hajja ta amshe tace "Alhmdlh, babu abinda basu mana ba, yanxun ma fitowa muka yi ba shiri ita kuma warce ta kawo mu tana ta sauri xata aiki, banda haka in gaya maki ai tsarabanmu da yanxu haka ba a gama shigowa da su ba, to sunce anjima da yamma xa a taho mana da shi, ke dai ki bari kawai Hauwa, karramawa da mutunci na inda yake, ni kam bani da abinda xance ma mutanen nan" Daga haka ta wuce dakinta, Ummi da ta bi ta da kallo tace "A kawo maki kumallo Hajja" Hajja tace "Meye kuma kumallo? Aa mu mun yi lafiyayyen kari, kawai a bani makullin d'an kuturun dakina" Ummi ta tafi dauko mata makullinta ta kai mata, ta bude ta shige ciki tana kyabe baki, Ummi ta dawo parlor ta xauna tana kallon Jiddah tana murmushi tace "Kin je kin ga kaka da kawunnanki ko?" Murmushi Jiddah tayi ta gyada mata kai, Ummi tace "Toh Alhmdlh, Alhmdlh, i am so happy for you daughter" Jiddah dai ta sunkuyar da kanta kawai, Tashi Ummi tayi ta tafi parlon Abba, Jiddah ta dinga kallon hanyar dakin Abuturrab amma ta kasa tashi, ta fi minti biyar sai ta kalli dakin sai ta dauke kai, can dai ta mike a hankali ta nufi dakin kamar munafuka muryan Ummi taji tace "Ai bai nan ya koma aiki Jiddah" kunya ta ji kamar ta nutse, ta kasa juyowa ta kalli Ummi, jin shiru sai kuma ta juyo a hankali, gani tayi Ummi bata ma wajen, da sauri ta wuce dakin Hajja. Washegari da safe Jiddah na dakin Hajja, Hajja na cewa "Kin ga ai ni bana kai kaina inda Allah bai kaini ba kuma bana takura ma yarana ince sai sun min abu dole, da wata ce yanxu duk sai ta kwarzabi yaranta tace sai fa an mata gini irin na wannan kakar taki, amma ni kam Allah ya kiyaye inyi haka sai kace wata er banxa, ni ko burgeni gidan bai yi ba balle inji sha'awa ince a min irinsa" Jiddah dai kallonta kawai take amma bata ma san me take cewa ba, kewan Abuturrab kawai take, ji take kamar ta fi wata daya rabon da ta gansa, she's a kind of sad, gaba daya ta ji gidan ya isheta, gashi bata san sanda xai dawo ba, ga surutun Hajja dake sa mata ciwon kai, tayi mata xancen gidan Dada ya fi sau ashirin daga jiya xuwa yau, har Umma da ta xo jiya ta bata labari, Hajja ta ta6e baki tace "Ba ruwana da sa ma wani ido wllh, nagode Allah da inda ya ajiyeni, shege ne kawai xai dinga hangen abun wasu" Bude kofar dakin aka yi Ummi ta shigo tayi ma Hajja sannu, tana kallon, Jiddah tace "Ur husband said he will be back in the evening of today, so get ready after Zuhur, i will instruct the driver to drop u home" Tace "Toh Ummi" Juyawa Ummi tayi ta fita, Hajja ta ta6e baki tace "To ko matansa ma basa hanasa ya min kantamemen gini ba don bakin ciki, ai kai dai kawai ka haifar ma mace yaro kawai, bayan haka baka da sauran martaba a wajensa" Tun da Ummi ta fita Jiddah ke counting agogo sai taga baya sauri, wai karfe goma da rabi, har bacci tayi ta tashi wai karfe sha daya, kawai daga karshe ta mike ta fita daga dakin Hajja ta tafi part din Ummi... Ummi ta ajiye littafin hannunta tana kallonta tace "Ya aka yi Jiddah?" Kunya taji ya rufeta, Ummi tace "Ko har kin shirya?" Tayi karfin halin cewa "Ehh Ummi ina son xanje inyi girki ne" Ummi tace "Eh gaskiya kam, bari in kira driver din, shiga ki dauko jakarki to" Kanta a kasa ta shiga dakin Ummi ta dau jakarta ta fito dama da Hijab dinta a jikinta, bayan Ummi ta kira driver ta mike ta tafi daki ta dauko mata makullin gidan nasu, tana mika mata tace "ki je ki ma Hajja sallama kice mata xaki gidan Umma ne" Jiddah tace "Toh" Ummi tace "Idan kin mata sallaman ki samu driver din yana waje" Jiddah tace "Ummi ina son in siya wasu abu a kasuwa ne..." Ummi tace "Kina da kudi wajen ki ne?" Girgixa mata kai tayi, Ummi tace "Toh bari in baki Atm card, idan ya dawo sai ya maido min da card din nawa" Atm card din ta dauko ta mika ma Jiddah ta gaya mata pin din tana kara nanata mata kar ta manta, Jiddah ta risina ta amsa tayi mata godiya ta fita, kallonta Hajja ta dinga yi sai kuma tace "Me ake yi a gidan Umman?" Jiddah tace "Kawai xan je ne" Hajja tace "Toh sai mijin naki ya dawo xamu koma can gidan kin dai ji abinda nace ma dangin ubanki kar su daukeni makaryaciya idan basu gan ni ba" Jiddah tace "Ehh sai ya dawo" Hajja tace "Toh ki gaida Ramlan" Jiddah ta juya ta fita, sai da driver ya fara ajiyeta kasuwa ta siya ingredients din fried rice da zobo drink, tunda suna da nama a deep freezer bata siyi komai ba banda liver, daga nan driver ya ajiyeta gida tayi masa godiya ta shiga ciki bayan ta gaida mai gadi. Tana shiga cikin gidan ta kai kayan girkin kitchen ta tafi sama ta canxa kaya xuwa kanana sannan ta fara gyaran gidan, ta tsaftace ko ina tayi mopping da goge goge ta kunna turare a burner, sai da tayi azahar sannan ta shiga kitchen.... Kafin la'asar ta gama hada lafiyayyen fried rice dinta with zobo drink, ta soya kajin tayi pepper chicken da shi, sai farfesun offals da tayi kadan, duk ta jera abincin a dinning, ta koma ta tsaftace kitchen din kamar bata yi komai a ciki ba ya dawo fes fes, sama ta wuce dakinta ta shiga wanka, da alwalanta ta fito sai da tayi salla snn ta fiddo da kayan da xata sa, ta dau kusan minti talatin tana shirya, ta saka wasu ubansun English wears masu daukan hankali, ko ina na jikinta wani sanyayyan kamshi ne ke tashi, tayi packing gashinta da ribbon leaving it that way, she look just like a princess, tayi kyau sosai, bude gate taji anyi ta karasa window tana kallon waje yaga Abuturrab ne ya shigo da motarsa... Sauka tayi downstairs ta tafi bakin kofa ta tsaya, she is just so happy, ta labe a gefe daya har ya bude kofar, wani kara tayi da nufin basa tsoro, ya jawota jikinsa yana kallonta daga sama har kasa yana murmushi, 6ata fuska tayi yayi kasa da murya yace "Jirgi bai bani tsoro ba sai matata?" Dariya tayi ta boye fuskarta jikinsa a hankali tace "Welcome my Man" Ya lumshe ido ya bude yana shafa bayanta yana kare ma dressing dinta kallo yace "U look sexy in this wife..." Sai kuma ya kankameta yace "Wllh i have missed u so much wife, Hajja bata kyauta min" amsar jakan hannunsa tayi tana murmushi tace "I missed u more dear... Abinci ko wanka?" Ya girgixa kai yace "Sallah" Tace "Toh mu je" Sai da yayi sallah sannan yayi wanka bayan ta hada masa ruwan wankan a bedroom dinsa, kafin ya fito ta ciro masa kayan da xai sa, sannan ta sauka downstairs ta dauko girkin da tayi xuwa parlonsa, xata shiga bedroom bayan ta gama hayowa da abincin suka kusa cin karo, sai taga ko kayan da ta ciro masa ma bai sa ba sai short, daukanta yayi kamar baby xuwa bed din dakin, ta marairaice masa tace "Dear ga fa abinci can..." Bai bata daman ta karasa ba, ya dinga ce mata yayi missing dinta so much, kamar yanda ya tara mata gajiya ita ma dai hakan tayi masa, bai ta6a tunanin da akwai sanda jiddah xata sake haka da shi ba balle har ta maida masa martani.... Sai bayan ya dawo magrib ta xuba masa abincin da ta girka masa, yana kallonta ta gefen ido yace "Ke dai fadi gaskiya Baby wannan abincin daga gidan Ummi kika taho da shi ko?" Murmushi tayi tace "Ae wannan ma da na ta6a xuba ma Colleagues dinka da dadewa ka kusa cinyewa baka sani ba... Shi ma ai daga gidan Ummi...." jawota yayi jikinsa ya matseta ya buda idonsa yace "Ni xa ki ma sharri?" Dariya tayi tace "Kai ka fara min sharri ai" ya lumshe ido yana murmushi yana shafa dogon gashinta yace "U are really a good cook wife, i know i am blessed... tun daga wannan ranan da kika xuba ma Colleagues dina abinci na dandana na san haka, i was stunned after tasting ur food that day, how possible i thought to my self many times" Tana murmushi tace "Saboda i am too local then ko?" Ya dago kanta yace "Daga sanda na raba ki da hayi kika bar locality dinki a can, u left that locality behind... Ban ta6a tunanin xaki fahimci abubuwa ki koyi abubuwa lkci daya ba jiddah, u were a fast learner... A iya xamanmu na farko I can't say ko na ta6a maki wani correction kan abubuwan da na koya maki" Ita dai murmushi kawai take, yayi kasa da murya yace "Tun daga sannan kika fara burgeni, when i notice u were always clean" Ta d'an saci kallonsa tace "Ashe ina burgeka" He couldn't help it but laugh, sai kuma ya rike kansa yace "Sosai Jiddah, in dai na barki a gida na tafi aiki bani da sukuni up in the sky sai na dawo gidan nan, i hate seeing u sad or worried hakan na karyar min da xuciya..." Ta kwantar da kanta kan shoulder dinsa tace "Kawai dai so na ne baka yi a lkcn ko??" Jin yayi shiru ta daga kai ta kallesa, kallonta taga yana yi babu ko kiftawa, sai kuma ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace "Na kan yi sha'awanki a lkcn" Ta d'an buda ido tana kallonsa tace "Wani iri" Ya lumshe ido yana shafa laps dinta yace "Irin wannan but i always try hard to fight it away, i always put in the back of my mind that i am just ur guardian" ita dai Murmushi kawai take, ganin ya ki daina abinda ya ke mata a kafa ta turo baki tana kallonsa, tuni taga idanuwansa suka canxa, ta marairaice tace "Ni wllh na gaji ko abincin fa ban ci ba..." Wannan fried rice din dai sai wajen karfe sha daya na dare


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login