Showing 12001 words to 15000 words out of 19716 words
biya masa muka shiga wanka muka ci abinci da ɗana da salloli, Daga nan muka bi Lafiyar gado.
Bamu yi zan Isa gare su da safiya ba dan haka muka huta sosai muka sha Barci, Sai da rana ta buɗe wajen Ƙarfe biyu na kammala shiri da Imraan shima na yi kyau sosai kamar ba ni ba, haka Imraan tamkar a sace yaron saboda yanayinsa mai shiga zuci ne.
Na ɗauki Face mask na saƙala ma fuskata tare da Jaka muka fito.
Na shiga motar Asibitin Turai 'Yar'adua muka fara nufa ina nuna masa hanya don nafi buƙatar ganawa da Dacta Jabir fiye da kowa.
Na yi sa'a yana nan Ofishinsa na kama hannun Imraan muka ƙwanƙwasa daga ciki aka bamu izinin shiga.
Na yi Sallama a hankali na kutsa kai ina jin ƙirjina na ɗagawa. Zaune yake yana amfani da na'ura mai ƙwaƙwalwa. Ya ɗago kai yana kallon mu, Sai kuma lokaci guda ya miƙe tsaye yana cire gilashinsa tare da waro idanuwansa duka waje yana nuno mu da yatsa.
Da ƙyar na janyo ƙafafuna muka kai zaune ni da Imraan bisa kujera Muna kallon juna cikin sanyin murya na ce, “Sannu Dacta!” Cikin sarƙewar Harshe ya ce, “Da gaske ke ce Ilhaam Khadijan Imaan??”
Yadda ya yi maganar sai da na ji wani iri na kauda kaina gefe ina bashi amsa da Ƙwarai ni ce.
Ya kai zaune kan kujerarsa yana Kallo na. Kai-tsaye ba zan iya tantance Yanayinsa ba sai dai na ture komai gefe na sake Gaida shi fuskata da ɗan murmushi.
Ya ƙawata fuskarsa da murmushi yana Yafuto Imraan ya matsa kusa da shi cikin raha yake tambayata “Ɗanki ne ko?”Na murmusa ina faɗar “Eh Imraan ne”
Ko a yanayina ya isa shaida bani da wata matsalar rayuwa ta ɓangarori da dama dan haka ya kasa haƙuri ya jera mini tambayoyi akan rayuwata da bayan barina Katsina. Tabbas yana ɗaya daga cikin 'Yan'adam ɗin da nake ganim ƙimarsu da darajarsu a duniyata hakan tasa ban iya ɓoye masa komai ba na abin da ya same ni na faɗa masa.
Ya dinga murmushi yana faɗin, Kin gan ki kuwa, Lallai Ilhaam ke ma kin gani maganar Imaan tana tabbata zaki samu hutu gashi Allah ya datse maki wahala.
Na dinga murmushi ina son tambayarsa akan Ummah ko yana da Labarinta amma ina jin wani kala, Ya tari numfashina yana jeho min tambaya.
“Alhamdulillah, Yanzu kenan kin dawo nan da zama ko??”
“Abin da ya dawo dani ba mai yawa ba ne, Ina son ƙwato mana haƙƙinmu na bincika Azzalumin da ya illata mana rayuwa, Ina son yin hakan ba a matsayina na tagwayar Imaan ba sai na Lauya mai kare haƙƙin Ɗan'adam ina son Tozarta ko waye na kawo ƙarshensa, Ina son juya ma Ummah ƙwaƙwalwa ba zan iya yafe musu ba, Haka ina son inganta rayuwar Abbah da Imraan. Dr this is what exactly brought me Katsina not to come nd stay”
Kalamaina sun girgiza shi har sai da na ga zufa ta yanko masa.
Ya jijjiga kansa yana cewa, “Hakan ya yi daidai Allah ya baki ikon hakan Ilhaam. Ina da nawa Albishir ɗin, Ko kina da Labarin An saki Abbahnku yanzu haka yana da rai”
Wani irin hooking kaina ya yi saboda yanda Furucinsa ya yi ziyara a kwanyata. Na dage na murza idona da cire Takunkumi ina kallon sa baki buɗe na ce,
“Dan Allah ka faɗa mun gaskiya kar ka yi mini irin wannan wasan, Yanzu yana ina ya tuna da mu??”
Sai hawaye sharr suka wanke mini fuska na yi ta ƙoƙarin tsayar da su na sake cewa “Dr ka yi magana yana ina??”
“Ilhaam yanzu ban sani ba, sai dai ina tabbatar miki yana Psychiatry, na dai yi iya ƙoƙarina wajen gano inda yake amma ban gano ba na haƙura, Amma abin yana damuna domin haƙƙin ya rataya ne a wuyana”
“Abbahn?? Abbahna fa haba Dr taya haka zata faru.,,”
Wani abu na dinga ji yana taso mini. Cikin salon tausayawa ya fara bani labarin tun daga Zuwan Ummah Ofishinsa da gidansu har bayyanar Abbah.
Bayan barina Garin da wasu 'Yan watanni ya ci gaba da aiki, Ummah tazo ta same sa bayan ta binciko shi Matsayin likitan da muke tare da zai iya ɓoye mu.
Ta zo masa da batu marar kan gado mai sarƙewa a zuci da barazana. Bai san inda ta samu labarin Rasuwar Imaan ba ta dai yi masa barazana da fallasa cewa shi ya kashe Imaan ya sace Ilhaam Allah ne kawai ya fidda shi amma ya fuskanci ƙalubale mai girman gaske. Daga nan kuma aka yi masa iyaka da kowa nata.
Wannan shi ne abin da ya shiga tsakanin su.
Abbah kuma ya dawo Dacta na bibiyar lamuramsa sai dai bai samu damar sanin yanda suka yi da Ummah ba ya samu labarin taɓin ƙwaƙwalwar da ya samu, Daga nan kuma yay ƙaura amma ana tunanin yana gidan Mahaukata..
Da gama bayaninsa na kasa riƙe hawayena duk kuwa yanda na so yin hakan zuciyata ta yi wani irin sanyi. Shi kenan yanzu miye ribar aikata saɓon Allahn da ya daɗe yana yi. Na kasa juya abubuwa masu kyawu dan haka na miƙe cikin wani yanayi ina masa sallama da faɗin zan sake dawowa.
Ya tabbatar mini da har yanzu Ummah Hindatu na nan gidanmu.
Tun da na tunkaro harabar asibitin inda Motar take zuciyata ke nanata mini Gidan Mahaukata Abbahn ne a Gidan mahaukata hawaye suka dinga zubo mini ina sharewa.
Direba yay saurin buɗe mini ƙofa ganin yanayina.
Na zauna ina maimaita Innalillahi zuciyata da jikina sun sanyaya.
Da ƙyar idan zan yi tunkarar Ummah a yanda nake haka yanzu. Wata zuciya ta kwaɓe ni da ƙalubalantata; Ni shi kenan haka zan ci gaba da rayuwa, To mene amfanin tsoron da abin da nake, Na sani fa duk abin da aka yi masa shi ya janyo kuma ba zan iya chanja ƙaddara ba, to mene amfanin Tauye gaskiya ya chancanci a hukunta sa, amna yanzu Abbah ne ya zama mahaukaci ko a wane yanayi yake ciki, duk ba abin da ya kamata na tsanantawa raina da su ke nan ba, Kar Ilhaam ta zama 'yar'adam mai raunin zuciya.
Ƙarar wayata ce ta datse tunanina da lissafina.
Na kalli mai kiran Rufaida ce na yi saurin ɗagawa ina jan ajjiyar zuciya.
Ta ce, “Ya kin je Asibitin da fatan babu matsala?” na bata amsa ina kwashe duk abinda Dr ya faɗa mini na gaya mata. “Abbah yana gidan mahaukata..” “Ya salam! Allah ya sa baki yi shirme ba. Yanzu da kika ji haka yanda zuciyarki ke zafi ku wuce Sabon Layin kawai, kada ki kuskura ki musu sanya ki juye musu duk wani abu da ya daɗe yana kankarar miki zuciya, Ki nuna musu Ke ma mutum ce Ilhaam!”Lokaci ɗaya na ji wani ƙwarin gwiwa na bata amsa da “Zan yi Rufaida, zan je da zafina fiye da wanda suka sani a lokacin da mahaifinmu yake tare da mu, I will surely surprise them!”
Na datse kiran ina share hawayen fuskata.
Kwantancen unguwar na yi ina nuna masa hanya har muka doshi Unguwar. Tun da muka fara tunkaro Layinmu Zuciyata ta motsa! Wasu shuɗaɗɗun Al'amura marasa mantuwa masu danƙarewa a zuciya da raɗaɗin gaske suka soma dawo mini da hoton Imaan gami da irin ƙuncin da muka shanye da tozarci.
Yanayin Mutanen da yanda suke gudanar da rayuwarsu sam babu abin burgewa. Hakan na nufin babu wani ci gaba.
Da ido duk suka bi motar daidai tana tsayawa Bakin ƙofar ɗan ƙurƙurin gidanmu. Na kama Hannun Imraan cikin dakiya na buɗe murfin motar na fito gaba ɗaya na.
Irin tafiyar da nake da zafin nama
kaɗai zai iya tabbatar da ina ji da jini a jika. Duk suka yi mini chaa da idanuwansu. Fuskata a bayyane take suka dinga bina da kallon ƙurilla.
Jikina har kyarma yake na saka ƙafata na shiga Gidan. Daidai lokacin Ummah ta fito da shirin fita muka kusa cin karo da juna ta dakata. Ban dakata ba na kutso kai, Tsaye na yi gabanta zuciyoyinmu na harbawa da ƙarfi yayinda muke kallon juna ido cikin Ido..
09117440993.
*ƘURARREN LOKACI*
(13).
Taya zan mance da macen da muke yiwa kallon uwa a da, Babu wanda ya wulaƙanta mana rayuwa ya nuna mana zallar ƙiyayya da tsana kamar ta, Ta azabtar da mu ba tare da laifin komai ba tare da haƙƙinmu ba ta bankaɗa sirrin mu, ta goranta mana a kan abubuwa masu yawa, Ta buɗewa sauran al'ummar da ke zagaye da mu ƙofar tozarta mu..Ta ci mutuncin mahaifiyar mu da zagika masu muni, duk a ƙurarren lokacin da ta riga ta bamu da wani gata a duk duniya sai Allah..
Haka ita ma ba za ta mance da yaran da ta tsana fiye da komai a rayuwarta ba, waɗanda takalmi ya fi mata daraja da su ta ya zata manta da mahaifiyarsu da Ubansu.
Kowane na ayyana abubuwa masu tarin yawa a kan Ɗan'uwansa.
Ƙwaƙwalwata ta dinga mini tuni akan rayuwata ta yanzu.
Sun kwashe fiye da Mintuna Biyar suna kallon junansu irin kallon da yake ƙona zuciya da tafasa ƙwaƙwalwa.
Ni na fara janye idanuna da suka fara tara wata ƙwallar fitina. Tabbas yau sai na tabbatar musu da ni Jinin Aliyu Aliyu ce.
Irin Kallon da ta ga mun yi wa juna da Yanayin shigata da Yaron da ke tsaye kaɗai ya sa tabbatar da.
Na gaba ya yi gaba, Na baya sai tsintar hula! Haka Ginshuƙin dutse kowa yay karo da shi sai ya faɗi. Abin da ya hautsina duniyarta kenan ta fara ƙwaƙulo abin faɗa. “Bani hanya” Na kafe ta da ido da fitina fal raina.
Ta bangaje ni da niyyar wucewa na tura Imraan gefe cikin zafin nama na ɗauke ta da tagwayen maruka huɗu hagu da dama lokaci ɗaya masu zafi mai ratsa ƙwaƙwalwa. Na tsaya gabanta ina kallon ta tana kallo na ko ƙyafatawa bata yi.
Ina shirin magana ta datsi numfashina da faɗin, “Da wannan salon kika dawo, Ni Hindatu kika mara dan Uwar Ubanki?” Bata rufe baki ba na sauke mata wani marin cikin zafin rai na fara magana.
“Hindatu na faɗa miki kuma zan sake maimaita maki! Har abada ba za mu taɓa mancewa da azabtarwarki gare mu ba, Haɗuwar mu da ke ba zata yi kyawu ba Hukuncinki zai yi muni, Sai na wulaƙanta ki na tozarta maki rayuwa fiye da yadda kika mana dan baki san Zafin haihuwa ba shi yasa zaki Ƙuntata mana, A yanzu Khadija Ilhaam Aliyu Aliyu da kika sani da ba ita ba ce, Ina tsaye gabanki ne matsayin Lauya mai zaman kanta da zata wargaza maki rayuwa!”
Ta so dakatar da ni sai kuma ta fasa sai da na kai aya. Kin gama?? ita ce amsarta. na wurga mata kallo mai bayyana ainahin tsana da ƙiyayya.
Kafin na yi wani yunƙuri ta yi waje. Ina jin kwaratsinta da ihu. Na kama hannun Imraan muka yo waje Idanuwanta da suka yi ja ta zazzaro tana ihu da nuno ni, Take duk matasan da matan unguwar suka ci gaba da faɗar.
‘ Ita ce, Ita ce wadda Ƙanjamau ta kashe 'Yar'uwarta 'Ya'yan Ali Tantiri, kar wanda ya bari ta kusanto shi Ta gama yawonta zata zo ta yaɓawa mutane bala'i‘ suka fara jifana.
Da sauri na shiga mota ya fara ƙoƙarin tada ta, Na dinga fitar da numfashi da sauri-sauri kamar zuciyata zata buga Imraan yay zuru yana kallo na. Duk iya dakiyata na kasa riƙe hawayena suka dinga kwarara na yi ta haɗiye ɓacin rai raɗaɗi na taso mini a maƙoshi.
Ya ɗau hanyar Hotel ɗin da muka sauka.
Ban yi wata-wata ba na saɓi Imraan a kafaɗa muka shige ɗaki na datse ƙofar. Na kwantar da shi ina faɗawa kan gadon.
Wata irin tafasa zuciyata ke mini tunanina ya tsaya chak.
Mece ce sunan wannan rayuwar Jahilci ne ko me?
Har tsawon wane lokaci ne zuciyoyin mutane zasu tsarkaka, Shin na chancanci wannan tozarcin taya zan ƙarfafa kaina na yi rayuwa kamar kowane mutum bayan baƙin tabon dake tattare da mu?
Da ace zan iya yin kuka da na ji sanyi amma na kasa hakan sam sai Tafasa da ƙirjina ke yi har numfashina na sarƙewa.
Kiran Rufaida ya shigo wayata na ɗaga da ƙyar ina kara wayar a kunnena na kasa magana saboda wani abu da ya dunƙule mini a maƙoshi.
“Meke faruwa ne Ilhaam??” Ta faɗa cikin ƙosawa.
Ban san ta ina zan fara mata bayani ba na dinga fizgar numfashina ina ajjiyar zuciya. Sai da na haɗiye wani abu mai raɗaɗi kana na gaya mata duk abinda ya faru.
Tabbas bacin ta san ba zan kwantata yi mata wasa haka ba da ba zata yarda akwai mutanen da zasu iya yin wannan Jahilcin ba. Ko a yanayinta ai zai shaida bata da wata cuta kuma tana cikin tsaftatacciyar rayuwa.
“Da gaske fa Ilhaam huh! na yi mamaki gaskiya ashe har yanzu mutane basu daina jahiltar cututtuka ba, Amma yanayinki ya musu kama da na mai Ƙanjamau anya suna da hankali da tunani ma kuwa?”
Na yi shiru ban ce komai domin ni ɗaya na san yanda nake jin zuciyata.
Muryar Alhaji Farouku ta katse mini tunani da faɗan,
“Me kika yi da suka ce haka?”
Yaya tambaya ma kake?
ya za a yi mutum ya iya yin wani abu, duk ƙarfin zuciyarka dole ka ji ɗaci da raɗaɗi haba 'Yar'uwarta fa da ta rasu suke aibantawa da ita kanta”
Abinda nake so su gane kenan. Ina tsananin son Imaan ko da bata raye zan ji zafi har cikin raina idan aka aibanta ta.
Ban san sa'adda na yi wurgi da wayar ba ina jin Kalamansu na dawo min cikin ƙwaƙwalwata. Haƙiƙa ina jin kewar 'yar'uwata irin sosai ɗin nan. Da tana da rai da yanzu ta lallashe ni ta yi mini addu'a. Shi ke nan ni ɗaya zan ci gaba da rayuwata Ina fata Ubangiji ya ƙaddara mutuwa ta zamar musu hutu Mahaifiyata da Imaan. Ko mahaifiyata bana tunaninta kamar yanda nake tunanin Imaan addu'a ce dai nake yi ma Mamarmu fiye da kowa don da tana da rai da duk wasu wahalhalun sun mana sauƙi.
Garin Katsina da na fi so ya mini baƙiƙƙirin babu Mahaifiyata Babu 'yar'uwata da Mahaifina ya zan ji daɗin rayuwar na ƙarfafa kaina. Dama mutane da ƙaddararsu ta yi kama da tawa basa farin ciki a rayuwarsu, Mahaifina fa da nake matuƙar so da ƙauna yake sonmu ne ya haukace al'amarin ya yi mini girma a ƙwaƙwalwata ta ya zan samun nutsuwa.
Kuka ne ya kufce min na ci gaba da raira shi kamar zai tafi da numfashina. Na tabbatar ma kaina ba zan iya yafewa duk wani wanda ya ƙuntata mana ba, Ya hana mu rayuwa kamar ko waɗanne mutane, kawai don an sani bamu da gata sai Ubangijin mu.
*
Ban san tsawon wane lokaci na ɗauka ina Barci ba, Ƙwaƙwalwata ta samu Nutsuwa sosai da hutu ban tsananta wa kaina da tunane-tunane ba na yi Sallah da cin Abinci na sha maganin Mura da aka sayo mini na Sake kwanciya.
Washe gari
Rana ta biyu da zan sake Fuskantar Ƙalubale.
Nasara ko Akasin ta.
Ban yi sanya ba na sake shiri ina ta amsa waya daga Rufaida dake iya bakin ƙoƙarinta na son taimkona na yi abin da ya dace Cikin sa'a na gwada lambar Dacta Jabir ta shiga. Muka gaisa a mutunce. Na yi masa tambayoyi akan Abbah ya bani amsa. Alhamdulillah kuma na gamsu, na ji daɗin bayanansa ƙwarai.
Na fito riƙe da Imraan yana ta min fira ina murmushi na sake basu Atm suka fidda kuɗin kwanakin da zamu ƙara.
Tun da muka doshi Unguwar nake jin wani iri ina tuno Imaan.
Ba layinmu muka shigo ba daga bayan wasu shaguna motar ta tsaya ina tunanin wa zan tunkara da maganar Abbah. Sai kuma wani tunani ya zo mini, in dai da kuɗi ba zan samu matsala ba, Na duba kuɗaɗen da ke jakata da na taho da su duka dubu uku ne na ɗauki Atm ɗina na fito ni ɗaya shagon wani Mai pos. Dubu ɗari na cire na bashi kuɗin cirewar na fito, Mutumin da ke zaune yana kallo na yay maza ya biyo bayana yana gaida ni.
Cikin kallo na ya ce,
“Hajiya ko ’yar wajen Ali ce da ake ɗimi kan ta tagwayen nan da aka ce ɗaya ta mutu?”
Na ji zafin furucinsa amma na daure. To me ake faɗi kan mu?
Na san dai duk wanda ya yi ma Abbahnmu farin sani ba na yanzu ba zai iya gane mai alaƙa da shi ta yanayin idanunmu da sheƙin fata.
“Ni ce!” na bashi amsa a da’kile.
Ya washe baki yana kame-kamen ta inda zai fara sai ya ci gaba da mini Addu'a.
Na amsa ina zaro dubu biyar na miƙa masa da ci gaba da tafiyata.
Tamkar zai mini sujjada saboda tsananin murna ya biyo ni yana min magana, “Hajiya na ce wai kuwa kin San inda Alin yake ne? dama abin da nake son ji kenan, “Cikin salon hikima na bashi amsa. A'a Baba ina kan bincikawa ne dai”
“To to, Gaskiya dai ina ga bai wuce Maraɗi, ina tunanin yana chan gaskiyar magana idan kuma baya maraɗi to sai dai fa a nemi Shamsu a bashi wani abu dan shi kaɗai ne zai iya faɗar asalin inda yaken. Na tsaya ina dubansa na ce, “To baba yanzu ya zan yi kenan idan naje Nijar ko?’ Ya washe baki ya ce, ‘Baki da matsala akwai ɗiyata Saliha da ke zuwa kasuwanci chan ta san Gidan yarin da muka zauna zan haɗa ku sai ku je tare”
Daga ƙarshe muka yanke Salihar zata zo hotel ɗin da nake bayan na bashi lambata a takarda da ƙarin dubu biyar ta kuɗin Abin hawan da zata hau, Ya ce yanzu-yanzu ma zai turo ta ai ba lahira zata ba lafiya qalau ne.
Tunanin abubuwa da dama na dinga yi lokacin da muka koma masaukin mu hotel. Sai dare wajajen ƙarfe Tara ta iso na buɗe mata ƙofa ta shigo muka gaisa sama-sama .
Kai-tsaye na yi mata tambaya kan Abbah ta tabbatar mini da Gidan kason da suka zauna akwai mutanen da suka san sa da inda yake zuwa a maraɗin.
Lalle kuɗi ba abin da basu yi, A daren har mun ƙarƙare da ita zamu yi tafiyar zuwa marɗi gobe duba da yanda hutun makaranta ke haramar ƙarewa.
Mun yi waya da Rufaida don Alhaji farouku bashi da lafiya mun tattauna da ita kan gobe da wuri zamu kama hanya. Ta yi mini tuni da ragowar kwanakin da muke da