Showing 24001 words to 27000 words out of 27913 words

Chapter 9 - HAMSHAƘIYAR UWA Book (1).

05 Jul 2024

3327

yamma." Hajiya ta ce Maman Nana kun dawo ne?" Mun dawo Hajiya sai muka kaji biki kamar daga sama. Hajiya ta ce Allah ya kawo lokacin. Maryam Tace to Allah ya kai mu, zamu shigo anjima da Dadinsu Nana yace in gaisheku kafin mu zo. "To Allah ya muku albarka amma kice masa nace dan Allah kar a zo da wata gudunmawa domin nasan halinsa." Maryam ta yi yar dariya Ɗazu yake ce min ya yi oder wata mota wadda zai bawa autanki a saka lefe a ciki a baiwa Amarya. Hajiya ta yi yar dariya ƙasaita. Ai ba irin wannan yarinyar bace, wata 'yar tsuntsuwa ya samo gata nan dai, kuma gidansu in aka kai wani kayan tsorata za su yi suga kamar za a sayar musu da 'ya, bare a haɗa da mota. Maryam tace Tofa! Bana kuma 'yar talakawa ya samo kenan? Hajiya ta ce haka ne sai dai kuma suna da dattako a yanzu, ba mu san ya zasu nuna a gaba ba." Maryam tace Allah ya sa su ɗore, domin haka mutane suke, in sun samu guri sai su nemi wuce gona da iri. To zan kira Maman Iman in faɗa mata wai ta saka order ta wasu lesuka. "Ki faɗa mata har A'isha duk ki sanar da su, kar kowa ta ɗaga hancinta,ankan wata gudun mawa, lefen ma an kai shi ɗazu. Nan dai suka yi sallama bayan sun tattauna tana Allah ya sanya alkhairi.

Shamaki ya sakko su Hassan suna tsegumin ba susan ya sakko ba, sai yaji suna fadin. Maigida wa yake so a cikin yaran nan Ɗahiru ya ce abin da mamaki irin fa yaran geto ɗin nan ne wasu kyamusassu shi da za ayi auran sa kwanan nan. Hassan ya ɗago daga kallon laptop ɗin da ke gaban shi ya ce "Kaji yadda ya ke min magana a gigice kuwa. "Hassan! ku tabbatar kun samo musu Ɗansahu su bar kasuwar nan. Suka kwashe da dariya bayan Hassan ya kwaikwayi muryarsa. Shamaki ya yi gyaran murya, nan da nan suka haɗa hankalinsu cikin kunya suka yi shiru. Yace "Gara dana ji ku, wadda zan aura tana cikin waɗannan yaran da ku ke yi wa ba'a. Kuma za ku je kuna neman wata alfarma agurinta wata rana. Hassan ya ce tuba muke maigida Allah ya taimaki maigida ayi haƙuri ba mu sani ba,sai ya fasa maganar da zai yi ya juya ya barsu cikin zullumi da kunya.

Washe gari Abbanmu yana fita Umma ta ce Allah ka gani saboda fita kunya zan fita ba izinin Abban Baby Allah ka sa muyi nasara. Lokacin da suka je sakatariyar bata fito ba, suka zauna suna jira kamar yadda Umman Amina ta bada shawara. Sunfi ƙarfin awa ɗaya sannan sai ga ta ta iso a wata mota. Har da duƙawa suna gaisheta, a wulaƙance ta kalle su,sannan ta kauda kai tana tambayar lafiya? Umman Amina tace dan Allah ki taimaka mana a matsayinmu na mata 'yan uwanki, mune muka zo shekaran jiya don Allah ki taimaka.
Ummansu Baby tace, Ki rufa mana asiri abin nan ya ƙarato gashi... Matar ta ce dan Allah ki min shiru ,me zan muku? Inje in buɗe store ince ga kaya ku ɗiba?" "Me yake faruwa?" Suka ji an tambaya daga bayansu. Duk suka waiwaya. Hajiya A'isha ce wadda Shamaki ke bi mata a haihuwa, kodayake ta bashi shekaru kusan takwas. Itace mai kula da ɓangaren Foundation ta kalli su Umma sun tsugunna a gaban Raliya. Tace ba yin Allah ku tashi,ke buɗe Office su shiga. Ta ci gaba da faɗa,bansan so nawa zan faɗa miki ba, ki daina wulakanta mutane . Wannan Office ɗin saboda su ne muka buɗe shi,kema kuma aikin su ki ke yi. In ba masu buƙatar me za mu yi a nan kenan? Raliya ta shiga bada haƙuri tana faɗin jiyan nan suka kawo takardarsu kuma suna maganar bikinsu sati mai zuwa. Umma ta kalli A'isha tace Hajiya kamar yadda Allah ya rufa miki asiri muma ki rufa mana, ba mu da wata mafita ne bamu zo da wuri bane domin muna sa rai cewa zamu iya siyan kayan .Sai kuma akayi rashin dacen samun kudin. Ko iya gado ne a taimaka Hajiya Aisha tace, "'yar waye a cikinku?" "Yata ce, inji Umman Baby. "To ina mahaifinta?" Ta jeho tambayar. Yana nan amma bashi da ƙarfi wallahi leburane ya buga ko ina amma bai samu halin yi mata kayan ba, ko iya gado ne ku taimaka mana sai mu kaita. To Shikenan zan taimaka amma sai na ga mahaifinta,sannan zan san ya za ayi a saka takardar ku acikin jerin na wannan wata ukun, duk wata uku mutum goma mu ke ɗiba mutum talatin a shekara ai muna ƙoƙari bafa gwamnati bane mu. Su Umma suka ce gaskiya kuna ƙoƙari muna godiya Allah ya saka da alheri ta ce "Ba komai ku zo da mahaifin nata sai munyi masa tambayoyi sannan mu bashi takarda ya cike. Ta dubi Raliya "Dakko min takardar su." Haka suka yi mata sallama suka tafi.

Tunanin Umma tun a hanya shine yadda zata tunkari Abban Baby da zancan nan gani take ba zai yarda ba. Umman Amina ta ce ki bari zanzo in same shi da maganar sai muji me zai ce,ai in ba wai ya samu wata mafitar bane ina mai tabbatar miki da gudu zai yarda. Ummansu Baby tace Allah yasa.
Sun dawo gida suka tarar 'yan Kurna sunzo ganin lefe,ni kuwa dawowar su Umma ta min daɗi domin Yaya na ta kiran waya ina cewa ya yi haƙuri zan kira shi masu ganin lefe ne suka zo. Umma na zama suna gaishe gaishe ni kuwa na miƙe na shige ɗakin mu da sauri na kira Yaya sai da ta yanke zan kuma kira sai ga kiran shi ya shigo. "Baby." Muryar shi ta ratsa cikin kunnuwa na, cike da kasala nace na am. Yace zan miki wata tambaya nace ina jin. ka. "Ke budurwa ce? Gabana ya yake ya yi wata mummunar faɗuwa, cikin rawar murya na ce Yaya ban fahimta ba. Yace kawai ki bani amsa,ke budurwa ce ko kuwa wani abu ya taɓa budurcin ki? Tambaya ta biyu kin iya girki?" Na ce, Kaji wani labari ne game da ni? Yace "Banji ba, amma akwai wata al ada wadda Hajiyata take rayawa,na tabbatar zata yi wannan al "dar a kanki kamar yadda ta yi a sauran mata na,ina son ku faɗa min gaskiya domin in ne mi mafita kafin ranar, saboda Baby wallahi ni kaɗai nasan me nake ji a kanki bazan iya fassara wa ba ai game da son ki." Na numfasa Yaya ina da tabbcin cewa ni budurwace amma bani da tabbaci akan budurcina. "Kamar yaya?" Ya katseni. Nace to ni dai ban taɓa ko wasan banza da wani namiji ko wasan duka banayi har bare ya kai ni ga ashsha, amma wannan ba shine zai sa in yi tutiyar budurcina ba tun da ance yana samun matsala da kanshi. Game da girki kuma irin namu dai na iya nasan kuma shi ku ke ci. Fara da wake mai da yaji, irin su taliya ɗinnan da manya. Kuma na iya tuwo harda ɗan wake sosai,jalaf ma dai zan ɗan iya tunda mukan yi jifa jifa. Ya yi shiru har sai da na ce kanaji na kuwa Yaya?


🖊️🖊️🖊️
[6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*


*Free Page 10 Karshen free Pages*


*DIJENGALA ENTERPRISE*
*07031121981*
*Ina Mata 'yan gayu masu son kayan gayu kuzo ga dama ta samu* *DIJENGALA ENTERPRISE ta kawo maku Kayan masu kyau da inganci indai mace tasan gayu to* *DIJENGALA ENTERPRISE ne wajen siyayyar ta.*
💯 London laces
💯 London lafaya
💯Switzerland laces
💯 Dubai laces & Lafaya
💯veils
💯 Atampha
💯 shadda
💯 Voile
💯yadika na maza
💯caps
💯 Necklaces etc...
*Kayan mu ba Wanda suka cika gari bane,bazaki gansu a ko ina ba shiyasa ake mana kirari da Auntyn Gayu ko me kika siya a gunmu zaki ji dadinsa* *07031121981 Ina Wanda zasuyi biki su rasa abinda zasu saka suna tunani kar suyi iri daya d wasu Don Allah ku tuntubeni* *07031121981 zaku Sha mamaki🤔sarkokinmu ba kowane wuri zaku samesu ba wlh sai wurin ya ansa sunansa, haka Laces dinmu ma na daban ne daga Company sai wajenmu💯🥰💞*
*DIJENGALA ENTERPRISE*



Umman Amina ta shigo ƙarfe goman dare ita da Amina, duk muna kwance tsakar gida saboda yanayin zafi. Abbanmu yana banɗaki, ta zauna suna ƙara tattauna yadda zasu yi wa Abba maganar. Ni kuma muna 'yar hira da Amina da Jamila,. amma hankalina baya tare da su, na kan tuno da Yaya ɗazu da muna waya. Bai kuma ce min ƙala ba ya kashe wayarsa, na kira bai ɗaga ba. Tambayoyinsa sun caza min kai kuma al adar da yace Hajiyarsa ta na da ita wadda ya tabbatar za ta gabatar a kai na, suma suna sani faɗuwar gaba. Zan so ya min bayani sosai, sai dai a yadda na soma karantar halinsa, ba lallai ya kuma ɗakko min maganar ba.

Jamila ta girgiza kafaɗa ta tana cewa Amina tana miki magana tunanin me ki ke yi? Na sauke ajiyar zuciya na dubeta me kika ce Amina? Tace Duk tunanin auren ne haka, ina tambayar ki ne za kiyi lalle a saukarku ne?" Nace a'a' ba zai fita ba har inyi na biki. Jamila tace gaskiya kam. Sam ban lura cewa Abba ya fito daga banɗaki ba,sai dai na ji muryarsa ya na faɗin gaskiya talauci na da lalacewata da rashin godiyar Allah na duk basu kai haka ba. Gara inci bashi domin nasan zan biya." Umma ta ce to amma kasan shima bashin ba a samun sa ko? Yace to in ba a samu ba sai mu kaita a haka domin shi yace baya buƙata,me zai sa mu ɗaga hankalinmu akan wannan. Har zuwa yanzu baya ga dubu hamsin kuɗinta da aka kawo bani da ko taro, kuma ban damu ba. Allah ne zai mata komai,amma bana son in kuma jin zancan neman tallafin nan,bayan mun karɓa sai munje 'yan jaridu sunyi hira da mu, an yaɗa a kafafen yaɗa labarai cewa gamu an ba mu, sannan mu yi godiya, ga Allah, shi mijin ya ji zai ɗauke mu da daraja ne?"

Umman Amina ta ce yanzu sai abarshi kenan Abban su Baby bayan ita mai gurin ta karɓi takardar... Ya miƙe tare da tsaki. "Ni kunga fita ta." Ya wuce abinsa. Umma ta ce kin gani ko wani Lokacin Abban su Baby hutsune, da ki ke ganinsa. Umman Amina tace da Abban su Amina zai yarda ai sai muje da shi a madadin Abban su Baby.Umma ta ce, da zai yarda ai da mun fita kunya. Ina jinsu abubuwan sun min yawa, banda ina jin wani mahaukacin son Yaya Allah da na fasa auren nan,kowa cikin damuwa da zullumi ga shi karatun saukar nawa ma duk na kasa nutsuwa inyi maraja'a a gida. Gashi daga gobe an gama sai kuma a filin sauka.

Shamaki ya yi jugum, bashi da wata mafita face ya gana da 'yan uwanshi matan nan su tattauna a samu mafita. Ya ɗaga waya ya kira Maman Umar ta ɗaga da faɗin autan Hajiya, yace Maman Umar fatan dai kina lafiya da yarana duka. Tace "muna lafiya Auta." Yace ba haushe dai yace Babbar ya Uwa ko? Tace "Tabbas." Yace to zan kawo kukana gurinku ku duka, ba ƙara zan kawo ba, fatan zaki banbance ko? Tace "Na banbance." Yace don Allah ki tara su zanzo da magariba gidanki zamu yi wani zama yau ɗaya a tarihi ba tare da Hajiya ta sani ba, kuma karma taji labari. Maman Umar tace "Baka da matsala auta yanzu duk zan kira su." Suna yin sallama ta kuwa kiransu ta sanar da su.
Tun biyar suka haɗu kowacce ta ɗauki mota ta zo. Suna ta hirar su abin gwanin ban sha'awa cikin wasa da dariya. Maman Umar tace "Ni yanzu ko ɗinki ban bayar ba bansan ma wane kayan zan ɗinka ba. Fatima tace naga wasu lessis da atamfofi na tashin kai, har nace zan kira Shamaki ya kamata su kawo irin su. Aisha tasan san Fatima da gayu ta ce Maman Iman a ina kika gansu? DIJANGALA ENTERPRISE Na sha mamaki kunsan ni duk inda kayan gayu yake zaku ganni a gurin kawai naga tallar kayan na duba naga laces yan London da lafaya da atamfofi abin dai sai kingani, naga Number wayar kamfanin, na kira da ta ɗauka mukayi magana ta turo min ke kinga atamfofi na tashin kai.Maman Umar tace kin gansu a hannu ne wasu fa duk hoto ne. Maman Iman ta ciro waya ta fara nuna musu kaya, tace sune na faɗawa Maman Nana cewa na saka Oder kayan London ai ba acan London ɗin na saka ba, gurin wannan kamfanin na sa, gobe zan karɓa. A'isha tace "In naga naki sai in siya nima amma dai in Hajiya taji zata ce duk irin kaya da muke da su a ZEENA baza mu bawa kanmu ƙaruwa ba. Maman Umar tace ai ko ita taga abinda ya birge ta ko muna dashi sai ta siya. Yasunan kamfanin ki ka ce? Maman Iman tace DIJANGALA ENTERPRISE Karki damu zan kawo muku kayan ku gani. Ni Ko tun a waya sun yi min. Suna ta labari har sai da sukaji kiran salla sannan biyu suka tashi suka tafi salla,biyun kuma suka ce basayi.

Umar ne ya shigo daga masallaci yake sanar da Momyn su tare da Uncle Shamaki suka yi sallar magariba a masallacin layinsu.Maman Nana tace har ya zo kenan. Umar yace e mana cikin massalacin. Suna cikin magana sai ga sallamarsa. Suka amsa suna yi masa sannu gami da sunan tsokanar da suke faɗa masa wato ƙaraminmu babbanmu. Yace ga ni nan a bi ni a hankali ko in ƙi sa wa kowa hannu a takardar. Suka sa dariya,ya zauna aka kawo masa abinci dana sha. Ruwa kawai ya ɗauka ya ɗaga robar ya sha kusan rabi sannan ya aje. Ya kalle su, halin da nake ciki bazai barni in iya jin yunwa ba.

Suka tattara hankalinsu akan shi cikin kula kowacce ta zaƙu ta ji menene damuwar ɗan ƙanin na su. Ya numfasa, kafin in yi maganar sai kun min alƙawarin cewa wannan iya ni da ku ne, Hajiya bazata sani ba. Suka ce karka damu. Maman Umar ta ce ranar da ba Hajiyar mune dai iyayenka ba wai ina mana fata bane. Sukace tabbas haka ne. Ya numfasa, Ɗazu ina kasuwa ka wai sai abin ya faɗo min, Hajiya kusan har yanzu akwai wasu al'adu da bata sake su ba duk da cewa ta amshi zamani. Maman Nana tace "Waɗanne iri?" Yace kamar batun cewa sai ta sani ko matar da na aure ta zo da budurci, saboda yanzu zamani da cima ba irin ta da ba ce likitoci suna ta bayani. Maman Iman tace "To menene abin damuwa akan wannan?" Yace dole in damu,karki manta aure na huɗu zan yi, kuma wannan matsalar ita ce silar rabani da Maman Meema mata ta ta farko tun daga tambayoyin da Hajiya tayi min a ranar farko da na kwana ɗakin na bata amsa tace gaskiya banyi aure ba, tace yarinyar ta gama bin mazanta ta ɗora mata karan tsana,wanda hakan ya janyo nima naji na tsane ta. Haka ta rayu da mu duk da bata rasa komai ba amma tana yaye Meema ta zaɓi ta bar gida kamar na mu mai cike da daula, ta koma gidan iyayenta duk da cewar suma ba wai talakawa bane. Haka nan na sallame ta Hajiya ta sa aka haɗa mata da goma ta arziƙi kamar dai yadda kuka sani. Kinji ɗaya. Ita kuma Maman Mubina kunsan daga girki a nan aka fara samun damuwa, domin da Hajiya ta yi min irin tambayoyin da tayimin a daren farko da muka kwana sai na faɗa mata irin abinda ta ke buƙatar ta ji, don haka sai tace to bisa al'adarta za a haɗa komai na girki ta fito ita ce zata ciyar da ƙawayen Hajiya da sauran "yan biki da girkin da ta yi da hannun ta. Sannan tazo ta zuba wa kowa da kanta. Wai manufar haka a ga ko ta iya girki,in kuma ta iya a gurin zubawa a gani ko marowaciya ce ko kuma zata iya jan ragamar gidan a matsayin ta na matar jigon gidan. In baku manta ba,itama anan aka soma samun matsala. Wadda ta zama kullum cikin faɗuwa a duk wata jarabawa da Hajiya ta yi mata. Bisa ga wannan dalilin itama ta ce ta gaji dole na sallame ta kamar yadda Hajiya ta bada umarni. Ya numfasa ta ƙarshe Maman Anisa. Ta tsallake maganar girki da wani budurci domin ita Hajiya sai da ta tsaya ta tabbatar ban yi mata ƙarya game da daren farko ba.Sannan Maman Anisa ta iya girki da kayan ƙwalam na fulawa ina ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login