Showing 6001 words to 9000 words out of 19716 words

Chapter 3 - ƘURARREN LOKACI (COMPLETE) BY K_SHITU

Unknown   

28 Jun 2024

3238

na bata ba zata yi tsayin rai ba, sai dai bana sa mata ran mutuwa kusa.

Hawan jini ya mata yawa sosai ga ƙananun shekaru dan Lokaci duka ba zamu wuce sha Takwas ba.


*
Numfashina ya dinga fizga sosai.
Ina tunawa Yanzu fa 'yar'uwata Imaan ta rasu sai Ni da Imraan...
09117440993.
K_SHITU MULTIMEDIA.

*ƘURARREN LOKACI*

(7).
Tabbas Akwai ƙalubale a gabana, Shi kenan 'yar'uwata ta mutu wahala ta gudo da ni daga Mahaifata na dawo wani garin, Mene Amfanin tsoro ya kamata na koyi juriya, Ina buƙatar tsayawa da ƙafafuna nima, Sai dai taya ban san kowa bani da wani gata sai Allah.

Na yi murmushi mai ciwo. Ina burin ko yaya ne rayuwata ta inganta, Ina son Taimakon Abbah ina son ilimi da hutun rayuwa ba dole sai Ƙyale-ƙyalen rayuwa ba A'a ina son yin salamammiyar rayuwa. Na samu ilmin duniya akan Rasuwar 'yar'uwata shi kenan yanzu da a ce ni ce na mutu ba abin da zai chanja na duniya.

Mafi tarin lokuta Ƙaddarori suna kutso kai cikin Rayuwa a Ƙurarren lokaci. Amma kana naka Ubangiji na Nashi.

Zan yi ƙoƙari ko yaya ne na tsaya da ƙafafuna, Ba zan bari zuciyata ta mutu ba, Allah ya bani lafiya da dama bani da wata nakasa..

*
Kwana Bakwai na yi gidan Maman Afrah mun zaga kasuwanni. Na ga ruwan karamcin da ya saka ni kuka, Mijinta ya sama mini aiki gidan Uban gidansa mai kuɗi sosai.

Yau mun je An nuna mini yanda tsarin aikin yake, Babban gida ne tanƙameme da ban taɓa shiga irin sa ba tun da na zo duniya aikina share-shre da girki.

An ɗauke ni aiki zan fara zuwa safiyar litinin chan zan dinga kwana. Na masu godiya har sai da na basu tausayi. Tana ta jana a jiki da koya mini wasu abubuwan da bana da wayewa kan su.

Sai dai na ce Alhamdulillahi. Imraan ma ya ɗan yi kumari da ni kaina haske na ya fito Kamannina da shi kamar na yi kaki na tofar.

*
Tun da garin Allah ya waye nake haɗa kayana da kimtsawa. Na gama komai tsaf Na gaishe da su suna ta tsokanata ina murmushi, Chan zan dinga kwana Suka mini nasihar riƙe gaskiya da kuma shagala da ƙyale-ƙyalen rayuwa na amsa idanuwana na tara ruwan hawaye, Tun da nake a duniya babu wanda ya taɓa mini nasiha bayan Abbah da Imaan.

Duk zumuɗin tafiyar sai na neme shi na rasa. Muka ɗauki hanya. Mun shiga ƙaton gidan bayan mun gama gaisawa da masu tsaron gate.

Babu ɓata lokaci ya bar ni na fara aikina kamar yanda aka nuna mini na yi shara da goge-goge na haura saman bene nan ma ɗakuna Biyu da ke da Falonsu sama na gyara.

Na duba Wata time table dake kitchen na girka Tuwon Shinkafa miyar ɗanyar kuɓewa da nama. Komai ina yi cikin taka tsan-tsan. Zuwa bayan la'asar na gama komai. Ina ta al'ajabin gidan komai akwai lallai mamallakin wannan daula Allah ya bashi aljannar duniya.

Na yi wanka a ɗakin da aka bani da Imraan. Sai na tsinci kaina da fashewa da kuka Zuciyata na raunata na kasa yin shiru, Ina tunanin 'Yar'uwata shi kenan, An shafe babinta..

Sai Bayan isha'i na ci Abinci Sannan Na fara jin jiniyar motoci na tuna da yanda aka sanar min ya dawo ke nan, Kawai na dinga jin faɗuwar gaba kaɗan-kaɗan. Dama a tsorace nake da duk girman gidan ni ɗaya a ciki. Sai waje masu gadi da Securities.

Cikin sanyin da na yi da tsoro na miƙe Imraan ya yi barci. Na shiga kicin na Ɗauki Kulolin daraja da na sa Abinci ciki na haura Ɗakin dake kallon ƙofar falo daga saman bene na tura ƙofar ƙamshi na min kutse cikin hanci na isa madaidaicin falon mai kyawun gaske.

Na jera kulolin bisa senta tebir da filattai.
Ina shirin fita ya turo ƙofar ya shigo.

Ban yi kuskuren kallon inda yake ba Na sunkuyar da kaina, Ya tako cikin natsuwa tsakiyar falon ya kai zaune bisa kujera yana dafe kai.

Cikin in'ina na ce, “Sannu ina yini” Ya kalli inda nake tsaye ya ce, “Zuba mun abinci” Na sunkuya tare da naɗe hijabina na ɗau bowl na zuba masa miyar dake ƙamshi, Na sanya tuwon a filet malmala biyu na miƙa masa gabansa.

Ya zaro ido sai kuma ya ɗauraye hannu ina ji yay bismillah ya fara ci, Kamar wasa ina zuƙunne ya cinye malmala ɗaya da rabi ya zare ido yana kallona.
“Wai taya na ci duk wannan tuwon?amma ya yi dad’i um”

Nay ɗan murmushi ban ce komai ba. Ya miƙe ya wuce yana cewa a bawa Securities da masu gadi nima in ci. Na amsa tare da tattare kayan.

Ina fita na sauke ajjiyar zuciya da alama zay yi sauƙin kai.

Kamar yanda ya ce hakan na yi, Na Basu nima na sake ci na yi Sallah na kwanta cike da gajiya don ba ƙaramin aiki ba ne.

Rayuwar duniya ba don hutu aka yi ta ba sai don ibada. Duk yanda mutum ke son jindaɗi sai ya yi haƙuri idan yana son rabauta a lahira gaɓɓaina sai kwankwatsa suke yi saboda fidimar da nasha. Amma Alhamdulillah na gode ma Allah.

Na yi addu'a na tofe jikina da ɗana na rufe idanuwana da son barci saidai tunanin Imaan da gizon da take mini ya hanani na dinga mata addu'o'i.

*
Kiran sallar asuba cikin kunnena dan haka ban ɓata lokaci ba na tashi na yi wanka da Imraan na kwantar da shi na hau aiki na gyara ko ina tsaf cikin ƙanƙanin lokaci, Na ɗaura girki na soya doya da ƙwai na haɗa na bawa masu gadi nasu na ɗauki na Mutumin na haura sama kai mashi.

Yanda na tarar da shi sai da gabana ya faɗi na daure na gaishe da shi na ajjiye Abincin jikina na karkarwa na fice.

Na gode ma Allah da bai tsaida ni ba.

Idanuwanshi a rufe bashi da jikin girma duka-duka bai wuce shekaru Talatin da biyu ba. Ya farfasa ƙaramin madubin da ke hanyar ƙaramin fanfon dabnake wanke hannu a falon hannunsa na fitar da jini.

A raina na ayyana; Ko dai bai da lafiya, Sai kuma na share zancen.

Da rana ban huta ba, Na ɗaura girkin Shinkafa da miya na gama komai tsaf cikin kiyayewa sai dai Abincin sam bai yi daɗi ba shinkafar ta chaɓe na sha wuya dan ban saba girki da gas ba dan ma Maman Afrah ta nuna mini da ban san ya zan yi.

Cike da fargaba na doshi falon riƙe da kuloli da filattai. Na jera gabanshi, Sai dai har lokacin yana inda yake zaune idonshi rufe ba alamar ya tashi.

Na ji wani irin kamar kada na masa magana sai na samu kaina da son tanka masa. Na ce a hankali. “Sannu da hutawa!” Na ji shiru. Na sake maimaita masa.

Wata irin ɗagowa yay har sai da na tsorata muka haɗa ido da shi, Idanuwansa sun rine sun yi ja sosai ya ƙure ni da ido hantar cikina har kaɗawa take cikina yay ƙara domin ya mini kwarjini wani iri nake ji.

Na ja baya ina shirin barin ɗakin da sarƙewar ƙafa.
Ya daka mini wata irin gigitaciyyan tsawa sai da na ji duniyar ta juya min.

Ban ankara ba na ji wata irin shaƙa, Ya buga mini kai da bango na fasa ƙara ina sulalewa ƙasa, Yana shirin damƙo ni na yi wata zabura na falla da gudu. Na faɗo ɗaki ina haki kamar zan shiɗe na datse ƙofa jikina na kyarma kaina na sarawa.

Na ƙarasa bisa gado inda Imraan yake yana mutsu-mutsu na rungume shi sosai ina fashewa da kuka.

Meke shirin faruwa, wace ƙaddarar ce kuma ta tullo ni Gidansa Ya Allah ka tsaya mini ni Khadija Ilhaam da ɗana..
09117440993
K_SHITU MULTIMEDIA.

*ƘURARREN LOKACI*

(8).
Har safiya ban fito ba iyakata cikin ɗaki tsoro ya gama lulluɓe ni da tunane-tunane. Ina son fitowa kuma ina jin tsoron abin da zan gani.

Ina tsaka da wannan tunanin na ji bugun ƙofa har sai da na razana na ƙarasa cikin ƙasa da murya na tambayi waye muryar direba da na ji ce ta sani buɗewa ina kallon sa.

“Kina lafiya, Ya aka yi baki sanar da mu Yallaɓai na cikin wani hali ba, Da ya illata kansa fa ya kamata ki dinga faɗa mana duk halin da yake ciki” Nayi shiru ina auna maganganunsa da hankali.

Ki girka abincin da za a kai masa Asibiti ya faɗa yana juyawa ya bar ni nan tsaye.
Jiki a sanyaye na shiga Kicin na fara aikin dafa farfesun kaji. Ina ta tunani to shi ina iyayensa amma zuciyata na kwaɓata kar na zaƙe ni miye nawa.

Na gama na sanya a kula Direba ya karɓa a cewarsa zai kai asibitin da yake na ce Allah ya bada lafiya ina tunanin abubuwa da dama.

*
Kwana na Huɗu gidan babu ɗuriyar Maman Afrah ko mijinta na sawa raina haƙuri da tsumayen zuwansu. Mutumin kuma bai dawo ba. A lokacin na fara tunanin ko dai matsalar ƙwaƙwalwa ce da shi sai dai na kan kauda zancen.

Na fara gane lallai babu wanda zaka ce ba zaka iya rayuwa babu shi, Shi kenan rayuwata da Imaan ta zama tarihi sai dai ba zata taɓa mantuwa cikin zuciyata da ƙwaƙwalwata da ruhina ba haka ƙaunarmu.

Amma yanzu babu ita ban fasa komai na rayuwata ba sai dai damuwa Lallai duniya ba tabbs.

Ban samun wata matsala sosai Ɗana yana ɗan wayau da gane ni, Yana murmushi kullum sai na masa addu'a da karatu.

Rayuwa ta ɗan ci gaba babu laifi, Yau kwanakina Ashirin cif a gidan. Ashe mutumin da nake yiwa Aiki Taɓin hankali ne da shi, Lafiya lau yake komai sai dai idan abin ya motsa masa ya bani tausayi sosai, Wajen direba na samu labarin.

Ina kiyaye duk wani abu da zai haɗa mu ina komai tsakani da Allah da iya gaskiyata.

Maman Afrah ta zo sau biyu ta nuna mini abubuwa sosai kuma Alhamdulilah na ƙara gogewa wajen girki. Kullum ina yiwa 'yar'uwata Addu'a Allah yasa mutuwa ta zamo hutu a gare ta, ta huta da ƙuncin Rayuwa.

Kwanci tashi babu wuya a wajen ubangiji Rayuwa na ta garawa Hankalina ya kwanta bani da wata matala na karɓi albashina dubu hamsin ranan na yi kuka na bawa maman Afrah da mijnta dubu talatin Na yi sayayyar dubu goma ta sutura da ɗana da Alƙur'ani.

Sun ji daɗin girmamawar da na musu don rantsewa na yi sai sun karɓa.

Ɗana ya yi wayau yana rarrafe ya gane ni sosai Mutumin da nake ma Aiki Alhaji Umar farouku yana ɗaukarsa yana matuƙar ƙaunar yaron idan lafiyarsa ƙalau wajensa yake wuni.

Mun ɗan yi sabo da shi Na faɗa masa Mamata ta rasu Abbah kuma ya ɓata daga nan kuma 'yar'uwar tagwaicina ta rasu shi ne na dawo Kaduna. Ya yi Alƙawarin taimakona ni ma ɗin na yi fatan haka.

Ya tamabayen miye burina na ce karatu daga nan bai sake bin ta kan Lamarina ba Na daina ganinsa sam.

Direba ya kawo mani ƙaramar jaka ya ce inji shi. Waya ce a ciki sai ATM ɗinsa da Pin ashe ciwonsa ne ya tashi yana wajen mahaifiyarsa.

Na karɓa cike da farinciki Ina tsaka da murna cikin kwanakin Mahaifiyarsa ta diro gidan na sha Zagika da cin mutunci Ashe ba musulma ba ce Babanshi ne musulmi kuma ya daɗe da rasuwa.

A taƙaice ranar na bar gidan ina kuka da ɗana Allah ya taimake ni na ɗauki wayar da ya bani da atm daga su ko tsinke ban ɗauka ba.

Na wuce gidan Maman Afrah suka amshe ni hannu biyu. Na yi ta godiya hankalin ya ɗan kwanta.
Sai washe gari ne yake faɗa mini maganar da ta kusa zauta ni saboda murna, Farouk ya biya mini Kuɗin makarantar da zan fara Germany tare da 'yar'uwarshi Rufaida A wata makaranta.

Na ji daɗi sosai ina ta musu godiya.
Ranar na shaida Allah na sona da Rahama yana ta chanja mini al'amura zuwa alkhairi.

Saura sati biyu tafiyata Muka samu saɓani da Aunty Fa'iza wanda ya tsaya mini a rai..
09117440993.
K_SHITU MULTIMEDIA.
*ƘURARREN LOKACI*

(9).
Masu iya magana sun yi gaskiya; Zuciya bata da ƙashi.
Tsautsayi ya kawo Mijinta ɗakin da nake yana roƙona na so shi shi zai iya aure na. Na dinga roƙon shi ya yi haƙuri ba zan iya yin haka ba, Daidai lokacin da yake sake mini magiya da faɗin shi har rabuwa da ita zai iya ta faɗo ɗakin. Zagi ta uwa da uba nasha da jifa na da munanan kalamai Azzaluma butulu na yi ƙoƙarin fahimtar da ita amma kishi ya rufe mata ido.

Ni ma da zuciya a ƙirjina Na kasa jurewa ina ta ƙoƙarin ganar da ita amma ta rufe ido tana surfa min zagi saboda tsabar kishi tun ina shiru ganin abun nata ba mai ƙarewa bane tana ta aibanta ni da gorika na fusata.

Na ci gaba da mayar mata da murtani munafukin yay tsit har ta kaimu ga doke-doke bai tanka ba ta nuno ni da yatsa tana zagina nima na zage ta tas ina huci. Nan take na ɗauki jakata.

Na fito tsakar gida na ɗau ɗana na haɗo da wata ƙaramar jaka da 'yan kuɗaɗena ke ciki na fita.

Zuciyata na zafi na kai babban Titi duk da ban san inda zan dosa ba amma na ji a raina na gama tako gidanta har abada. Ban wani jima tsaye ba ya biyo ni daga baya ya dinga bani haƙuri kai-tsaye ban masa wani kwana-kwana ba na ce ba zan iya komawa gidansa ba ya janyo mini bala'i yanzu kawai zan tafi mun haɗe kawai har lokacin tafiyan mu.

Ban san ina zani ba na dinga addu'a ina tafiya har na miƙa sosai.

*
Na yarda da Farouku sosai da sosai, Allah jeho mini shi duk da baya cikin yanayi mai kyau amma ya fahimce ni, na shiga motarsa Imraan na ta kuka ya wuce da ni wani gidansa da yake hutawa. Yana ta dafe kai shi yasa ban iya yin dogon zance da shi ba.

Tun da ya tafi ban sake ganin shi ba sai bayan kwana goma cir. Ban leƙa ko ƙofar gida ba na gode Allah da abinci da ruwa matsalata kaya kawai.

Ya same ni muka tattauna sosai na masa godiya.

A ranar ya mun siyayya sosai aka yi Fasifot na tafiya Tun da asuba zamu tafi Abuja gobe daga chan zamu wuce germany ɗin.

Hakan ta kasance tun da asubahi na gama shiryawa, Direba ya zo ya ɗauke mu da kaya da ni da Ɗana zuwa Abuja Ina ta addu'o'i da gode ma Allah.

*
Wani hani daga Allah baiwa ne, Ban taɓa tunani ko da a mafarki zan tsallake Sabon Layi ba. Yau ni ce ubangiji ya karrama haka a ƙasar da ubana bai taɓa zuwa ba bare uwata Allah ya jiƙan ta.

Na yi kuka kamar raina zai fita na godewa Allah Rufaida ƙanwarsa mai kirki da ita, Muna wani gida mai kamar kwatas mu huɗu ne a ciki Rufaida a ƙasa ni saman bene, sai wasu mata da mijin turawa su biyu.

Mun shiga da himukin kayan da ya sake danƙara mana kowace ta jera aka kawo mana abinci daga wani restaurant mu ka ci mu ka yi hani'an kowace ta yi wanka muka kwanta barcin gajiya.

09117440993.

*ƘURARREN LOKACI*

(10).
Babu abinda zan ce sai Alhamdulillah. A gaskiya duk tsanani yana tare da sauƙi a rayuwa. Kamar ba Ilhaam ɗin Imaan da su jiƙu da wahalar duniya da gwagwarmaya ba, har na yi 'yar ƙiba da Imraan ɗina.

Muna cikin Mako guda da zuwanmu ƙasar komai gwananin ban sha'awa ba hayaniya. Ga son Imraan da duk suke yi wai kamar ni na yi shi saboda bamu da banbanci sak ni ce sai dai nay murmushi.

Babu ruwan wani da wani Rufaida nada fara'a sosai ta kan shigo mu yi hira ni kum duk sanda na girka wani abu sai na sauka na kai mata.

Horo muka fara samu daga wasu Turawa Mss Lara da Mr Macheal. Suna koyar da mu turanci ne yanda zamu wasu darussa idan mun shiga babbar jami'a.

Burina ya ta'allaƙa ga son zama Lauya wacce zata kare haƙƙin Ɗan'adam Ina burin ba don komai ba sai don ci gaban ƙasata da jiharmu ta Dikko. Na sani abubuwa suna kwaɓewa sosai, Ana aikata ɓarna, Ina son tsayawa 'yan'uwana mata wajen ƙwato musu haƙƙinsu, Ina burin wayarwa da Maza da mata masu shaye-shaye kai.

Zan iya cewa Bani da wata matsala. Ina fahimtar duk abin da suke koya mana sosai.

*
Wata biyu da zuwanmu Mamar Rufaida da Farouku sun zo amma bamu haɗu ba, Ta kawo mini aimishon ɗin muka samu a wata jami'a zamu fara zuwa ɗaukar darusa.

Na kwana kuka da tunanin 'yar'uwata, mahaifina, mahaifiyata, Sai dai duk wata daƙiƙa da na kalli Imraan ina jin sanyi a raina da zuciyata.

Mun fara zuwa ɗaukar Darasi a babbar jami'ar da ke cike da mutane mabambanta daga ƙasashe daban-daban na duniya har ma da mazauna nijeriya kamata.

Na kama kaina ko yaushe da Rufaida ta kaimu makaranta zan sauka na kai Imraan Ɓangaren rainon yara da abincinsa da duk wani abun buƙata na wuce Ɓangarenmu ita ma ta wuce nasu sai kuma mun haɗu babban Canteen ko Mall sai kuma ƙarfe uku ta maida mu gida bamu yin yawo karatu muka sa gaba ba kama hannun yaro mun kuma rufawa kanmu asiri bama mu'amula da wasu mutanen banza. Sofia kaɗai nake magana sosai da ita kasancewarta 'yar nijeriya Barno ita ɗin ma ban saki jikina da ita ba Maza kuwa daga turawan har baƙaƙen fata na mini kutse dan Haskena da kyawun tsarin halitta da Allah ya mini ya fito sosai ina samum masu zo mini da bututuwa dan bana kulawa kuma na kama mutuncina ina kuma fahimtar komai da ake mana. Babu wanda zai ce Ilhaam ɗin Khadija Imaan ce da ta jiƙu da wahalhalun rayuwa Cikin ƙanƙanin lokaci Ubangiji mai kowa mai komai ya sauya al'amura.

Wato ita duniya cike take da tarin darusan Rayuwa. Ni da na tashi da burin ƙyale-ƙyale da rawar kai duk da bai yi yawa ba Imaan da Abbah suke mini Huɗuba ko da yaushe ni ce A ƙasar turawa da rufin asiri nake da damar yin komai nake so, Amma yanzu babu abin da ke burge ni duk wani ƙawa da shiriritar duniya basa kaina ina rayuwa salun akun ba tare da wani ya gargaɗe ni ba, Yaushe rabon da Wani ya yi mini faɗa ko ya dungure mini kai, Yaushe rabona da samun Runguma daga Imaan da addu'ar kariya.

_This is Life! i remember

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login