Showing 9001 words to 12000 words out of 19716 words
some of our memories she is always saying; ‘Ilhaam u re special gift from almighty Ya Rabbi murmushinki dariyarki da su ake fasalta Imaan Ke ce Imaan, Imaan na ƙaunar Ilhaam da ranta, You're my hope Allah ya tsare mini ke ya shirya ki, Yah Allah ya ƙaddara abubuwa su zo miki da sauƙi da ikonsa a kowane lokaci, dama ace zamu rayu tare har ƙarshen rayuwarmu sai dai Ubangiji da nashi ikon ƙaddara da nata tsarin, a kowane yanayi da lokaci duk tsanani ki tuna da ni kiyi mun addu'a always thank God say Alhamdulillah ala Kulli hal. Jikina da raina baya bani zan yi rayuwa mai tsawo Idan Allah yasa na rasu ki yi haƙuri i'll say it morethan one time ki yi haƙuri ki yi mun addu'a zaki yi farin ciki a rayuwa in sha Allah’_
Tana rungume ni ta shafa kaina like mother nd daughter. Sai mu yi kuka tare i don't know why she's always talking about Matuwa, rasuwa.
Idan bana da lafiya ta bani abinci a baki, Ta shafa kaina ta yi mini faɗa ta yi mini addu'a ta dungure ni ta cije ni idan na yi ba daidai ba ta ce da ni 'Yar farii.
Kuka ya kubce mun _Na yi ƙoƙarina na shanye abubuwa masu girma da tsanani akanta shisa take ƙaunata na sani ba zan iya haƙuri da wani abu ba irin haƙuri mai cin rai saboda wani ba, sai Imaan na yi ƙoƙarin danne zuciyata akanta Na nuna mata halacci marar mantuwa akan cutar da kowa ya ƙi mu muka fuskanci matsananciyar tsana da ƙyamata ban taɓa ƙyamatarta ba ko sau ɗaya ko yanayina ya sauya na muhimmanci da kulawar da nake bata ko da zan mutu zan abin da zata ji daɗi faɗi tashina da wahalata duk a kanta ne ta yi farinciki kar ta sanya damuwa a ranta Ƙaunarta a zuciyata Allah ne ya dasa ta, A wannan duniyar babu wanda nake kallo kuma nake yiwa Ƙauna mai sarƙewa da numfashi irin Imraan. I’ll make sured i take of him as she wished nd said 'abinda na haifa naki ne' zan tabbatar da hakan in sha Allah_
Ina yawan shiga tashin hankali idan na tuna da Abbah a kowace Rana yaya zai ji Rasuwarta da Silar hakan Fyaɗe cuta, haihuwa Mutuwa! Allah ya bashi ikon ɗaukar abun da sauƙi dan yana matuƙar sonmu. Shin ko yana da rai har yanzu? Allah ka tsare shi.
Na yi mata alƙawari da Ubangijina da Rayuwata sai na Tozarta ko waye ya yi mata haka ko da ƙarshen numfashin zai tsaya ta dalilin hakan, Sai na tabbata ya tsani duniyarsa kafin ya bar duniya a kanta da wahalar da tasha na ƙuduri aniyar Kisan azzalumin da ya Lalata mana rayuwa.
Ko ma mene Ai bamu chancanci haka ba, Ko waye dole ace ya san mu dama, ba a tausaya ma halin da muke ciki ba saboda matacciyar zuciya da rashin Imani a sake Illata rayuwarmu a ƙurarren lokaci da aka san bamu da gata sai Allah.
*
Ba don wani abu ba da na ce Allah yana son Imaan yana Amsar addu'o'inta ko dan tana sanya Yaƙinin Allah ya riga ya amsa. Bata taɓa addu'ar tsawon rai ba sai dai ni ta yi mini, Idan na matsa mu yi addu'a mu rayu tare cikin farin ciki ta dinga roƙon tsawon rai a gaba sai ta yi murmushi ta ce idan Akwai alkhairi a rayuwar Allah ya bata in babu Allah ya sa khulihin musulmai su cika da imani mutuwa ta zame musu hutu.
Yanzu abin da nake buri da fata inganta rayuwata da ilmi da Ɗana, daga bincike akan Abbah da azzalumin da ya bar mana baƙin tabo.
Na ɗauko Wani ɗan litafi na fara rubutu da manyan Harufa na rubuta HIV (Cutar ƙanjamau, Cutar Sida, Cutar mai karya garkuwar ɗan'adam). Ina son bincike kan cutar ina son samun sani sosai a kanta da dalilin da yasa mutane ke ƙyamar wanda ƙaddara ta yi ma cushen cutar.
Alama ta farko Mura da tsananin tari da yafi sati uku, Ciwon Wuya.
Bayan Zuwanmu Asibitinsu Dacta Jabir Yay gwajin da yayi mata kai-tsaye ya gano cutar sai dai bai rikita mu ba ya faɗa, ya yi ƙoƙarinsa wajen siya mana magunguna muka dawo gida.
Rashin natsuwa da wani irin mugun ƙaiƙayin jiki da Rashin cin abinci da ta dinga fama da su da Ciwon ƙafa da ƙuraje.
Abin ya zo da tsanani saboda rashin Tsaftattaccen muhalli da kulawa da wadatar abinci har numfashinta ya tsaya ba zata taɓa mance raɗaɗin da suka danƙara da ƙyamata da tozarcin Mutane 'yan'uwansu ba dan ma Allah ya taimake mu Dacta Jabir ya muna tsaye kan Al'amarin.
Har ɓullowar cikin jikinta da matsi da wahala da ƙuncin da muka fuskanta zuwa tsayin watannin da Allah ya amshi rayuwarta.
Na sauke ajiyar zuciya Ina jingina da kaina da wassafa abubuwa da dama a zuciyata.
*
Barin Ilhaam Garin Katsina Haihuwar Imaan da Rasuwarta duk babu wanda Ummah Hindatu bata samu labari ba. Jikinta ya kai ƙarshe kuma ƙololuwa wajen yin sanyi ta kuma rikice ta razana a safiyar yau saboda samun Labarin da ke barana ga numfashinta.
Taya Abubuwa zasu kutso mata kai masu muni cikin Ƙurarren Lokaci. Ɗan Alhaji Tahir da ke ƙasar India yana samun kula daga ƙwararrun likitoci ya diro gidan da barazana kala-kala na son ɗaukar fansar asarar da su Ilhaam suka jaza ma Ubansa.
Yana mata barazana da faɗin idan bata bayyana masa inda yaran suke ba sai ya wulaƙanta mata rayuwa daga nan ya bar gidan.
Babban Abin da ya fi damunta bata so Imaan ta mutu ba saboda babu tabbacin Ubansu yana da rai ko ya rasu, Sai kuma da Zuleey aminiyarta ta faɗo mata da mummunan labarin Ganin Aliyu Aliyu yayanta a Nijar da kuma sa ran dawowarsu da Ake yi kowane lokaci.
Ta fi kowa sanin baƙar zuciyarsa da zai iya komai idan ya fusata babu mai sarrafa shi duniya ko ya bar wani abu in ba Imaan ba, Yana mutuwar son 'ya'yanshi fiye da komai ya damƙa mata yardarsa duka amma ta ci amamarsa ta yi butulci mai muni.
Ta shagala sosai da jin daɗin Duniyarta tana yawan mancewa da Wani Aliyu saboda daɗin Shagalin duniya da sharholiya.
Tunaninta ya kwance ta fara saƙa da warwara akan mafita, Abin da ya kamata ta nemi Ilhaam ta san yanda zata yi da ita kar a samu matsala, daga nan ta tsara masa ƙarya da gaskiya ya yarda mutane kuma duk wanda ya faɗa masa ainahin zance zata ƙaryata da kuka da makirci, Ya kamata ma ta tashi daga Unguwar tun kafin ya dawo ya samu mummunan labari.
Anya hakan zai yiwu ba za a samu matsala ba?
Abin da yay ta yawo a zuciyarta ke nan ya hana ta fita sharholiyarta da yawo Ranar.
Ta san duk iya shegenta Aliyu ya shanye ta ya dafe ta a Masifa da fitina..
09117440993.
*ƘURARREN LOKACI*
(11).
Bayan Wani lokaci..
Rayuwa ta ci gaba sosai da daɗi babu da daɗi tare da ci gaba da tarin nasarori.
Shekara biyu da wata Bakwai ke nan da zuwana Germany Na samu ci gaba sosai Makarantar manyan malamai da ɗalibai duk sun san ni na samu kyaututtuka da karama daga Makaranta saboda ƙwazon da na nuna.
Na yi kuka da hamdalah ga Allah yadda aka dinga nuna mini ƙauna daga ni sai Ɗana bani da wasu 'yan'uwa ko mahaifi sai Rufaida.
Na yi ƙoƙari wajen ganin ban ɗaura ma Alhaji Farouku ɗawainiyata ba na nemi aiki ƙarƙashin Canteen ɗin da muke sayayya, bayan tashin mu daga Makaranta ina musu aikin share-share suna biyana, Na tara kuɗaɗe sosai.
Yau kuma Jirginmu zai sauka Abuja birnin tarayya da ikon Allah.
Na sake lumshe idanuwana ina istigfari na fesar da iska Abubuwa masu daɗi da akasinsu na faɗo min a zuciya. A hankali jirgin ke sauka ƙasa bugun zuciyata na tsananta hawaye na taruwa a idanuna Na karanta addu'a ina buɗe idona.
Na dinga Kallon tsarin Airport ɗin ta cikin Tagogin Rufaida da Imraan na ta hotuna suna annashuwa hankali kwance.
Jirgi na sauka aka buɗe mana fasinjoji suka fara fita, Airport ɗin ta ɗan cika da masu zuwa tarbar 'Yan'uwansu. Na kwashi kayanmu da Akwatuna biyu sai jakunkunanmu ita kuma ta ɗauki Imraan da wasu kayan.
Na saka ƙafata ta dama bisa matattakalar ina karanta addu'a na fara saukowa a hankali cikin nutsuwa tare da gyara mayafin Abayata.
Wata iska mai daɗi ke ratsa ni tun daga tsakiyar kaina ina jin wani yanayi, lokaci guda hawaye suka cika idona ganin yanda Iyaye ke tarbar 'ya'yayensu suna rungume juna cike da farinciki.
Na yi tsaye na kasa ƙarasawa inda Rufaida suke tsaye da Alhaji farouku yana murmushi sai da Imraan ya ɗan taɓa ni yana kallona kamar wani mai hankali ya riƙe ni muka ƙarasa inda suke ina tafiyar a hankali. Cikin sanyin murya ina haɗiye wani abu na gaishe shi ya amsa mini yana mana sannu da sake ɗaukar Imraan. Babu ɓata lokaci muka shiga motar da aka zo ɗaukar mu da ita. Kaina na ƙasa na kasa ɗagowa saboda wani iri da nake ji haka nan nake Tunawa da Imaan, da ace ita ce na yi tafiya ta zo tarbata sai mun rikita filin jirgin da murna tun daga nan zata fara muna mini tsantsar farin cikinta da Murna gami da Addu'o'i masu sanyaya zuciya.
Yanzu na dawo Ƙasata ko yaya al'umma zasu amshe ni wane ƙalubale ne a gabana ta ina zan fara neman Mahaifina da yanzu idan na yi lissafi daidai rabonmu da shi Fiye da shekara goma.
Sai da Rufaida ta yi mini magana kana na fahimci mun iso Na sauke ajjiyar zuciya na buɗe motar na fito ina ƙare ma Gidan kallo. Direba da masu kula da gidan ne suka kwashe mana kayanmu. Muka doshi ƙofar Falo Tare muka shiga Rufaida na ta murna da faɗin gaskiya tsarin gidan da aka chanja ya yi sosai.
Ina ji ya bata umarni mu yi wanka da Sallah sai mu fito cin Abinci.
Sai da Rana ta yi sanyi muka gama hutawa muka ci Abinci ne Rufaida ke sako mini zancen Asaad sai koɗa shi take da faɗan irin arziƙin gidansu.
“Dan Allah sister kar ki yi mishi wulaƙanci shi fa mugun sonki yake da Imraan, Wallahi cewa yay zai aure ki, zai muku duk abin da kike so indai bai fi ƙarfin rai da kuɗi ba, ga nutsuwa da iya kalamai Wallahi ya haɗu zaki huta”
Da mizanin hankali na fara auna kalamanta, 'Zan huta' ita ce kalmar da ta ɗan sosa mini rai ba da manufar fushi ko ɓacin rai. Sai dai abin da na
tabbatar a yanzu duk wani wanda ya zo duniya ba hutu ya kawo shi ba. Waye ma zai burin aurena idan ya ji Baƙin tabon da aka laftawa rayuwarmu, da kuma Rashin ɗabi'a ta mahaifinmu?
“Kina tare da ni?”
Ta faɗi tana katse mini tunanina.
Na ja numfashi ina faɗar “Anya kuwa Rufaida da kamar wuya hakan ta kasance, Ba fa komai na fayyace miki na daga rayuwata ta baya ba.,”
“Na roƙe ki Sister please don't give up”
Ban sake cewa komai ba sai murmushi mai kyau nake.
A wunin mu na biyu cikin gida muna kwana ɗaki guda nida Ita da Imraan babu wata matsala muna gaisawa da shi da gajeriyar fira akan karatu da wasu ƙalubale da suka kutsa kai kafin tahowar mu.
Duk da har yanzu bani da wayewar rayuwar mai yawa amma ƙwaƙwalwata na bambance abu mai kyau da akasin sa. Zaman mu waje ɗaya da Namijin da ba muharramina ba a matsayina na wacce bani da gata sai Allah ba kuskure ba ne, Ita ƙanwarsa ni kuma babu wata alaƙa sai kyakkyawar fahimta, A fahimtar da na yi tsawon zamana basu da kula akan addini da al'ada ina jin tsoron wani abu mara kyau ya faru duk da na damƙa musu yarda ɗari bisa ɗari amma Rayuwa babu tabbas yake nan idan mahaifiyarsa ta sake arba da ni a karo na biyu? Amma abinda ya fi damuna idan ban tsaya a nan ɗin ba ina zan dosa wake gare ni? A yanzu dai ban shirya tunkarar Ummah ba ina son zuwa gare ta da cikakken 'yancina na 'Yar'adam tsaye a kan ƙafafuna! Abin da ya fi dacewa fara Neman mahaifina da bincikena kan Azzalumin da ya illata mana rayuwa.
Hum! husawa suna faɗi kowa ya san filin sukuwar ingarmam doki ba na sukuwar gurguwa Jaki ba ne, Ta ina zan fara?
Ina ma ace zan samu wani wanda ya san Raɗaɗin da nake ji da zafi ya fahimce ni mu tattauna da shi.
Na lumshe ido hawaye na zubo mini Rayuwa cike take da ƙaddarori haɗe da Ƙalubale. Ji nayi ana share mini hawaye na buɗe idanuna na ga Imraan na goge mini fuska da fararen yatsun hannunshi irin na Imaan ɗita, Gashinsa da zubinsa ko mai iri ɗaya da nawa Farin Imaan kawai ya ɗiba da yanayin sanyinta.
Na rungume shi sosai ina jin wani irin sanyi tamkar dai Imaan ɗita ce a gabana cikin hausarsa da bata fita sosai ya ce, “Ummina Ki hakuli” ya maida fuskarsa ta tausayi ba shiri na saki dariya Rufaida ma ta shigo ɗakin tana tambaya ta.
“Sister what's wrong please tell me?”
Na sauke sa daga kan cinyata cikin sanyi na soma magana da iya gaskiyata “Rufaida I need to go nd find where Abbah is, but i don't even know from where am i going to start, nd i need to do so many things, Ina jin tsoro ban manta tsanani da wahalar da muka sha A Katsina ba bana son zuwa chan haka kawai, za a iya samun matsala ki faɗa mun ya zan yi?”
Ta kalli Imraan ta ce ya je gun Daddy wato Alhaji farouku ya fita da ɗan gudunsa.
Ta fuskance ni cikin son kwantar mun da hankali ta ce, “Yanzu akan hakan ne kike shiga tashin hankali da yawa, kar fa ki jaza ma kanki hawan jini? Akwai mafita Sister. Abu na farko ki cire Tsoro! tsaro ne yake ƙwaran ki wai ma kin kuwa taɓa ganin Barrister matsoraciya sai kin dage fa kin sa tsaurin ido. Zaki je Katsinan da Salo mai ban tsoro wanda zai gigita su, su gane lallai kin samu muhimmin ci gaban rayuwa Khadijan da suka sani a da ta bambanta da ta yanzu, you have to remember always,, now you know your right nobody will break yur mind kin fi ƙarfin kowa a cikinsu”
Duk kalamanta sun yi tasiri a zuciyata amma tuno irin rayuwar da na yi ke dagula min lissafi na sake ce mata,
“Ki gane Roufy ba tsoronsu nake ji ba yanda zasu amshe ni kuma ni gaskiya sai dai na ɓoye kaina bana son mas,,”
Ta ɗaga mini hannu tana mini kallo mai kama da harara.
“Kina nufin ba zaki bayyana kanki ba? What's the meaning of this Dan Allah Ilhaam ki gane mana; Duk wannan abin da kike yi sam shirme ne! Wa ya isa ya miki wani abu ko maganan banza ko kallon ƙasƙanci, duk basu isa ba don Ubansu ke fa yanzu matsayin Lawyer ce mai zaman kanta, Immediately you finish your studies the story will change duk ƙwazonki ashe ke matsoraciya ce i'm surpise malama..Gaskiya wannan ne abin da zaki fara yi da zai ƙara miki kaifin basira a kan aikinki, Kina tunani zaki kai wani matsayi idan kina jin tsoron ƙananan ƙwari, what if aka kawo maki case ɗin Kisan kai ba zaki iya ƙwatar haƙƙin Ɗan'adam ba kenan answer me?”
Gaskiya take faɗa mini sai dai ba zata gane ba, Ita cikin gata da 'yanci ta tashi bata da wata matsalar rayuwa ni fa duka fa Allah ne ya dube ni ya chanja mini al'amura na samu salama shi ne har zan fara fito-na-fito da waɗanda nake shakka, Atleast ban taɓa tunanin samun ci gaba irin haka ba, bani da wani makusanci fa.
Tunowa da irin cin zarafi da tozarcin da muka shanye ne ya saka ni jin wani ƙwarin gwiwa na dube ta na ce,
“Roufy Zan cire tsoro na yi abin da ya kamata in sha Allah, Na gode sosai da kulawarki”
Ta yi niyyar sake magana ganin yanda ƙwallah ta cika idona ya sa ta miƙe tana faɗar,
“Wannan kukan ma ya ci ace kin daina, Bai kamata ki dinga zubda Darajajjun hawayenki akan wasu Jahilai ba ki daina bari rauninki na bayyana a gaban kowa ki shanye duk wata fargaba da tsoro, haba mana, ni da nake Scientist ma na fiki confidence”
Yanda ta ƙarashe furucin ta na ƙarshe tana dariya ne ya saka ni murmusawa ta fice tare da rufo mini ƙofa.
Na sauke gaɓɓaina bisa gado ina lumshe idanuwana da son hutun ƙwaƙwalwa ta yanda zan saƙa abubuwa na nemi mafita mai ɓullewa.
09117440993.
*ƘURARREN LOKACI*
(12).
Ban taɓa sanin a duniya akwai mutanen da suka san darajar Ɗan'adam masu kirki ba sai da na haɗu da su Alhaji farouku. Gaskiya ba zan kasance cikin mutane masu mance alkhairi ba In sha Allah. Sun nuna mini Karamcin da ya tsaya mini a zuciya.
Yau tun da sassafe na kammala shirina cikin Doguwar rigar Atamfa na ɗaura doguwar hijabi a sama da jakata da ke ɗauke da waya da ATM ɗina da aka loda mini 'yan kuɗaɗena da aka chanja mini kafin mu koma Germany Imraan kamar yay ta rawa saboda Murna Ummi za ta yi tafiya da shi.
Bakin mota suka tusa ni gaba da addu'o'i tare da ƙarfafa mini gwiwa Alhaji farouku ya ce da ni duk yanda muka yi na sanar da shi ta waya idan na isa.
Na amsa musu tare da godiya suka rufe mana murfin motar Direba ya tada ta muka bar gidan muka ɗauki Hanyar garin Katsina.
Tsayuwar mu sau biyu muna sallah Imraan yay barci har ya gaji ya tashi mun ci Abincin da muka saya kan hanya, Bunu-bunu dai sa kira su tambaye ni ya hanya da Imraan. Sai wajajen Tara muka isa Cikin babban birnin Katsina ta Dikko ɗakin kara.
Ina ta hamma ni kaina na gaji Direban ma haka, Muna nufar wani hotel kiran Roufy na shigowa wannan karon ma Imraan ta fara tambayata sai kuma hanya na shaida mata mun iso ta sake ƙarfafa ni yanda zan tunkari Ƙalubalen da ke gabana. Sannan muka yi Sallama shi ma Alhaji farouku ya kira ni yana mana Ya gajiyan hanya sannan muka biya kuɗin ɗaki direba ma na