Showing 3001 words to 6000 words out of 19716 words

Chapter 2 - ƘURARREN LOKACI (COMPLETE) BY K_SHITU

Unknown   

28 Jun 2024

3240

roba ta ce na samu na kimtsa na bawa yarona ya sha shi ma.

Sai na ce mata ina son yin sallah, ta buɗe mini ɗakin hanyar kicin ɗinta ta aje min abincin ta juya ta fice.
Sosai ya bani tausayi na san yayi haƙuri dan haka na kurɓi ruwa kawai na saka masa nono a baki a runtsa ido, Ya fara ja cikin jin yunwa duk da ba ruwa amma bai saki ba. Na ji ƙwallah ta cika idona ina jin zafi sosai amma na daure zan iya jurewa saboda Imraan ɗina. Cikin ikon ubangiji ruwa ya fara zuwa, Na yi mamaki sosai, sai dai bani da wani sani ya sa na yi shiru na san wani taimako ne na ubangiji. Na dinga cin abinci yana shan nono har ya ƙoshi sannan na bashi ruwa. Na kwantar dashi saman sallaya.

Na yi Alwallah da sallah. Na zauna ina addu'o'i sosai da tausayin kaina da ɗana. A haka ta shigo ta same ni muka sake gaisawa na dinga mata godiya ta ce, “Hala dai baki san kowa a garin nan ba?” Na gyaɗa mata kai na ce, “Yar'uwar tagwaicina ce ta rasu, Inda nake kuma akwai matsala iyayenmu sun daɗe da rasuwa shi sa na taho nan ɗin”

“Allah ya gafarta musu. To amma so kike ki zauna nan dindindin?”
“To gaskiya sai kin tashi tsaye kin nemi na kanki ko ki nemi aiki”
“Dan Allah ki taimake ni idan kin ji wasu na buƙatar mai aiki zan iya in sha Allah” Ta amsa mini sannan ta fice daga ɗakin.

Da dare na ga karamci ƙwarai ta kawo mini kunun tsamiya da Shinkafa miyar taushe da ta ji tsoka zaƙo-zaƙo sai Pampas. Na yi godiya Na ci na ƙoshi ɗana ma haka, ina gode muka kwanta barci.

K_shitu Multimedia.
09117440993.

(Ku yi haƙuri masu ƙorafi, haka salon labarin ya xo🫣)

*WaTtPaD@KSHITU*
Vote, Comment nd Follow Please..


*ƘURARREN LOKACI*

(5).
Idan ubangiji ya nufa sai abubuwa su yi ta faruwa tamkar almara. Bayan na cire rai da sake jin daɗi ko kwanciyar hankali Allah ya chanja mini al'amarin.

Tabbas har in koma ga mahaliccina ba zan mance da halaccin Maman Afrah da Mijinta ba.

Ni ce cikin inuwa zaune ba tare da Imaan ba. Hawaye suka wanke mini fuska na kasa riƙe kukana na dinga raira shi a hankali ina shessheka.

Abubuwa masu muni waɗannan da suka shuɗe cikin rayuwarmu da ƙaddarorin da suka kutso kai cikin Ƙurarren Lokaci suka dinga dawo mini cikin ƙwaƙwalwata tamkar a lokacin ne komai ke faruwa..

*
Aliyu Aliyu Shi ne sunan Mahaifinmu wanda ya haife mu. Kaf Unguwar da muka zauna babu wanda bai san Mahaifinmu ba Gogagge ne a harkar Caca ba shi da wata sana'a da ta wuce ta, Mahaifiyarmu Khadija ta rasu bayan ta haife mu 'yan tagwaye da mu. Abbahnmu yana tsananin Ƙaunar Mahaifiyarmu wannan ne dalilin da ya sanya bayan rasuwarta ya mayar ma tagwayen da ta Haifa masa sunanta wanda mutane suka dinga mamaki. Khadija Imaan, Khadija Ilhaam su ne Yaran da aka haifa masa.

Ba za a ce Zuciyarshi ta mutu murus ba domin bai ragi 'ya'yansa da komai ba, bugu da ƙari Allah ya hore masa ilimin addini matuƙa; Sai dai talauci ne ya sauya masa halaye, Ƙwaro ne a harkar saide-saiden Miyagun ƙwayoyi da ƙananun laifuka.

Wannan ita ce sana'arsa da kowa ya masa farin sani da ita. Yana kuma shan wahala matuƙa wajen jami'an tsaro, Da yake abokan harƙallansa manya ne idan aka kama shi baya daɗewa.

Mu dai tun da muka taso da Abbahnmu mun san Mahaifiyarmu ta rasu sai Ƙanwarshi Hindatu wacce Muke kira da Ummah.

Kaf layinmu ba uban da ya isa taka mu, Muna makaranta mai tsada islamiya ma haka. Bakin gwargwado muna shanawa domin Mahaifinmu na tsananin sonmu.
Khadija Imaan Tana da kyau sosai dangin Mamarmu ta ɗauko 'yan Sumaila.

Fulani ne masu kyau da gashi, Sai dai Abbahnmu sam bai taɓa yarda mu je ba ko su su gana da mu hakan ya sa suka haƙura da mu.

Imaan tana da sanyin hali da haƙuri sosai, Bata da matsala Tana da kyawawan halaye masu siye zuciya, Kalamanta tamkar zinare Ubangiji ya bata baiwar sarafa harshe tana da lafazi mai tasiri matuƙa. Burin Rayuwarmu Abbah, Ilhaam, Imaan.

Ilhaam Tana da sanyi da zafi bana ɗaukar wulaƙancin da Imaan xa ta ɗauka, Ina da kyawawan halaye Sai dai Zuciyata bata jurar cin mutuncin Imaan da Abbah.

Wata irin ƙauna muke wa juna da bamu san iyakarta ba, Allah ne ya dasa mana son junanmu, Burin Imaan a rayuwa Ilhaam, Burina A rayuwa komai Imaan duk da ƙarancin shekarunmu a lokacin bama jin daɗin ɗabi'un Abbah.

Zubinmu ɗaya kyawu ma haka sai daa Imaan ta fi ni Fari sosai dan shi ne ma abin da ya banbanta mu. Muna da farin jini kamar hauka saboda kyawu da kuma yanayinmu.

Sai da kowace cikinmu tayi hankali sannan muka fara fahimtar abubuwa da dama, Mun sani A duk duniya babu wani wanda yake tsananin sonmu da ƙaunarmu tsakani da Allah irin soyayyar nan mai narkar da zuciya irin Abbahnmu, Baya iya ɓoye sonmu gaban kowa.

Bashi da kyawun hali Amma yana da shi a wajenmu, Duk irin yanda yake bamu kulawa da lokacinsa duk da baya zama tare da mu ko yaushe amma bamu isa fahimtar komai na al'amuransa ba, komai nasa a sirrance yake gudanarwa.

Daga sanda muka fara fahimtar Lallai Ummah fuska biyu ce da ita Ƙaunar da muke yi mata ta ragu soaai.

Bamu gasgata hakan ba sai da rayuwa ta ci gaba, Muka samu wayewa da kaifin ƙwaƙwalwa.

Ta kowane ɓangare bama da wata matsala sai wadda baa rasawa, duk wani mai son kawo mana cikas to ya san Abbahnmu ya dame shi da tashanci ya shanye shi sa muke samun sauƙin mutanen banza.

Bamu cika shiga harkan kowa ba Muna rayuwa ne a wadace. Cikin jin daɗi.

*
Bamu taɓa zaton samun wata matsala daga gurin kowa ba sai da Muka wayi gari Babu Abbahnmu.

*
Rayuwar maraici akwai wahala sosai. Duk da mahaifinmu bai mutu ba Amma rayuwar da muke Bamu da maraba da marayu, Marayun ma waɗanda basu da wani gata sai Allah.

Ashe Ubanmu shi ne Katangarmu kuma Inuwa da garkuwar rayuwarmu. Sai da Aka kama shi aka bar ƙasar da shi ne muka Gane hakan.

Rana tsaka aka ce mana Hukuma ta damƙe shi, Faɗar irin tashin hankali da Masifar da muka shiga ba abu ne mai yuwa ba sai Wanda ya ɗanɗani Ƙuncin da muka ɗanɗana ne kawai zai san hakan.

Duk wata ƙaddararsa Ummah ta siyar da zabban gwala-gwalai da ya siya mana ta saida, Kuɗaɗensa ta harharɗa mu dai bamu sani ba Ba zai dawo bane shisa ta yi hakan Amma mun gigita da Muka gane Munanan Halayenta.

Sa'adda muka yi wata biyu babu Abbah babu labarinsa Ta cire mu daga kowace makaranta, dama ba wasu maƙudan kuɗaɗe ne da shi ba amma ya tara dukiya wadatacciya duk ta handame ta, Ta mayar da gidanmu dandalin 'yan isa da karuwai.

Rayuwa tayi mana zafi irin wanda gwara ƙuna da shi, Sau ɗaya take bamu abinci.

Mun fara samun barazana ta kowane ɓangare daga maza da matan da ke sintiri cikin ƙaramin gidan namu, Kowane mara imani babban burinsa ya lalata mana rayuwa amma Allah na tsare mu.

Wata irin ƙiyayya take mana da bamu san dalilinta ba, Takalminta ya fimu daraja da soyuwa a wajenta.

Cin mutunci da tozarci babu irin wanda bama gani tsoro da barazana sun hana mu tunkarar kowa da batun neman Mahaifinmu tun bayan da muka gane Yanda kowa muka raɓa ke son Tozarta rayuwarmu.

Shi yasa Ake so Ɗan'adam ya shuka Alkhairi babu mai tausayinmu kowa aibanta mu yake da Abbahnmu ta dalilin azabar son duniyarsa bamu da ikon tankawa. Tun daga ranar da aka kama shi har muka yi wata shida ko kare bai kula mu ba bare a tunkare mu da maganar Abbahn.
Tsarewar Allah ce kawai ke bibiyarmu bayan haka da Rayuwarmu ta yi Lalacewa mai Muni. Kyawun Halitta da tsarin kyawu na matuƙar jan hankalin sheɗanun Maza gare mu da maganar banza iri-iri. Amma bama kulawa sam, muna suturta jikinmu da zuciyoyinmu Duk tsanani bama neman komai daga kowa.

Sai da Ƙawayen Ummah su biyu suka dawo Gidan da zama ne matsi da tsanani ya ƙaru ta ko'ina ba sauƙi bala'i da masifarsu kamar ya kashe mu.

Wani mataccen ɗaki da Abbah ke ajiyar tarkace muka koma.

Duk tsanani da masifa bamu ɗaga kai mu yi ko tari. Duk da kuwa abin na cin zuciyata. Amman mukan yi kuka sosai mu ce ashe haka duniya take Mene laifinmu a rayuwa da muka chanchanci uƙuba da ƙiyayya haka.

Muna Addu'a mu kai wa Ubangiji kokenmu.

..Rana mafi muni A rayuwarmu Da ta zo mana a ƘURARREN LOKACI wacce har zuciyata ta tsaya da bugawa numfashina ya bar gangar jikina na Bar Duniya ba zan manta da ita ba.

*
Safiyar wata Laraba Ummah ta yi tafiya daga mu sai Anti Zulai a gidan Imaan ta tashi da matsanancin Ciwon kai da zazzaɓi sakamakon ruwan sama da aka tsula ya ƙare kanta dalilin aikenta da Aka yi.

Tana ta kyarma jikinta yay zafi sosai ko yatsarta bata iya ɗagawa, Hankalina ya tashi rauninmu ya bayyana, na dinga kuka babu ko tsinke da zamu ci ban san yaya zan yi da ita ba.

Na kai ɗakin Anti Zulai da suke tare da baƙonta ina kuka na ce ta taimake mu Imaan zata mutu numfashinta har fizga yake. Ta wanke mun fuska da mari ta hankaɗo ni tare da zagika masu muni.

Na dinga kuka ina roƙonta, Amma basu saurare ni ba. Na fice cikin gaggawa ina zagawa cikin layi kowa na tunkara sai wulaƙanci.

Har dare yay ban samu wanda ya dube mu da niyyan taimako, Hawayena sun ƙafe zuciyata na wata irin tafasa da ƙuna jikina na karkarwa. Na dawo gidan na tarar ba kowa sa ita ta yi suma yafi sau nawa. Ina shirin sake fita Sai ga wani mutum da ban iya ganin fuskarsa ba cikin duhu.

Ya ce Zai taimake ni ya ɗauki nauyin komai namu ya bamu kulawa amma da wani sharaɗi guda zan amince masa mu yi zina. Na ji a raina lokacin ƙwaƙwakwata ta daskare ban ga amfanin wulaƙanci da tozarcin da muke ciki ba zan iya sadaukar da abin da ya fi rayuwata in dai akan Khadija Imaan ne.

Na amince masa kai-tsaye, Ya bani Wata kwalba ya na shanye abin da ke ciki.

Na kwankwaɗe, Daga nan ya jani ɗakin mu, Kaina ya dinga juyawa idanuwana na rurrufewa, Ya tuɓe cikin rashin imani ya fara ƙoƙarin lalata min rayuwa.

Zuwa lokacin hankalima baya jikina komai yake mini bana iya ko motsi, Sai da muka ɗau tsawon lokaci haka bai kai ga cinma nufinsa ba.

Kamar a cikin mafarki na dinga jin Muryarta, Tasirin Muryata a jinina da numfashina yake haka muryata a gare ta.

Allah da ikonsa ya bata dama ta ɗauki kwanon sibla ta rafka masa a kai. Ya saki ƙara tare da murginawa yana dafe kai, Ta dinga buga masa kwanon.

Ranshi ya ɓaci daga nan ya fara kai mata tagwayen maruka, ya rufe ta da duka, Lokacin ban san inda kaina yake ba, Daga Ƙarshe ya keta mata haddi ya lalata mata Rayuwa yay mata Fyaɗe.

Washe gari da na dawo duniyata, Idan na ce zan Fasalta ko yin bayanin yanayin da na shiga Wallahil Azim na yi ƙarya.

Bugun zuciyata ya dinga fita da wani irin sauuti har cikin ƙwaƙwalwata, Gani nake kamar babu rai tattare da ita, Ƙwaƙwalwata ta yi wani irin hooking na wucin gadi..
Wannan shi ne mafarin komai na Ƙaddarori da jarabta.
09117440993.
Free book
K_SHITU MULTIMEDI.

Share Pls🌝

*ƘURARREN LOKACI*

(6).
Babu kowa a gidan, dan haka na nutsu na fara suturta mu Sannan na ɗauki damin kuɗaɗen dake yashe ƙasa na saka a jaka na fita daga gidan cikin sauri kamar zan kifa. Ƙirjina na duka, da taimakon mai adaidaita muka kai ta asibiti.

Ganin irin uban jinin da take zubarwa ne ya sake raunana mun zuciya. Mun isa asibiti sai dai bamu shiga kai-tsaye ba mai adaidaitan ya nema mana wani likita da ya sani ya fito muka masa bayanin abin da ke tafe da mu. Sam ya ƙi amincewa a cewarsa sai da jami'an tsaro da ƙyar ina kuka ya yarda aka tura ta ofishinsa.

A sirrance ya duba ta a ofishin ni dai ina zaune daga farko ya shige chan ciki ina ta kuka kamar raina zai fita ƙirjina na wani irin zafi.

Na ji na tsani komai da rayuwata tamkar na kashe kaina saboda ba zan iya jurar ganin ta cikin Mummunan yanayi ba. Ya daɗe ciki sannan ya fito yana share gumi tare da cire safan hannu ya kalle cikin wani yanayi yana jefo mini tambaya.

“Ina iyayenku?”
Sai da na ji ƙirjina ya yi duka mai sauti na daure cikin shaƙaƙƙiyar muryata da ta gama sanyi na bashi amsa.
“Mahaifiyarmu ta rasu Abbahnmu kuma ya ɓata”
Cikin mamaki da jimami ya jinjinga kansa.
“Yar'uwarki ce ko?. Tana da aure ne garin ya haka ta faru gaskiya akwai matsala baku da wani ɗan'uwa na kusa ko dangi?”

Na haɗiye wani abu da ya tokare mini maƙoshi na ce, “Bamu da kowa daga ni sai ita” Na labarta masa abin da ya faru daga rashin lafiyar da ta same ta safiyar jiya zuwa yanzu, Daga ƙarshe ya tambayi ina Ummahr take na faɗi masa irin rayuwar da mu ke gidanta.

Ban tsammaci jin ƙai ko tausayi daga gare shi ba saboda yanda yake mini magana cikin kaushi da faɗa. Ashe ban mashi kyakkyawan zato ba. Idanuwanshi har ruwan hawaye suka tara ya dinga ƙarfafa ni da nuna tausayinsa.

Karon farko na samu damar fayyace ma wani Ɗan'adam damuwarmu da matsaloli ya fahimce ni ya saurari kukana ya ƙarfafa Mini gwiwa Wani irin sanyi na ratsa ni damuwata ta ragu.

Ya fice ya dawo hannunsa ɗauke da Ledoji ya bani abinci na ci, Muka shiga inda Imaan take tana ta barci ta yi haske sosai ya sanya mata ƙarin ruwa ya yi mata ɗinki hankalina ya kwanta sosai.

Sai dare ta farka tasha magunguna da ruwan shayi mai kauri da abinci zuciyata cike da fargabar irin kallon da zata yi mini.

Mun yi kuka tare sosai kamar numfashinmu zai tsaya daga ƙarshe muka gode wa Allah. Na kasa sakin jikina ta rungume ni tana ƙarfafa ni har abada ta sani ko dabbar Imaan Ilhaam ba za ta iya yi ma kallon wulaƙanci ba balle cutarwa, Imaan tana yi wa Ilhaam ƙaunar da bata ganin laifinta kuma ba za ta bari wani abu ya cutar da ita ba, Zata sadaukar mata da rayuwarta.

Dr Jabir ya tausaya mana sosai ya bamu kulawa irin wacce ta sanya mu kuka. Ya nuna mana halaccin da har abada ba zamu manta da shi ba. Ko ƙwandala bai taɓa amsa daga gare mu ba komai ya mana yana faɗi don Allah ya yi.

Abin da ya kwantar mini da hankali dawowarmu Cikin Asibitin ɗakin jiyya. Sai da muka yi sati biyu kana aka sallame mu, Ya bani waya ƙarama da layi a ciki da kuma alƙawarin taimakonmu.

Bata sanya ma ranta damuwa ba saboda ni, Dan haka nima Na kiyaye sa damuwar da zata ɓata ranta.

*
Faruwar Al'amarin da Kwana Ashirin da biyu mun dawo gida sai dai har sannan Ummah bata dawo ba, mun ci gaba da rayuwa da daɗi ba daɗi don kullum cikin ciwo Imaan ɗin take.

Ashe wani mummunan tashin hankalin mai daskarewa a ƙwaƙwalwa da ruhi na tafe cikin Ƙurarren Lokaci.

Ciki ya bayyana lokaci guda tare da cuta Mai karya garkuwar jiki. (Hiv/Aids. Human immune deficiency Virus. Acquired Immune deficiency Syndrome).

Wallahil Azim ita take ciwon Amma na fita gigicewa da zarewa tamkar na samu matsalar ƙwaƙwalwa haka na koma ta yi wani iri Alamomin sun bayyana jikinta.

A wannan lokacin ubangiji ne ya tsaya mana Dacta Jabir ne ya tsaya mana. Shi ya kwantar mana da hankali ya hana mu ɗaukar abun wani shahararren lamari ya nuna mana haɗarin sanya damuwa ya ɗaura mu bisa magunguna.

Duk da haka sai muka amshi ƙaddara hannu bibiyu. Amma me Tozarcin mutane da cin mutunci ya hanamu shaƙar iskar duniya da kyau, Ƙyamata da aibantawa iri-iri da wulaƙanci haɗi da mummunar ƙiyayya. Zuciyoyinmu ba duwatsu ba ne, Ta fini ƙarfin zuciya tana dakewa ta shanye Kowane irin Tozarci da ƙasƙanci. Amma ni zuciyata ba za ta iya ɗauka kan Imaan ba.

Ba zan manta ba wani lokaci da Ummah ta gaggaura ma Imaan mari wanda ya kaita ga ciwo ya rife ta mai tsanani. na fusata na kasa riƙe fushina jikina har jijjiga yake na kai mata maruka huɗu hagu da dama tare da maganganu masu ƙona rai.

Na yaɓa mata magana da zagika.
“Ban yi tunanin butulcinki da rashin imanin naki ya kai haka ba sai yau tana cikin mummunan yanayi, Kin tona mana asiri kin fallasa ma duniya halin da muke ciki bai ishe ki ba, Kina tozarta mu bai ishe ki ba kina zagin mahaifiyarmu da yi mana ƙazafi kala-kala duk basu ishe ki ba sai kin haɗa da duka saboda Daƙiƙanci da mutuwar zuciya, Mene laifinmu da muka chancanci baƙar tsana da ƙiyayya haka daga gare ki, Mi yasa kike zaluntar rayuwarmu, Ba mu miki laifin komai ba, Da yardar Allah sai kin yi mutuwar wulaƙanta sai kin tozarta tun gidan duniya Ya Allah ya Wul..,” Ban ƙarasa ba matan gidan da ita suka rufe ni da duka.

Zagika suka dinga jifanmu da su da munanan kalamai da goranta mana akan Son kuɗi irin na ubanmu da kwaɗayi ya kai shi ga halaka gamu nan tsinannu.

Na yi tunanin A halin da muke ciki zamu samu wani ya tausaya mana, Amma bamu samu ba sai tagomashin ƙiyayya.

Dr Jabir ne yay tsaye kan lamuranmu shi yake ciyar da mu, Dan tuni ta daina bamu tsinke nata, sai wahalar da mu da take.

Dr Ya sha tambaya ta ya kamata mu fito mu ƙwaci 'yancinmu mu nemi Mahaifinmu, Sai dai Imaan ta yi murmushi ni kuma na yi ta faɗa masa bama da wannan damar..

*
Haka muka ci gaba da Rayuwar Matsi kullum cikin raɗaɗin ɓacin rai, dan ma ko da yaushe tana yawaita nuna mini mu goda ma Allah.

Raina baya bani Imaan zata rayu amma ita a ko da yaushe ni ce burinta da fatanta a rayuwa tana burin na samu salamar rayuwa na ji daɗi, Ni kuma ita na fi tausayi fiye da komai a rayuwa.

Tana yawan faɗa mun jikinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login