Showing 15001 words to 18000 words out of 19716 words
su na komawa saboda wani taraining da ake son fara bamu.
Na kwanta raina fal murna ban tsammaci abubuwan zasu zo mun da sauƙi haka ba ina ta addu'a da zumuɗin wayewar gari.
*
Tun da asuba na yi shiri na gama na yi ma Imraan wanka na saɓo shi a kafaɗa na fito direba na jira na. Sabon Layin muka biya muka ɗauke ta daga nan Muka hau tafiya..
09117440993.
*ƘURARREN LOKACI*
*©K_SHITU*
(14).
Mun yi Chanjin kuɗi da taimakon Saliha mun shiga Maraɗin ina ta addu'ar dacewa. Sai dai Mun yi yawo sosai har faɗuwar rana gidan Kason da duk suka zauna babu wanda ya san inda yake, Daga ƙarshe muka yanke shawarar kwana da safe mu juya.
Na kasa riƙe hawayena sai da suka zubo tun da muka zo ban iya cin komai ba saboda zumuɗi kuma ba a dace ba, Jikina ya yi sanyi sosai na kasa magana da yin fira da Ɗana har ya gaji yay barci.
Washe garin ranar muka kama hanyar Katsina muka koma jikina a mtuƙar sanyaye na sallame ta muka yi zata dawo da Zancen Shamsun da ake sa ran ya san inda yake abu ya zama kamar musifa.
Haka ta dawo Ta ce Shamsun ma ya ce bai san inda yake ba. Har sai da ya rage kwana ɗaya ya rage mu koma na yi addu'a daga nan na haƙura dan ban san na yi wasa da karatuna.
*
Mun dawo Germany mun ci gaba da karatu babu kama hannun yaro na sama ma Imraan wata islamic primary school ya fara nursery one.
Cikin ikon ubangiji rayuwa ta ci gaba da daɗi ba daɗi soyayya mai ƙarfin gaske ta shiga tsakanina da Asaad ɗan Galadiman Kano Wanda nake matuƙar jin sa a zuciyata irin yadda ban tsammata ba mun shaƙu da shi sosai. Na samu ci gaban rayuwa da har nake farin ciki ko yaushe wanda hakan ya matuƙar yiwa Rufaida daɗi.
A sannan ne take labarta mini ainahin Lalurar Alhaji farouku da ta sanya shi son kaɗaici dw rashin son mutane Ba taɓin ƙwaƙwalwa ne da shi ba, Aljannu ne suke matsa mishi kuma tun da Abbin su Ya rasu ba a sake neman masa maganin muslunci ba Mahaifiyar su tafi yarda da Na bature. Ita kuma bata da damar tankawa akai.
Na yi musu addu'a da ƙarfafa mata gwiwa akan zai samu lafiya in sha Allah. Abin da ya fi damunta Yayanta babu ta inda Allah yay masa tawaya ga arziƙi ga Kyau da kyawawan halaye sai matsalarsa kawai da tsattsauran ra'ayi na tsanani irin na mahaifiyar su.
*
Allah da naShi ikon Rayuwa cike take da ƙalubale da kuma nasarori masu tarin yawa, Yawan Gode ma Allah ma yana ƙara wadatar zuci yau ni ce Matsayin cikakkiyar Lauya Barrister Khadija Ilhaam Aliyu Aliyu wacce duban jama'a ke nuna wa tsantsar so da ƙauna, Na rungume Rufaida da Imraan muna hawayen farin ciki.
Da wane idon zan dube su da ɗunbin karamci da halaccin su taya zan mance da su, Ina kewar Imaan da Abbah na san da suna a raye da sai sun fi kowa nuna mini zallar farin cikinsu, Asaad ma ya nuna mini murnarsa da Alhaji Farouku.
Mun shigo jirgi mun baro Germany cikin matsanancin farin ciki tare da Karamcin turawan da buƙatar mu yi aiki tare da su musamman ma Rufaida da take likita.
Kwanaki Huɗu da dawowar mu na sami Alhaji Farouku na yi masa godiya akan hidimarsa da addu'a.
Yana kan cuku-cukun fara nemar mini aiki ƙarƙashin wata Kotu. An yi nasara na samu Aikin a nan cikin garin Katsina Imraan kuma yana makaranta a Gobarau Academy Katsina. Muna zaune wata unguwa mai suna Ƙofar Kwaya.
09117440993.
*ƘURARREN LOKACI*
(15).
Ko kusa ban yi tunanin samu wata matsala ba ta ɓangaren Aikina har wata guda da na fara amsar Albashi. Sai da wani case ya ɓullo na wata matashiyar budurwa da aka yi wa fyaɗe, Mahaifiyarta da ita kanta suna kuka cikin ofishina suna roƙona na tsaya musu basu da wani wanda zai tsaya musu an fi ƙarfin su babban mutum ne ya illata musu rayuwa ƙarfin su bai kai ƙalubalantar sa ba. Na tausaya musu sosai har na ji zan iya tsaya musu da dukkan ƙarfina wajen ƙwato musu haƙƙin su.
A cikin wannan Case ɗin na fuskanci ƙalubale sosai na nuna jarumta da taurin zuciya har na cin-ma Nasara. Al'amarin da ya zo mini da sauƙi shi ne 'Yar mutumin da ta bani haɗin kai ta bankaɗa sirrin mahaifinta da wasu hujjoji ta tabbatar mini ba karo na farko kenan ba ya aikata laifi irin wannan.
Shari'a ta yi zafi sosai na ƙarfafa kaina na ƙalubalance su wanda kai tsaye Muka yi zaman shari'a tare da Lauyan da ke kare Alhaji Yusuf Ma'aji babban lauya ne mai lasisi bai taɓa faɗuwa a shari'a ba.
Mutane na matuƙar yaba jarumtata da tsaiwa kan gaskiya da na yi duba da yanda Iyayen Yarinyar da nake Nemar ma Haƙƙin ta Bilkisu basu da ƙarfi.
Duk irin arziƙin Alhaji Yusuf ɗin na gaban misali sai gashi na yi nasara kan su a shari'a Alƙali ya yanke masa hukuncin zaman Gidan kaso na shekaru masu tsayi sosai. Da kuma tara mai yawa da ɗaukar nauyin Ita Yarinyar.
Ƙarara za a iya fahimtar fusatar makusantansa da lauyan sa. Na yi farin ciki matuƙa da iyayen yarinyar suka dinga jera mini addu'o'in fatan sa'ar rayuwa da nasara har sai da na yi hawaye.
Na yi mamakin yanda shari'ar ta zagaye Gari da gidajen talabijin da na Rediyo ta ko ina ana jinjina wa ƙwazon Matashiyar lauyar.
Ƙalubale na farko da na fara fuskanta; Cin mutuncina da bibiyar rayuwata da Mutane biyu ke yi Matar Alhaji Ma'ajin da Ɗansa suna ta bibiyata da goranta mini a kan mahaifina na rasa inda zan tsoma kaina na ji daɗi.
*
Ina tsaka da bibiyar su Ummah na ci karo da abin da ya kusa dakatar mini da numfashi.
Dattijo mai matuƙar kamanni da Imraan ɗina ta fuskar gashin jikinsu da yanayin maganansu, sai dai ba kowa ne zai iya gane hakan ba sai mai zurfin tunani da kaifin ƙwaƙwalwa Domin dukkanin zanen fuskarsa nawa ne.
Ta ina zan fara bayyana wa Duniya ɗana ba ta tsaftatacciyar Hanya Aka same sa ba, Sunan sa Imraan Aliyu Aliyu. Na so na haƙura saboda kar na tuno da wasu abubuwa da suka shuɗe marasa daɗi a rayuwarmu sai kuma na dinga jin ban yiwa Imaan Adalci ba.
Me sunan abin da na yi kenan. Idan ta tabbata lallai Mahaifin Mutum mai karamci da girma a idona ne ya lalata mana rayuwa?
Abin yayi mini girma a ƙwaƙwalwata ta ina zan fara Ina tsananin ganin girman Dacta Jabir a idona Ya yi mana halacci a rayuwa bai duba rashin gatan mu ba ya cutar da mu ya tausaya mana yay tsaye kan al'amuran rayuwarmu ya bamu kariya ya ciyar da mu ya ƙarfafa mu, ya nuna mana muma mutane ne kamar kowa har abada ba zan mance da Karamcinsa ba ina matuƙar jin kunyar sa.
Shin nayi masa sakayyar mutuntaka idan har na tona wa mahaifinsa asiri a idon duniya, bana fata wani ya kunyata a rayuwata sai a kan wanda ya wulaƙanta mana rayuwa ya jefa 'yar'uwata cikin mummunan yanayi a Ƙurarren lokaci da aka san bamu da gata sai mahaliccin mu an cuta mana
Yanzu abin da yake mini yawo ya hana ma idanuna runtsawa yake mini barazana a kwanyata shi ne ta ina zan fara, Shin shi Dacta Jabir ɗin yana da sani akan al’amarin idan bai sani ba fa, kenan ni ce zan jefa shi cikin ƙunci?
Innalillahi Wa'inna Ilaihi raji'un kawai nake maimaitawa, na rasa wa zan tunkara na faɗa wa Matsalata.
Cikin watanni huɗu da nayi da Fara aiki na ji zan iya ci gaba da rayuwa cikin 'yanci da farin ciki don a gani na bani da wani dalili na ƙuntata duniya ta komai muƙaddari ne daga Ubangiji.
Amma yanzu na yi ma kaina adalci idan na binne wannan al'amarin a zuciyata ni ɗaya, Ban manta ba kuma ba zan mance ba har numfashina ya tsaya zuciyata ta daina bugawa Irin wahalar da Imaan ta sha Bana fata ko maƙiyina ya ɗanɗana ta.
Gaba ɗayan rayuwata na tashi da burin ganin bayan ko waye ya wulaƙanta mu haka, Har 'yar'uwata ta rasu da ƙaddarar samun Ɗa Namiji.
Tun da na mallaki hankalin kaina ƙwaƙwalwata ta kan banbance abubuwa masu kyau da akasin su. Na sani dai Ummah ba zata taɓa nuna mana wannan zallar ƙiyayya da tsana hakan nan ba ina yi mata uzuri ba don ta chanchanta ba, Sai dai ni a iya sani na ba mu taɓa aikata mata wani abu ba daidai ba wanda har muka chancanci wannan ƙin.
*
Na ɗauki hutun sati biyu wajen aiki saboda na nutsu na samu hutun ƙwaƙwalwa abubuwa sun cunkushe mini.
09117440993.
*ƘURARREN LOKACI*
(16).
Ya zan yi na bayyana irin farin cikina?
Ko kusa ban yi tunanin ganin Abbah ba. Duk da tsayin shekarun da muka kwashe ba tare da juna ba ba zan taɓa manta shi ba har abada.
Ina sa ƙafata ɗaya waje muka haɗa ido da shi yana tangaɗi zai shigo gida da ƙyar.
Lokaci ɗaya zuciyoyin mu suka harba! na dafe bango ƙirjina na ɗagawa. Ya Rahman wa nake gani haka Abbah ne a wannan yanayin ko dai idanuna ne.
Duk kyan fatar sa da sheƙin ta da ƙyalli da kyawun fuskarsa da kwarjinin sa da tsafta babu su yayi wani iri fuskarsa cike da gashi sosai da furfura Idanuwansa sun jeme sosai suturarsa ta yayyage baƙiƙƙirin da dauɗa.
Ya buɗe idanuwansa sosai yana kallo na ya ɗago hannunsa na kasa jurar yanayin ƙafafuna suka yi wani irin sanyi na zube bisa gwiwoyina ina jin wani ɗaci a maƙoshina.
Na rasa mene abin da zan aikata.
Ya janyo ƙafarsa ya matso ni har gabana yana faɗuwa ƙasa. Tamkar an datse mini harshe na kasa furta ko da kalma ɗaya ce sai wasu zafafan hawaye da suka dinga bin kuncina suna zuba, wasu shuɗaɗɗun al'amura na dawo mini.
Tun ina kukan a zuci mai matuƙar ciwo har na fara raira shi fili da ƙarfi idnuwana na rurrufewa na rungume Abbah shi ma ya fashe da kukan cikin wani yanayi.
Ina shirin fara magana ya dafe kansa yana wani irin abu da ƙoƙarin ihu amma ya kasa zuciyata ta dinga bugawa da ƙarfi kamar numfashina zai tsaya.
Ina son kai shi asibiti a duba mini lafiyarsa Amma zuciyata na mini gargaɗi kan Dacta Jabir
To Me na yi kenan.
Cikin Kwan uku kachal Abbah ya samu kulawata sosai sai dai Ya kan kirayi sunana ya ce Khadija Imaan ina Ilhaam sai zuciyata ta rauni na ci gaba da kuka wani lokaci kuma ya dinga wasu abubuwa masu tsoratarwa.
An sallame mu Mun dawo gida ban ƙyamace shi ba Imraan ma haka ina kula da shi sosai Na rage damuwa sosai sai dai tunanina kan rayuwar mu da zamu ci gaba ce nake tunani mun yi magana da Rufaida, Alhaji farouku, Asaad duk na sanar musu da dawowar Abbah suna ta tambaya ya aka yi amsar dai Ban sani ba na gan shi ne zan fita baya cikin yanayin da zai mini bayani sai natsu sosai.
*
Rayuwa ta ci gaba. Wata ran mu yi magana lafiya lau wata ran kuma baya cikin hayyacin sa.
Ranar wata Alhamis cikin Dare yake mini wasu maganganu da har abada ba zan mance da su ba.
'Imaan ki yi haƙurin na so na rayu daku amma ban samu wannan damar ba. Hindatu bata yi laifi ba duk abin da ta yi muku sai dai baku ya dace yi wa ba ni ne na ƙuntata rayuwarta ba ku ba, Ni na yi sanadin Mahaifiyarta. Ki yi haƙuri da rayuwa kar son Ƙyale-ƙyalen duniya ya rufe idanuwanki, Ni kaina na yi Nadama a Ƙurarren Lokacin da ake yawan guje mini da tuba na ba zai mini rana ba. Zan sake maimaita miki kar ki bari Ƙyale-ƙyalen Rayuwa ya rufe idonki kar ki rama sharri da sharri ki rama shi da alkhairi.
A washe gari Mahaifina da ya rage mini ya rasu.
Idan na ce zan misalta raɗaɗin da na ji na yi ƙarya ko kare bai zo mini gaisuwa ba idan aka cire Dr Jabir da Rufaida da yayanta.
Na yi alhini har na gaji kuma ban samu wani sani a kan dangin Mamarmu ba.
*ƘURARREN LOKACI*
(17).
Rayuwa ta ci gaba.
Bayan wasu shekaru na rage damuwa sosai muna soyayya mai zafi da Asaad.
Na yi tunani sosai a kan rayuwarmu, ko da yaushe ina jin ciwo a zuciyata a kan abubuwan da suka shuɗe na rayuwarmu sai dai ina samun farin ciki ta ɓangaren mutane da dama.
Ina so na tunkari Ummah mu yi magana da ita. Tunda nake a rayuwata ban taɓa ƙin wani mutum ba sai ita kuma ta cuta ma rayuwarmu sosai. Amma zancen Abbah ya chanja tunanina da abin da zuciyata ke yawan ayyana mini.
Abu ɗaya da na sani a rayuwata cikin halayena ina yiwa Ɗan'adam uzuri Duk girman cutarwar da yay mini. Ita ma 'yar adam ce kamar ni irin ƙiyayyyar da ta nuna mana da zalunci ta yi yawa akwai zuciya a ƙirjinta kuma ita ma mace ce kamar mu.
Ba zan yi mamaki ba idan har tsawon lokaci tana tare da miyagun halayenta ba tsanar da take mana ba ta sauya ba, Na rasa gane wani dalilin ta a duniya da muka cancanci Azabtarwar ta.
*
Yau gani gaba da gaba da Ummah a mutunce.
Ina son mu tattauna akan wasu al'amura. Da farko kamar ba zata bani haɗin kai ba sai da a ga alamun ba shirme ya kawo ni ba ta saurari abin da ke tafe da ni.
Sai da ta gama saurare na kamin ta yi 'yar dariya ta ce, “Ilhaam Kenan ban yi niyar faɗa maki abin da ya sa na tsane ku fiye da kowa ba sai da ubanku ya mutu”
“A saninku ni ɗin Ƙanwar Mahaifinku ce ko. To ko kusa bamu da alaƙa ta jini hanya ko a rafi kindirmo ko a ƙwarya!”
Ni 'yar asalin Ingawa ce. Aiki na zo yi birni muna sayar da abinci. Ina da shekara Sha shida na fara ganin Ali wanda kyawunsa da iliminsa suka ruɗen sai da muka yi nisa a soyayya kana Na fahimci munanan halayyarsa ban damu ba saboda ƙarancin ilmi da wayewar rayuwa da kuma soyayyar gaskiya da nake yi masa.
Ya nuna mini kuɗi da wayau Ya ci galaba kaina da soyayyarsa. Ban taɓa sanin yana da Mata ba sai da na biye ma zuciya da sakarci ya lalata mini rayuwa. Ya bini da daɗin baki na yaudara ban damu ba saboda ƙuruciya muka ci gaba da soyayya na wani lokaci ban ga sauyi a mu'amalar mu ba. Ba zan ja ki da tsayi ba, Sau biyu Mahaifinku na tarayya da ni ba tare da igiyar aure ba. Wanda son da nake masa ya rufe idona na kasa gane kuskuren da nake tafkawa. Sai da Ciki ya bayyana jikina matar da nake yiwa aiki ta gane hankalina ya tashi na tsorata.
Ta kore ni zuwa garinmu iyayena suka mini korar alla wadai na dinga jin tsoro sosai na bazama neman Matarsa. A lokacin na ji a raina ba zan taɓa mantawa da halaccin ta ba, tana da hali mai kyau lokacin da Ali ya san da cikin Ya ci mutuncina kamar wata Akuya ya tozarta ni ita ta yi tsaye ta ce sai ya aure ni tunda shi ya ɓata mini rayuwa. Bata taɓa nuna mini wani kishi ba ko ƙi. Cikina ya kai watan haihuwa inda ya dinga nuna mini ba cikinsa bane rantsuwa ba kalar wadda ban masa ba amma sai dai ya tsawatar mini cikin fushi da zagina. Ban yi tunanin Rashin imaninsa ya kai ya dake ni da ciki ba na yi kuka sosai a lokacin na fara samun wayewa da fahimtar abubuwa masu tarin yawa. Na haife Ɗana mai kama da Ƙanwata Jamila Ali ya nuna babu ruwan shi da ni. Na sha wahala sosai aka samu matsala yaron ya zo da taɓin Ƙwaƙwalwa.
Na sha Wahala irin wadda ba zan iya misaltata ba wani irin ciwo Mamman ya dinga yi yana wari da ƙarni An ƙyamace mu ni da shi, Mun fuskanci tozarci da ƙasƙanci maran mantuwa irin wanda ku baku sha shi ba har yanzu Duk ta dalilin mahaifinku ya sake ni. Lokacin da mahaifiyarku ta samu cikinku ta wulaƙanta ni da gori ta hanani raɓarta da ɗana wanda hakan yay silar mutuwar Mamman.
Kamin ta kai aya hawaye sun wanke mini fuskata na rasa me ya kamata na yi.
Me yasa abubuwa suke faruwa haka ne ya zan yi da raina.
Na yi ƙoƙari yanda zan iya na ƙi zubda hawayena. Ina son adalci kuma bana fatar yin zalunci a rayuwata dan haka zuciyata ta karye Ko nice abin da zan yi kenan. amma mu bamu muka yi mata laifi ba da Imaan da ta rasu.
Cikin ƙanƙanin lokaci ƙiyayyar da nake yi mata ta zagwanye ban san me ya kamata na aikata ba yanzu a rayuwata. Amma ko mene bamu chancanci a lalata mana rayuwa ba 'Ya mace nada daraja fyaɗe aka yiwa 'yar'uwata idan tana da hannu ba xan iya yafe mata ba.
Na bar gidan ban sake waiwayarta ba tsawon lokaci..
*
Nasarar da ba zan mance ta ba da farin cikina da na yi sai nasara a kan Shari'a da na yi da Mahaifin Dacta Jabir wanda yayi silar rayuwar 'Yar'uwata ta dalilin fyaɗen da yayi mata, Dacta Jabir da kansa ya bani damar shigar da ƙara yana kuka bayan ya bani haƙuri.
Na yi kuka sosai lokacin da kotu ta kawo ƙarshen rayuwarsa na ji farin ciki duk da ba irin wannan mutuwar na so yayi ba sai dai da na tuna da raahin yafiya baya da kyau sai na sassauta ma zuciyata.
Abubuwa masu yawa sun faru ciki har da ci gaba da na samu da ɗaukaka a fannin aikina da ƙawatar haƙƙin Mata 'yan uwana.
09117440993.
*ƘURARREN LOKACI*
(18).
Duk da ciwon da nake ji a zuciyata na abubuwa masu yawa na rayuwata amma idan na tuna da Duk yadda mutum ke burin tsara rayuwarsa Ubangiji da nashi ikon Ƙaddara da nata tsarin sai na yi haƙuri.
Na kan zauna a duniyata nay tunanin mene amfanin matacciyar rayuwa da burin ƙyale-ƙyalen duniya da zarar na tuna irin wahalar da muka sha ta dalilin Mahaifin mu, Na daƙile ta dalilin abinda ya aikata, me yasa bai duba goben sa ba da zuri'arsa, Bani