Showing 18001 words to 19716 words out of 19716 words
da wani Dangi da zan kalla na ji daɗi. Shisa Masana suka tabbatar abin da ka shuka shi zaka girba.
Wacce riba na samu da farin ciki a rayuwata tun da na tashi Mahaifina ya rasu ba a daina aibanta shi ba, Shi yasa ake gujewa Ɗan'adam nadama a ƘUARREN LOKACI ina ace zai dawo duniya ya ga yanda al'amura ke wakana. Bani da wani bango majingini taya matsayina na mace budurwa na yi rayuwa ni kaɗai da aiki ba abu bane mai yiwuwa.
Matsalata Asaad. na san ina matuƙar son shi amma Abubuwan da ya tsira a kwanakin nan sun sha min kai bana son duk wani abu da zai kai ni ga Da na sani a ƙurarren lokaci.
Dare da rana ina yiwa Iyayena da 'yar'uwata addu'a ubangiji ya ƙaddara mutuwa ta zame musu hutu. Kullum damuwa na danƙare a zuciyata na rasa nutsuwar rayuwata.
Ashe daman haka rayuwa take?
Mahaifinmu bai shuka alkhairi ba, Abin ya dawo mana, Bamu aikata wani mummunan laifi ba amma saboda shi da ya aikata ma 'ya'yan wasu da iyayen wasu abin ya dawo kanmu da 'yar'uwata wanda yay silar rasa rayuwarta, Shi ma ya rasu, Ya tuba a ƘURARREN LOKACI. idan haka za a ci gaba da yin rayuwa ba za a taɓa ci gaba ba har abada!
Abu mafi dacewa duk abinda mutum baya fatan ya same sa kar ya aikata laifin da zai munana rayuwarsa ta gaba.
Daga Lokacin da al'amura suka fara daidaita na sa haƙuri a rayuwata na fahimci dukan duniyar nawa take kowane lokaci ma mutum zai iya koma wa mahaliccin sa. na daina damuwa da wasu abubuwa marasa muhimmanci.
Zuciyata na matuƙar son Asaad da Ƙaunar sa Ta ɓangaren sa kuma ba hakan bane ba tsakani da Allah yake so na ba. Na yi duba na hankali da irin matsayinsu da darajar su taya zai iya aure na abin da yafi mutuntaka mu rabu da juna na fuskanci rayuwarmu da Ɗana.
*
Ban sha wahala ba rabuwar mu da Asaad ta dalilin Alhaji farouku da ya nemi aure na. Na yi kuka na gode wa Allah na so na ƙi, Amma na ga ban yi ma ubangiji butulci ba duniya ba jindaɗi aka zo yi ba na amince da auren sa. Alƙalinmu shi ne ya zama wakilina ya bada aure na. Muka tare a Abuja babu wani shagali ban tsawalla ba.
Kuka muka yi sosai nida Imraan bayan ɗaura aure na. Ina tausar zuciyata sosai Ya zan yi rayuwa da mutum mai irin lalurarsa ba kowane lokaci yake hayyacin sa ba.
Rayuwa ta miƙa muna zaman lafiya da mahaifiyarsa duk da ba musulma bace, ban taɓa samun wata matsala daga gare su ba.
Haka imraan ɗina babu wanda yake takura sa yana karatu.
*ƘURARREN LOKACI*
(19).
Alhamdulillahi.
Tun da muka tare daga ni sai shi a gidan Imraan na wajen Roufy babu wata matsala har tsawon Sati uku.
Ranar wata laraba ya tashi da matsanancin ciwon kai daga nan kuma ciwon sa ya tashi, na ruɗe sosai. Na natsu bana son ɗaga musu hankali na natsu da fatan ƙoƙarina ya samu sauƙi. Wata Likita na kira Dr Faryda da ta zama ƙawata na buƙaci ta zo mini da allurar da ke sanya barci ta yi masa daga nan ya samu barci tsawon wasu awanni. Daga nan kuma bamu sake samun wata matsalar ba.
Cikin Shekara guda da aure na na yi Shari'a Biyar akan Cases ɗin Kisa da kuma fyaɗe babu laifi na samu ɗaukaka sunana ya fara zagawa har wajen Kano.
Yau ne kuma Gidan Rediyon Farin wata da ke Abuja suka gayyace ni domin zantawa da ni. Na shirya na je muka fara shiri da farko na ji daɗin tattaunawar sai da ta jefo mini tambaya.
“Barrister yaya mu'amalarki da mata 'yan'uwanki da kuma Alhaji farouku maigidanki?”
“Alhamdulillahi, ta kowane ɓangare ba matsala sai fatan alkhairi wa juna” Na bata amsa cikin daidata muryata domin babu wanda a yanzu bai san lalurar mijina da ake liƙawa Taɓin ƙwaƙwakwa ba. “Masoyanki na matuƙar alfahari da ke barrister! Amma taya har kuke rayuwa da Alhaji bayan lalurarsa da ake jin tsoro?”
Sam tambayar bata dace ba, Babu ita ma a tsarin shirin babu ikon tambaya akan rayuwar mutum sirrinsa. Sai dai in tayi ne domin cin fuska na ɗan murmusa kaɗan nace,
“To Alhamdulillahi bamu da matsala kuma bama fatan ta sai Alkhairi, Kuma komai yana tafiya daidai sai dai abinda ba a rasa ba na yau da kullum” “Masoyanki sun sha tambaya shin kuna gwada Magungunan Musulunci” Tambayarta ta sauka cikin kunnena kamar an watsa mini ruwan zafi.
Na yi shiru ban ce komai ba fin minti uku daga haka suka rufe shirin da waƙa ba tare da an ƙarisa ba. Ban bada amsa ba ita ma bata sake yi mini wata tambayar ba.
Na dawo gidan zuciyata na mini zafi ban ji daɗin abinda suka mini ba na gama fahimtar lallai don a ci mutuncina aka gayyace ba domin komai ba. Da na faɗa masa ya lallashe da ƙarfafa ni akan lallai dama Kowace nasara na tafe da ƙalubale.
Tun bayan faruwar wannan al'amarin na bazama neman ilmin addini sosai. Cikin Ƙanƙanin lokaci Malamina ya fara bani rubutu da wani Hayaƙin habbatussauda na dinga yiwa Alhaji farouku.
Allah da nashi ikon ba a haura Shekara ba ya warke aljannun da ke matsa masa suka fita daga jikinsa. Sheikh ya ɗaura da nasihar kula da Azkhar sosai da muhimmancin yawaita karatun alqur'ani.
*
Har muka yi Shekara biyu ban samu kwanciyar hankali da kulawa ba sai da muka cika shekara Uku da Aure.
A nan ne muka kwantar da hankalinmu mu duka muka samu hutu zuwa ƙasar Malaysia anan muka yi wata guda cikin aminci da kulawa mun samu hutu sosai da jin daɗi dukanmu mun yi ɓulɓul saboda kwanciyar hankali.
Haƙuri yayi. yadda nake jin ɓacin rai idan ina wasu abubuwan da zasu faranta rayuka sai na yi haƙuri gashi yau Allah ya bani kyautar Ɗa namiji. wanda Aka bawa Imraan zaɓin sunansa ya zaɓa masa Umar Farouq za a ce masa Uooh cewar Kakarsa.
Mun samu ci gaba ta arziƙi gami da kwanciyar hankali sai abinda ba a rasa ba. Ana taya mu muranar samun ƙaruwa.
*
Ina yaye Uooh muka fara shirye-shiryen bikin Roufy.
Ana saura sati Biyu biki muka shirya Tafiya Maraɗi Da ita domin zaga Dangin Angon nata Khaleel.
Kusan suma na yi sa'adda muka yi arangama da Mahaifiyar Khaleel ta miƙe tsaye tana kallona nima ina bin ta da kallo zuciyata na bugawa.
Hawaye suka wanke fuskokinmu lokaci guda cikin muryar kuka ta ce, “Da gaske Khadija ce?” Na ji wani irin sanyi cikin zuciyata sanda ta kira sunana na jinjina kaina hawaye na bin kuncina nace, “Ni ce Khadija!” Wata irin runguma ta yi mini muka fashe da kuka a tare.
Ta shafa fuskata fuskarta na fallasa tsantsar farin cikinta. “Da gaske Ali yake ke ɗin ce Jinin mu Khadija Imaan ko?” Na jinjina mata kai.
Sauran 'Yan'uwa suka dinga nuna mini ƙauna na yi kuka sosai ganin dangin mahaifiyata.
Sai da aka natsu da dare sannan muka gane Khaleel ya riga ya gane ne shisa ya matsa mu zo tare da Rufaida.
Dangin Mamarmu suka dinga nan nan da mu kamar a goyani saboda so. Imraan ma haka duk wanda ya tambayi sunana Khadija Imaan naka faɗa duk sun nuna mini karamci da kulawa.
Na ga yayun Mamarmu maza biyu Baba Naziru da Baba Sulaiman. Da Mama Falmata Ummin Khaleel. da ya kasance ɗanta ɗaya sai sauran 'yan'uwan.
Na saki jiki sosai an yi shagalin biki an gama lafiya na tsaya Maraɗin na ƙara sati biyu aka haɗo ni da sha tara ta arziƙi mun zanta sosai da Ummi kan abubuwan da suka wuce. Na ji ƙaunarta har cikin raina ko yaushe muna waya da ita. Imraan na chan na bar shi sai an koma hutu makaranta a maido shi.
09117440993.
*ƘURARREN LOKACI*
©KHADIJA MUHAMMAD SHITU (K_SHITU).
09117400993.
ƘARSHE.
(20).
Gaba ɗayan Rayuwata Darasi ne mai zafi ga mai kaifin ƙwaƙwalwa!
Ban tashi cikin jin daɗi da mutanen ƙwarai ba.
Na samu darussa masu yawa cikin rayuwata, Abu na farko ba zan mance da Ummah ba wacce take ɗauke da Cutar Ƙanjamau a halin yanzu!
A da na ɗau alwashin ba zan taɓa yafe mata ba sai dai a yanzu da take cikin mummunan yanayi ba zan wulaƙanta ta ba zan yafe mata domin rashin yafiya ya janyo mana matsaloli da dama; Duk wanɗanda take rayuwa da su sun guje ta da tozarci.
Bata tausaya mana ba duk da Halin jarabtar da muka shiga mai haɗari.
Gashi yanzu tana Nadama a Ƙurarren Lokaci da ba zata yi mata rana ba bata nemi yafiya dubban Jama'ar da ta zalunta ba musamman Imaan.
Duk girman laifin da muka aikata mata bamu chancanci ta Goranta mana ba da cutar da ƙaddara ta mana kutsen ta, Ta baiwa sauran al'umman da ke zagaye da mu ƙofar zaluntar mu Yanzu gashi ita ma Tana ɗauke da ita.
Ban saki kuɗaɗe ba domin kula da ita ina bada abin da naga zan iya saboda ina fata wannan ya zama darasi ga 'yan baya.
Ba zan ɓoye ba muna zuba soyayya da Alhaji farouku sosai da sosai mai tsafta tare da Ɗanmu guda Umaar. Mahaifiyarsa ta karɓi Addinin musulunci sunanta ya dawo Aminatun.
Babu wata matsala sai dai yau da gobe.
Duk waɗanda suka karrama ni na saka masu da akhairi ni ma, Na taimaki Dr Jabir bakin iyawata da ma wasu mutanen. Ina da Wata Gidauniya shahararriya ta kare Haƙƙin mata da Yaƙi da Shaye-shaye.
Alhamdulillahi na samu ɗaukaka da nasarar rayuwa mun riƙe addu'o'i da taimkon na ƙasa da mu.
Lokauta masu yawa ina tuna kalan wahalar da muka sha. A yanzu ni Khadija Imaan, Ilhaam ce da dangi, Wanda kuma nake kan bincika dangin Abbahna.
Duk da wadatar da muke da ita ban chanja zuciyata ba da son ƙyale-ƙyalen Duniya.
Ba lallai ba ne mutum ya iya cire son Ƙyale-ƙyalen rayuwa a zuciyarsa ba domin kowane ɗan adam na burin Jin daɗin duniya.
Bakina bai huta ba saida Alhajina ya biya mana Umrah ni da shi da kuma Yara.
*ƘARSHEN LITTAFIN ƘURARREN LOKACI.*
Alhamdulillahil Lazi bi ni'imatihi tatimmus salihat.
Ma sha Allah! Ubangiji da nashi ikon ya bani dama na kammala wannan littafin nawa.
Abin da na rubuta daidai na ƙoƙarin faɗakarwa Allah ka bani lada kuskurena Allah ya yafe mini nima Mutum ce ajiza. Waɗanda na ɓata wa su yafe mini.
Duk wacce ta karanta ta yi mini addu'a ina ƙaunar masoyana saboda Allah🥺♥️.
Ayi Following Accounts ɗina
Arewabooks
Wattpad.
#ƘURARREN LOKACI
#KHADIJA MUHAMMAD SHITU
REAL K_SHITU
#7th- friday, June - 1:AM.
www.kshitu@gmail.com
#09117440993.